CIN AMANA KO FANSA Book Complete By Zahra Muhammad Surbajo.txt

Author :  Zahra Muhammad Surbajo Category :  Arewa Pen

Chapter   13 / 14

36K to 39K   out of 39.7K words

shiga toilet ta shige tayi wanka sannan ta dawo ta bud'e akwatin lefenta ta zab'o wasu riga da wando tasaka,rigar hannu d'aya gareta yayinda ko cibiyarta bata rufeba, shikuma wandon irin jeans d'innanne dake tsayawa Dede k'asan mazaune,wandon ash color rigar bak'a, tana gama saka kayan gaban mirror taje ta tsara kwalliya tasaki gashinta yasauka har gadon bayanta,k'arewa kanta kallo tayi tasaki wani killer smile sabida ganin yadda hips d'inta suke awaje abun gwanin burgewa,wani takalmi tasaka bak'i me tsini wow abun se wanda yagani turaruka kalakala tagama feshe jikinta dasu.

Sannan tasamu gefen kujera ta zauna waya taciro takira Fatima bayan sungaisa ne take sanar mata abinda ke faruwa.

Dariya Fatima tayi sannan tace,

"Yasmeen baki da dama wlh yanzu shine kika gudu gidan mijinki ba sallama dan kishi nacinki? nide ba ruwana wlh kyayiwa Umma bayanin da kanki".

Magiya Yasmeen taringa mata akan tacewa Umma Hydar ne yad'auko ta dakyar Fatima Ta amince sukayi sallama.

Tananan zaune taji motsin fitowar su Hydar, ta window ta leka ilai kuwa sune rungume da juna sunnufi k'asa,sakin labulen tayi k'irjinta na bugawa da k'arfi.

Hydar da Khairat kuwa abinci sukaci suka dawo falo suna wasanninsu,khairat k'in sanarwa Hydar sak'on Abba tayi dan tagama gano Yasmeen ce take nemannasa, hasalima itace ta kulle masa wayoyin dan kar Yasmeen ta kirashi.

Suna tsaka da y'ar jefawa junansu fulo suka fara jiyo sautin takalmanta tana sakkowa,tsorone ya kamasu dan sunsan Bakowa a gidan sesu kad'ai,cigaba da sakkowa take tana tafe tana kad'a k'ugu hips d'inta se rawa suke tana taunar cingum a bakinta har tagama sakkowa.

wohoho duniya.

Khairat sanda tayi arba da Yasmeen kusan fad'uwa tayi, dan tsananin firgitar da tayi da irin had'uwar da Yasmeen tayi,cije baki tayi ta ce aranta"why always am looser?,why?".

Maman Yusuf.
📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓


Zahra Muhammad mahmud


*This page is dedicated to,Maman Hanifa,Nusaiba Abdulkadir Dan madaki(my daughter),Rahmatu Muhammad mahmud(my sis),Allah ya tsareku a duk inda kuke nagode*

*page 73-74*

Yasmeen cigaba da tahowa take cikin takunta me d'aukar hankali,shiko Hydar suman tsaye yayi don tunda yake da Yasmeen bata tab'a yin dressing irin wannan ba, ba ma hakaba tunani yake ta yadda akayi tazo nan bayan yasan tana Kaduna.

Yasmeen ko Hydar ta nufa tana tafiya tana kashe shi da murmushi,tana zuwa rungumeshi tayi ta manna masa kiss a kumatu,sannan tasak'ala hannayenta akan kafad'arshi bayan ta kamo nashi hannayen ta d'ora akan k'ugunta, cikin shagwab'a ta fara magana.

"Haba my love shine tunda muka dawo baka nemeniba? tun jiya bangankaba se yanzu to yakake?".ta fad'i gami da k'ara rungumeshi tana kukan shagwab'a.

Hydar tsintar bakinshi yayi da cewa, "am sorry princess baccine yad'aukeni kinsan nagaji".

Khairat da gudu ta haura sama tana kukan takaici wato dama ashe tare ma suka taho amman dan munafunci irin na namiji be sanar da ita ba,wannan wacce irin masiface Hydar ya had'ata kishi da ita?.

