Author : Maman Teddy Category : Read Hausa Novels
Hamma Abdoul.
Haka ta shiga moton nata wanda sai da tafara gaba sannan ya biyo bayan ta".
Bangare na da Oumma na kuwa da fitan Aysha ne Oumma tafara tambayana mai yafaru.wanda
nan na fada mata komai da ya wakana a gidan,da yanda Sir Khaleed yace yana sona,don duk
shine musabbabin fitinan.
Wani dogon tsaki Oumma taja,kan tace" Tom mai zata iyah mana eye,ta je tayi iko da d'an ta ne
bakye ba,ai ba ita ta haifan mun ke ba,Suhaimart ki sani ke amana ce a gareni,kuma Wlh baxan
bari a cutar mun dake ba,kuma sannan bance ki Wulakan ta Khaleed ba,amma kisani ko
mahaifiyar sa bata fito da wannan Abu ba,ke da Khaleed da Akwai banbanci,ya fiki kaman
sama da kasa. Amma bance ki Wulakanta shi ba,don mai kaunar ka ka kanauce shi ko yaya
yake,Amma kififita Addu'a fiye da komai a yanxu".
Tom Oumma na nafadi cike da Karaya.Maza tashi kije kiyi Alwala ki dawo kici Abincin ki,da tom
na bita sannan na mike hadi da ficewa daga Dakin namu.
Tunda su Aysha da Yarima Abdoul Manan suka isah gidan Hjy Zaituna bata kuma komawa
barayin Khaleed ba,don side din Hjy Zaituna ta nufah shi kuma Abdoul Manan ya wuce side din
Aminin nashi,Haka ta shiga izuwa babban falon ta,ma'aikata sai aikin su suke,da ganin ta kowa
ya hau gausheta,nan ta hau Amsa su cike da mutuntawa,da isan ta taga wayam ba Hjy Zaituna
anan, zuciyar ta ne ta Raya mata,tana can barayin Khaleed don tasan yau baxasuyi baccin
Dadi ba.
Dan karamun tsaki tajah,kan daga bisani ta tattara kayan ta ta nufi Dakin ta danata ne wanda
duk in tazo gidan take sauka a ciki,tana Riyawa ae Dad ya kusa dawowa wlh shi bazai ta
kuramu ba".
Ialai kuwa maganar Aysha dutse don Hjy Zaituna takoma kamar zararriya,don tunda Iftyhal taji
magnar cike da dacin rai ta bar side din nashi hadi da barin gidan gabaki daya,babu kirar da Hjy
Zaituna batayi mata ba,amma tayi mata banza don ko waiwayo ta batayi ba". Tuni yan aikin
kowa ta ware don kar fushin wani yashafi wani". Ai ko nan Hjy Zaituna ta fara cewa" Khaleed baka hayyacin ka ne mai zakayi da Wannan
yarinyan talakan ka...cikin sauri ya katse ta da Mom ita ni dai nakeso...
Tsayawa tayi sororo na tsawon Mintina don sam tarasa ta ina zata fara controlling din yaron
nata,gashi ita tunda take dashi bata ta6a tsawata masa ba,balle kuma wai har tayi masa
fada,rasa abunyi yasa ta matsawa gare shi tana furta Okay son,ka kwantar da Hankalin ka
kaji"?
Kallon ta yayi sannan yace Kin amince mun da Suhaimart a matsayin mata na?.
Da kyar ta iyah hadiye wani abu kan daga bisani ta daga masa kai,alamar Ehhh".
Rungume Mom din nasa yy yana kissing din kumatun tana dariyan dole,don a ranta tasha
Alkawarin 6atar da Suhaimart da Ahalin ta.
Shiko Huday ganin komai yake a tafin Hannun sa,duk wani bariki na Hjy Zaituna kallon ta
yake,kuma shi ya lashi takobin ganin babu wani abu da zai samu Suhaimart, yana ganin ta
tamkar jinin sa ce". Murmushi kawai yake bin su dashi irin na bakaken Miskilan nan....
Aha Hjy Zaituna ta mike daga zaunen tana mai furta Bari na hada maku Lunching don yau babu
inda zani ina tare da yara na". Dariya suka saka suna fadin Mom da ko minji dadi,don munyi
missing din girkin ki, Kallon su takuma ta na fadin Aiko yau Mom zata yi maku wanda sai kunyi
santi fah,don nasan fevorate din kowa,tafadi tana mai ficewa daga falon,sukuma suna dariya".
