Author : Hassana Bamalli Oum Aphanan Category : Read Hausa Novels
yadani ,jiya mummy tace ni twin
sister din Saudah ce ,saida na fara murna ,ina farinciki na samu sauyin rayuwa kuma sai kurum
ka bijiro da wata magana ,kun nemo wain su mutane da ban sansu a rayuwa ta ba ,claiming
that wai su iyaye nane,to duk kuje na yafeku,Ku barni Allah zai fitomun da iyayena na haqiqa
inma ban samuba na dangana,nabi shawarin maaiki (s.a.w) dayace idan masifa ya same ka
kace innalillahi wa inna ilaihi rajiun,nayi kuma ina jiran sakamako don fadin Allah ne ,innallaha
la yudi'u ajral muhsinin "
Tuni dakin suka rushe da kuka ,dady yusuf (PA) da ya kafe a bakin qofa akan shi lallai bazai
shigoba,zuruf ya shigo dakin ,yaje ya fincikeshi a jikinta ya maye gurbin wajen sa da kansa
"twinkle kinga yanda na koma ko? Farida ta cuceni tayi nasarar koranki a rayuwa ta, na
zawwace akan Neman ki ,saidai kash a lokacin da naji labarin samuwar ki,sai iyayenki suka
bayyana maki,twinkle yanzufa so suke su rabani dake ,nikuma bazan iya rayuwa in babu
keba,kice su kyalemu mu koma gida mu cigaba da rayuwarmu na baya,muyi wasanmu tare,ki
mun kwalliya in baki shawara koba haka ba?" Tsinkewa tayi da kuka "dadynah inason ka ,kuma
bansan kowaba saikai don haka kai zanbi na yafe duk Wanda zasu biyo bayan kai matsayin
iyayena ,koda sune na gaskiyan na yafesu tunda sun hofuntar dani lokacin da Nike bukatar
tallafinsu ,kai kuma sai ka maye mun gurbinsu,akan me yanzu ga kai sai in koma ma wasunka
,ina ,,,,aima sai hakkinka ya kamasu"
Tasowa Gimbiya diyanah tayi ta saka gwuiwoyinta a qasa tareda kamo hannun su'adah
"khalisat karki yimun haka ,kinsan ko ke wacece? Kinsan waye mahaifinki? Kinsan kukan
mahaifiya kuwa akan 6atacciyar 'yanta,?"
Sai a wannan karon mai martaba ya samu zarafin magana cikin sassanyar murya cikin
dusashiyar muryarsa na girma da madarar izzah "Ya Isah haka ,Diyanah mike ni zan mata
bayani" mikewa tayi ta koma mazauninta ,a take kowa ya nutsu har shi PA din duk suka
zazzauna kamar dalibai a gaban malaminsu. "Wannan itace mahaifiyar ki ,bisa bincike da hujjoji ,amma tabbatuwar nine mahaifinki ,wannan
ni sai anyi DNA test saboda nima ji nake ke din ba d'iyata bace ba,don nafison diyanah fiyeda
duk wata 'ya da zata kawo mun matsayin d'iya ,matsawar watannan zata zama silar shigarta
damuwa,kinsan wuyar da ta shiga sanadiyyar ki? Ta rayu cikin ciwo da hauka duk saboda ke!
Tsawon shekaru goma bata da sukunin ruhi a yayin da ke kike rayuwa cikin farinciki ,wannan ba
gata bane ba Allah yayi maki? Kinsan halin mutu kwakai ko rai kwakwai din da zaki shiga da
ace kina tare da ita? To ki sani ni na barwa su PA da VP din ke ,in wuya ta isheki da kanki zaki
nemi masarautar Azajadar don nan ne rufin Asirinki,mu kuwa munada Wanda zai maye mana
gurbinki,kingan sa d'an Albarka" ya qaresa kausasan maganganunsa yina nuni izuwa ga Dr
Khalid, bai tsaya sanyaba ya umurci Dr Khalid da Gimbiya diyanah da su fito su tafi ransa a
mugun 6ace .
