Jinin Sarauta Book 2 Complete By Oum Aphnan

Author :  Hassana Bamalli Oum Aphanan Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 10

21K to 24K   out of 27.4K words

da butan a hannu.
Abban diyanah kenan shidai ba dai sababiba,ammafa in akan gaskiyarsa ne.


**
Sai bayan da ya komo daga masallaci ne ya na shigowa tundaga bakin get yike qwalla mata
kira


"Er albarka maza shirya ki tafi,yanzu shugaban makarantan yake fahimtar dani a masallaci
alfanun zuwan naki,gashi yace En uwan nakima sun wuce...ki Sauri ,gidan shi d'an sarkin ne
dai nikeji"


Kwa6a kwa6a tayi kamar zatayi kuka "baba wallahi bansan zuwa irin wannan wajen....kuma ma
ni bansan gidansa ba"

Raunana murya yayi "I hakuri kinji..shirya ki hau Babur dina in kaiki ,ai mu mazane mun sani"


**
A bakin get din gidan ya ajeta saida yaga shigarta sannan ya juya ,sanye take cikin doguwar
rigar Atamfa ,na ankon saukansu da sai daga baya aka kawo mata da farin hijabi,sabo"


Da sallama ta shiga gidan ,tana tafiya sand'a sand'a,ko ina shiru kamar ba mutane ,mamakine
ya kamata,to ina d'aliban koda yike ai ba hayaniya zasuyi ba suma.

Wani gaban varendar ta 6ullo ,Mai tsananin kyau anan taja tunga ta tsaya tana tunanin
komawa

Gimbiya zulaikha tun shigowar ta take kallonta ta kitchen, ganin tana waige waige ,sannan ta
fara sand'a yasa tayi saurin kiran "ke ! Zonan" ta fad'a tana kware glass din windown.


Dam ,gabanta ya fad'i ,ta tsaya cak tana muzurai ta kasa motsawa .

Ran zulaikha ne ya 6aci a hasale ta zagayo da Sauri ta fito haraban,tana zuwa gabanta batayi
wata wataba ,ta sharareta da mari

"Ke 6arauniya ce?"
A take ta tsaya cak dafe da kunci tana kallonta,a take idonta ya qeqaeshe ta nemi d'igon
hawaye ta rasa, sai zogi da idon ke mata kamar wacce aka watsa mata borkono.


"Ke kuchaka ,ba dake Nike magana ba? Waye ke? Er gidan uban waye ke,da zaki shugomun
gida kimun sata!"

A sanyaye tace "Me na Satan maki"
"Ubanki kika Satan min,kawai bansankiba zaki shigomun gidane,inba sata kika zo yiba,to wajen
wa kika zo,nine dai kad'ai matar yarima to wajen wa zakizo"


"Wajen me gidan naki Nazo hajiya"
Salati ta rafka tana tafa hannu "Nashiga aljannah ni zulaikha....qarshe duniya En mata sun fara
biyo maza har gida...sa gwuiwarki a qasa ,zube daon ubanki,yau saina koya maki darasi
zakisan baa tunkarar mijina a kwana lpy"
..

Ta soma gargagi tana kwalla ma balki kira,wai a kulle mata get,takira mata mai gadi.


Gofana tayi akan gwuiwoyinta tana sauraran ikon Allah


Hayaniyarta ne ya ishesa cikin izzah da fusjar da ke nuna kinfa dameni da hayaniya ya
tunkarosu,shi Sam vaima lura da diyanah ba


"Zulaikha me kika sha yau?..duk kin hana mutane barci?"


Nuno masa diyanah dake kan gwuiwoyinta tayi
"Yarima dole a takawa mai gadi birki ko a kaisa garden ya koma kulada furanni tunda qofa ya
gagaresa ,taya zai ringa barin wainnan ,nasty in responsible nonnative individual din suna
shigo mana gida,to da tayi mana sata bacin na kamata


Da Sauri ya waigo ya kalli Diyanah, yina yamutsa gira kamar ya ta6a ganin fuskar


" ke lafiya, garin yaya hakan ta faru?"
Sai a sannan ta samu hawaye suka soma gangara mata a fuska

Cikin shesheka ta soma magana amma kuka yaci qarfin ta ta kasa


"Wal..wallahi niba 6arauniya ba..ba..bace, daga islamiyya aka turomu wajenka...shine fa.."
Hawaye ne suka cigaba da ambaliya,amma ta kasa cigaba da maganar.