Shi kam Khaleed dora kansa yayi a saman kujera ya rasa abunyi,anyah yau zai iyah Hakuri
baiga Suhaimart ba,Ina sam,tuno da Marin da Iftyhal tayi mata,da kuma irin cin mutuncin da
Mom nashi tayi mata Again yasa shi rintse ido, kanshi na sara masa".
Huday ne ya kalle shi hadi da cewa" Plz Khaleed ka kwantar da Hankalin ka,in shaalllh
Suhaimart Takace,kuma wannan Abun basan bazata juya maka baya ba".
Kallon Huday yy kan daga bisani yace" Huday Suhaimart bata bani amsan tayin Soyayya r
danayi mata ba,indai na rasa Suhaimart tom tamkar na rasa Rayuwa ta ne gaba ki daya. ni
bansan ya zanyi ta soni ba,gashi yanxu Mom ta fadata mun komai ya zanyi"?.
Dariya Abdoul Manan ya sheke dashi yanayi yana karawa,wanda da kyar ya tsagaita sannan
yace" Khaleed anyah ba hakkin yan matan daka saba yaudara bane zai kama ka,don yau na
hadu da Zeebu itafa har yanxu tana kan bakanta". sai ya kuma kwashe dariya".
Kallon sa Khaleed yayi cike da takaici da ya Auri zeebu ai gomma ya karke rayuwar sa babu
Aure,cike dajin Haushin dariyan da Khaleed ke masa yace" Stop Abdoul,bana so".
Saurin sada kai kasa Abdoul Manan yayi yana fadin tuba nake ranka shi dade,amma
kyakykywan Albushir Suhaimart fah ita ta amince da Soyayya r ka tuni,don ita sam bata da
zabi,kuma babu tangarda Mr. man, in wani Abu ya biyo Baya tom daga kau ne".
Cikin sauri Khaleed yace Plz Abdoul Stop Playing,da gske ta amince mun. Murmushi Abdoul
Manan yayi sannan yace" Tun isowan ta nan da Amin cewa ta zo,sannan kuma kaje ka tambayi
Aysha ita nasan bazaka aza wasa zata fada maka kaman ni ba,tunda ita da bakin ta sunyi mgn
da Suhaimart, kasan k'anwar tamu da iya shishshigi,don da tana nan bazaka wani sha wahala
ba,ita da kanta zata dasa maka fulawan ka.
Bai tsaya bin Ta Abdoul Manan ba yayi waje hadi da nufan Side din Mom Zaituna. Yayin da
Huday ya bishi da kallon tausayi tabbas yana masifar Kaunar Yarinyan".
Niko Suhaimart da futana ina a tsugunne ina Alwala sai ji nayi numfashi na na daukewa,nan
take Jini yafara zubo mun ta hanci.
da Sauri na saka Ruwa ina wankewa,hadi da saurin nufan Daki na,can kasan Katifa ta na daga
na dakko wasu kwayan mgnin ta tafara afawa. kusan mintuna biyu sai jinin ya dauke,komawa
nayi na bi lfyn Gado,hawaye nabin kuncina babu kakkautawa". A haka bacci yayi awon gaba
dani".
Shiko Sir Khaleed da yaji duk yanda sukayi da Suhaimart a bakin Aysha bai san lokacin da yace
Aysha ki fadamun ko wata kasa kkso na raiki ki a watannan,wannan Albushir da kk mun bana
da kamanki.
Dariya tayi sannan tace" Ni Yah Khaleed Saudiyya zanje inaso nayi Umrah,don a tunanin ta
kota tasamu tayi Addu'a wanda takesi ya sota itama".
Angama Aysha a satin ki shirya". Kallon sa tayi gami da zaro ido tana cewa kaman bikin Yah
Huday nan da Sati biyu ne masu zuwa,ae sai an gama sannan sai na tafi".
Sosa kyeya yayi sannan yace" Na tuba Aysha ngd Allah yy maki Albarka".
Amin yaya na".
Tace suna mai sakkowa kasan falo don nufar dirning da Mom keta kwala kirar su,akan komai ya
kammala su ake jira".
Kai wannan Rana dukkan su,dangane da Khaleed, Huday, Abdoul Manan, Aysha duka sun
tsinci kansu cikin matsanan cin farin ciki". Don haka suke cin Abincin su suna zuba santi hadi da
fira suna dararraku,ita kam Hjy Zaituna mmki ne ya cika ta,wai dukansy suna goyan bayan
Khaleed kenan? Haka dai tayi ta Dauriyya itama Ana dan taba firan da itah".