Yasmeen ko tana ganin Khairat ta bar gurin tasaki murmushi alamar nasara,kwace jikinta tayi ajikin Hydar d'in takoma d'akinta, da sauri Hydar yabita abaya kamar wani bindi.

Tana shiga d'akinta tasamishi kuka,gabad'aya rud'ewa yayi yarasa yadda zeyi kamota yake tana kwacewa,tana cigaba da kukannata.

"Haba my baby meyasa kikeson d'agamin hankaline?kinsanfa banason kukanki, Amman seyi kikeyi pls ya isa haka kiyi shuru".

Nanfa yashiga rarrashinta dakyar tayi shuru sannan tace.

"Shine kataho kabarni ko?".

"Ay nace kitaho mutafi kika k'i to yazanyi dake Baby?".

"Ni nad'auka da wasa kakemin ashe da gaskene, se yau naita kiran wayarka akashe har Abba naje na fad'awa yakira Khairat shine tace wai kana bacci ka kulle wayane,niko danaji haka shine nace to bari inzo In tayaka baccin". Ta k'arasa zancan tana dariya.

Shima dariyar yayi sabida abunnasu Khairat da Yasmeen dariya yabashi wato Khairat ta rufe waya dan kar Yasmeen takirashi sega Yasmeen tazo da kanta itama Ta rama lalle shi d'an gatane.

"To baby yanzu komai ya wuce kinjiko? Anjima inada magana daku after dinner".

"To my love but yanzu yunwa nakeji,kuma ni ice cream nakeson sha so kazo muje ka kaini nasha".ta fad'i cike da kissa tana wani jujjuya mazaunai.

"OK to yi sauri kishirya kifito muje bari naje nama Khairat magana ko zata je".

Ranta besoba Amman seta share tace "To".

Fita yayi yanufi d'akin Khairat kuka yasameta tanayi da sauri yakamota yana tambayarta meyasameta, cikin masifa tafara magana bayan ta kwace jikinta daga nashi.

"Wlh kayi asara Hydar,menene ribar munafuntata dakayi?ashe tare da Yasmeen kuka taho Amman ka b'oyemin? wlh kaci gaba, Allah na kallonka nasan kuma baze barkaba".

Shareta yayi dukda maganganun sunyimasa zafi amman yadaure yace mata.

"Kizo muje musha ice cream inzakije kitashi kishirya yanzu".

"Babu inda zanje tsohon munafuki kawai kaficemin a d'aki".

Ba musu yajuya yafice lokacin Yasmeen tuni ta shirya Danhaka hannunta yakama suka fice a gidan se huci yake alamar ranshi ab'ace yake.

Yasmeen cikin kissa, takwantar da murya tace.

"Yanzu dannace ka kaini shan ice cream shine kake wannan fushin? Tunda ranka bayaso mukoma gida nafasa zuwa".ta fad'i hakane dan tanason gano meyasashi b'acin rai.

"Badake bane baby,nida Khairat ne, dan kawai kinyi wannan maganar ta d'azu shine yanzu danaje akan tazo mutafi karkiji zagin datamin".mitssu yayi tsaki.

Killer smile ta saki alamar buk'ata tabiya, dama dantaji ne yasa tayi hakan kuma gashi tajin.
Amman afili ruk'o hannunshi tayi tana dariya tace.

"Kayi hak'uri my love komai lokacine inya wuce shikenan, pls amata Afuwa",har wani fari take da ido Wanda ya tilastawa Hydar cewa.

"Bakomai baby yawuce".

Sun isa gurin shan ice cream d'in suka siya, Amman Yasmeen cewa tayi sede su zauna acan susha ayko hakan akayi dan basu shigo gidaba se magrib.

Khairat suka samu a falo ita da Iman, tana ganinsu tare wani takaicinne yasake kamata,itako Iman da gudu taje ta rungume Yasmeen tana murnar ganinta, d'aki Yasmeen taja Iman.

Iman naganin sun nufi d'akin Amaryar Daddynta taja burki tace.

"Ke baki da kai ne? nanfa d'akin Amaryar Daddyne".

murmushi Yasmeen tayi sannan takamo Iman suka k'arasa shigewa d'akin.

Seda suka shiga Yasmeen ta juyo tabata amsa da cewa.

"To ay nice Amaryar Daddyn,wacce ya Aura".