Jinjina kai yayi ,tabbas sai yanzu ya wayeta,watannan hafizar?


"Ya Isah...Tashi ki biyoni!"




*Posting sai Asabar inshaallah*
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: *Jinin sarauta*

66 - 70

"Yarimana ,kasantane? Waye ita? Bai kamata kana yayo kowasu tarkace kana kaisu parlourn
ka ba ,that is your privacy, so plz saurareta nasan taimakone ,basu suje ,Allah shi kyauta..."


Wani mugun kallo ya jefeta dashi masu ma'anoni kala kala
Murya can kasan maqoshi "I need a sakina ,so plzz...kawai sai ya taune sauran maganarsa ya
wuce hanyar part dinsa

Cikeda ixzah yike mulmula jiki tamkar mai jin nauyin jikinsa, naman wuya ya wani sama waje
kaman toron sa.

Itadai diyanah binsa tayi da ido ta kasa motsi.

Itakuwa gimbiya zulaikha wani mugun kallo ta watsa mata,kafin taja arnen tsaki ta wuce tana
qwafa,hakan ya sashi waigowa still tana duqe kamar miskiniya


Juyo da jikinsa yayi gaba daya, ya saki timbinsa tareda daura hannuwansa a qugu ,yina
kallonta.


" uhum" ya fada yina dage mata gira,sum sum ta mike tabi bayansa.

°°°
Wani kasaitaccen falo suka shiga, duk dakiyar diyanah saida ta Nuna qauyencinta a sarari, ta
kasa zama a kujera saidai ta xauna a qasan shifid'ed'en darduma kirar Saudi mai taushi gaske
kamar katifa,sannan ta sunkuyar dakai tana gaishesa tareda gabatar masa da ko ita
wacece,dakuma dalilin zuwanta

Zama yayi mai kama da kwantawa ,a jikin wani qasaitaccen royal kushin,yina sauraronta ta
gefen kunnensa amma idon sa na kan screen din wayarsa,ya hade cunkusashen gashin
giransa tamkar baya appreciating maganarta


Amma a badini yaba komai nata yike,ladabinta da komanta,yes yasan zulaikha tafita kyau
kamar sama da qasa,amma kuma tanada sassanyan kyau kuma akwaita da kyawun hali, ai
wannan shine abunda ake nema wajen mace ta gari ba fitsara da budewan idoba...sannan
kuma abinda yafi so awajen mutane a girmamasa ,itakuma ba girmaba har muryarta kyarma
yikeyi saboda kwarjininsa a idonta.


Tunda tagama wassafa masa dalilin zuwanta ta duqar dakai ,shiru taji yayi magana amma
shiru,a hankali ta dago idonsu ya sarqe da na juna


Da sauri ta sauke kanta qasa "amm,ehh toh,wai na ce ina ne En uwan nawa suke, sai in je
wajansu?"

Dariya ta basa, yadan murmusa kadan


"A cikin list din ajendar na nayau,ba list din kar6an makarantanku,so mun tura wani ya
wakilcemu ,suna can fada"

Yina ta wani sa harafin jam'i tamkar ba shine shi ,shi d'aya ba.

Yunkurawa tayi a hankali tamike tsaye "tom shikenan Nagode ,bara inje" ta fada tana soma
tafiya.

Shiru yayi bai tamkataba yina shafa qasumba,"wow yariyar nan akwai kayafa,koda tana cikin
hijabi" bai auneba ya ga takai Kofa,gyaran murya yayi


"Amm na ce ba?"

Dakatawa tayi ta waigo tana kallonsa


"Inkinje gida kineman mu izini wajen baba"
Qwalalo ido tayi waje.
"Ban...fahimce kaba yalla6ai"

"Eh ko wani ya rigani ne?"

"Mene ranka ya Dade?"


"Diyanah ni ba yaro bane,banso in shiga sahun manema,while akwai me nema,so kicema
babanki inason zuwa in gansa da kaina"


Kantane ya dauki nauyi gingiringim ,Sam ta kasa gane manufarsa ,amma kurum saita jinjina
kai.

Kije compound ,zan waya, zaa maidake gida,kuma daga yau na haramta maki fita, ke daya zan
turo maki da driver"


"Ranka shi Dade...nifa er ba kowa bane"
"Bani magana biyu,kuma ki sani daga ynx duk motsinki yina cikin kulawata,so a kiyaye"


Bata kuma magana ba ,ta fita da sauri.