Niko Suhaimart ko da gari ya waye,wanda Ranar ta fado ran Alkhamis kenan,kuma a wannan
Rana A gidan Hajy Zaituna yafi mata kowacce rana,don bak'aramun wahalar Aiki muke sha
ba,saboda a daren Juma'a mai gidan nata wato Gen. Yak'ub yake dawo wa". Don haka tun safe
sulaim ta shigo mun akan na shirya na tafi,amma Oumma na sam tak'iya,Acewan ta in Yau na
koma kuma ai kilah sai duka ko kuma kaini Station,ita sam bata da Arzikin jayayya dasu,don
sun fi karfin mu,ayau koda tana dashi bata ga dalilin tashin hankli ba,don haka ne tace mani
nayi zama na,zuwa gobe na naimi wani wajen aikin.
Haka Oum Sulaym ta tafi jiki babu kwari,wanda koda ta je gidan Hajy Zaituna,bayan ta
kammala koman ta ne,tana cikin saka ma zuciyan ta inda zasu tafi itada Suhaimart niman aiki
kawai saiga Nana Aysha ta zo side din Sir Khaleed din". Cike da zakuwa da son ganin
Suhaimart tafara tambayan Oum inda Suhaimah n take,Amma cike da inda² Oumu Sulym ne
tace" Yau bata samu zuwa ba". Kan Nana Aysha ta bata amsa ne sukajiyo muryan shi don duk
basusan da Zuwan sa ba yana mai cewa" Sulym menaji kina cewa? ina Suhaimaet?.
Shiru Sulym tayi kan daga bisani tace" Yau bata samu zuwa bane Ranka yadade".
Yana a tsayan gami da kafe ta da ido,don san fahimtan wani abu,kunsan Abunka ga Arctist tuni
yayi Observing din Abubuwa da yawa dan gane da maganan Oummu Sulaym don haka sai ya
saki wani murmushi mai ciwo gami da mgn can kasan makoshin sa yana furta Maiye Dalilin
Rashin Zuwan nata?".
Sir Khaleed Wlh ban sani ba,ina tunanin Wani abun ne".
Kallon ta yy hadi da bin Aysha dake tsaye nan suka hada ido,a ransu duka suna maimata
kalmar kila wani abun ne!" wani abun mene??. Tambayar da duka suke mawa kansu kenan".
Ohk Zaki iyah tfy". Yace mata a gajirce yana mai nufan Dirning shida Aysha,don Abdoul Manan
Bai kwanan gidan ba,a gidan Huday ya kwana".
Zama Aysha tayi,bayan ta jah masa kujera,nan wasu ma'aikata wato Cook suka taho don su
fara Aikin Serving nasu,amma sai ta daga masu hannu alamar no need,don haka nan suka juya
hadi da komawa bakin aikin su,wasu kuma suka nufi side din Mhiss Caterine don sanar mata da
kammalawan su".
Sulaym kuwa tuni tayi nisa da barin Side din Sir Khaleed ta nufi nasu barayin".
Itako Nana Aysha bayan ta zuba masa break din sane,nan ta kalle sa duk da tasan abune mai
wuya ya iyah yin break din nasa a halin yanxu". Haka amma ta daure Wurun cewa" Yah
Khaleed Bismillah". No Aysha kiyi break din naki kawai,yanxun ni zan wuce Company".
Da jin haka yasa ta a sanyaye mikewa tana mai cewa" Plz yaya ka natsu wlh Suhaimart fah
zata dawo gareka,kuma gobe ma Daddy zai dawo duk mu huta".
Wani kayataccen murmushi ya sakar mata kan daga bisani yace" Aysha nasani,nasan
Suhaimart ta wace,ni kuma kadai,vabu mai kwace mun itah,but ki sani,baxan iya cin Wannan
Abuncin ba ne,saboda Harshen ne yasa ba dajin dandanon ta,a halin yanxu girkin ta kawai
nake bege bana bukatar na kowa". ki kwantar da Hankalin ki my littale,zan dawo cikin Koshin
lfy". yana fadin haka ya juya hadi da ficewa daga dakin".
Itako Aysha Zama tayi dabas a kan kujera ta kasa motsawa,tayaya zata fara ganin ta faran ta
ran Yayan nata ne,amma bata sani ba".