Kuka Gimbiya diyanah ta fashe dashi suka soma firfita har akaxo kanta itace ta qarshe ta waigo
ta kalleta "Princess khalisat, Sarki jabbar ,fushinsa dawamammiya ne,gabansa tabbataciya
ne,ina umurtanki daki gaggawar Neman yafiya da afuwarsa ,kuma ki kawo kanki fadar Azdajar
a nan kusa" tana kaiwa nan ta kulle kofa ta fita tana hawaye . Kuka ne mai gunji ta fashe dashi ,ta fara qoqarin cire hannunta daga jikin qarfen "Wayyo Allah
dady ,Abbah na ,kukaini wajen mahaifiyata da yayanah wallahi,had'iyan zuciya zanyi in mutu
idan sukace sun juyamun baya ,inason mahaifiyata da yayahnah me sona"
Sai a wannan karan ummah ta soma magana cikin ranta tanajin zafi za'a d'auke mata su'adah
ba tareda burinta ya cika a kanta ba "kiyi shiru su'adah ki bari ki warke ,ni da kai na, nayi
Alkawarin kaiki har gaban mai martaba ki roki yafiyarsa muma bamusan ke 'yarsa bace ba ,sai
a 'yan awannin nan ,amma dole zamu maidake don mai martaba uban kowane a wajen
nan,koda ke ba 'yarsa bace,bamuda hurumin ya roki mubasa 'ya mu hanasa bare ke da hujjoji
sun tabbatar da hakan "
"To nidai naji kawai Ku kwance ni in bisu" hawayene ya cigaba da gangara a idon PA ,shikenan
yasan ya rasa daughter dinsa,rasawa na har Abadan ,kuka mai gunji ya kamayi yaje ya kwance
hannunta daga jikin qarfen tako fita da gudu tana qwalla kiran "Nannah ,yayahnah!"
Tuni PA ya shiga buga goshinsa a jikin garu yina ihu tareda fadin "Why ? Fareeda why?,kin
rabani da daughter da,kin tafi yawan dandin ki...Allah ya sakamun da duk namijin da matarsa ke
zambatarsa a bayan idonsa,irina . Allah ya tona asirinsu,harsai duniya tayi tirrrrr dasu" gaban
ummah ne ya ringa fad'i dam dam! ,kardai yusuf ya gane abunda mukeyi da fareeda ne?
**
Fushi sosai mai martaba yikeyi ,sai dakyar Dr Khalid ya shawo kansa amma dukda hakan saida
yasa aka bada jininsa Dana Su'adah akayi DNA test aka tabbatar da shidin ne mahaifinta kafin
ya sakar mata murmushi, ya bude hannu ,da gudu su'adah ta kwace hannunta a hannun
Gimbiya diyanah taje ta fad'a jikin mai martaba "Barka da zuwa d'iyar albarka cikinmu fatan
tsawon rai da lafiya hadida ilimi mai amfani Allah ya haskaka rayuwar ki ,ya dausashe qudurin
maqiyanki akan ki, yau zamu wuce fada kuma za mu warware labarin komai gaban Wanda suka
aikata"
Murmushi tayi "nagode babana" suma duk godiya sukayi har yusuf da goshin sa yayi sintsir an
nade da bandeji
**
Qarfe takwas na dare,helicopter dinsu su'adah mai martaba ,saudah da gimbiya diyanah ,ta
tsaya a qatuwar filin bayan cikin gidan sarautar mai kamada lambu ko gidan gona mai daukeda
dogayen bishiyoyi da ruwaye kala kala da qoramu ga shanaye daga can gefe cikin wajen su
,filin wajen zaka rantse a wata kwarya kwaryan jajin turawa kake mai kamada na gona,ba a
gidan sarautaba. Jirgin su bai gama daidaituwa ba ,saiga na PA ,VP da ummah da Dr Khalid
,daganan suka dunguma hanyar da zai sadaka zuwa cikin gidan tsundum ,Wanda yike da
tazara mai nisa a tsakani.
[7/27, 5:30 PM] Bamalli✌️: *JNS 2*
31-35
Masauki mai kyau aka sauke dukkan su,shikuma Dr Khalid ya hau mota ya wuce gidan sa
,dukda tafiya ne Mara tsayi sosai,don a cikin fadan yike amma can ta qarshen katangar,amma
Sam baya iya zuwa da qafa ,yinada bayi da barori masu kula dashi ,Abu dayane yayi masa
cikas shine rashin macen aure da wasu damuwoyin cikin gidan yasa Sam baya sha'awar
aure,don shekaru biyu da suka wuce anso a had'a sa aure da qanwar Gimbiya zulaikha, saidai
ana kwanaki ya gudu ,baa sake jin duriyarsa ba saida aka shaida masa an aurar da ita.
