Zuma Da Madaci Book By Maman Teddy

Author :  Maman Teddy Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 14

18K to 21K   out of 41K words

duniya, gaba daya shigar ta babu na kwarai ta saka wasu damammun
Riga jecy da wandon jean kanta da wani siririn mayafi. Sarai ta ganeni don randa da taxo har
fada ya kauraye tsakanin ta da wata karuwar tasa mina wurin don har dani cikin wanda suka
serving nasu, kauda kai na nayi gyefe ina kiyaye ma kaina mutunci na".

Heeeee....." abun da tace mun kenan,wanda dajin hakan nasan dani takeyi yasani waigowa ina
kallon ta. Arch.Khaleed na nan kuwa???... ta fadi tana wani ya tsina mun baki hadi da wani farrr
da ido sai kace nine Sir Khaleed din. Daga mata akai nayi alamar ehhh,sannan ta juta hadi da
nufan cikin gidan yanda ko take karkada duwawuka sai da naji mata kunya don girgixa kai nayi
na wuce ganin yanda sojojin gidan da masu aiki maza ke bin Duwawun nata da kallo.
Haka kam fa fitowa na na fara takawa a kasa don a yau bana da na abun hawa,shiyasa nake
takowa tundaga gidan Hajy Zaituna har cikin Layin mu.

Jiyo Horn din moto a baya na yasani Saurin juyowa hadi da tsayawa cakkk a wurin don ganin
waye ke bina da Horn".
Fuskan sa sake yanda nasaba ganin sa ya fito hadi da yi mun Murmushi yana furta Har kin
tashi?
Dan murmushi nayi masa ina mai kara bin sa da kallo,hadi da ce masa ehhh Yahh Huday
yanxun nafito".
Kirjin sa ne ya buga jin kirar sunan da nayi masa, a zuciya n shi yana son tuno inda ya taba jin
wannan murya dakuma mai kirar sa da wannan Sunan Amma ya kasa".
Ganin haka yasa shi saurin sosa kyeya yana furta tom shigo na kai ki gida" kinga yamma tayi.
Kallon sa nayi gami da dan zaro ido na waje kan daga bisani nace a'a nagode yanzun fah zan
kara ka.
Daure fuska yayi gami da ce mun" okay ni wato Suhaimart ba yayan ki bene,bana da matsayin
da Zance kiyi abu kiyi,amma idan da Khaleed ne ai zaki shiga ".
Shiru nayi bance masa komai ba,sai kawai na nufi moton inajin ba dadi akan tirjiyan danaso
masa,Murmushi yymun cike da miskilamcin sa da ya zaman masa jini tun fil azeem ya bude
mun murfin moton nashi,yana mai rufowa....Tunda muka shiga moton bai kuma cemun komai
ba,sanin hali yasa ni nima Shiru ina mamakin miskilanci irin na Huday,don narasa wayafi wani
tsakanin sa da Sir Khaleed.

A dai² PZ wuraren Chiken republic ya tsaya,kallona yayi yana furta mun ina zuwa Minti buyu.
yana fadin haka ya fice daga moton hadi da nufan cikin wurin Chicken Republic din. Baifi yan
mintoci ba sai gashi gidan baya yafara budewa sannan ya rufo hadi da dawowa gidan gaba

wurin maxaunin sa yajah moton muka tafi.

Har kofar gidan mu ya sauke ni,sannan nayi masa sallama zan tafi,anan ya daka tar dani yana
fitowa hadi da bude moton yana dakko wasu manyan ledoji guda biyu hadi da
mikomun,Suhaimart ga wannan ki gaida Oumma". Tsayawa nayi na kasa amsa,wanda ganin
haka yasa shi kawar dakai yana shan mur. a hankali nasaka hannu na amsa ina masa gdy
sannan nayo cikin gida,Murmushi yymun kan na shige ne yakira sunana.
A sanyaye na waigo.
Buden bakin shi cewa yayi innako ma mai zan ce kince a fada ma Khaleed???.
kasa basa amsa nayi sai dai dan Murmushi danayi ina mai kutsa kaina cikin soron gidan mu.