Jinjina kai zulaikha tayi bayan ta gama la6e tana jinsu


Da sauri ta koma dakinta ,ta kame Baki saboda wani kuka mai sauti da ya zo mata


Tana zuwa ta tsallake En aikinta ta wuce bedroom, ta saki wani marayan kuka.


Ni kam me zanyiwa yarimane yayi tasiri akansa?
Duk izzar yarima shine zai qarewa watannan yarinyar er talakwa ,mummuna?
Duk dagawarsa ,ban ta6a jin yayiwa mace kalma ya wuce biyuba ,har su gama zance,yau shine
yace zaibi baban yarinya gidansu don Neman aure, a maimakon saidai yasa a kirasa ,kuma ya
ringa turawa ana dakko yarinyar zance parlournsa?

Wannan yarinyar ba hakanan ta shigo ba,akwai sa'an da ta kar6a,ji fa zamana dashi kusan
shekaru bakwai zan iya cewa sau uku ya ta6a takowa dakina saidai ni in bishi ,amma ya hakan
,cikin qanqanin lokaci ya nuna zalamarsa gamida kishinsa akan watanan mummunan halittar?


Telephone din dakinta ne ya dauki ruri,ranta a 6ace taje ta d'aga
"Hello...AF salamu Alaikum" tai maza ta sauya furucin hello dinta don tasan bayason ta ce masa
hello


"Uwargidata ,kina ina kika bar mijinki cikin kewa bayan kinsan na tashi" ya fad'a cikin nishadi

Jan hanci tayi ,saboda toshewa da yayi sakamakon kukan da tayi.


Kaji makiri,wai kewata ? Kewar waccn baqar dagan dai


"Ayyah na bari Ku gama zancen ne,ko har amaryar tawa ta tafine"

Dariya ya saki da qarfi har yina doka qafa,shikansa ya rasa me yasashi nishadi ,saidai ya
alaqantashi da haduwa da muminan mace mai tsananin son addini


"Ya akayi kika gane amaryankine zulaikha? Toh bamu tabbatar ba ,adai samu cikin addu'a Allah
yasa baba ya amince"


Siririn tsaki taja a hankali
"Hmm yarima kenan,ai labarin zuciya a tambaya fuska,kuma ita yarinyar bata shaida maka ko
tanada manemiba? Kufa sarakunan musuluncine masu kamanta adalci,kar a tauyesu"


"Madalla ga samun mace mai hikima da hangen nesa, tunanin hakan da nayi shi yasa na nemi
ganin babanta ,don na lura wannan amaryar taki mai kunyace,anyama zata iya kula da miji?
Inajin dai sai kina daurata a hanya"


Mere Baki tayi ta cire kan telephone din a kunneta ,ta babballara ma abun harara


"Hmmm Allah yasa abokiyar zamace"
Kawai ta kife kan ta kurma ihu,tareda fincike dankwali kamar zararriya

"Allah ya hadani da namiji mai Zara da son aure aure...wai baba ,baban budurwansa ma tun
yanzu yina kiransa da baba ,nikuwa saidai yace babanki...








_Mun dawo ba sa'a,ba banda chaji ,kuma anmun wiping komai na wayata,plz manage_
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: 71- 75

*Jinin sarauta*

Yarima kamar yanda ya fad'a kuwa yaje ya samu baban diyanah ,da tambayar izinin aure.

Da fari baban fir ya nuna qin yardarsa dukda dai babu wani tsayayye dake zuwa,saidai gudun
wulakanci inasu ina dan sarki? Saidai nacin yarima ,don yarima suittt ya sauke girman kannan
,kullum yina jelen zuwa bada haquri tamkar Wanda matarsa tayi yaji ,saida ya shawo kan baba
adamu da qyar ta hanyar bin manyan unguwa da En uwansa maza .
Shikam baba yasan yinayi don fir,diyanah ta nuna batason auren yarima,a cewarta matarsa
zata iya kassarata,amma da lallashi da ban baki aka shawo kan ta.

Viki kam sati biyu jal aka saka,da iyayen diyanah Suka nuna basu da qarfi yace shi diyanah
yikeso ba kayan dakiba,so yayi alkawarin zubawa diyanah komai,amma bai hanasuba in zasu
qara mata da wasu abun.