Ba idoba hatta hanci da baki seda Iman ta zarosu.

muje zuwa.

Maman Yusuf.📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓

Zahra Muhammad mahmud

*This page is dedicated to,Maman Al-ameen,Maman Imam,Jameela Abbas,Maman Faruq,thanks for the care and support I really appreciate.*

*page 75-76*

Hurewa Iman ido Yasmeen tayi wanda hakanne yadawo da ita daga tunanin data shiga.

"Yasmeen kinsan bama irin wannan wasan dake don Allah kifad'amin gaskiya".

Yasmeen wayarta ta ciro ta nunawa Iman hotunan bikinsu da Hydar sannan tace.

"To yanzu kin yarda ba wasa nake mikiba ko?".

Rage murya Iman tayi alamar rad'a tace.

"Yasmeen keda Aunty ba Y'an'uwa bane?".

"Y'an'uwane mana".

"To meyasa kika auri daddy bayan kinsan mijin tane?".

"Saboda Daddyn ki yanuna ze iya mutuwa idan ban yarda na aureshi ba, koko laifine danna ceci rayuwar Daddyn ki?".

Da sauri Imam ta girgiza kai sannan tace.

"But Yasmeen"

"shshshsh, keep your mouth shut,just answer me, are you happy for having me as your new Mum or not? just tell me".inji Yasmeen.

"I really happy for having you as my sweet Mum,Allah yabaku zaman Lfy, dukanku".ta fad'i tana dariya. Rungume juna sukayi.

Ranar Yasmeen da Iman guri guda suka kwana yayinda Hydar yake tare da Khairat dan tuni suka shirya dama ance tsakanin mata da miji se Allah.

Al-amura sunci gaba da tafiya yadda yakamata, Yasmeen kissa take zubawa bata wasaba yayinda Khairat itama ba'a barta a baya ba, tabi sawun Yasmeen d'in Amman dayake ita Khairat tana da saurin fushi Yasmeen tafi cin galaba akanta dan ita Yasmeen koda taji haushin bata bari kowa yagane.

Yau Yasmeen ce da girki,dan haka tun safe take aykace aykace a gidan,hydar yafita gurin ayki tun da sassafe.

D'akin Hydar taje ta gyara ta feshe shi da turaruka masu k'amshi,sannan tajawo k'ofar ta rufe,tanufi nata d'akin tana cikin gyaran d'akin taji amai yana taso mata da gudu ta nufi toilet tafara kwara aman kamar zata amayar da kayan cikinta, da kyar tasamu ta gyara inda ta b'ata ta dawo d'aki, kwanciya tayi a k'asa tana hutawa bata tashiba seda taji ta dawo normal, sannan ta nufi kitchen ta fara hada-hadar d'ora girki.

Bayan tagama d'ora komai ne tanufi d'akin Hydar domin ta manta bata kwaso kayan wankin shiba akan kujera ta barsu danhaka taje kwasowa,sede me tana zuwa seta tarar ankulle k'ofar d'akin ancire key kuma tayi imani Khairat ce zata rufe,alhalin ranar girkinka kai kake da iko da d'akin dan haka falon Khairat d'in tanufa.

A zaune tasameta ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana karkad'awa hannunta rik'e da mukullin d'akin tana jefashi tana cafewa.

"Aunty dama key nazo kibani na d'akin Daddy dan inaso zan kwaso kayan wanki nabada a wanke".

Cike da masifa da bala'i Khairat tasoma magana,dan dama cike take da Yasmeen d'in.

"D'akin na Ubanki ne da zaki zo kitasani a gaba akan in baki key?".

Ran Yasmeen ba k'aramin b'aci yayiba, kuma dama ba wannanne Karo na farko da Khairat ta zagi Ubanta ba tasha yimata bata kulata, Amman yau de kam se abinda hali yayiwu takaita bango,dan haka tabata amsa azafafe.

"D'akin bana Ubana bane, kamar yadda yake kema bana Ubanki bane, dan haka yazamarmiki dole kibani key d'in d'akin Mijina".

Jikake Tass Tass Khairat ta wanke Yasmeen da Mari sannan ta hankad'ata ta fad'i tabita tafara dukanta iya k'arfinta,Yasmeen har ta d'aga hannu zata rama sekawai ta fasa ,dan koba komai taci darajar mijinsu.

