Author : Maman Teddy Category : Read Hausa Novels
ne keson ganin
ki yana compound. Ohkk tom nace da itah,nan na nufi inda Ya Zaid ke tsaye yana aikin Huci
kaman zaki. tunda ga nesa na hango hakan. A hankali da isana na furta Ya zaid Barka da
Rana". batare da yabani amsa ba,ya fara Auna mun Zagi,kehhh dan ubanki Ina Kudin da nace
ki nemomun ehhh. Jiki na ne ya hau rawa don nasan tabbas a yanxu Zaid har duka na zai iyah.
Cikin Sauri na Hau cewa" Ya Zaid kayi hakuri xan samu inshaallh.
Ba wani inshaallh ne nake son ji ba,kar ki dawo gida sai kin tabbarmtar ma kin samo mun
#3000 nan. yana fadin haka ya juya a fusace ya barni nan tsaye.........
Kwallah ne ya ciko mun ido,amma sai na maida su,jin an tabo baya na. Suhamart ". Oummu
Sulaym ce mai wannan mgn. Waigowa nayi kaman ba komai na sakar mata murmushi. nan
naga ta zaro ido waje tana Furta Suhamart jini a hancin ki,dukan ki ne Zaid yayi?. Cike da mmki
Na girgixa mata kai alamar a'ah. nan tasa Hannun ta idon ta tuni ya fara fidda hawaye tana mai
Goge Ha6on dake gangaromun. Saka hannun nayi ina goge mata Hawayen dacewa Oummu
na ki kwantar da Hankalin ki Ha6o ne. Murmushi tayi mun kan tace tom Suhamart don Allah
kudaina damun kanki kinji?. anjima muje asibiti adub...a'a Sulaym bafa ciwo bane,kawai habo
ne. Na katse ta ta hanyar kwantar mata da Hankali. Itako sai ta mun Murmushi na ni yarinya
ce,don sam ban fahimci mai take nufi ba. A shekaru Oummu Sulaym xata kai 20 a duniya,don
haka taban kusan yakai shekara 3.
kama mani Hannu tayi sannan muka fara nufan Cikin gidan.
Sam bana kallon Gabana illah kici6us da naji nayi da mutum,saurin dago kaina nayi don ganin
ko waye,amma nan naga kwarjinin da kamalan su duka ya rufeni,Huday ne na buge nan na
sidda kaina kasa,wanda kaman wanda aka tsikareni nayi saurin kara dago kaina ina fito dasu
waje akan fuskan sa. Shima kuma ni yake kallo...... Amma ban gane nufin hakan ba.
Hmmm muje zuwa masoyana,labarin har yanxu ba'a fara komai va,yanxu ne xa'afara
chakwakiyar tsakanin ZUMA DA MAD'ACI.... Don tabbas nasan labarin nan zai taba zuxiya
matuka ban dariya da Tausayawa,ban face ayi kuka ba aha....
duk tausayin ki ga Suhamart ki daure bayan Wuya sai Dad'i.
Littafin Zuma da Mad'aci na kudi ne,Zaki turo #200 VIP, 300 SPC,100 NORMAL GRP. duka
MTN ta wannan WHASTAAP Numbern 08081202932./09137392680.
*Maman teddy*
*✨ZUMA DA MAD'ACI✨*
Na
*Mmn teddy*
*Page 7/8*
*ALHERI WRITERS ASSO.*
*A.W.A*
https://www.facebook.com/100186388252056/posts/100188104918551/
```Kungiya masu aiki da Nazari da kuma ilimi,Alheri sai d'an Alheri.```
_______________________________
*Dedicated to my Sweatheart Layla...*
_Wannnan labarin kirkirarrene,banyi shi don cin zarafin wani ko wata ba,illah don na
fad'akar,wa'axantar nakuma ilimantar. Kuma banyar da Ajuya mun Labari ba tare da Sani na
ba..._
*~DANGANE GA LABARIN...~*
Labari ne mai cike da tsatsan tausayi wanda nasan mutane da yawa xasu xubar da Hawaye ga
Wannan labari,don nasan tabbas bakaramun ta6a zuciya labarin zaiyi ba. Labarin Zuma da
Mad'aci labari ne da yakuma kunshi zallan Makirci kiyyayya dakuma wani irin Mahaukacin
Soyayya da nasan Zaku jajan ta ma wannan irin Soyayyah ta wannan littafi. Hmm nikaina bana
cewa komai,don Rubuta labarin nake amma komai ganin sa nake irin na halin da muke ciki ne
ayau da kullum. Nace xan sanar daku komai da labrn ZUMA DA MAD'ACI ya kunsa to nasan
xamu 6ata Awowiyi bai kare ba. Amma Hajiya ta daure kici gaba da bin Wannan littafi mai
Dunbin Basirori da wayar da kan Yaya mata a wannan Zamani..