Zaune na hango ta,sanye cikin wasu dakakkun Bowel lace masu masifar kyau,wanda suke
dauke da Launin Cofee brown,Daurin Ture kaga tsiya ne ta tokaro shi,yayin da fuskan ta ke
dauke da Kewayayyan farin glss kuma dan siri wato medical. Dattajiwace wanda ashekaru
bazata Haura 50 ba aduniya. duk da hutu ya boye wannan shekarun nata,don bazaka ce ba sai
an fada maka, mata ce wanda da kaganta zaka fahimci irin matannan ne masu harkan
gske,fatan jikin ta kuwa luff² yana sheki da kashe ido.komai nata karr²..... Da ka ganta kaga
farar Bafullatana,fara kuma mai Farar Aniyya,Bakowa bace wannan mata Illah Hajiya
Huwaila,Amarya kuma Uwar gida ta wajen Ahj. Muhammad Harun. Wato mahaifiya a wajen
Arch. Huday da Iftyhal".
"Ohk mashaallah". Tom dear ina jiran isowan ki fah,ta gumi zaman jiran isowa,sai kuma tasaka
dariya". tana mai datse wayan nata hadi da mika shi ga Wata Assistant nata".
Da kuka ta shigo falon hadi da nufan Upstairs da dan gudu".
Bin bayan ta Momy tayi cike da damuwan ganin diyar tata cikin wannan halin tayi saurin kirar
Sunan ta da Baby Ifty.." Ifty na". Nan Hjy. Huwaila ta fadi gami da mikewwa don nufan Upstairs
don ta lura da daru Autan nata ta shigo.
Koda ko taje tun a bakin Bedroom din Iftyhal ta tadda a gar make,wanda bugun duniya taki
budewa,haka tayi ta Bata baki amma nan shiru,babu abun da take jiyota tana furtawa sai
kalmar Sunan Khaleed".
Shiru Mumy tayi gami da juyawa tana nufan kasa,wanda da saukan ta dai² Maryam da suka
gama waya tana shigowa,da sauri tana nufo Momy tana Rungumeta gami da cewa" Oyoyo
momy na, I really miss u".
Murmushi momyn Huday tayi kan daga bisani ta sha fuskan Maryam tana furta Nima haka
Daugther na ya Mom din ki,tana lfy?".
Lfyl,ta bata amsa a takaice. Momy ina Iftyhal?.
Nisawa Momy tayi sannan tace" Yau ifty yan darun na kusane,amma tana sama kije ki lallashi
Aminiyar taki ko kila ta sauko inta ganki".
Tom Momy,ta fadi hadi da nufan Upstairs...
Niko Wuraren Karfe 5pm ne Oummu Sulym tazo mun,akan itama tunda na janye aiki gidan Hjy
Zaituna tom itama ta janye,amma a yau taji labarin Wata Company na daukan ma'aikata masu
goge² da shara,don haka su shirya da sassafe su tafi can".
Sosai Oumma na tayi na'am da maganan Oummu Sulym yyn da nan ta kalkeni gami da cewa"
Suhaimart kin gani ko? ae duk bakin da Allah yatsaga baya taba hana sa Abincin da zaya ci". ki
natsu inshaallah goben zakuje can". Da tom na bi Oumma na,kan daga bisani mu cigaba da
taba hirar mu da Sulaym mafi yawa dai dariya nake sha,don duk mgn ce akan inna Atine.
wanda daga karshe mukayi sallama akan sai goben.
Dako Sulym ta isa gida,sai da aka ta6a daru da inna Atine acewanta dole sai sulym ta debo
masu Ruwa,ita kuma tace sam bazatayi ba,ga inna Wuri nan tayi,sosai Sulym tayi ta amayar da
abun da ke cikin ta ganin babu Inna Laure da Baba. itako Mama Atine daki tashige don yau ta
lura Sulym din dai ² da ita take a gidan".
Da safe ko kaman yanda mukayi da Sulaym karfe 80.00am muka bar gida yyn da Oumma na ta
bimu da Addu'a sannan muka fito".
Me Napep muka tara hadi da sanar masa da companyn da zamu nufah a yanxu wanda yake
can wajen gari,wuraren Samaru kafin ka kai Abiation.
Bangaren Ko Iftyhal dajin muryan Aminiyan nata ne ta bude kofahn da sauri hadi da koma ta
fada kan makeken gadon ta tana mai jawo teddy jikin ta tana wani irin kuka mai dacin gske".
