Jinin Sarauta Book 2 Complete By Oum Aphnan

Author :  Hassana Bamalli Oum Aphanan Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 10

27K to 27.4K   out of 27.4K words

akazo gargada
"Kai wallahi na gaji kar kaje ka gwara mun kai da wannan emerciated keken naka,ka watsar
mun da haqora,waima kasan no wacece? Nifa Matar sarkin garin nan ne,yanzu haka a pos
dinnan inada kudin da zan siye kekenka da kai kanka goma ,to karka wahalar dani"

Fakan idonta yayi ya kalla jakan hannunta mai daukan ido
"Wow ga dama tazo".... Jan Wata arnen burki yayi ya dawo baya ragwaf ,aiko ta bugu kum

idonta wasu tartsatsin wuta sukayi mata flashing ,kafin ta dawo hayyacinta ya fito da gudu ya
warce jakar da gudu ya cancani hanya


Ihu ta fasa ta daura hannu aka" Na shiga uku ya kwacemun jakata, Ku taimaka mun" ta bisa a
guje ko ganin gabanta batayi ,jama'a ma suka Dane masa baya din a kamosa


Sambatu ta kamayi "Wannan jakar shine ya qunshi duk fatana in ba'a kamasa ba shikenan
,nida gidan sarauta har Abadan ,don banda kudin siyen baqaqen karnukan da zaa yankawa
Aljannu susha jini suji dadin yin aiki da zafi zafi" ai kamar Wanda aka mintsina ta kara yankawa
da gudu ,batai auneba saidai taji mota tayi sama da ita ,kafin ta yunkurawa ta mike,Qatuwar
motar daf tazo ta murtsiketa akan kwantan.


Haka kanta ya dagargaje namanta ya manne akan kwalta jini na sharara


Shikenan Allah ya kar6i ransa
Gimbiya zulaikha ta rasu batareda ta cimma burinta na komawa fadanba bare ta cutar da
khalisah kamar yanda ta ci buri



FOUR YEARS LATER

Abubuwa da yawa sun faru masu dadi da maras dadi ,ciki kuwa harda haihuwan En biyun
gimbiya diyanah duk maza, Dr Khalid an masa auren gida da er uwansa dukda baiso yanzu
haka yarinyarsu kwananta sittin, suna qasar Spain yaje karo wani course rabonsa da 9ja
shekaru hudu kenan,sai a wannan karon yike fatan dawowa da matarsa Habiba da diyarsu little
diyanah

PA ma ya dawo da Haj Farida ,bayan yaje har gidanta yaga irin rayuwar da takeyi, sannan yaji
labaran kyawawan dabi'unta a bakin makwftan ta da abokan aikinta ,yanxu haka suna zaune
lafiya ,Haihuwane dai babu


Saudah kam da Gimbiya khalisah an zama manyan babes ,tamkar En shekaru ashirin nonuwa
ya cika kirji ,suna gwara kan manyan maza .

A kuma wannan karon ne ,PA Yusuf ya harraqo da kudurinsa na son Aurenta
Shima kuma yanzu haka VP ya kasa ya tsare kawai aurenta zaiyi ,dukda hidimar za6e yataso
bays samun zama amma ya turawa khalisah text msg cewar yina cikin layin manema

_Mu Had'e a littafi Na uku don jin Rayuwar Khalisah bayan girmanta kuma Waye zata aura_

Taku har kullum Hassenart Bamalli
(Oum Aphnan)

10 / 10