Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
Tace." To meye wallahi babu matsala kuna gani dai kowa da gurinsa to me zai dame ku."
SAFAH ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta da murmushi a fuskarta tace." Zinatu rigima
kin ga tashi kiyi mana Jagora cikin gidan mu gaisa dasu. ke kanki kin san abinda kike bukata ba
mai yuwu wa bane.
Cike da rashin dadi ta tashi ta shiga daki domin dauko mayafi, nan Aunty Hussana ta bita dakin
ta bata wata leda dake cike da turarukan wuta da humra masu kamshin gaske, sai kuma
kaninfari da yawa cikin wata leda a d'aure, tace mata ta jika cikin wani abu tana shan ruwan.
Godiya sosai tayi mata kafin su fito daga dakin a tare.
Uwale tsohuwa mai dattako! ta kar'be su hannu biyu tana ina a saka ina a sauke dasu.......Da
yake basa rabo da abinci ta sanya Hamra'u ta had'a musu abinci wanda zai gamsar dasu.
Haka nan suka saki jikinsu suka ci abinci wanda Hamra'u ta sarrafa sosai Allah yai mata baiwar
iya sarrafa abinci ko wane iri ne a zahiri suma sun yaba sosai kuma ci sun gamsu.
Itama ZINAT din taji dadin yanda aka karramasu ta saki jikinta tamkar akwai sabo a tsakaninsu,
har tana jan Hamra'un da hira, wanda hakan ya basu mamaki mutuka, to itama dai Hamra'un
saki tayi kamar wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninsu ba.
Tafiyarsu keda wuya ya kira wayarta yana tambayarta.
Tace." Ai har sun tafi."
Cike da mamaki yace." Sun tafi."?
Tace."Eh nima wallahi babu yanda banyi dasu ba su kwana amma sun tafi kamar ana korarsu."
Ya girgiza kai da rashin jin dadin hakan, yace." Me yasa da zasu tafi baki kira ni kin sheda min
ba, sai na bar duk abunda nake nazo mu gaisa."
Tayi shuru domin ba tasan me za tace ba.
Yace." Laifin duk naki ne Zina kwata-kwata banji dadin tafiyarsu ba naso mun gaisa da juna
sosai."
Tace." Kayi hakuri amma ai sun gaisa da Uwale har suka ci abinci a gurinta.
Yace." Hakan ma yayi amma Uwale daban ni daban."
Tace." Hakane kuma." Shuru ya ratsa tsakaninsu kafin tace." Daddare me kake bukatar ci."?
Kai tsaye yace." Towon dawa da miyar kuka."
Iya gaskiyar sa ya fadi maganar.
Amma sai ta kyalkyale da dariya da fadin." Towon dawa! gaskiya ni ban iya ba."
Yace." Aikuwa ki koya domin shine favorite d'ina mussaman dumame towo ko wane iri ne ina
sonsa.
Tace." To shikkenan kada ka damu yau ma da kaina zan maka abincin insha Allah."
Yace."Okey da can bake kike ba kenan."?
Da sauri ta gyara maganarta tace." Ni ce mana ina nufin yau na mussaman zanyi maka towon
da kake so.
Yace." Idan da akwai matsala ki zauna ki huta kin san baki da koshin lafiya."
Murmushi tayi da fadin." Naji sauki ai ina bukatar samun ladan aure."
Murmushi jin dadi yayi yana juyi kan kujerarsa yace." Shikkenan yau da daddare za muyi hira
kenan."
Tana 'yar dariya tace." Sosai irin wacce ba mu ta'ba yin irinta ba."
Yace." Alhamdulillhi na gode Allah da ya bani ke a matsayin matata."
Tace." Nima haka amma dai ka yafe min laifi na ko."?
Ya gyara zamansa da fadin.'' Na yafe miki kuma da ikon Allah zan d'aga miki ki shiga aljanna
Bakya laifi a guri na GIMBIYATA."
Tace." Na gode *Mazan Fama!* Allah ya barmu tare." ya amsa da "Ameen wani irin farin ciki
na ziyartarsa.