Murmushi yy hadi da nufan moton shi wanda bai tada ba sai da ya kira Khaleed ya sanar masa
da ya kawoni gida sannan yajah moton,don dama a idon shi yana kallona ta Windown sama da
zan fita nice bangansa ba,ganin na fita yasa shi sanar ma Huday da yake kan Hanya akan ya
maidoni gida".
Bangaren Oummu Sulaym ko batayi mmkin ganin Babu Suhaimart ba,don sarai tasan Halin ta,
Murmushi tayi mawa kanta,kan daga bisani ta tarkato kayan ta hadi mawa Mhiss Caterine
sallama sannan ta dau hanyar tafiya gida".

Itako wannan karuwa da shigan ta side din Sir Khaleed direct falon shi ta kutsa kai kaman dakin
Uwar ta,haka sauran Ma'aikata ke gayar da ita amma bi ta kansu ba tayi ba,burun ta kawai ta ci
karo da Sir Khaleed yanda ta debo fitinan ta da magungunan da tasha ma cikin ta to ta sauke
jarabar ta akan shi don duk don shi tayi wannan aiki... Tafiya kawai takeyi amma jin ta take a sama,banda tsiyaya babu abun da takeyi...sai Uwar gumi
da take futarwa". Fitowan sa daga Privacy kenan daure da towel a kugun sa daya hannun sa
kuma yaba dauke da karamin towel yana goge sumar kansa...
Nufo sah kawai tayi gadon gadon tana wani fixgar numfashi kaman numfashin nata zai dauke
duka.......

Littafin Zuma da madaci na kudi ne,VIP da Normal #200.
Transfer #200 SPC 300.Duk ta wannan number 08081202932.09137392680.



*#SHERE TO ANOTHER GROUPS*

Mu tare a episode na gaba.

