Author : Hassana Bamalli Oum Aphanan Category : Read Hausa Novels
sannan ya zame nadin da akayi masa
ya rufe masa baki don ya samu damar shaqar iska
Fadawane da malum malum dinsu combination ja da blue,suka tashi suna katangesa ana jero
masa sannu da Nema wa dan saqo yafiya
Sum sum dan saqon ya sulale ya gudu ba tareda sun ankareba
**
Ranar Laraba
_(Ranar Haske inji Malunmammu)_
Gabadaya makarantan ta cika ta batse,da dalibai ,da manyan mutane da suka gayya ta
An qawata wajen 6angare 6angare ,6angaren dunjimin En yaye dabam ,dukkansu sunsa ankon
koriyar atamfa da hijabi milk
Ga wajen manyan baki an aje manyan kushin ,sai kuma na malamai da iyayen yara.
Da damuwa diyanah ta shigo filin makarantan ,kasantuwar bata samu dinkin yayen ba,don
maman ta bata samu cikon kudin amso dinkinba,dole hakuri ta bata,shine ta saka jallabiya baka
da milk din hijabin.
Tana zama ,cikin rukunin dalibai saiga tawagar yarima sun shigo.waje yayi tajin tajin
Kafin kusan Rabin awa ,a natsa ,mai gabatarwa ya hura lasifika yina mika sakon barka da zuwa
ma yarima tareda yawun daukacin mazauna wannan wajen.
Sannan ya dauki jadwalin programs din da za'a gabatar
"Ba tareda 6ata lokaci ba ,zamu kira Diyanatu Adam don tazo ta bude mana fili da karatun
qur'ani,mimma tayassarah....Diyanatu Adam...."
Shiru diyanah tayi tana rarrabe ido ,tana tuna kashejin baba "Diyanatuh ,karki qara fitarda
sautinki a lasifika da sunan gasan karatu ko wani abu wannan tamkar bidi'ane da nuna iyawa,ke
kuma kina karatune don Allah da ma'aiki"
"...Diyanatu Adamu in tana kusa ta fito"
Had'e ido da malamin ajinsu tayi,da Sauri ta duqar da kai taqi fita .
Zagayowa malam khidir yayi ,cikin rashin tsammani yazo ya zuba mata Ranqwashi a ka.
Karaf a idon yarima,qyam ya tsaida donsa a wajen
Had'e hannunta tayi guri guda alamar roko
"Malam kayi hakuri,tunda za aje tishi ,na fada maka bazani ba,tunda babana yace kar in sake
yi,kuma kai kace in zauna,ni na saki jiki kun cireni ,wallahi banyi muraji'a ba,don haka don Allah
a za6a wata cikin En bitanku"
Tsawa ya dokamun "Tashi ki fita kina 6ata mana lokaci,Ai da acikin En tishin mun sama Wanda
zata iya da bamu fidda ke ba".
Mikewa tayi tana sharar qwallah da bayan hannunta,tasan babanta na kallonta ,wani kunyarsa
zataji in taje tayi abunda baiso ,qiri qiri yina ganin ta?
Ballara mata harara sauran d'aliban da baa fiddasuba sukayi ,kawarta shafa ,ta riko
hannunta,tana murzawa ,a hankali ta kalleta,sai ta gyad'a mata kai
A sanyaye ta fita bayan ta sassaita kanta kamar ba komai.
Cikin wani irin Taku take tafiya a sanyin gaske tamkar Wanda qwai ya fashemawa a ciki,ko me
tausayin qasa.
Zuwa tayi ta dan russuna ta kar6i lasifikan ,ta hura a hankali
Sannan ta fara,Rairayo qira'a cikin suratul Aaraf.
A take waje yayi tsit ana sauraran daddad'an muryarta Wanda take dan tauna halshe ,a yayinda
masana'a qur'ani suke jinjinawa kaifin basirarta ,da tasan yanda ta zaqulo suranda zai dace da
zaman
Musamman yarima mu'iz dake son suran saboda yanda Allah ya fara da yabon kansa,da
Qur'aninsa sannan ya fara jero sunayen annabawa daki daki da gwagwarmayansu ,tundaga
kan Annabi Adam ,nuh haka har Annabi Mohammed (s.a.w),tun tana karantun tana girgiza kai
,kawai tana zuwa kan na Annabi Mohammed (s.a w) idonsu ya sarqu dana babanta da yayi
tagumi yina kallonta ,waje yayi tsit bakajin ko tari sai zazzaqan muryarta
Tana ganin ya zabga wannan tagumin kawai sai ta tsinke da kuka ,ta cigaba da ayar da takeyi
Shehunnan malamai a take suka soma jinjina mata,lallai yarinyar ba rakadin karatun ta samuba
harda ilimin tafsiri(fassaran Qur'anin)
Shi kuwa yarima tsumasa ta ringayi kaga baiwar Allah tana karatu ,taji abun tausayi ta kece da
kuka,tamkar a sa'udiyyah don dai shi a qasar nan bai ta6a gani ba.