Aikuwa kamar yanda tayi masa alkawari, da kanta ta shiga kicin din, ta sanya Marakisiyya ta
harhad'a mata komai wanda zata bukata, yau abunda bata ta'ba yi ba zata kwatanta.
Ita kad'ai a kicin din tana gwagwarmaya! duk ta jigata, sai gumi take abunka da wanda bai saba
ba.
Akayi rud'e kalau! aka rufe ruf! sannan aka shiga had'a miya, tayi dubarar silala naman da
albasa da kayan 'kamshi amma bai wani dahu sosai ba, ta zuba su daddawa da kayan miyan
data murza a gireta, ta zuba uban farin mai tamkar me shirin yin jar miya.........Can rud'en dake
rufe ya fara za'bal'bala kafin kice me murfin tukunyar yayo sama talgen ya fara kumfa yana
zuba saman gas din, da sauri take k'okarin cire murfin aikuwa ta 'kone a hannu!! baya ta
matsa tana ihu!! taje ta kwance famfo tana wanke talgen daya kona ta. kuka ne kawai ba tayi
ba fatar hannunta tayi jajawur! ido jawur! ta fita daga kicin.
Ta zauna kan kujera tana mayar da numfashi..........A'a abu kamar wasa hannu ya fara tashi!
ga wani irin zafi da yake mata......kira ta kwalawa Marakisiyya tace mata maza taje ta k'arasa
ita tayi abunda zata iya.
Tashi tayi ta shiga d'aki ta kwanta, tana jinyar hannunta.
Daf da zai shigo gidan ya kira wayarta, ta daga su gaisa yana tambayarta jikinta, tace." Lafiya
amma garin yi maka towo na k'ona hannu.
Yace." Subahanallahi garin ya hakan ya faru."?
A shagwabe tace." Talgen ne ya dinga zuba naje bude tukunya ya zubo min a hannu."
Yaji duk wani iri a jikinsa yace." Sannu my love amma ba sosai bane ko."?
Tace."Eh ba sosai ba amma har ya tashi sai ciwo yake min."
Yace." Yi hakuri kinji bari yanzu zanzo nai miki addua insha zaki ji sauki."
A sanyaye tace." Okey my darling na gode sai ka shigo." kashe wayar yayi yana Allah-Allah ya
isa gidan.
Wanka tayi ta kimtsa domin bata so ya shigo ya sameta babu ado, tunda tasan yana san haka
shiyasa ta mayar da hankali gurin yi masa ado da kwalliya na kece raini.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malamí ½í¸Š: *Assalamu alaikum warahmatullahi masoya yan uwa na
musulmai...*
í ½í°«í ½í°«í ½í°«í ½í°«í ½í°«
í ½í°«í ½í°«í ½í°«í ½í°«
í ½í°«í ½í°«í ½í°«
í ½í°«í ½í°«
í ½í°«
*Tabbas wani kaya sai amali ,busa sai sarewa jiniya sai a gidan gomna ,ina kuke mata ma'abota
tambayar ina wannan shahararriyar y'ar mutan nijer wato mali ,wacce akafi ma lak'abi
da...*```í ½í°«BUZHUWA EMPIREí ½í°«```
*Ina kuke matan Aure n mu masu fuskantar tangard'a tare da k'alubale a gidan mazajen Auren
mu??í ½í²ƒí ½í²ƒ.*
*Ina kuma y'ammata masu buk'atar farin jini ta hanyar samun mijin Aure?? Don raya sunnar
manzon mu SAW...Nasan duk kunce gamuuu!!!.* *Gafa BUZHUWA EMPIRE ta* *taho
maku duk don share hawayen dake kwaranya akan fuskokin ku ta hanyar kawo maku sirrin
mallaka tare da* *magani ,haka ma y'ammata ga sirrika nan da maganin shi ,wanda anyi
mutane babu adadi kuma anzo anyi* *godiya....ki tambaya wacece Buzhuwa empire ga dukkan
wanda* *yasanta ,zakuji karin bayani daganan. Muna bada mallaka ta hanyayoyi dabam*
*dabam ,wanda da alfarman annabin rahma xamu sha mmki.* *Mallakar tamu akwai na 3k