Maman teddy
*Typing...✍*




*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_


Na
*Maman teddy*

*Episode 12*


*_________________________*


*ALHERI WRITERS ASSO.️*

*A.W.A*


```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri```

*___________________________*


مسب* الله رلا نمح رلا *ميخ


_Dedicated to my teddyWannan pagen taki ce y'a d'aya tilo._


*_Domun samun Littafin Zuma da mad'aci tun daga farkon sa har karshe zaki tuntubi wannan
number 09137392680/08081202932._*
_*Ma'ana zaki turo #200 idan VIP,idan kuma SPC ne #300,100 kuma NORMAL kenan....*_

_*Plz don't miss dis novel,the latest Hausa nvl in 2021.*_
_*Do not miss this Novel Hajiya ta,idan baki karanta ba an barki a baya Hajjaju....*_

*_____________________________*

Sai a sannan ya ankare da isowan ta bedroom din nashi,don haka cikin mugun tsawa da yake
firgita su ya daka mata wannan tsawa ta hanyar daga mata hannu yana mai cewa"Heee Stupid
get out my Hause".
Ya fadi maganan ta hanyar yi mata nuni da kofah wato ta fice ta basa wuri".
Kallon sa tayi cike da Rashin fahimtan anyah Khaleed din ta ne,Khaleed din da ta sani ne ko
wani ne dai da ban. Bin jikin ta tafara yi da kallo,ko shigarta ne batayi atracting nasa ba. ganin
komai nata ya baiyana masha'allah babu wani mahalukin namji da xata gufta ta gaban sa bai ji
wani iri ba yasa ta kara sauke idon sa akan na Khaleed da har ilah yau Fuskan sa take a
murtike kaman bai taba sanin yanda ake dariya ba".
Bakin Zeebu har rawa yake da kyar ta iya furta masa Khaleed youuuuu???.
Mtssswwww wani dogon tsaki yajah hadi da nanata kalmar I said you should get out to my
Hause,Idan kuma ba haka ba i will call my guid to fushh you away... ya fadi yana kama hanyan
nufan falon sa". Saurin shan gaban shi tayi gami da furta Khaleed Da gske kk na tafi na bar ma
gidan ka?" Ko dai kasha wani abu ne???, Bai bata amsa ba illah ra6ata da yy ya wuce ta
gyefen ta yana mai nufan farfajiyan gidan Had'i da kwala kurar Securities maza guda
biyu,wanda su ke da alhakin shigar kowa Side din sa". Cike da tsawa ya fara masu bayani akan
daga yau kar su sake barin wata y'a mace ta shigo side nashi ba tare da amincewar sa ba,kuma
su zo su fitar masa da wancan matan". yana fadin haka ya juyahhh fuuuuu hadi da shigea
ciki,wanda a falo suka ci karo da Zeebu tana mai mmkin wannan dabi'a ta Khaleed da ya bijiro
mata dashi lokaci guda,don abun jin shi take tamkar a mafarki. Kafin tayi masa mgn ne tuni
Security ya daka mata tsawa ta hanyar cewa" Hajiya Outt".....
Kallon Securityn tayi wanda da kaganshi kaga yare hausa bata ganshe sa ba. da kyar cike da
dacin rai tace" Heee do you know Who I'm i!!?? I think you are Nonsence,ibeg give me chance
to go"..tana maganan ne cike da matsanan cin bakin ciki da tashin hankali". Shi dai security
matsawa baya yayi hadi da ce mata Oyyah go Out Hjy...Out". yanda kasan yana kada karya. Haka tasa Kafan ta ta fice daga side din tana mai nufan Farfajiyan gidan don ta shiga moton ta
ta sulale babu kwarin gwiwa".
Suko sauran ma'aikatan barayin nashi kowa haka ta kama kanta,don yau sun san Sir Khaleed a
zuciya yake da kowa,tunda har ya bata ran ta gaban goshin sa Wato Zeebu". kowa a zuciyan sa
tambayan kansa yake mai ya kawo mawa Sir Khaleed wannan Sauyi lokaci guda ne?.

Niko Suhaimart da shigana gida na tadda Oumma na tana Zaune tsakar gidan mu tana
sukola,da ganina ta hau mun murmushi yyn dana furta Oumma na Barka da gida".
Da murmushi da kuma jin dadin yanda na koma kaman bani nayi ciwon ba tace lfyl Suhaimart
ya aikin naki"?
Aiki Alhmdllh Oumma na".
Ajiye kayan hannuna nayi gyefen dakin mu ina mai cire hijab din jikina da furta Oumma bari na
karke Sukolan!!.

Na rabaki Suhaimart " jiya fah aka sallamomu daga asibiti,ae bar sukolan nan sai kinji
