Author : Hassana Bamalli Oum Aphanan Category : Read Hausa Novels
business yanzu suke ciren huge task ? In ba haka ba I see no reason matarka zata wahale ta fice hayyacinta har haka....”
“Topah wata sabuwa! Ni banci bashin kowa ba ,haka zan mutu salin alin,in kwanta kabarina ba zullumin bashi ya jamun rataya a kabari ,don kinsan musulunci ya tabbatar da cewa duk wnada ya mutu ana binsa bashi Mala'iku rataye shi zasu yi a kabari bashi ba samun niima sai an biya masa....”
“Dallah yimun shiru ,irinkune kuma ranar lahira ake tula maku tarin iliminku a ka tamkar jaki da kaya.... kwatankwacin ilimin da ba aiki dashi kenan...”
“Innalillahi shiyasa akace matayenku da ƴaƴan ku fitina ne ,fahajiruhum! Ku kiyayesu!.....yanzu gashi tana nema ta hardasa mun rashin jituwa tsakani na dake ...me tace nayi mata ? Hajiya? Nasan dai mun rabu dake lafiya”
“Batace kayi mata komai ba ,but allow your woman to breathe....” _President Bola tinubu's quote_😆
“Au yanzu na shaƙe mata maƙoshine? Taja numfashinta daidai kyauta ne daga ubangiji...mata tana rayuwarta daidai Ni banga ma aibunta ba amma tunda na aureta taja mutane nata gallaza na da magana....”
Komawa tayi kan kujeran da take kai tayi relaxing
“Ashe ma ba nice na fara fada ba.....Huuhhhhh (She sighs) ynz dai ina buƙatar dubu ɗari biyu”
Gabanshi ne yace ras!!! Da sauri ya kame ƙirji “Dubu ɗari biyu kuma ? Me zakiyi da marga_margan dukiyar nan?hectan Fili ne kike son ki sake siya?”
“Kana haukane? Dubu ɗari biyun ne zai siya mun fili? To tunda ka tambaya,so Nike in bawa salima ,atleast zata siya wasu abubuwa datake da bukatar su... ”
“Mama😳In Baki dubu ɗari biyu ki baiwa Salima...dubu ɗari biyu fa? Hmm tirƙashi to wannan dubu ɗari biyun zai siya mun wata sabuwar saliman. Ras Zan biya sadaki inyi hidimar biki in auro wata macen sabuwa fil a leda da dubu ɗari biyu....”
“Ehoow yanzu na gano inda ciwon yake....wato a wancan karon auran gata akayi maka ,tundaga sadaki ,gaisuwar uwa da uba ,lefe ,muhalli abincin taron biki komai yin maka akayi shiyasa baka ɗaukan ta as worth as she deserves...........Miqdad ?! Zaka bani 200k ko bazaka bani ba”
“Hum hum mama don Allah mubar maganar nan don Allah”
“Miqdad I'm deep in serious ,bazan taɓa barinka ka tafi ba wlh tallahi sai ka bada kuɗin nan”
Ɗaura hannu yayi aka “Wayyo Allah na shiga uku! Hajiya kiwa girman Allah ki bar maganar kudin nan🥹 ,wallahi zuciyata na zafi zaku ɗaura mun hawan jini...😔”
Salati ta fara yi tana masifa cikin Muryar kuka “Ya Allah mijina ya azabtar da zuciyata da maƙo🥹 na jure ina addu'ar kar Allah yasa wani cikin yarona ya biyo halinsa ....amma cikin rashin Sa'a gani Allah ya bani kai miqdad😭” kawai sai ta fara sharce hawaye
Ga furgice Ya Sheikh ya sakko daga kan kujera yasa gwuiwoyinsa a ƙasa shima kamar zai kuka
“Kiyu hakuri karki mun kuka in ɗaiɗaice...na yarda zan bada amma ki mun uzuri ,in bada dubu ɗari ɗaya don Allah🥹🙏🏻”
Ɗauke fuska tayi ta miƙe taje ta buɗe diary dinta ta ɗauko acc detail dinta ta ajiye masa
Jikinsa na rawa ya kwashe ya tura mata 100k ,idonsa jajajir ya kalleta na tura hajiya”
Ƙirrr taji shigan kudin asusun ta ,tsaki taja ,ta koma wajen messages tayi copyng account Number din Salima ta tura mata duka . Tana turawa ta kira ta
“Hello sannu hajiya” ta dauki wayar cikin Muryar barci
“Ayyah sannu ƴar nan na tasheki kina barci ko....nasan gyaran gidan nan ba sauki sannu ko? Da sannu komai zai daidaita har mai aiki zaki samu ,yanzu ki duba wayarki na turo maki dubu ɗari kya rage wasu hidimomin....”