Bai auneba saidai yaji kabbara alamar ta ajiye sifikan ta gama, Bin ta da kallo yayi tana tafe
,tana had'a hanya.....
Ji yayi ko nawane yaba wannan makarantan don su ringa qyanqyashe masu irin wa'innan yaran
masu tsananin taqwa da tsoron Allah.
*Don Allah abar fita da Littafinan*
```Kardai Ku sha'afa Wannan littafin Zazzafa ne daga cikin gwarazan zafafan Alheri
writers....Wanda suka had'a da:```
_*K'WARYAR SAMA* zazzafa daga Alk'alamin *Maman teddy*_
_*JININ SARAUTA(the gorgeous royal blood)* zazzafa daga Alkalamar *Hassenart Bamalli(oum
Aphnan)*_
_Idan kinason biyan *NORMAL PAYMENT* ne ,to kowanne littafi d'aya *#100* ne duka biyun ne
*#300*_
_Idan kuma *VIP* ne kikeson biya toh,kowanne daya *#200* ne ,in kuma duka biyunne *#500*_
_Idan kuma *SPC* ne kikeso toh kowanne d'aya *#300* duka biyun kuma *#700*_
_Zaki iya biyan kudinki ta daya daga cikin wannan hanyoyin biyan:_
_*BANK PAYMENT*_
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb
_*VTU TRANSFER*_
09065990265
_*MTN CARD PAYMENT*_
09065990265
_*SAI KI TURA SHAIDAR BIYANKI TA HANYAR SCREEN SHOTTING EVIDENCE DINKI
TANAN:*_
08081202932
_SAI MUN JIKU MASOYAN AMANA,KUYI ZUWA DAYA KU KAFCI RABONKU CIKIN
SASSAUK'AR FARASHIN GASKE_
_Maman teddy_
_Oum Aphnan takuce_
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: *Jinin sarauta 2*
56 - 60
Haka programs suka cigaba da tafiya,Wanda ba za'a kira d'alibai set uku ba sai sunan Diyanah
ya shigo ciki,daga karshe aka soma raba kyaututtukan gwarazan d'alibai daga wajen malaman
su Wanda aka gayyaci uban taron ,yarima Abdulmu'iz abdulganiy zai bayar da hannunsa.
Miqewa yayi da qyar kamar me ciwon kwankwaso,dogarai suka wani yi daddafe dashi,kamar
za'a d'aukesa
wohoho mulki,mutum ba babba ba,sarauta zai kama kwankwaso,tashi da qyar?
_Bafa dakai nikeyi ba,malami,ooops happy sallah ya mu'iz,still waiting for mah raqumin
layya_
Daga qasan mataki aka fara ,zuwa manyan mata kai,wannan shine fitowarta na hudu kuma na
qarshe.
Saida malamin ya gama kuzuzutata "Yara manyan gobe,dan kwiykuyon da zai kyan kiwo tun
farkon tashinsa ake ganewa,Kaman duk shekara,makaranta ta saba fitarda gwarzo/ gwarzuwan
shekara ....A wannan shekaran gwarzo/gwarzuwan shekaran tamu,ya samu lambar yabone
bisa abubuwan lura kamar haka,Shaidar girmamawa da tsantsan ladabin dalibin /daliban ga
malaman su kai harma da dalibai En uwansu.
Jagorancin sharan masallaci fisabillillah
A wannan matsayin ta rubuta baitin yabo ga sayyadina rasulullahi cikin harshen larabci ,baiti
mai tsayin shafi goma.
Ta fito gasan musabuqu na kasa da kasa sau biyu tana kar6owa makaranta ,kambin na biyu da
na d'aya ....Lallai dole makaranta tai kewa gamida kishin rabuwa da wannan
dalibi/daliba...kamar koda yaushe ba kowa bace face DIYANATU ADAM..Attakabir
Wani ihu akayi ,ana sowa shafa kawarta da hafsat suka rakota kar6an kyaututtuka ,kanta a
sunkuye tana hawayen da bata San ko na menene ba.
Zuwa tayi ta tsaya a gabansa ,ga jerin tulin littafai a gefensa ,na sahihul Bukhari da sahih
Muslim ga qur'anai masu fassara,sai wani qaton kwali an rufesa cikin Leda da rangadeden
sunanta da larabci.