Washegari fada ta dinke da Al'umman annabi kowa kagani yazo taya murna ana son ganin
princess wasu kuma suce Gimbiya khalisat, Ita kam ado akayi mata na usulin gidan
sarauta,tana fitowa manyan baqi da malamai da suke zuwa ganin ta suna mata Addu'oi da
kyaututuka , tana zama wata kuyanga datafi manne mata zatazo tace anzo Neman ta,kai saida
ta gaji don kanta ta wulle ta tafi sashen Dr Khalid, itada Saudah ,anan suka bararraje wani bawa
ya zauna ya lanqwashe kafa yina koro mata matsayin ta a wannan masarautar tun ranar da dan
saqo ya aiko da sallahun haihuwarta ,yina shaida mata yanda ake mulki ,ba dariya ba
barkwanci.sudai in yayi yayi sai su had'e hannunta da bai karyeba Dana Saudah su kashe
kamar shashashu.
Shikam Dr Khalid tunda yazo baiyi dariya ba ,ba wannan wasan da yikeyi dasu ta rasa dalilin
sauyawarsa,amma ta zuba ido tana ganin gudun ruwan sa.
Qarfe hudu na la'asar dangi na kusa da na nesa suka had'u a wani mashahurin fili gab da gidan
Dr Khalid, duk a cikin fadan bayan anyi decorating wajen an kafa tantuna,sosai kuyangu suka
cika gaban kowa da drinks da samosa da spring rolls sai ruwa da Rabin kaza, su su'adah ma
mamaki suka kamayi sanda akaxo canja masu shiga cikin wani shigar alkyabba tasha ado cikin
shadda maroon Riga da wando yasha aiki harta qafafun wandon,gaba d'aya ta sauya kamar
namiji ,banbancinta da namiji kwalliyar fuskarta da adon gwalagwalai.
Wata baba saratu da kanta ta shigo mata jijji6e6iya ana zuwa bayanta barorine cikin uniform
mata,
Daidai su'adah zaa fito da ita suna gyara mata zaman Alkyabban itakuma ta shigo "Ina d'iyar
d'an uwan nawa? Dama da rabon zan ga jinina?" Kurum saita fashe da kuka ta rungumeni
tamkar ba wannan isashiyar matan ba...kam ta rikoni cikin jikinta muka shigo wajen taron,Anan
ne gasskata sarauta gaskiya ne,yanda duk inda muka saka qafa manyan mutane maza da mata
masu kudin gaske ke gaishemu,bayi na zubewa cikin sallamawa, take su'adah taji wani abu na
tsirgar mata ,Izzah na hawanta kanta yina girma ,Ana gaisheta tana lumshe ido maimakon ta
amsa ,har saida ta ajeta a wani madaidaicin kujeran royal mai adon blue da gowldin ko ina ya
dauki haske masu chanja kaloli, da adon furanni.
Maimakine ya kamata to yaushe ne akayi duk wainnan abubuwan cikin gajeran lokaci? Gaskiya
wainnan snacks da kajin saidai in ordernsu akayi ba a cikin gidan akayi ba, Ashe basu saniba
,mai Dubai hotel ne ya dauki nauyin duk wani cima da za'a ci na iyayen gidan sa ,kowafa ya
hallara zallah dangi d'aya kowa ka gani da kwaya kwayan zanen mallanci bibbiyu a gefen
kuncinsu....familyn ,kyawawane amma sun rabu kala biyu,da masu dogayen hanci masu
matsaikaitan ido farare tar ,da masu matsakaicin hanci da qwala qwalan ido,don haka dukkansu
irinsu gudane ,dole dan dangin na shigowa akwai kalar Wanda yike kama dasu .Quri quri
,Saudah tayi da ido tana kallon masu kama da bestyn ta,ada tana jin ita watace yanzu kuwa da
taga yanda sarauta yike ,saita gane cewa mulki ba komai bane. Saida aka bud'e taro da addu'a
kafin sarki ya fara da godiya wa daukacin dangi na kusa da na nesa da suka sama halartan
taron gaggawan da aka kira ,saboda VP da iyalansa da komin dare zasu juya Abj yau .
