Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
ikon fad'in gaskiya ka kuma basu ikon adalci)*
Ya gama kashe mata jiki da mayaudarar kalamansa zuciyarta tayi sanyi ba tayi wani dogon
nazari ba ta amince da kalamansa...........*(Kada soyayya tasa mijinki yayi miki dadin baki kan
cewa shi dake kad'ai zai rayu, 'karya yake! domin wallahi zuciyarsu a haka take haka Allah ya
hallicesu da son mata, zakiga namiji da mace hudu a gidansa duk mallakinsa amma ba zaki
rabashi da wasu a waje ba............shakulatun 'bangaro zakiyi dashi a duk sanda yazo yana miki
wannan manganganu, idan kuwa ki ka yarda da labarin k'anzan kurege! to kina ruwa In ji
(HAMISU BREAKAR) sai dai kiji ana ayyyyyiririiiiii!*
Soyayya suka dinga bugawa! irin wacce take bala'in so da kwakwa! dan idan wani sa'in ta rike
wuta har makara yake a gurin aiki, Asp yay ta tsokanarsa, shi kam murmushi kawai yake daga
zarar kuwa ya samu sauk'in aiki zai kira wayarta suyi ta jifan junansu da zafafan kalaman
soyayya.
Hamra'u tsantsar tashin hankali da damuwa ta shiga dan ganin yanda mutumin nata ya ajiyeta a
gefe.........Da farko ta d'auka matsala ce zata afku, tun bayan da Uwale ta sheda masa abun da
yake faruwa.
Amma abun mamaki sai taga a washe garin ranar be ma fita aiki ba, yana tare da matarsa tun
safe bai shigo in da suke ba, saboda tsabar bin diddigin da take masa har fita tayi ta tambayi
direbansa cewar ya fito daga gidan ko kuma yana ciki.
Budar bakin direban yace." Ai Oga yau ba zai fita ba domin tun safe ya kira ni yake sheda min
hakan.
Jikinta a sanyaye ta koma gidan........koda ta gifta sashen sai taji a zuciyarta kamar ta shiga
domin ganin abunda ya ha nashi fita.
Da 'kyar! ta iya kai kanta dakinta, tayi kwance a saman gado tare da tsirawa rufin dakin
ido......zafafan hawaye ne suka shiga tsere a saman fuskarta.
Can yamma! taji maganganu a falo...ta d'auka baki sukayi koda ta fito........Sai kawai tayi
tozali dasu, suna zaune kujera daya sunci uwar kwalliya mussaman ita Gimbiyar kamshin
turaransu duk ya cika gurin.
A take gwiwarta tayi sanyi kafafunta suka dinga wani irin rawa, bango (garu) ta dafa jin tana
neman zubewa a gurin.
Babu yabo babu fallasa yace." Kanwata kin fito."?
Kallonsa tayi tana danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin ita ya za tayi da wannan
kaddarar....Mutumin data ci wahala a kansa ta b'ata lokacinta a kansa shine yake rayuwar aure
da wata akan idonta...........Kanta ya dinga juyawa! take ta zube a gurin bata san in da kanta
yake ba.
Gigicewa sukayi gabadayansu mussaman shi ya kai ya kawo a gurin hankalinsa ya tashi ainun!
bai san lokacin daya dauketa ba ya fita da ita Uwale ta rufa masa baya tana gyara yafan
mayafinta.
Tsayuwa kawai tayi a gurin tana mamakin abinda yayi.
Yarinya baliga kuma ba muharramarsa ba ya wani dauketa har da mannata a
kirjinsa........Takaici da bakin ciki kamar su kasheta, tayi kwafa tare da girgiza kanta, sashenta
ta nufa tana tunanin irin hukuncin da za tayi masa idan ya dawo domin ita ba zata yarda da
wannan iskancin ba.
Abin mamaki! jininta ne ya hau sosai! lokacin da likita ke sheda musu hakan, abun sai ya basu
mamaki! shin wane irin tunani yarinyar ta sa a ranta haka wanda har zai janyo mata hawan
jini.....Ita dai Uwale ta zargi wani abu, shine dai har yanzu beyi hasashen cewa rashin adalcinsa
ne ya janyo mata kamuwa da lalura ba.
Da kanshi ya bukaci cewar ta kwanta a asibitin zuwa gobe domin ta sake samun sauki sosai,
domin a zahirin gaskiya hankalinsa ya tashi da al'amarin, yana tsoron kada yar mutane ta had'u
da lalura a hannunsa.
Sai bayan isha'i ya bar asibitin.........Yana shiga barrack din Asp ya fito daga block d'insa da
waya a kunnansa.