akwai na 5k ,akwai na 10k da sama ma da haka. Mudai fatan mu shine babu cuta babu cutarwa
, kamun mu biya* *maki bukatanki sai kin mana rantsuwa akan bazaki cutar dakowa* *ba
,mallaka matan aure muke ba zallah. Na farin jini kuma na y'ammata ne ,shi munayin shi akan
5k ne da kuma na 10k.* *Zakuna iya tuntu6an wannan numbern domun karin
bayani...09061466409/08081202932.*
*Ga kad'an daga cikin mallakar da muke amfani wajen yinsu.*
*Mallaka ta hanyar K'wai.*
*Mallaka ta hanyar nono*
*Mallaka ta hanyar zobe*
*Mallaka ta hanyar guru*
*Mallaka ta hanyar turaruka da dai sauran su.... Sai kin taho domun share hawayenki daga
kunci zuwa farin ciki....* ```BUZHUWA EMPIRE taku ce!!!```
~08081202932 ko 09061466409~
*95&96*
Cikin shirin bacci ya sameta zaune a bakin gado ta zabga tagumi! fuskar nan a had'e! da alama
jiran kiris take ta fashe da kuka! ya 'karasa ya zauna kusa da ita tare da kiran sunanta, bata
amsa ba sai ma janye jikinta da tayi, hakan beyi masa dadi ba, amma sai ya daure tunda hakan
ba sabon abu bane a gurinsa.
Hannunta ya laluba ya rike cikin nashi murya a tausashe yace."Me yake damunki.''?
Kawai sai hawaye ya fara zuba a saman fuskarta!
Ya zuba mata ido yana mamakin kukan da take, shi dai yana kokarin kiyaye abinda zai had'asu
rigima ko wani tashin hankali, burinsa a yanzu bai wuce ace ta kwantar da hankalinta ba dan
ingantuwar lafiyarta.
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya janyota jikinsa yana rarrashinta bai kuma fasa tambayarta
damuwarta ba.
Ta cire jikinta daga jikinsa tana share hawaye! tace." Nifa ban shirya haihuwa yanzu ba."
Gabansa yana faduwa yace." Bangane abunda kike nufi ba."
Tayi kokarin hadiye yawun bakinta kafin ta sake maimaimata masa maganarta.
Yasha mur! kamar bai ta'ba dariya ba yace." Okey to da baki shirya haihuwa yanzu ba ya kike
so ayi? kin san dai rayuwar kaf ba a hannuki take ba ballanatana kice za kiyi yanda kike so.
Shin meye ribar aure."?
Shuru tai masa ba tace uffan ba.
Ya sake maimaita maganarsa...."Ki bani amsa nace meye ribar aure."?
Tayi 'kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Murmushi takaici yayi ya girgiza kai tare da fadin." Kiyi hakuri ki bar wa Allah ikonsa kada ki
butulce masa mutane da yawa suna can suna nema ido rufe bai basu ba, amma ke ya fifitaki a
kansu yayi miki kyauta mai muhimmanci amma ki nuna bakya muradi kada kiyi haka, kawai kiyi
addua Allah ya saukeki lafiya yasa kuma abunda zaki haifa cikon addinin musulunci ne."
Duk wannan maganganun da yake bai sa ta saduda ba kawai dai tana jinsa ne amma ba zata
janye kud'irinta ba.
Ya dinga kwantar da murya yana rarrashinta da kalamai masu sanyi duk a tunaninsa shurun da
tayi tana d'aukar nasiharsa, sai dai kuma washe garin ranar yana fita gurin aiki ba da jimawa ba
kiran wayar gaggawa ya sameshi cewa yazo gida babu lafiya.
Magashiyan! ya sameta a kwance tana murkususu! cikinta ya d'aure sai wani mugun ciwo yake
mata gabadaya ta fice daga hayyacinta!.
emagency suka nufa cikin gaggawa aka bata taimakon gaggawa! anan likitan ya gane lallai
tasha wani abun domin yunkurin zubar da cikin jikinta.