Shikuma yaje ya gyara part din zulaikha ya maidata sama da yafi yawan dakuna ,itakuma part
din zulaikhan ya gyarawa amarya diyanah

Biki na matsowa yayinda duk istikharan da yarima zaiyi akan diyanah yake tabbatar masa
,gareta akwai wani haske amma an kasa gane ko menene.

A gefe guda kuma zulaikha ta lashi takobin bata barin diyanah ta shigo mata gida don babanta
ya shaida mata tanada qwari ,asiri kafin ya cita da wiya ,hakan yasa ta fitini babanta itafa lallai
saiya yi asirinda zai raba diyanah da yarima,ga biki nata matsowa ,ganin abun baban kamar
yayi sanyi kurum shine ta roki jakadiyarta da taimata hanyar malamai Amma saita kwantar dakai
"Lantana bawan Allah Nike nema Wanda xai duba mun yiwuwar xaman lfiya da yalwar arziki da

watannan yarinyar ,in babu a farraqasu "

"Aah uwar dakina wallahi irin wainnan yaran da naga makircinta ya firgitaki,yafi sauki kije wajen
rikakken kahurin boka,kinga ni nasan wani boka ana ce masa hatsabibi ,aikinsa kamar yankan
wuqane amma fa akwai kauce hanya,amma gimbiya wajen biyan bukatarka sai ka hada da En
duba, an tayaka da du'ai ,alabarshi in bukata ya biya ayi istingifari"
Murmushin kissa tayi
"Hmmm lantana ina tsoron zuwa wajen mutanen nan marasa imani,du kwaso qarya su Fada
maka,a ringa hadamu Fada da abokiyar xamata da mijina"


"Karki damu na yi dayane" haka suka shirya suka wuce wajen boka ta labarta masa komai
dangane da aurensa harda rashin shiga dakinta da bayayi

Anan ya tabbatar mata dole aurensu diyanah saidai ko ayi masu firaqu gamida shashatau
yanda kwata kwata zuciyarsa zai kauce a kan ta
Godiya tai masa suka juyo gida.


Aikuwa suna shigowa zamanta ba dadewa saigashi kamar an bugosa
Jakadiyarta na kasanta tana marmatsa mata qafa

Da sauri ta mike "Yarimana Kaine a dakina?...wow dole in hada party na murna ,yau watarana"
"Ina kikaje Nazo nemanki bakya nan" kame kame ta fara
"Ya isah zanje sallah ynx ,innadawo ki sameni a daki, inaso ki shiryamun list din kayan lefe naki
da na amarya"

"Angama yarimana"

Yina fita ta daka tsalle ta rungume jakadiya kawai saita fashe da kuka
"Jakadiya Nagode,wai yau ni yarima ya shiga dakina? Har yike tambaya ta shawaran lefe،ke
nicema zanyi list?...gaskiya in komai ya tabbata kyautarki na musammanne lantana"


°°°
Ta 6angaren diyanah kuwa tundaga ranar yarima bai qara kiranta a wayaba,bare yazo
gida,kuma kota kira bayi dagawa ,tun abun bayi damunta harya dameta har gobe biki bako lefe
,gida ya cika da jama'a En tsegumi na zundenta banda masu taranta sunayi.


Wata abokiyar wasanta ne ta ga giftawar diyanah zataje yin alwala a bakin tank

"Oh oh su diyah anfa tara kayan ruwa ,hajiya diyanah ...oh princess diyanah Matar yarima
,yarinya anyi manyan duwawuka ga kayan ruwa sun cicciko qirji"

Hawaye ne suka surnano mata a ido kurum saita cigaba da alwala .

Wato kallon er iska sukemun ,yarima ya yaudareni ya kwashi gara ya ware,to Allah ka zama
gatana


Da sauri ta wuce daki ta shimfuda darduma ta fara wadha tana jero addu'oi a sujjuda


°°°
Ranar daurin aure karfe shadaya zaa daura ,amma yarima sai yayi kwanciyarsa a daki wai
bashida lafiya aje akar6i auren ,sannan ya dauko akwatunan da gimbiya zulaikha ta hada set
biyu duk tarkace kuma ko cika basuyi ba ,yace akai da 200k wai tayi hidima.