Motar ya tsayar ya sauke gilashi yana kallonsa har ya k'are wayar ya mayar da ita aljuhu ya
k'araso bakin motar .
Hannu ya mi'ka masa suka gaisa kafin yace." Yanzu mutuniyar ta shiga gida ai ta jima a
gurinmu kasan Zeey mutuniyarta ce."
Yay jim yana kallonsa da nazarin maganarsa.
Shima Asp din ya fahimci wani abu, sai jikinsa yayi sanyi yace." Akwai magana kenan dan
naga kayi sak! kodai bata fada maka ba."?
Bagarar da maganar yayi kafin yace." Ina cikin damuwa wallahi yarinyar nan Hamra'u ce take
kwance a asibiti babu lafiya."
Da sauri yace." Subahanallahi me yake damunta."?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya furzar da wani irin huci daga bakinsa yace." Haka kawai ta
yanke jiki ta fadi yanzu likita yake tabbatar min da cewa jininta ne ya hau."
Asp din ya jima yana kiran sunan Allah da jimanta al'amarin.....Yace." Jininta ne ya hau akan
wane dalili kodai tana da damuwa ne."?
Yayi shuru yana nazarin abinda kwakwalwarsa ke tuna masa tunda ya fito daga asibitin yake
nazari da tunani.
Yace." Baya rasa nasaba da mu'amula ta da matata kasan mata da kishi dasa abu a rai mybe
wannan ne ya janyo mata matsala.
Ya kalleshi da fadin." Hakane yanzu kai wane hukunci ka yanke? a zahirin gaskiya idan ba kayi
wani abu ba akan yarinyar nan ba to hakkinta yana iya kama ka da kowane lokaci saboda haka
ka zauna kayi nazari da tunani a yanda kake bani labarin hallacin da tayi maka yaci ace kayi
wani abu wanda zai nuna mata cewa lallai kana da niyyar auranta."
Murmushin takaici yayi kafin yace." Wallahi gabadaya kaina ya kulle Asp na shiga rud'u! ina jin
tsoran auran yarinyar azo ana tashin hankali abunda bana bukata kenan bana son matsala ko
yaya take.
Ya dinga kallonsa yana girgiza kai kafin yace." Ka zama namiji mana abokina rigima kake gudu
to bari kaji da kayi aure da ba kayi ba, kullum a cikinta kake, domin ba zata daina zarginka ba,
gwara ma kayi da hujja! amma ban ta'ba tunanin cewa Zinatu zata dinga baka tsoro ba a yanda
na sanka haba *Jan wuya!* kada ka bani kunya mana."
Dariya kawai yayi yana girgixa kansa, lallai akwai rikici a gabansa dan wallahi idan ya tuna
Gimbiyar tashi gabansa har wani faduwa yake.
Sallama sukayi da juna yaja motar ya bar shi a gurin yana daga masa hannu.
Yana shiga dakin kafarsa ta cake! da kwalba! duk da a cikin takalmi take sai da yaji rauni jini ya
fara zuba ya rike kafar yana d'ingisawa, gefe guda ya matsa yana bin dakin da kallo.
Komai a hargitse duk ta farfasa masa manyan turarunkansa masu tsada! kayansa muhimmai ta
watsar dasu a kasa, dakin dai tamkar anyi yak'i a ciki!
Kafin ma yayi wani yunk'uri ta turo kofar dakin ta shigo........Kallo daya yay mata ya hango
tsantsar tashin hankali a tattare da ita.
Jarumta! ya aro! yayi bala'in shan kunu! da fadin." Meye haka! waye yayi min kaca-kaca da
daki."?
Ta nuna kirjinta da hannu " Nice nan."! da karsashi da kwarin gwiwa ta fadi maganar!
Yace." Kece akan wane dalili? ko kina hauka ne."?
Wani b'acin ran ya sake turnuke ta! tace." Kaine mahaukaci butulu maci aman...........Ya wanke
fuskarta da lafiyayyan mari! yana wani irin tsuma! ya nuna kansa da fadin." Ni kike zagi
saboda baki da mutunci."?
Hawaye na zuba share-share a saman fuskarta........Tace." Kai waye da ba za'a zage ka ba
maha'inci kawai."!
Ya sake fusata! amma beyi yun'kurin dukanta ba saboda baya so ya saba da hakan ya danne
bacin ransa yace." Ki fada min abunda nai miki wanda ya janyo har kike kira na da sunaye
masara ma'ana."
Taja hanci tana shashshekar kuka tace." Ba ni da lokacin zama na fada maka abunda kayi ai
kai mai hankali ne ka zauna kayi nazari da tunani mtssswww!." ta k'are maganar da dogon
tsaki! kafin ta juya ta fita zuciyarta kamar ta fashe saboda bacin rai!