A inda yike tsaye,wani bafadensa ke miko masa shikuma ya bata,a sanyaye take dukawa ta
kar6a,kanta a k'asa, har yanzu bai tantace idonta ba ma,itakuma inta kar6a ta bawa su shafa su
rik'e,har aka kawo kan wannan kwalin ,qyam ya tsaya yina kallon sunan,a hankali bakinsa ya
furta "DIYANAH"
Gigif ta dago idonsu ya sarqe da na juna,dan murmushi yayi don ya gane tayi mamakin sane
Bakinsa ya motsa a hankula "BARAKALLAH"
Hawaye ta sharce da hannunta a maimakon ta bashi amsa,sai kurum ta kama zata
kar6a,rikewa yayi saida mai cameran ya daukesu tar,sannan ya sakar mata ta wuce, ba kamar
sauran ba da ko kallo basu ishe shiba.
Taro sai son barka,bayan an gama da d'alibai ,sai kuma manyan baki,da iyayen yara suka
soma kar6an sifikan suna tofah Albarkacin bakinsu,tareda bawa makaranta gudunmawar da
suka buqata.
Shikam yarima komawa yayi ya zauna tareda dan kwanta wa akan bayansa,sosai tsayuwar da
yayi ta gajiyar dashi.
Anzoda sifika yafi sau nawa baice komai ba,sai a qarshe ,ya mik'e ya kar6a sifikan
"Diyanatu Adam".
Ras gabanta ya fad'i ta fara waige waige,to me yasa yike kiran sunana?
" ke diyah ,ki fita dayallah ki fita" cewan dalibai En uwanta
Mikewa tayi ta soma ratsowa cikin filin.
Harta qaraso gabansa ,kar6an wasu mukullaye guda biyu yayi a hannun bafadensa ya riqe
sannan ya soma magana a taushin gaske tamkar ance yayi dole.
Jinjina ya fara da yiwa makarantan ,sannan ya d'aura da "A maimakon fadan mai martaba, fada
ta baiwa wannan makaranta kyautan filin tsohon stadium na garin nan ,don yin makaranta mai
yalwa fisabillillah,kuma ni yarima mu'iz na d'auki nauyin ginin ,za'a fara daga ranar jumu'a
inshaallah.... Wani kabbara aka dauka amma kasa shiru ya cigaba,saida aka fara duka kafin
aka natsu.
"... Bayan hakan still dai,na baiwa daukacin yaranda aka yiwa yaye kyautan dubu Goma goma
da turamen atamfa da shadda,in mun tashi yanzu za'a shigo dashi kafin taro ya watse.
Sai kuma a qarshe a karan kaina na yiwa Diyanah Adam, kyautan makullayen nan guda
biyu,d'aya gidane kyauta ma iyayenta,na godiya ga barinta karatu da suka yi .
D'aya na motar da nazo a cikine ,kyauta ma yarinya ,kasancewar ta gwarzuwan shekara da
kuma kujerun umrah guda uku"
Hayaniya na bar muku my fans,koni na gigice musamman kyautar motarsa da ya bata,saboda
motar motace mai numfashi yau d'innan ya fara hawanta ,fakafakan mai kudi bai isa ya iya
hawanta ba.
Sunkuyar da kai baba mai hura tayi cikin tafukan hannunta ta fashe da kuka
"Ooh haihuwa mai rana,yau mun bar gidan gado zamu zauna gidan kanmu, yarinyar da tafita
cikin damuwar rashin anko,zata dawo da kyautar mota ,gida da kujerun Makkah?
Kasa godiya tayi saidai tayi shiru tana kallon makullan cikin tafukan hannunsa ,mika mata yayi.
A hankali muryarta na rawa " Nagode ranka shi Dade ,babanah yahanani kar6an duk wani
kyauta da aka bani don karatuna,in na kar6a zaneni zeyi"
Tana kaiwa nan ta ruga da gudu cikin dalibai
Murmushi yayi,yarinyar ta burgesa,tarbiyyan ta ya qayatar da shi,dama bata cancanci kar6an
wannan kyautan a hannunta ba.
Don haka aka kira babanta ,da kyar ya fito yina sumbatu,don yina cikin matsin talauci amma
akwai qana'a wa ubangiji
Shima saida aka matsa masa ya kar6a tareda jero godiya,kamar zai ari baki
Haka dai taro ya watse,kowa ka gani suna cikin farinciki
Hotuna kuwa har Wanda basu magana da Diyanah yau sunzo daukan photo da ita,baiwa kenan
daga Allah
**
Yarima d'aya daga cikin motocin En rakiyansa ya shiga ta kaishi gida.