Haka En daurin aure sukaje mata da maza ,maza a waje mata suka kai akwatu da kudin biko
Baba saratu ,ta ja diyanah gefe ,ta bata wani magani "ki karanta fatiha qafa arbain da daya,kina
tofawa akan garin nan ,sunanshi sassaqen gamji,sai ki sha da nono a cikin motar da zaa kawoki
kinji ,da niyyar zaman lpy da mijinki da er uwanki ,ki riqe addu'a shine makaminki ,karki yarda
da kowa sai ranki a cikin gidan nan ,ni sunana Sarah qanwar me gidanki ,naji sonki qwarai
araina in mun hadu zamu tattauna "


Godiya tayi mata ta kr6a ,aiko tunda ta shiga daki batafitoba saida ta gama, na fatihan haka ta
kasance sukuku har lokacin tafiya da ita,tayi kuka sosai shikenan zaa kaita gidan maqiyinta
tana sane.

Bayan isha'i saida ta gabatar da sallah raka'a biyu kowanne da fatiha da qulhuwallahu ,tana
idarwa ta maida goshinta a qasa ta jero _Lailaha illah anta subhanaka inniy kuntu
minazzalimin_ 41 ,sannan ta jero addu'oin saa a gidan aurenta tana kuka ,hr saida akazo tafiya
da ita sannan ta dago daga sujudan ta daga hannu tayi addu'ointa ta shafa ...suka wuce gidan
ta.




°°°
Tunda aka kaita yina tsaye a gaban window yina kallonsu har suka gama shigowa ,amma baisa
ya ji son ya ganta a ransa ba ,don yanzuma baqin auren yike gani.

Washegari gidan ya watse ,aka barta ita daya har bayan magriba.

Anan gimbiya Sarah ta shigo ,da wake danya kusan tiya duk an zaneshi da sunan Allahu...


"Tashi ki dafa da kanki da jar kanwa ,gashi ki farfesunshi ,kici iya cinki yanzu sauran kibani inje
ayi maki sadaka"
Hakan kuwa akayi,saida ta tabbatar ta ci komai sannan ta kar6i ragowar ,tasata ta sake wanka
ta bata kalan kayansu na sarauta daganan ta kira wayarsa

Kamar bazai daukaba ,sai kuma ya dauka "to yaya gani a dakin amaryanka ,kodai in tafine
bazaka samu ganina ba nima,zalunci dai ba kyau kuma in ka yi wa 'yar wasu gani er uwanku
nima a Wata masarautan Nike za ayi mun,sannan ai ba auren Cushe bane kai ka ganta kai
raayi "
Shiru tayi tana sauraransa
"Oho dai in bazaka shigo ba sai inje in shaidawa mai martaba yazo a maida yarinya gidansu tun
da girma da arziki ,kafin ka saketa daga baya ,ka 6ata mata suna ana mata kallon qaramar
bazawara"


Kashe wayar tayi ta amsa da "toh"

A jaka ta dauko turare mai kamshi a dan kwalba da 'ya'yan idon zakara ,ki shafe a fuskarki in na
fita kafin Ku hadu da yayan ,ni gobe zan wuce ga numberta ,ma ringa waya"


Godiya tayi mata sosai wannan shi ake kira haduwar jini











Oum Aphnan✍️
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: 76 - 80

*Jinin Sarauta*



To ba laipi a dai ranar anyi Abubuwa,daganan bai kuma bita dakinba,in zaifita saidai yabi ta
kofan baya, in kuwa ya zama dole sai ta dakinta zaibi ,to bawai itaba dakinma bayison had'a ido
dashi haka zai d'auke kai ya karkatar ta wani gefe,har ya wuce,in saqone saidai yaba gimbiya
zulaikha ita zata aika mata ,gadara nau'i nau'i ,kwanan ta duk ta handame kullum ita keda
miji,amma dukda hakan wata zubin in ya zauna sai ya ringa jin kamar rayuwarsa
incomplete,wannan yasashi d'araran kansa,kullum inya ke6e saidai ya rafka tagumi ,bai san
tunanin me zeyiba,gabadaya ya susuce.


A 6angaren diyah kuwa tun ranar farkon da akayi komai ,ya zura kwallo a raga ,ita koda taga
bata period duk tunaninta dai matsalane da sauyin wajen zama ,zai kuma gyaru musammam da
bata ciwo ta d'ashe ta kode ,yanzu cikinta yana Neman Wata biyar, ita kadai take rayuwarta har
barorin gidan sun juya mata baya,ba mai gegen dakinta ,komai ita takewa kanta tundaga tsaftar
muhalli har komai dasu girki.


A Wata ranar larabane gimbiya Sarah tazo

8 / 10