Khairat ko zagin Yasmeen take Ta Uwa ta uba tana dukanta fad'i take.

"Yau senaci kan ubanki a gidannan, duk wata rashin kunya da rashin mutunci dakike tak'ama dashi yau zan sauke miki su, shegiya tsinanniya me mance halacci".

Yasmeen ta daku a hannun Khairat,tayi tayi ta kwaci kanta a hannunta Amman ta Kasa, sabida Khairat tafita k'arfi nesa ba kusaba,hakan yasa Yasmeen tagaji ta saduda tabarta tana ta dukanta, wani naushi da Khairat takaimata k'asan mararta shiyasata kwalla wata razananniyar k'ara sannan ta fad'i k'asa sharab, hakan yay dai-dai da shigowar Hydar falon, jini ya hango yana zubowa daga k'asan k'afafuwan Yasmeen yayinda Khairat ke zaune akanta tana duka.

Muje zuwa readers.

Maman Yusuf.📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓

Zahra Muhammad mahmud

*This page is dedicated to,Maijidda,Esha Umar,Rahama,Ummu fa'eez,Hjy Maimuna Keffi,Maman Afnan keffi,Hameeda,thanks for the care and support.*

*page 77-78*

Da gudu Hydar yak'arasa gurinsu wani wurgi yayi da Khairat gefe guda ya sunkuya ya d'auki Yasmeen wacce zuwa lokacin ko numfashi batayi.

Da gudu yanufi mota da ita ya kwantar da ita yaja motar zuwa Asibiti,da isarsa Asibitin Ma'aikatan Asibitin suka fito suka amsheta.

Emergency room aka kaita,likitoci suka rufu akanta,Hydar ko se safa da marwa yakeyi hankalinshi atashe yama rasa wanne hukunci zewa Khairat fatanshi Allah yatashi Yasmeen lafiya.


Likitane yafito yace Hydar yabiyoshi office,marawa likitan baya yayi har suka isa office d'in suka zauna,hannu likitan yamik'a masa suka gaisa sannan yafara yimasa bayani kamar haka.

"Ranka yadad'e a binciken damuka yi mungano madam tana d'auke da ciki na tsawon wata biyu,amman sanadin duka ko fad'uwa da tayi ko akamata akan cikin yasa cikin ya zube,yanzu Muna buk'atar jinin da zamu k'ara mata dan tayi asarar jini da yawa".

"Inna lillahi wainna ilaihirrajuun", itace kalmar dake yawo akan bakin Hydar,lokaci guda ya rikid'e yazama Aliyun ko likitan seda ya tsorata da ganin yanayinsa.

Jininsa aka gwada yayi dede da nata dan haka nashi aka d'iba aka samata,ana gama d'ibar jinin afusace yanufi motarsa yajata zuwa gida.

Khairat ko ba k'aramin tashin hankali tashigaba ganin jini nabin Yasmeen lokacin da Hydar ya d'auketa,gaba d'aya tagama firgicewa tama rasa abinyi se safa da marwa take yi a falo shigowar Hydar ce ta dawo da ita seti,tun kamin tayi wani yunk'uri ya rufeta da duka,be kyaletaba sedan kanshi dayaji ya gamsu.

Kuka Khairat take ba na wasa ba tana rok'on shi yayi hak'uri,mari ya kifa mata lafiyayye wanda har tuntsurawa tayi sannan yace.

"Tur da kishi irin naki Khairat,yanzu ko nagama yarda hundred percent cewa zaki iya kasheni ma ba Yasmeen ba, tunda har zaki iya yimata dukan da ciki ze fita ajikinta sabida tsabagen son kai irin naki, Khairat baki da imani kwata kwata dan da kina dashi da bazaki haikewa yarinyar da kikasan ba k'arfinku d'aya ba, Da kina da imani da tuni kinjima da yarda da k'addarar kasancewar Yasmeen abokiyar zamanki, nagaji Khairat dan haka ki tattara ina ki inaki kibarmin gida *na sakeki saki d'aya*,yanzu ba se anjimaba kificemin a gida"ya k'arasa zancan hawaye na zuba daga idanuwanshi.