sauki,maxa shiga daki yanxun zan shigo nima". Tom Oumma na ga wannan!!'.
Nan na miko mata ledojin da Huday ya bani,cike da mmki Oumma ta saka hannu ta bude

ledojin da nan taga daya kaji ne cikin sa,dayan kuma kayan makulashe nd iri².

Kallona tayi wanda cike da daurewan kai Tace mun Suhaimart a'inah kika samu wa'annan
kayan?.
Shiru nayi na kasa cewa kala" don sai na tsinci kaina da kasa furta mata da Huday ya bani".
Muryan ta Naji tana cewa" A wurin aikin ne aka baku?.

Saurin daga mata kai nayi da ehhh,sannan kan ta bani wata tambayan nayi saurin shigewa
dakin nata...Itako Oumma sam Zuciyan ta bata bata ba,amma tarasa ta hanyar da zata fasalta
mawa Ranta dangane da wannan kaya dana bata".

Don tana da 100% garanti akan Tarbiyan da tabani,tasan baxan je nayo abun da zai bata mata
ba,amma kuma ranta cewa take dole takuma kula da Suhaimart, don Suhaimart tamkar amana
ce Allah ya bata". Bata da kowa sai itah da Zaid,shi kuma ga yanda yake,girman ajiki yake
kadai.
Bangaren Sir Khaleed kuwa sosai yakejin tsanar duk wata y'an matan sa na banza,dama
wanda suke masa true love duka ya watsar da lamaran su,burin sa kawai yaga ya mallaki
Suhaimart, wanda da ya rufe idon shi fuskan ta kawai yake gani tana masa gizo,tana sakar
masa da wannan kayatattciyar murmushi n nata,mai sakar masa da Kasala,dajin Zuciyan shi
cikin Annashiwa da jin dadi".

Rufe i don shi yy yana mai furta I Really love you Suhaimart ". Sai kuma kaman wanda aka
tsikara ya mike hadi da nufan wani Daki dana gani daga gyefn bedroom din nasa,bin bayan sa
nayi wanda da shiga na naga ashe Achitect Room din shi ne, Wani bord ya dauka hadi da
daukan kayan colouring yafara zanata a kan bord din yana mai jin duk wani dakika son ta
nakuma nikkuwa a cikin Zuciyan sa, a sarari kam Addu'a yake Allah yasa Suhaimart ta kaunace
shi koda kuwa kwatan son da yake mata ne, don shi sai a yanxu dayaganta ya tabbatar da itace
komance fatan shi,kwanciyar hankali,kuma tabbas ya yarda da rasa Suhaimart a rayuwan shi
Babban Illah ne wanda sam baxai iyah jurema hakan ba".
Haka dai yake ta drawing nata abunka ga Archetecture tuni yayi nisa yana zanata hadi da binta
da kalaman masoya masu kwantar da hankali kaman tana gaban sa".

Hmmm muje xuwa masoyan Maman teddy. Don nasan Tabbas zakuyu jinjina ga wannan
labari mai taba zuciyan masu karan tawa. Koya Lamarin Khaleed da Suhaimart xai kasance
Allah masani,muje dai Xuwa kar ku mance nice dai taku har kullum mai maku fatan Alkhairy da
nuna kauna gare ku: Wato Ayshatou Moh'd ( Mmn teddy).
******************************

*JIHAR GOMBE*

Nana Aysha wai tunanin me kikeyi ne haka?". Tun da yarintan ki kar kifa dorama Zuciyan ki

damuwa".
Dagowa Aysha tayi hadi da kallon Ammaie da take tsaye rashin karkashin y'an nata duk ya ishe
ta.Da kyar Aysha ta iya kakalo murmushin dole ta hanyar cewa" Ammie wlh bakomai,kawai dai
Rayuwar Yarima Abdoul ne yake damuna,wai ace Ammie mutum har ya isa musali ya isa
munxali,anki bude masa Sirrin da aka rufe tsawon shekaru,inba a sanar masa yanxu ba tom
yaushe zai sani,yaushe zai shaida ni y'ar uwar sa ce ta jini,kullum yana mun kallon bare,wlh na
gaji da wannan Buye masa matsayuina da akeyi". Ta fadi tana mai cuno baki gaba".

Murmushi Ammie tayi tana mai zama gyefen Diyar ta ta, A hankali ta fara mata magana cike da
taushin murya,Nanah Aysha ki fahimceni,sam bana son Karajin wannan mgn daga bakin
ki,kisani idan maganan nan ta fita nice za'a kira da babban kawai,wannan sirri ne datake Rufe
tsawon Shekaru 30 da dori,kuma ni na sanar dake tsakanin ki da Yarima Abdol Manan ne
badon komai ba sai don Ki samu soyayya daga gareshi,ta haka ne zamu shayar da fulani
mmki,kuma abun da take ganin baxai yiwu ba,xataga tayiwu". Amma idan kikayi gaggawan
sanar mawa Da Abdoul Manan cewa" Fulani ba mahaifiyar sa bace,tom wazaki ce mahaifiyar