Kar dai ku manta Maman teddyn ku ce,wannan dinnan da kuka sani, da tasaba Zankado
maku littafan ta mai sanya ku nishadi tare da fadakar daku kan Abubuwa da dama.A wannan
Karan ita takuma zuwa maku da Sabo mai sabon Salo....Wato ZUMA DA MAD'ACI, Yar uwa kar
ki sake a baki labari.
___________________________
مسب* الله رلا نمح رلا *ميخ
Cikin Sauri don Bakina banda karkarwa babu Abun da yakeyi da kyar nakuma iya furta masa yi
Hakuri Ranka ya dade". Bai bani amsaba illah tsayawa da yayi ya mun kur da ido,wanda ni
kaina ban fahimci Hakan ba saboda nima duniyan Tunanin da na Fad'a. Muryan Mumy Zaituna
ne ya katse mu,wanda sam cikin mu babu wanda yaji shigowar moton ta bare kuma isowan ta. My Huday Saukan yaushe?. Wani faduwar gaba naji ya ruskeni,A take Kwakwalwa ta ta fara
tuno mun da Abubuwa da yawa a baya. Jah da baya nayi saurin yi don Sam ban fahimtan Wani
Abu,balle har naji Maganan da Wanda naji an kira da Huday ya bada Amsa. Abu daya kawai
nakeji na mun Amo a kunnuwa na shine Muryan da Baxan ta6a mance shi a Rayuwa ta ba". Ki
tafi mun da itah Nany,Karki Bari wani Abu ya sameta,na bai maki Amana kar ki Zalince
ta,Marainiya ce a Yanxu,ki tarbiyar tarmun da ita ta farki mai kyau da zan Alfahari da ita a ranar
gobe kiyama". A'a Ranki yadade Zan kula da ita tamkar Gudan jinin dana Haifah. Ki gudu kiyi
nisa da Baby na Don Allah". Mum....." Mummm Baxan iya Rayuwa babu Suhaimart ba,mutuwa
zannnn......." Karar ne Napep da yake bina da Horn yasa nayi saurin ankarewa don sai a
sannan na dawo daga duniyar Tunanin da na Afka.
Hajiya Tafiya ne?" Ina ne xan kai ki?. Sai da na shiga daga cikin Napep din sannan nace masa
Cikin Zaria. Tom Angama" Ansan da ya bani kenan kan yaja Adaidaitan shi ya hau kan Kwalta.
Bangaren Mumy Zaituna kuwa Rungumo Huday tayi tana mai shaida masu da Anan zasu yi
Lunching don Haka babu inda xasu tafi a yanxu, sai dai Su koma,Haka suka juya don nufan
Side din mumy Zaituna,wanda Oummu Sulaym kam ta muzan ta,don babu irin gaisar da Hajiya
Zaituna da bata yi ba,amma Ko Arzikin Kallon ta bata samu ba. Don Duk miskilancin Huday
shine ya amsa mata. Shikuwa Khaleed ya dade da sanin Halin Mahaifiyan nashi,don Haka ne
sam bai damu da ganin Abun da tayi ma Oummu Sulaym ba,tunda tasaba yin mafiyin wannan.
Haka dai oummu Sulaym ta tafi sum² jiki bb kwari,don ita abun da yafi damun ta shine Yanayin
da Suhamart ta shiga lokaci guda.
Bangaren ko Hajiya Zaituna a wannan Rana sam ta rasa ina zata saka kanta don farin cikin
ganin yaran nata,sosai take farin ciki,don rabon da ta gansu sun zo nan gida Nigeria ita kanta ta
manta. suna can kasar Waje. Rayuwar su Ya tattaru ya kare a Abroad. Shiyasa yau kan ta tsinci
kanta cikin jin dadi matuka. Haka nan suma Su Huday din,don a wannan karon da son Ransu suka dawo Kasan tasu.