Ihu Khairat ta saki ta ruga ta Kama k'afar Hydar tana fad'in.

"Wayyo Allah na shiga uku!!!Hydar karufamin asiri kayimin kowanne kalar hukunci Amman banda na rabuwa dakai, wlh bazan iya rayuwa ba babu Kai, kuma wlh bansan Yasmeen nada cikiba kayarda dani da bazan daketaba,Hydar wlh in Abba yaji wannan batu kasheni zeyi karufamin asiri kamaidani d'akina don Allah",ta fad'i cikin matsanancin kuka tana rik'e da k'afarshi.

K'wace k'afarshi yayi sannan yace mata.

"Wlh da Abba ze kasheki senafi kowa murna, dan Allah yace "annafsi bin nafsi",kinga kema kisan kan kikayi,dan haka nagama magana idan kika bari nadawo nasameki wlh sekin raina kanki"yana gama magana yajuya yafice a gidan yanufi Asibiti zuciyarshi na tafasa.

Kuka Khairat take kamar mahaukaciya gabad'aya ta kid'ime ta gigice tana neman agajin ubangiji, ganin tarasa mafitane yasa ta d'auki abinda zata iya d'auka ta zuba a mota gamida y'ay'anta Arfat da Meema ta kama hanyar kaduna tana kuka kamar zata mutu, Allah ne kawai yakaisu lfy.

Gidan Fatima ta nufa dan nanne kawai take tunanin samun sassauci dangane da hukuncin dazata fuskanta daga sauran dangi.

Ko a fuska bataga chanji ba daga Fatima hannu bibbiyu Ta amsheta,itako se kunyarta takeji k'arshema de rushe mata da kuka tayi,tashiga zayyana mata abinda yafaru ta k'arashe zancen dacewa.

"Wlh Fatima ke kad'aice zaki yarda dani Wlh bansan Yasmeen tana da cikiba wlh bansaniba".

Hankalin Fatima in yayi dubu yatashi jin Hydar ya saki Khairat akan Yasmeen.,sannan ga Yasmeen can a asibiti rai a hannun Allah kuka Fatima itama tasa tana fad'in.

"Why Khairat? why always you?me yasa kika lashi takobin dole se kin haifar da tashin hankali tsakanin Iyayenmu?me zumuncinsu yay miki kikeson ruguzashi?, duk abinda Yasmeen tamiki kece kika siya da kud'inki bawai kuma ina fad'amiki hakan bane dan ina bayan Yasmeen, gaskiyace dole nafad'amiki Khairat bakyawa kanki da Iyayenmu da Mijinki adalci"ta k'arasa zancan tana kuka.

"Wlh Fatima base kin maimaitaba nasani nice banida da gaskiya,duk abinda mijinka yanuna yana so nuna masa zakayi kai kafishi so da na ja Yasmeen ajikina wlh nasan haka bazata faru akainaba,Fatima nashiga uku don Allah kitaimakamin ki rufamin asiri insu Abba sukaji zancannan kasheni zasuyi kitausayamin don Allah".

True love gaskiyace.

Fatima rungume Khairat tayi tana kuka tana mata alk'awarin insha Allahu babu mejin wannan maganar ta kwantar da hankalinta.
.D'aki Fatima taba Khairat ita da yaranta sannan tashiga tunanin ta ina zata fara shawo kan wannan matsalar? Amman Bari taji daga Hydar d'in inde yakira waya ya sanar da Yasmeen tayi B'ari to ko tabbas dole asiri ya tonu amman idan be kiraba shine abin zezo da sauk'i.

Hydar yana isa asibitin yatarar Yasmeen ta farka se kuka take mararta na ciwo,da sauri ya isa gurinta ya rungumeta yana rarrashinta gami da kwantar mata da hankali har ciwon ya lafa.

Kwananta uku a Asibitin aka sallameta ta warke sarai kamar ba itaba sede d'an abun da ba'a rasa ba, koda suka isa gida tayi mamakin ganin Iman ce kawai a gidan,bayan tayi wanka Ta hutane taci abinci Hydar yashigo d'akin yabata maganinta sannan yatambayeta abinda ya had'ata da Khairat ba musu ta fad'amishi komai iya gaskiyarta.