Da sauri Maryam ta saki Wasu doguwar rigar Gown da ta riko,ala dole taxo nuna mata shi duka
zasu saka aranar Get togethern da zasuyi shi yasu yasu nan da Kwana Uku,wato su kadai
kaman Ita Maryam,Aysha,don dama Aysha kawace a wurin Maryam tun bayau ba,sai
Iftyhal,Abdoul manan,Huday,Khaleed sune kadai zasuyi wannan Get togethern wanda duk cikin
shagalin bikin da zasu fara Gabatarwa ne.
Hmmm niko Maman teddy nace anyah na za'ayi bikin nan kuwa,naga wuta tafara ballewa ne ta
ko inah. Inajiyo Addu'ar ku gareni da kuma gdyn ku ,nima ina gdy kwaran gske,Allah yabar mun
ku yabar kauna".
Cike da matsananncun damuwa Maryam ta nufeta hadi da tambayan ra lfy? meya sameta".
Da kyar Iftyhal ta samu ta dai² ta na tsuwarta tafara koramawa Maryam zancen komai da yafaru
dangane ita da Suhaimart.
Wani dogon tsaki Maryam tajah,hadi da jawo Asha riyya tana Auna ma Suhaimart dacewa" Yar
matiyata kawai,wlh ki bari sai mun batar da wannan Yarinya". Amma ki bari ba yanxu ba,for now
ki kwantar da hankalin ki,ki nuna kaman komai ya wuce maki,idan kikayi haka shine nan koda
anyu komai vaza'a zargemu ba".
Kisani nan da Kwana 13 ne biki na da Huday, amma kifara kirga rayuwr wannan yarinya da
Duk Dangin ta yazo karshe. nayi maki Alkawarin wlh sai munyi bikinan cikin Kwanciyar
hankali,kuma kafin nan kinsan Khaleed ya zam naki har Abada".
Dariya suka sheke dashi,wanda Huday da yake bakin kofah don Momy ce ke sanar masa da
zuwan Maryam shiyasa ya nufo bedroom din Iftyhal din,kansa ne ya sara masa rasss....
Dajin mugun nufin su akan marainiyan Allah,wani tausayin Suhaimart ne yaji ya tsirga masa".
da kyar ransa yagama baci sosai ya juta hadi da nufan varayin sa. a Zuciyan sa yana mai
wasiwasin anyah ya samar ma y'ay'an sa Uwa ta gari kuwa??".
Hmm muje Zuwa fans..í ½í²ƒí ¼í¿».
Niiko da Oummu Sulym bamu isah wannan Company ba sai Wuraren 9.00am.
Mun dan sha wahala matuka kan Abar mu muka shifa daga cikin companyn,don mun sha
bincike har mun gode Allah, don da kyar duk da hakan suka barmu,banda bin mu da kallon
wulakanci babu abun da wa'annan securities sukeyi, Suna kare ma surfaffun Atamfan jikin mu
kallo,wanda ya dade da fita kamannun sa". Bakar hijab nasaka amma aaboda koda gar jajjah
takeyi daga sama".
Da kyar dai suka bar mu muka shifa don ni nayi ta masu magiya akan su taimakemu. A haka
suka hadamu da Shugaban Masu Cleaning din da share² n da kyar.
Itama kam fa ba wani arziki ne da itaba,amma abun ka ga mutanen Nigeria da sungan su wani
matsayi sai su nima taka mutum,nan itama ta bimu da kallon Wulakanci don taji mai ya kawo
mu". Office nata ta nufah damu,hadi da bamu ma sauki. Tana mai mana wasu yan tambayoyi,da
tambayar mu inda muka da kata da Karatu,anan duka muka bata amsa da Secondary muka
tsaya,don ni a SS 1 na dakata,har gomma Sulaym takai SS3.
Muna a Zauna ne wani mutum sanye da shigar sa ta court ya shigo,wanda nan naga tayi saurin
mikewa hadi da dan Rawar jiki tana furta Weldone Sir".
Ammm Mhiss Zayyad Muna son ganin ki yanxu".
Okay Sir ".
Abin da tace kenan hadi da saurin bin bayan Wannan Mutumi da babu shakka ko ba'ace ba
wannan bayahude ne. nine mai fadan haka a Raina".
Zama mukayi mukayi shiru,babu mai magana,don Oummu Sulaym hankalin ta