Wannan bayananin yayi masa yana kara jadadda masa da cewa lallai ya sanya ido ya kuma
kula da kyau domin dai cikin ya kai matakin da idan akace dole sai an zubar dashi za'a samu
matsala.
Hankalinsa ya tashi ainun! gabadaya ma ya rasa wane irin tunani zai yi, ashe kiyayyar da take
masa har ta kai haka.
Koda suka koma gida bece mata komai ba sai da ya tabbatar da cewa taci abinci tasha magani
sannan ya koma gurin aiki tare da tunanin matakin da zai dauka.
Sai da ya dan samu nutsuwa tukkuna ya lalubi number mahaifinta gwara ya shedawa iyayenta
abunda yake faruwa kada ta kashe kanta suga laifinsa.
Cikin mutumci da mutuntawa suka gaisa da juna Maimartabar ya dinga yi masa addua tare da
cigaba da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya..
Jikinsa ya mutu! ya dinga tunanin yanda za'ayi ya sheda masa abunda yake faruwa, mutumin
nada kirki sosai kuma baya so ya tayar masa da hankali domin duk uban da yaji cewa ga
abinda 'yarsa keyi a gidan aure dole hankalinsa ya tashi, amma ya zama dole ya sheda masa
domin hakan shine mafita.
Iyakar abinda ta aikata a yau din ya sheda masa amma ya boye sauran laifukan da take masa!
a ganinsa duk basu kai matakin da zai kai 'karar ta a kansu ba.
Maimartaba yayi shuru yana jimanta al'amarin...... sai ya shiga tunanin abinda ya shud'e!.
Danne 'bacin ransa yayi kafin ya shiga bawa UMAR din hakuri tare da fadin ya cigaba da kai
zuciyarsa nesa a kan yarinyar yana kawar da kansa kuma ya cigaba dayi mata adduar shiriya
insha Allah komai zai wuce, shima kuma a matsayinsa na mahaifinta zai dauki mataki akan
abunda ta aikata.
Suka rabu cikin mutunci tare da jajantawa juna koba komai ta tayar da hankalin iyayenta domin
a ranar Gimbiya Aysha kasa rintsawa tayi abu biyu suka dameta bakin cikin abinda 'yar ta keyi
sai kuma tashin hankalin da mijinta yayi mata a cewarsa duk abunda ZINATU keyi abunda ta
aikata ne a baya tarihi yake maimaita kansa, ta tsani wannan kalmar tana fitowa daga bakinsa.
Bai shedawa Asp abunda yake faruwa ba, sai da suka had'u gaba da gaba domin maganar ba
zata yuwu a waya ba.
Shima Asp din lokacin da yaji maganar ya girgiza ya dinga nanatawa yana al'ajabin
al'amarin.........Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Yanzu ya jikin nata."?
Yace."Da sauki alhamdulillhi kuma likita ya tabbatar da cikin yana nan bai fita ba, amma ni har
yanxu ban sanya raina a kansa ba, ina ganin za ta iya bin wata hanyar ta zubar dashi.
Yace." Insha Allah hakan ba zata faru ba, sannan kuma idan ba damuwa inaso kayi min jagora
zuwa gareta."
Kai kawai ya daga masa yayi gaba sai ya rufa masa baya dukkaninsu zuciyarsu babu dadi.
Shi ya fara shiga ya sheda mata zuwan Asp din ba tare daya jirayi amsar ta ba ya fito daga
dakin dan bala'in shaushinta yake.
Ta fito cikin dogon hijab kamar wata mutuniyar arziki, saboda tasan bata da gaskiya har kasa ta
durkusa tana gaisheshi bai kai ga amsawa ba kawai ta fashe masa da kuka!
Ido kawai ya tsira mata tausayi yarinyar take bashi ya dinga raya wani abu a cikin zuciyarsa,
wani sa'in idan mutum na aikata abubuwa marasa kyau! da akwai hali amma kuma akwai sanya
hannun aljanu a ciki.