Da d'ingishi ya fita domin kwalbar ta cake shi sosai! d'aya daga cikin hadimanta maza ya kirayi
d'aya shi ya jagoranceshi har cikin dakin ya bashi umarnin cewa ya gyara masa, ya zauna
kujerar falo yana duba kafarsa, dole sai anyi dressing din gurin domin duk da ya cire kwalbar
gurin yana bukatar gyara.
Da yake a barrack din suna da likitocin dake duba lafiyarsu sai kawai ya kira daya daga cikinsu
yazo ya dubashi ya bashi maganin rage zugi.
Allah yasa ya gabatar da sallolinsa, kawai sai ya kwanta saman kujera yana mayar da
numfashi..........Ya riga ya gano dalilin da ya sanya ta aikata wannan haukan! bai san wane irin
kishi ne da ita ba.....hakika auranta yana nema ya zame masa matsala. shi kuma irin tashi
jarrabawar kenan.
Washe gari da ciwon jiki ya tashi domin k'afar ta tashi ta kumbura! haka nan ya daure yayi
shirin fita domin baya tsammanin zai iya zaman gidan saboda gudun tashin hankali.
Bai fita ba sai da ya nemi inda take saboda baya so ko yaya Allah ya tuhumeshi da hakkinta.
Tamkar bata da damuwa haka ya sameta ta cakare! tayi gayu na kere sa'a! jikinta da dakinta in
banda kamshin turare babu abunda yake.......Cikin zuciyarsa yake fadin *( D'an Adam tara yake
bai cika goma ba)* Allah yai mata komai amma bata da kyawun hali.
Babu yabo babu fallasa yai mata sallama........Gabanta ya fadi ganin yana jan kafarsa babu ma
takalmi sai safa kawai! kafafun, yana tafiya da d'ya yana dingisa daya, ta tsirawa kafafun ido
har ya k'araso kusa da ita bata sani ba.
Babu walwala a tare dashi yace." Zan fita gurin aiki ina fatan baki matsala."?
Idonta ta janye tana jin wani irin a tare da ita.......Ashe rauni yaji mai yawa! cikin zuciyarta take
maganar..
Ganin ba tace komai ba kawai sai ya kama hanyar fita.
Ta bishi da kallo 'kwalla na ciko idonta.....duk abunda tai masa shi ya janyo.......Idan ta tuna
abunda ya faru kamar ta mutu da bakin ciki.
Bai shiga headquarter nasu ba, sai da yaje asibitin ya dubata, babu shakka yaji dadin yanda ya
ganta tayi garau! suna hira da Uwale. wacce take kwantar mata da hankali gami da bata
tabbacin cewa ta kwantar da hankalinta Umaru kamar ya aureta ya gama.
Maganganun Uwale sune suka sanyayar mata da zuciya.....Shi kansa likitan dake dubata yaji
dadi sosai. nan ya cigaba da bata shawarwari masu kyau.........
*Kuyi hakuri ina zuwa makaranta, shine dalilin da yasa bakwa samun update akan lokaci
NAGODE*
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malam: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 4k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*91&92*
Wannan ciwon jikin da ya fita dashi ashe sa hannun zazzabi ne. domin koda ya zauna a ofis
din kasa katabus! yayi kawai sai ya koma kan doguwar kujera ya kwanta zazzabin na sake
k'arfi a jikinsa wani irin bacci mara dadi yana fizgarsa.
Shigowar Asp ofis din ne ya zaburar dashi! ya bude jajayen idanuwansa yana kallonsa har ya
k'araso gurinsa da wasu takardu a hannunsa.
Ganinshi wani iri ya sanyayar masa da jiki da ya shigo da 'kwarin gwiwa sakamakon samun
rahoton mutumin da suke ta nema ruwa a jallo.
Gefansa ya zauna da fadin." Jarumi wai shin me yake damunka ne tuntuni nake kiran wayarka
babu amsa wannan dalilin ya sanya kawai na yanke shawarar zuwa ofis din naka.
Ya mike zaune da 'kyar! yana ya mutse fuskarsa yace." Bana jin dadin jikina wallahi zazzabi da
ciwon jiki ke damuna."
Maganar yake amma shi Asp din hankalinsa yana kan k'afarsa dake kumbure!
Cike da al-ajabi yace." Rauni kaji ne babu labari."?
Mirmushi takaici yayi yana danne b'acin ran dake taso masa yace.'' Jiya bayan rabuwarmu ina
shiga gidan.......duk ya kwashe komai ya fada masa.
Ya dinga girgiza kansa yana mamakin al'amarin yace." Yanzu Zinatu da hankalinta ta aikata
wannan d'anyan hukunci. koda yake ko shakka ba nayi da sanya hannun Zainab domin yini
sukayi a tare wa yasan irin abunda suka shirya.