tasa?

Dole ne mu cigaba da Rufe wannan sirrin Har Allah ya nuna mana lokacin da komai zai fito
sarari makiya kuma suji kunyah,dan hakin dama daka raina shike tsone maka ido. Nanah Aysha
kicigaba da hakuri,duk hantaran da Abdoul manan zai nuna maki kar ki damu,kisani bayan
wuya sai dad'i".
Nisawa Nana Aysha tayi kan daga bisani tace" Ammie shin kinji Labarin tafiyar Hamma Abdoul
kuwa??.
"Wai naji ance zai tafi Zaria ne,but bansan maiye manufar Zuwan sa can din ba".
Dariya Ammie ta sakar ma diyar ta ta,kan daga busani tace" Naji lavarin hakan Aysha,Don
maimartaba oready ya sanar mun,Sannan zuwan Abdoul Manan Zaria ki sani ba wani avu bane
zai kai sa illah dawowan Aminan nasa wato Huday,da Khaleed.
Ammie da wayyo dadi da gaske???, indai ko Haka ne A satin nan zan tafi Murmmyn Khaleed".
Nayi mata Hutu can,cox Ammie na nasan In Hamma Abdoul bai sauka gidan ta ba,to kilah
baxai wuce gidan yah Huday ba".

Dan murmushi Ammie tayi cike da jin dadin maganan Ayshan,da cewa xataje yima Yayar ta
wato Hajiya Zaituna Holiday don sam Aysha bata son shiga cikin jama'a,amma yau sanadin
Yarima Abdoul zata je har ta jima can Garin Zaria. kai masha Allah". Abun da Ammie tace
kenan,kan ta mike tana furta Aysha Abban ki na kan Hanya,bari naje na cigaba da shirin
dawowan sa!!".

Tom Ammie nima yanxu inna kammala Duba magazine din nan zan fito".

Wahhh ke din ce zaki fito,bayan kin fara duba Magazine din ki na fama"!. Hmm ae nasan
fitowan ki ba yanxu ba". Dariya Aysha tayi tana mai cigaba da Gyara Medical glass din ta,tana
karanta wasu news.

Ita kam Ammie Juyawa tayi tana mai rufo mata kofah,a ranta tana jajan ta hali irin na
Aysha,kullum ka ganta a koke duba Jaridu,idan baka ganta anan ba,zaka ganta tana watching
News...Ae wannan ko shi SENATE IBRAHIM DUTSE wato ma haifin Aysha bai wannan
Resarch din irin nata lokacin yana da Kuruciya haka". Haka Ammie tayi ta zancen Zuciya har ta isah Tanfatsetsen falon ta da yasha Ado da kayatuwa
har ya gaji".

Ma'aikatan ta ne suka fara mata barka da isowa",yayin da nan ta amshe su cike da karramawa
irin ta matan da suka san darajar dan Adam,don yanda take masu sai da na fada duniyar
tunanin Anyah Ammie Safiya da Mum Zaituna yaya da kanwa ce???. Hmm Hakan ne tunda da
bakin ta Ammie Safiyya ta fadi".
*GARIN ZARIA*
Bangare na kuwa ni Suhaimart A washe gari da sassafe na kammala shiri na na tafiya wajen
Aikatau dina dana saba,don haka bayan nayi mawa Oumma na sallama ne na yo waje hadi da
tare me napep gudun kar na makara na samu wata matsalan dan gane da aiki nah".
A haka muka shigo G.R.A zaria,wanda jefi² nake kallon wurare dabam².
Ido na ne ya sauka kan wani gida,wanda nan take naji kirjina ya yanke ya buga,saurin dafe
kirjina na nayi,ina mai karanto Ayar Allah,har na samu natsuwa,wanda duk da hakan girman
gidan har Ilah yau bamu wuce ta ba,gida ne mai mahaukacin girma da tsaruwa,wanda gaba
dayan sa yake mamaye da Sojoji da jami'an tsoron lafiya.Zufah ne ta hau karyomin ta
koinah,tabbas a jiki na inajin na taba Rayuwa a wannan gida". Amma kuma a yaushe a wani
lokaci ni ban sani ba!!!.

Dafa kaina nayi ina mai son tunowa amma na kasa,Wage dankareren gate din da akayi yasa
mai Adaidaita danake ciki dakatawa don wanda aka bude ma gate din gidan ya fito sannnan
muyi gaba".

Idona ne ya sauka akan sa,wanda a sarari na furta la shakka dama nasan kaine Ya Huday ".
kawai sai naji zafafan hawaye na bin koinah na fuskana. Ta jikin madubin me Adaidata na kare
ma Fuskata Kallo,yanda nake a kode a kuma jeme,ga wani baki da nayi,uwa duniya baxaka
taba cewa Ni Suhaimart fara ce karr ba". Share Hawayen kan Fuska ta nayi ina mai bai Uzuri A rayuwa,don tabbas wanda yasanni
abaya baxaya taba cewa nice dai Suhaimart ba'.

Tayarda da

7 / 14