Suna shigowa harabar gidan Gimbiya zulaikha ,na zaune can ta qarshen gidan ,karkashin wani
rumfa mai kamada bukkah ,an kawata cikin rumfar da carpet da tim tim na Alfarma,a kishingide
take kuyangi na marmatsa mata yatsun kafa ,wasu na mata firfita da hira,wanda rabi duk hiran
cikin gidan ne,suke kawo mata tsaigumi
Da Sauri ta miqe,suka saita mata takalminta tabi bayansa da Sauri, su kuma ta wuce suna
zind'enta
Dasauri ta saita kafadarta da nasa ,which a duniya yinason a girma masa.
Itakuma daukan sa take a banza tunda ta auresa
"Barka da dawowar shalelen yarima na"
Murmushi yayi mata na saman le6e ba tareda ya ce mata komai ba
Harara ta aika masa da saqonsa,inda sabo ta saba da mummunan miskilancinsa da har ita
matarsa yike gwada mata.
"Ga dukkan alamu cikin duhu akwai magana...Na kasa tantance hakan,wai shin mai ya
haddasawa mijina farincikine har ya shamakantar da idonsa wajen ganin Adon tauraruwar
ziciyarsa bare ya yaba?"
Ta watsa masa tambayar daidai sunkai gaban varendar part dinsa,da ya tsaru tamkar ginin
bankin zamani.
Juye mata daqwadaqwan idanuwansa na gado yayi akanta ,ya qare mata kallon sama da qasa
sannan ya shige qasaitaccen falon ,ba tareda ya tankata ba,ya nemi wajen zaman sa na
dindindin ya zauna ,yina furzar da numfashin huce gajiya.
Itakuma da Sauri tazo tana kwance masa nad'in kansa
"Cikakkiyar matan aure,takan sadaukar da komai nata don farin cikin mijinta,ko kanaso kace
min na rasa wannan daman matsayin ne a zuciyarka yarima na?"
Qasaitaccen murmushi ya jefeta dashi ,mai halshen damo,hakan ko a take yasa gabanta
fad'uwa
"Kyakyawar rayuwa daga yau ake mata tanaji, kuma cikakken uba shi yike Samar wa ,zuriyarsa
uwa ta gari Wanda zasuyi Alfahari da ita tun anan gidan duniya har zuwa qiyamah,tafe Nike da
wannan ma'anin a koda yaushe"
Murtuke fuska tayi tana hararan iska
Sannan ta fara magana cikin inda inda
"ban ..ban fahimcekaba Prince, kardai kace min ka sake d'ebo kiya da karashin da kasa ba
rakatowane,masu son 6ata maka suna da sarautanku"
Fuskarsa ba yabo ba fallasa
"A'ahfa zulaikha kiyiwa bakinki linzami ,nadade INA umurtanki da Wannan ,kuma shi sha'anin
Aure hada shi
Ake tundaga sama"
Had'iye wani malolon takaici tayi da qyar.
"Me kake nufi? So kake kace min auren yaran mutane zaka sake yi, kwana kad'an su Mace?"
"Lokaci shi zai gwada mana hakan zulaikha"
Eaidu kum Kareem
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: *Jinin Sarauta*
61 - 65
_Don Allah kuyi haqury banson karya Alqawari ,kunsan hidimar sallah mutane ,basu bani
damaba,lokacin da zan maku kuma darene ,ba chaji dan Wanda na samu dashi nayi maku
typing..._
"Amma yarima..." Dakatar da ita yayi da hannunsa
"Ammmm inason in huta" sosai ranta ya 6aci tayi masa qur da ido
Ganin hakan yasa ya had'e hannunsa guri guda don yayi mata fifitan maganan da ya sossoka
mata "Don Allah dai"
Murmushin yaqe tayi ta tashi ta fita
**
Shiru yayi cikin tashin hankali bayan farka wa da yayi daga wannan mummunan mafarkin.
Itadin dai ya hango cikin wani irin surquqin baqin daji ,ga wata yarinya can da bazata wuce
shekaru ukuba,tana miko mata hannu tana kuka .
Itakuma ta kasa qarasawa gareta ,saboda baqin Aljanin da ya kamata yina ciccijeta.
Da qarfi take qwalla kiran sunansa "yarima...yarima Mu'iz ka ceci jinin ka!"
Rashin makama yayi,gadai ita a hannun Aljani yina cizonta,ga kuma yarinya a can nesa
bakowa tare da ita tana kuka,to wa zai kama?