*Wacece Hajiya Zaituna*
Hajiya Zaituna ta kasance mata A wajen Gen. Yakub d'an larabawa. Wanda ta kasance masa
mata daya tilo a rayuwar sa,don ita ke dashi ita daya. Sai dan su Khaleed da shima ya kasance
shikenan masu gaba da Baya a duniya. Shiyasa suke nuna masa so fiye da tunanin mai
tunani,sosai suke kaunar Dan nasu. Shiyasa suka sangar tasa,tun da yaranta,sam bai taba
niman abu yakasa samu ba. sai ya sameshi duk rintsi. Haka nan Sir Khaleed ya kasance
Matashin Saurayi mai ji da isah Izzah ga kuma mahaukacin Arxiki da wasu ke masa kirari da
yaro mai tashen kudi,Don a Yanxu ma so yake ya shafe iyayen nashi,duk kuma fadin Nageria
babba da yaro babu wanda bai san Waye Arch. Khaleed d'an larabawa ba. Hajiya Zaituna ta
kasance cikakkiyar likita ce,don Haka ne take Rayuwar ta a nan Zaria,don har aikin ta Asibitocin
ta duk a Zaria Suke,yyn da Gen.Yakub yake Zaune a Abuja don can ne nadafan shi,wanda bai
tahowa Zaria sai a ranan sati. Tunda shi ba irin mutanannan ne masu tsauri kan Ra'ayin su ba.
Shi dai burun shi yaga ya Faranta ran iyalin shi,shiyasa duk abun da suke so sukeyin shi
Openly. kuma Salin su duka Hajiya Zaituna da Gen. Yakub yan Adamawa ne....
Ba wata kuma Alaka ce tsakanin Khaleed Da Huday ba,illah Abota,tabbas Aminai ne na Rai²
wanda sanadin Hakan har Abota ya hadu tsakanin Hajiya Zaituna da Arch.Huwaila,wato
Mahaifiyar Huday. wannan kenan maji Sauran bayanan A gaba.
Niko Suhaimart tun da na isa gida naci sa'a Zaid baya nan,don sai asannan na tuno da sharadin
da ya shimfida mun akan na nemo masa kudin. Nufan Daki na nayi na cire kayan jiki na,ina mai
Daura wasu atampha sannan na fito na dauki buta don nayo alwala in yi sallah.Da kammala
Alola na ne na nufi daki na don nayi sallah wanda bayan yan lokuta kalilan na Ida sannan na fito
don nufan Dakin Oumma na". Da shiga na dan karamin dakin nata wanda yake dauke da ginin
soro,nan na tadda ta Kwance kan wani yagalgallen tabarma wanda ya cinye ga tsufa da yayi.
Kan ta ko ta tada shi da wani kullun kayan ta data daure da Dankwali.Baccin ta kawai takeyi
don bama tasan da shigowa ta ba sam. Sai da na kare ma Dakin Kallo ina mai tausayama kan
mu sannan na nufi inda take cike da tako a hankali gudun wai kar ta farka daga Baccin. Zama
nayi gyefen ta,ina mai daukan Kafan ta ina dora shi jikina,sannan na dauko dayan duka na dora
jikina. A sanyaye na fara mata tausa,don nasan Oumma na bakaramun gajiya ne tayi ba. A
haka nayi ta mata Wannan tausan ta yanda nasan zata kara jin dadin baccin ta,wanda ina a
haka sam ban san sanda Bacci yy awon gaba dani ba. ****************************
*MASARAUTAR SARKI AHMADU MAI LAFIYA*
Cikin garin Gombe kenan,wani masarauta ne na gani da girma da tsarin sa gakuma Kwarjinin
sa duk sai da suka dauke Hankali na wajen tsayawa ina bin wajen masarautar nan da Kallon
Mmkin irin Gidan Sarautar. Tabbas ko ba'a fadamun ba wannnan masarauta Babban masarauta
ce,wanda ta kwashe shekaru aru² Da kuma manyan ajiyoyi gare ta. Kutsa kai na na hauyi batare da na bi takan Fadawan da suke ta zare mun ido ba. don gaba
daya hankali na yayi gaba,burina daya in ganni cikin Wannan masarauta. Haka nayi ta kutsa
kaina ina bin koina da Ido. Ina kuma mmkin Ganin yanda kowa bawa ka gani a cikin wannan
Masarauta Yana rayuwa ne cike dajin dadi da kwanciyar Hankali. Wanda da'alama Wannan
Sarki Ahmadu mai Lafiya sarki ne Adali,mai kyautata ma Talakawan sa,shiyasa tun daga wajen
Masarautan nake jiyo kirarin mutane a gareshi,kowa da salon nasa gaisuwan karamci da
girmamawan da yake bin Wannan Sarkin dashi... Ganin wata mata nayi sanye cikin wasu irin
dakakkun yadi mai irin Karfin nan wanda yafi shige da saken fulani Baki,ta wani kinkima Dauri
kaman Saraauniyan Dahhh.... tafiya take Zafff zaffff kaman zata tashi sama. Bin bayan ta nayi
da kallo yyn da najah baya na tsaya don ban san inda zan saka kafafuna ba kuma. Muryan
wasu Barori mata dake gyefe na ne naji suna cewa junan su cike da Rada,kai Jakadiyar Fulani
ce,muje mu cigaba da Aikin mu. Ae da jin Furucun su nan nayi saurin bin bayan wanda aka kira
da jakadiyan Fulani,don dama neman inda zan rakube na tattaro maku bayani akan wannnan
Masarauta na keyi.