"Alhmdllh waqa a bakin mai ita yafi dad'i, zamu so jin yanda, Al'amuran ta kasance a bakin
Gimbiya diyanah Tindaga haihuwar magajiya (Su'adah) har zuwa salwantarta,sannan da yanda
ta bayyana ,harma shigowar su VP cikin al'amarin,A taqaice dai zamuso jin labarin wannan
masarautar" Da addu'a Gimbiya diyanah tafara da bude taron da addu'a kafin ta d'aura
*Egypt 1999*
Ina farfad'owa daga barcina bayan an fito dani daga aiki an fuddamun Khalesat a cikina ,Nurse
na kamo hannunta na fara da tambayar ta abunda na Haifa , Murmushi tayi ta shaida mun
macece amma tana dakin Hutu.A take naji zuciyata bai baniba bansan sanda na shiga roqonta
don Allah ta kaini inga d'iyata ba. Muna shirin shiga dakin naji Gimbiya zulaikha, gatanan da ranta tanajina ,tana umurtan
jakadiyarta da sukazo tare da ta bankawa dakin wuta duk jariran su qone ,sai ace akasine
gobara ya tashi,amsawa tayi da to uwar dakina saidai zanje innemo fetur ke kuma kibar wajen
nan kar zargi ya shigo, had'a ido mukayi da nurse d'in, kafin inyi wani magana nurse din ta
janye ni da Sauri muka 6uya ,muna kaucewa na fashe mata da kuka ,nurse ki taimakeni ,don
Allah likita yace wannan itace kad'ai qwan mijina a duniya da zai iya qyanqyashewa ,itama din
dashenta akai mun dukkanmu rauni garemu ,karki bari mu rasata don Allah ,mijina dan sarkine
,yina azaban son haihuwa don Allah " rarrashina ta hauyi "karki damu er uwa yanzunnan zan
miko maki erki kuma dama su ukune a ciki zan sa ma'aikatan a kaisu BCG sauran na cikin
kinga in wutan ta tashi yaran mutane sun tsira "
Godiya na dinga mata ina rizgar kuka ,harta kawo mun babynah ,atake na koma daki da abata
saidai muna shiga naji ban natsu ba nasan tabbas ana farautan ranta kuma komun koma gida
Nigeria saita aiwatar da nifinta akanta ,nan ne ma take da daman,a take wani bahagon tunani
ya fad'o mun nikuma ba tareda na aunaba ,na miqe naje na d'auko akwatin kayan haihuwa ta
na zazzage ,na debo duk gwalagwalan da nazo dashi na watsa ,na dakko open check nayi
rubutun zunzurutan kud'i ,sannan na dauki Biro mai gold ink nayi rubutu na kalmasa na saka
cikin farin envelope ,shima bayi rubutu a saman ,na kira nurse din ta taimaka mun muka dauki
akwatin da basket din ,na roketa ta taimakamun in cika qudurina ,ita ta taimakamun muka fita ta
qofan baya,tafiya kadan muka riski wani waje ,anguwane mai dogayen gine gine da manyan
bishiyoyi da dan shiru anguwan ,alamar dai unguwar nasu natsuwa ne.
Dan lungu na samu na aje kwandom. Babyn da feeding Bottle daukeda madarar yara a gefe
,nasata tayi mun gadi,itadai nurse da ido take bina.
Sai bayan nayi hakan na dauki wannan akwatu naje gefen hanya na aje ,sannan na daura
envelope d'innan na danne da dutse .da Sauri na dawo nacewa nurse din duk mu tashi a wajen
mu 6uya ,nikuma saman bishiya na hau.
Saida na kwashe kusan Rabin awa kafin wasu En matan larabawa sukazo wucewa ,har sun
gifta sai qaramar ta soma mata magana da larabci "ukhty kinga wani akwatin qarfe me ruwan
gwal ,kai gaskiya ya bani sha'awa ban ta6a ganiba sai a TV in muna kallon film din masarautun
India, zo muje mu gani" bige hannunta tayi "Ke bazaki sauyaba ko? Kinfa San layin nan sunyi
qaurin suna akwai Satan mutane,kije ki ta6a kya 6ace dama gashi magriba ta kusa" haka suka
wuce ba tareda sun dauka ba.wannan magana tayi mugun tsoratar dani ,a take na yanke
shawarin inje in dauki d'iyata ,amma kafin nan na hango wani matashi tafe yina amsa wayar
hannu irin Samsung d'innan Nada kalar ja, ga dukkan Alamu Sauri yikeyi,cikin rashin kula yayi
tuntu6e da akwatin ,dutsen da na danne envelope din ya fad'i masa a qafa ,envelope din yayi
gefe,saurin riqe kafarsa yayi ya zauna gefe yina kashe wayar ,saman fatar qafarsa ta
zabtaro,yina cikin jin zogin ya hangi akwatin ,kallon akwatin naga yayi na En daqiqu kafin ya