Ya girgixa kansa da fadin." Kada ka zargi kowa domin yarinyar abunda yafi haka ma zata
aikata, na shiga dakina na samu ta tarwatsa min ko'ina wannan shine dalilin da ya sanya na
samu rauni a kafata.
Yace." To wai shin ma me ya had'a ku ne har hakan ta faru."?
Tsaki yaja kafin yace." Bak'in kishi ne da jahilcin dake damunta, tana zargi na dan haka
zuciyarta take raya mata, amma ni nasan abunda na aikata ba haram bane domin da niyyar
taimako nayi kuma ko'ina hakan na iya faruwa ballanatana a cikin gidana, Asp mutukar naga
abunda zai cutar da wani musulmi dan uwana mace ko namiji sai inda karfi na ya kare."
Yace." Maganar kake a du'kun'kune ka fayyace min makasudin abunda ya janyo matsalar."
Kallonsa yayi na second biyu kafin ya fara warware masa abunda ya faru.
Yace." Gaskiya ne baka aikata haramci ba kamar yanda take zarginka, kayi hakan ne da niyyar
taimako amma kasan mata idonsa yakan rufe akan kishi basa tunani akan kowa sai a kansu
amma meye laifinka dan ka dauki Hamra'u kasa a mota shin so take ka bari ta mutu ko yaya."?
Yace." Nima dai haka na gani meye laifina anan? wallahi banyi hakan da wata manufa ba sai da
niyyar taimakon musulunci."
Yace." Umaru wallahi kwata-kwata bana k'aunar alakar Zainab da Zinatu domin dukkaninsu
basu da kirki! maganar dai guda daya ce akwai sanya hannun Zeey dangane da faruwar hakan
kuma zanje gidan na sameta."
Yace." Aa kada ka yanke hukunci cikin fushi! na fada maka fa cewa.......Koda babu Zainab a
cikin rayuwar *ZINA* to zata iya aikata abunda yafi haka wannan shine dalilin da yasa tun kafin
muyi aure nake da shakku akanta saboda gudun faruwar matsala irin wannan......Ban auri
Hamra'u ba haka tana faruwa to inaga kuma na aure ta."?
Yace." Kai dai zaka zage damtse ka tsaya a matsayinka na namiji ka nuna mata bambanci
sosai amma naga duk ka wani susuce! wai shin ko tsoronta kakeji ne."?
Murmushin takaici yayi kafin yace." Asp mu rufe maganar nan dan Allah! muyi abunda zai yuwu
domin ina so na tafi gida na kwanta na huta."
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ai shikkenan tunda ka fadi haka amma ni kam dole
na tauna tsakuwa domin aya taji tsoro."
Shuru kawai yayi masa yana jin wani irin takaici a ransa.........Wai yana tsoron yarinyar, wannan
maganar ta sosa masa rai mutu'ka! shin akwai wata mace da zai ji tsoro a fadin duniya, Uwarsa
ce kuma bata raye.
Takardun dake hannunsa yake bud'ewa, wata doguwar takarda ya fito da ita da hoto kati daya,
mika masa yayi kafin yace." Ka duba hoton sosai ka kuma duba rahoton dake jikin takardar.
Saman takardar kawai ya duba yaga an sanya *AMINIYA GIDAN JARIDA KANO STATE*
Ya kalleshi da fadin." Wani abu ne yake faruwa a jahar *KANO."?*
Yace." Duba dai amma ka fara nazarin hoton mutumin dake hannunka."
Ya 'kurawa hoton ido yana ta so ya hasaso kowaye.....ya girgiza kansa da fadin." Bangane
waye ba wallahi."
Asp din ya kar'bi hoton da fadin........
*UBAN DABA NE."!* A zabure! ya kar'bi hoton yana sake dubawa, kafin kice kwabo gumi ya
fara tsatstsafowa a saman goshinsa.
Tabbas idan ba wanda yayi masa farin sani ba ba zai ganeshi ba domin duk kammaninsa sun
sauya......duk babu wannan 'kasumbar! yana sanye da kayan hausawa riga da wando harda
hula sai dai jikinsa lullube yake da wani farin mayafi irin na maza wannan shi ya hana bayyanar
nakasar dake tare dashi .........Tabbas shine domin k'wayar idonsa basu sanja ba suna nan
yanda suke gwala-gwala masu tsananin ja! kamar garwashin wuta!
Ya kalli Asp din da fadin." Ya akayi yanzu meye abin yi."?
Asp din yace." Nafiso ka karanta rahotannin kafin mu tsaya a matsaya ana bincike ne a kansa
da yaransa da suka sauka a