Kurum sai ya tsinci kansa da afkawa aljanin da duka,waigowa yayi a zafafe kamar zai
mazgesa,saidai yina dumfarosa sai wani tartsatsin wuta ya ringa fitowa a ranqwalelen zoben
Azurfansa yina nufar jikin Aljanin ,wannan shi zaisa ya kauce a kansa ya qara shaqo ta,ita din
dai.
Kuka still takeyi tana nuna masa yarinyar ,kamar an kimsa masa a baki yaji ya fara jero Ayatul
kursiy,in yakai ya dawo ,kafin ya kai qarshen na biyun ,saiga Aljanin ya falla da gudu.
Itakuma yarinyar sai gata ta tako zuwa inda suke duka,a take ya rungumesu cikin farinciki
"Iyalina ,kune Alfahari na"
Daganan ne gigif ya farka,zufa na tsatsafo masa,dukda sanyin AC dake huda d'akin
A hankali ya shafi zoben hannunsa "Royal ring" ya fad'a a hankali,kawai sai ya miqe,daga cikin
blanket d'in ya qara jibgawa zulaikha dake gefensa,sannan ya fad'a toilet don d'auro Alwala
,saida ya fito ya shimfida sujudah kafin,ya waiga ya kalleta ,ta dad'a qudundunewa a ciki da
alamu sanyin dakin ya soma yi mata yawa.
A hankali ya taka ya rage acn sannan ya tada sallah Nafila,cikin sujudansa yina roqon
masu,haihuwa shi da zulaikha, a gefe guda yina rokon Allah ya bayyana masa hasken da ke
cikin lamarin watannan yarinyar har aka kira sallan subahi
Sai sannan ya tashi bayan yaji qarfi a ransa,ya je yayo wanka ya wuce masallaci ,bayan ya tada
ita ta hanyar zungurin qafarta da hular hannunsa
Tsaki taja ta juya ta d'ayan 6arin ,ranta na suya ,ta tsani wannan d'abi'ar wai don yayi alwala
shikenan bazai ta6eta ba? Humm!
"Ki tashi lokacin sallah yayi,nasan kina jina" ya fad'a cikeda gadara,kafin ya juya ya barta cikin
6acin rai
**
Bayan kwana uku En murna sun gama zuwa yiwa su Diyanah da iyayenta murna,sai kuma
batun komawa sabon gida ya taso,da fari fir baban yace bayi komawa wai shi talakane,in ya
koma wannan gidan 6arayi suka biyo sa me zai basu?....Saida En uwa suka tarun masa kafin
ya yarda ya koma ,mota kuwa ,ya barta a cikin makarantan su Diyanah har wannan lokacin ba
aje an d'akko sa ba.
Sun tare lafiya ,Diyanah ta cigaba da zuwa makarantan bokonta ,Agefe guda kuma tana
qoqarin shiga Assanawiyyah(Islamic secondary).
Katsaham saiga malaminsu har gida wai In ba damuwa ,Diyanah zatabi d'alibai aje fada ayi
godiya .
Mutseke ido baban yayi yina tsiya "Haba kar amaida mun yarinya kamar Amalanke mana...su
sauran d'aliban En uwanta ba mutane baneba? Suje su kad'ai ko dai saida ita saboda ga
fatararru an bamu kyautan gida?"
Haquri sukayi ta basa suka juya suka tafi,a gida haka yayi ta fad'a kamar zai ari baki ,kowa tayi
shiru suka zabga tagumi suna saurarensa ,saida ya idar din kansa kafin Diyanah tace
"Toh Abbah kayi hakuri, nima ko sunzo ra'ayinmu dayane ,bazani ba"
"Yawwa er Albarka jeki d'ebomin ruwa a buta inyi Alwala" take anan fuskarsa ya washe ya fara
fara'a kamar ba shiba
Saida ummanta ,baba mai hura taga wucewarta kafin tace "Malam ,kar mu zama butultattu
mana! ,aidai ko,munci arziki tunda gamu cikin wannan tamfatsetsen gida Albarkacin
tabarraki,sai don Ance aje godiya ne zakace sunyi ma ba daidaiba,? Bayan mune nan yafi
cancanta da muje d'in ?..."
"A'ahahh kinga dakata! Dakata! Kinaso yarinyar ki taita yawo bad'ad'a kenan gidan sarakuna,ke
bakisan illan hakan ba ko? To diyanah ba maroqiya bace da zasu fake da 'ya'yanmu suna zuwa
maulah"
"Ya ilahiy♀️Malam maulah kuma? To shikenan Allah shi gyara"
Da Sauri yace "amin" kafin ya qwalla ma diyanah kira "Wai ruwan yaqi d'ebuwane?"
Da gudu ta taho