Wani sasa naga ta nufa,wanda tun da na kutsa kaina ido na ke Rawar kyerma dan gane ga
Zinaran da akayi adon su tundaga wajen Sasan,bama akai ga shiga cikin wannnan Sasa ta
Fulani ba. Yanda naga ana Barori na Zube mawa Jakadiyan Yasani sakiin Baki ina cewa a raina
lallae duk inda wannan mata takaiga a gidannan tom da akwai bayani a tare da itah,wannan
Zube mata kaman zasuyi Sujjada, ai ko Matan Sarkin Fulani sai Haka,Amma bari na kama baki
na gudun kato6ara,don bansan ita kuma Sarauniyan Ya ake mata ba,kilah ita kwantawa kasa
suke saboda Girmamawa.
Wani irin falo naga ta shiga da yagaji da kayan mulki dana Alatu da more Rayuwa. Yayin da na
hango wasu mata Xube a kasa,wasu kuma suna Dauke da irin wani Mafirci mai bangaje,wanda
daga kasan shi akayi masa a don zinarai,kai abun sai dai muce mashaallh. kutsa kaina nayi
ixuwa inda wata mata ke a kishingide wa'annan Barori na mata firfita a hankali,yyn da ita kuma
ke aikin baxa isar ta da Mulki. Zubewa Jakadiyya tayi a gaban Fulani tana aikin barbadancin
gulman data saba. Na gaisheki Gimbiya matar Sarki mai Zamani mai karfin mulki,matan sarki ta
gavban goshi kowa dole yy bayan ki kice a gaba,sarki mai Adalci mai Tausayin Talakawan sa.
Hutawan ki lafiya uwar Daki na. Allah yakara nisan kwann..... Ya isah haka Jakadiyya". Fulani
ce tace hadi da daga mawa jakadiyya Hannu,wanda inda Sabo ta saba da yarfin mulki na Uwar
dakin nata Fulani. Risinawa ta kuma yi tana mai sidda kan ta kasa jikin ta har kyarma yakeyi irin
na munafukan matannan, na ta furta Allah ya wuci Ranki yadade". Fulani ce ta rankafa kanta
tana mai kara kishingida yyn da Barorin ke dada yo mata sijjada hadi da cigaba da aikin bautan
su babu kakkautawa. Hmmm nisawa Fulani tayi tana mai gyara alkyabban jikin ta dake wani irin
Walwali da sheki, jikin ta ko inah walwalin Zinarai yakeyi. A cikin wata irin murya da tafi kama
dana gadara ta furta Jakadiya ki maza ki sanar da kowa Na gidannan dawowan D'ana Yarima
Abdul Manan". domun nan da yan awanni kadan zai sauka a gidan Nigeria. kai masha'allah,lale
marhaban da dawowan yarima mai jiran gado". Allah dai ya sauko dashi lfy.