Kali envelope din , dukda gari ya fara duhu ban iya kallan fuskarsa ,amma naga hakan.da Sauri
ya daga bangon envelope din ya karanta ,kafin ya farke ya karanta ,shiru yayi dafe da kai,ni
kuwa qirjina sai bugu takeyi ina duk addu'a da yazo kaina ,can naga ya mike ya dauki akwatin
ya jefa takardan a aljihu,sannan ya biyo inda na aje khalisata ya dauketa a kwando ya tafi,ina
ganin ya wuce na durko don inga sabon uban da Allah ya za6awa d'iyata ,saidai INA! Ashe
gaggawa yike ya shiga motarsa ,ina zuwa saidai naga hayakin motarsa ya bar wajen ,a take
anan na duqe na ringa rizgar kuka ,da shesheqa nadama ta bijiromin na sallama d'iyata a
hannun Wanda ban sanshiba ,danasani ta kamani yanda ko hoto ban mataba da watarana nace
na haifi yarinya nima ,ana haka Wannan nurse din tazo ta dagani muka wuto hanya tana
rarrashina ,anan Nike shaida mata damuwata rashin sanin makoman yarinyata,kuma banda ko
hotonta "karki damu munyi mata photo muje zan baki copy" kunji yanda mukayi da wannan
nurse din ,aikuwa muna shiga naga dakin yara ana kakabi ya kama da wuta da jaririya guda
d'aya, kuka na fashe dashi na gurfana gwuiwoyina a qasa "khalisat na rabaki da wannan wutan
,saidai bansan hannunda na jefakiba qilama yafi wannan wutan zafi a gareki,kilanma yanzu
kema an kashe ki,Allah ne masani" abunda nayi ta sambatu akai kenan ,ina cikin wannan halin
kurum sai ga zulaikha da jakadiyarta fuskarsu fal annuri suna ganina suka kya6e fuska irin na
tausayawa ,zulaikha ta rungumeni tana hawaye "kiyi hakury diyah ,nafiki jin radadin rashin
khalisat NASA rai da yarinyar nan,tunanin muma gidanmu zai armashi samun kukan jaririya a
jikinsa Amma mai Afkuwa ! Ta afku sai hakuri" Jinjina mata kai kurum nayi na wuce dakinna fara
had'a kaya na,don kuma bansan amfanin zamata a qasar ba,ni kad'ai na dawo nabar masu
zaman kar6an jaririya da taryata a can,yarima kuwa yina Asibitin baisan inda kansa yikeba.
Sai bayan kwana biyu suka dawo ,lokacin damuwa ta ,ta ragu ba fawwala ma Allah saidai in
natuna bazamu sake haihuwa ba musamman yarima sai in dauki hoton khalisat in ta kalla ina
kuka, Daganan bala'u irida kala dukaita samuna ,wannan ace mayuine suka kamani ,wasu
suce asiri wasu ace wankan jegone bansamu da kyauba,jinya safai safai yaqi jin magani ,har
saida na koma gida jinya ,shine silar kar6an khalid a hannuna,aka ba zulaikha ,saida na kwashe
shekaru takwas a haka ,amma dukda hakan yarima na qulafucina ,ana wannan sarki mahaifin
mijina ya rasu gashi mijina bayida kwanciyar hankali yamace baison sarautan aba qanin
babanshi ,shi bai cancanci sarautan ba tunda baida magajiya ,shinefa aka Nada baba Abubakar
,shima shekara d'aya bayan nan aka farka aka wayi gari ya mutu kuma a ranar nikuma na
haukace,a take aka yimun sharrin ni na kasheshi saboda baqin cikin ba mijina ya hau gadon
sarautan ba,shiyasa hakkin jinin sarkin yasa na haukace,En uwansu suka yimun caa ,ga haka
tu6uran a lokacin sukace lallai sarki ya sake ni in bar masu gida annoba amma sarki ya
qiya,yace in kuma har aka matsa saina bar gidan to shima zai gudu yabar masu sarautansu
,hakan nan aka kyaleni saidai an canjamun daki can karshen gida,wai bazasu zauna da
mahaukaciyaba ,amma a hakan sarki dani muke mu'amalar aure kuma bani mishi haukan,koda
akagane sarki na kwanciya dani ta hanyar sokanan haukan da zan ta zubawa ,sai aka
shamakantar da ganina ,sannan haukan ya dada ta azzara sai an daddaureni ,wannan lallurar
shine ya cigaba da bibiyata har wainnan kwanakin da nayi arba da hoton da na Adana Ina
kallonta don debe kewa, ana cigiyarta matsayin 6atacciya ,ganin hotonta shi ya dawo mun da
ganina kuma haukanma ya gudu ,kunji taqaitaccen Abunda ya faru....tsit wajen yayi masu kuka
nayi ,lallai hakki bala'i ne,mun zargi baiwar Allah cewan baba saratu ,to Zulaikha saidai kika ga
diyanah tayi lafiya kuma Allah ya dawo