Tausayinta yaji yakamashi ashe akan tanason faranta mishine akamata asarar ciki wanda har yanzu Batasan da batun zubewar cikin ba hasalima batasan tana da cikin ba dan Hydar be fad'amata ba dan baya so ta tsani Khairat a ranta kodan zumuncinsu.

Fatima jin shuru Hydar be fad'i Yasmeen bata da Lafiya bane ya kwantar mata da hankali,uwa uba wayar da sukayi da Yasmeen d'in itama batace mata Khairat ta doketa ba,shi yabata kwarin guiwar son dedeta tsakanin Khairat da Hydar batare da sanin Iyayensu ba, Fatanta Allah yasa ta dace da hakan.

To Fatima muma muna miki fatan kidace.

Maman Yusuf.
📓📓📓📓📓📓📓📓
*CIN AMANA KO FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓

Zahra Muhammad mahmud

*Dedicated to,Bilkisu S Ahmad Kaduna,Amina S Ahmad Kaduna,Asmau Muhammad Mahmud Kaduna,inasonku Yan uwana Allah ya albarkaceku duniya da lahira,#one love*

*page 79-80*

Fatima number Hydar ta kira.
Bayan sungaisane ta soma da cewa.

"Hydar naji duk abinda ke faruwa tsakaninka da matanka,kuma a gaskiya hukuncin da kayiwa Khairat bedaceba ze jawo mana tashin hankali sosai adanginmu don Allah kayi hakuri kamaida ita dakinta batare da iyayenmu sunji ba dan tunda ta taho a gidana tasauka gudun bacin zumunci".

"hmm Fatima kenan,yanzu duk laifin da Khairat ta aykata min kikeso namanta naci gaba da zama da ita to wlh dasake inda kin tilastani yin abinda bansoba to yanzu ni ba yaro bane dazaki tilastani,ko wancan lokacin ma yarintace tasa naamince, dan haka inzaki iya sa ido kiyi kallo kisa kicire kanki acikin wannan maganar",yana gama fadamata haka ya kashe wayar gaba daya.

Hankalin Fatima tashi yayi dajin kalam Hydar hakan na nufin dole se zancan yakai ga iyayensu kenan.

Yasmeen kwananta biyu da dawowa gida Amman bataga Khairat da yarantaba, koda ta tambayi Hydar cemata yayi taje Kaduna ne,be sanar da ita komai,fatan Allah yadawo dasu lafiya tayi.
Yasmeen ce zaune gaban computer tana latse latsenta,a dakin Hydar,kamar ance taba kawai seta shiga inda mutum zega abinda ke faruwa a gidan wato CT camera old videos tashiga.

Hydar tagani yana dukan Khairat,har zuwa lokacin dayace yasaketa,har batun zubewar cikinta duk seda taji.

Tashin hankali baa samishi Rana.

Ita bata cikin takeyiba sakin da akayiwa Khairat a dalilinta shi yafi daga mata hankali,da sauri taciro wayarta takira Fatima tana bata labari gami da tambayar ina Khairat din take.

Kwashe duk abinda yafaru Fatima tayi tabata labari har yadda sukayi da Hydar,Yasmeen bataji dadin abunba sam,kamin suyi sallama seda Fatima ta roki Yasmeen akan ta roki Hydar yadawo da Khairat dakinta.

Hydar yana dawowa daga gurin ayki yaga Yasmeen atsaye tana kallonshi babu alamar walwala a fuskarta, karasawa yayi inda take ze rukota da sauri ta bige mishi hannu sannan tasa mishi kuka tana fadin.

"wanne kalan suna kakeso duniya takirani dashi,sokake zumuncin gidanmu ya rushe a tsakanin iyayenmu,mene naka na sakin Khairat dan munyi fada,kana tunanin wai dan na aureka bana son tane,cikina da ya zube daga Allah ne ba ruwan Khairat wacce nayi imani da tasan inada ciki bazata dakeniba,".tacigaba da kukanta.

Hydar ya rasa abinyi wato yanzu Yasmeen tasan abinda yafaru kenan waya fada mata,rasa amsane yasa yawuce dakinshi, da shigarshi dakin ya fahimci inda

13 / 14