Ganinta tana kuka yaja tsaki ya kama hanya ya fita a ganinsa ba ita ya dace tayi kuka ba, shine
kuka ya dace dashi duba irin wasiwahsin da ta jefa rayuwarsa a ciki.
Asp din ya bishi da kallo yana gyada kansa, sam bai ga laifin abunda yake ba, domin an shiga
huruminsa
Ya kalleta tana ta aikin share hawaye wasu na zuba, ita kanta tasan abunda tayi ba daidai bane
to za'a tayi da zuciyarta gaskiya ita ba taso ta haihu ta tsufa da wuri shiyasa tayi yunkurin zubar
da cikin tun beyi kwari ba, ashe tana da rabon shan wahala! domin ita kadai tasan irin bakar
wuyar da taci sakamakon abinda ta aikata.
Yace." Zinatu abinda ki ka aikata ya sa'bawa shari'a kin aikata mummunan laifi irin wanda Allah
baya so, yanzu da Allah ya dauki rayuwarki sanadin zubar da cikin halak me za kije kice
masa."?
Wasu hawaye masu zafi suke sake wanke mata fuska, sai kawai jikinta ya shiga karkarwa!
Ya cigaba da cewa. Kiyi istigifari ki roki Allah gafara akan abinda kika aikata Allah gafurur
rahimu ne zai yafe miki sai abu na gaba ki nemi afuwar mijinki! sannan kuma kada ki sake
yunkurin aikata mummunan aiki irin wannan! wannan ce kawai shawarar da zan iya baki."
Kasa cewa komai tayi kawai kuka take tana girgiza kai tare da istigifari a cikin zuciyarta.
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ki daina kuka bashi ne mafita ba. kukan zai iya janyo miki wata
matsala.
Da kyar ta iya bude baki tace." Na gode sosai Ranka ya dade insha Allah ba zan sake ba.
Yace." Allah yasa Allah kuma ya yafe miki kuskuranki." Ta amsa da "Ameen tana kokarin tsayar
da ruwan hawayen dake zuba.
Abokin nasa ya kira yace yazo shi zai tafi......minti biyar sai gashi har yayi wanka ya sauya kaya
bakar jallabiya mai karamin hannu da botira kansa sanye da hula tashi ka fiye naci.
Ya kalleshi da fadin." Naga kasa hula sai kace wani balarabe fita za kayi ne."?
Kansa ya girgiza tare da kokarin zama a kusa dashi yace." Babu in da zani.
Yace." Okey ga tanan tayi nadama kuma tace na taya ta baka hakuri, kasan dan Adam ajizi ne
kowa yana kuskure don Allah ka yafe mata."
Shuru yay bece komai ba ya tsirawa tv ido haka kawai baya son kallon fuskarta.
Ganin yayi shuru beyi magana ba, yasa Asp din duba agogon hannunsa tara shaura na dare,
ya mike da fadin." Ni zan shiga gida Allah ya kiyaye gaba."
Ya kalleshi da fadin." Ameen ya Allah na gode sosai Allah ya saka da alkairi a gaishe min da
Daughter."
'Yar dariya yayi tare da jin dadin yanda yake nuna kauna da kulawa a kan 'yarsa yace." Nabila
za taji da kyau insha Allah."
Bayan fitar Asp din da minti biyu ta kalleshi gabadaya hankalinsa nakan tv kamar bai san da ita
a gurin ba.
A sanyaye taje ta zauna kujerar da yake zaune da yake 1sitar ce sai suka takura jikinsu ya hadu
sosai.
Bai kalleta ba ballanatana ya tanka mata still bai janye idonsa daga abinda yake kallo a tv ba.
Sajen dake kawace da fuskarsa ta fara wasa dashi ta dora kanta saman kafadarsa, murya na
rawa tace." Kayi hakuri don Allah."
Sanyi yaji a zuciyarsa amma bai nuna a zahiri ba, ya janye jikinsa kanta ya sauka daga