Kehhhh Jakadiyya mai nekejin Bakin ki na Furtawa ne? Waye yarima mai jiran Gadon,ae duk
kan Masarautan nan babu wani mai jiran Gado da ta wuce ni,ni na cancanci na mulki Wannnan
Garin ko bayan kaucewan Mai martaba". Ko kin taba Ganin D'an Kwarkwara ya gaji Sarki???.
jin yanda Fulani ke daga muryan da bata saba ba,yasa jikin Jakadiyya ya hau rawar kyarma
cikin Sauri ta furta Allah ya wuci Zucuyar ki ranki ya dade. tuba nake". Tana fadin Haka ta juya
sim² ta fice daga Sasan don ta isar da sakon Uwar Dakin nata". A ranta ko tana tunanin
maganganun Fulani,wai itace kadai xata gaji masarautar Mai lafiya? tom ko ta yaya hakan xai
faru ohoo!!! nan ta cigaba da sakawa tana warwarewa a zuciyan ta, don Sarki bai da d'a namiji
ko guda daya sai Yarima Abdul Manan da ya fito ta bangaren Kwarkwara ae a tunani na Shima
da ne". Tunda shikenan masa a Rayuwa namiji sai yaranki mata Uku. to yara mata ae baxasuyi
mulki ba,kuma yanxu duka kowa tana dakin mijin ta. Uhmmm wannnan Masarauta da rikici
gsky. Haka Jakadiyya tayi ta zancen zuci,kan ta nufi Sasan Barorin gidan don ta shaida masu
dawowan Yarima Abdulll.... Fada ko tuni Aka nufi airport don taryan Prince Abdul Manan.
Bayan yan Awanni da Isan fadawa da securities don taryan shi jirgin Prince Abdul Manan ya
sauka. ai nan na kara firfito da idanuwana waje don ganin Prince Abdul Manan. Wani
kyakykyawan Matashi ne wanda a shekaru baxai Haura 35 ba ya fara sakkowa daga wannan
jirgin,yyn da tuni fadawa da sauran masu tsaron lafiyan sa suka nufesa. Mtssww dan karamin
tsaki yayi hadi da Gyara bakar glass din Fuskan sa da yy,a ranshi kam yana mai cewa shikenan
yadawo gida xa'a fara damunshi da hayaniyan wannan abun. ya fadi yana bin Algaitan hannun
wani ba fade da kallo. Niko kara kare masa kallo nayi,don sai da yake matsowa kusa damu na
kara kallon sa da kyau. Fari ne wanda da ka ganshi kaga fulanin Gombe. shi kuma ba dogo ba
can,sannan baxaka kira shi da mai jiki ba,kuma ba suriri ba. dai dai namijin da ake kira da
ingarma. wasu fadawa ne sukayi saurin Rufa masa Alkyabba don sai a sannan naga ashe
kananun kaya ne jikin shi. Daure fuska yy tamau kaman wanda bai taba dariya ba,ya na
shigewa moton da aka bude masa. a ransa ko yana mai jin Haushin shikenan yanxu xai fara
saka kayan nauyin nan da yafi komai tsanar su a duniya.
Zaune take tana aikin bin fuskan ta da Kwalliyan da ta saba,gyefe kuwa masu hidimta mata ne
kowa tsaye cirko² don sunfi awa daya a haka. Itane goga wannan itace goga wancan. Muryan
Ammie n ta taji daga bayan ta tana furta mata Nana Aysha wannan kwalliya haka sam bakya
gajiya kaman kin san da dawowan Yarima Abdul Manan?. Saurin juyowa Nana Aysha tayi tana
furta Ammie da gaske yau Hamma Abdul zai dawo?". Murmushi Ammie tayi tana mai juya baya
hadi da furta mata dayake nasaba fada maki karya? yanxu haka ma yana fadan Mai martaba.
Wani ihu Aysha tasaka. wanda nan Ammie ta fita tana murmushi hadi da mmkin irin kaunar da
Aysha ke mawa Dan yar uwan ta. Itako Aysha da fitan Ammie ta daga Wayan ta tana mai kirar
Khaleed wanda kira daya biyu Khaleed dake Zaune kusa da Aminin nashi Huday ya daga
Wayan yana furta Ahhh,wannan murna Haka ae ko baki fada ba nasan Abdul Manan ya sauka".
Dariya tayi cike da kuma jin kunya ta datse wayan tana furta masa Hmm bakomai shine babu
sanarwa ko ?. Kan ya bata amsan ne ta datse wayan tana mai kara ca6a ma Fuskan ta
Ado,hadi da Addu'an Allah yasa Ammie ta bar ta a yau taje