Wani ihun murna tayi “Hajiya dubu ɗari? Duk nawa? ”
“Eh karki manta da maganar mu kinji ƴata, sannu da ƙoƙari Allah ya baki ladan haƙuri”
Har Hajiya ta kashe wayar Salima na zuba godiya ,fuskarta taf hawaye
_Allah baka bani dacen miji ba ,amma ka bani dacen suruka ,ko anan I thnk You God_
Hajiya dawo da kallonta tayi kan ya Sheikh da ya gurfana kamar Almajiri sai zufa yakeyi ,duk ya buɗe botiran gaban jallabiyarsa ya cire hulan kansa sai fifita yake da hulan
Dukda fankokin da suke ta gudu a ɗakin amma zufa yake tsatso masa .
“Tashi na sallame ka”
Ta masa magana cikin tsawa
Zumbur ya miƙe“To Hajiya Nagode Allah ya huci zuciyarki"
Ya fice sunsunsun,ai yana shiga mota ya daddage ya kurma ihu
“Wayyoooooooooo🙆♂️”
Its Oum Aphnan
#BAD BOYS
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki...*_
_*It's #500 Regular*_
_*09065990265*_
022
____________________
Salima!
Salima!!!
“Ina zuwa🏃♀️” ta dirkako da gudu daga saman benen zuwa bakin main door din ta sa key ta buɗe ƙofar .
Muryarsa yayi rauni sosai kamar abun tausayi ,sam bata iya magana da ƙarfi “Haba Salima kina sane na kwaso rana amma kika barni a gantale duk maƙota sunaji ina kiranki ki buɗe ni”
“Ya Sheikh Alal aƙalla sau biyu ka kirani”
“Yawwa kina kal kal da baki kamar reza iyayen gaddama,ana magana sai kin bada amsa Ni ban hanya....washhhhh” yaje kan kujera ya zauna ya saki tumbi a gaba ya goya hannunsa akan tumbin yana karkaɗa ƙafa in readiness to battle with Salima.
“Har ka dawo daga gidan maman?”
“Hum ki bari kawai ,mama tana da ban dariya ɗan ciwon kai sai tace zata tafi ganin likitan ta a Cairo ,Kamar mai tsoron mutuwa ko yanzu tayi booking new appointment fa Ni bansan wannan abun na menene ba ,ke jiya kinga tana da alamar ciwo?”
“ha'ah jikin girma ne fa Ai sai tana maintaining health status dinta ,Abun da tayi abune me kyau gaskiya”
Ɗaga murya ya somayi cikin masifa masifa “Zakice haka mana , tunda ta fara koya maki yanda ake asarantar da kudi unnecessary..”
Sarai ta Gane a ƙunba yake don haka tace “Allah ya baka haƙuri ,kawai mubar maganar” ta juya zata haye stairs Abinta
“Ehen Salima!” a gajiye ta waigo
“Na'am sheikh”
“🫵🏻Wannan kudin da mama ta tura maki ,ki ƙara adana su da kyau a account dinki kinji”
“Ban gane ba🤨me yasa? ”
“Eh mana🤗 Duk wata sai ki ringa biyan kuɗin wuta da kudin ruwa a ciki da siyan en kayan miya da su maggi ,mu gani ko zasu shekara bai ƙare ba?!”
Daka tsalle tayi ta fara diddirke ƙafafuwarta a ƙasa “Kambu ,ai wallahi bazan yarda ba ,wannan kudin kudina ne kyauta ta bani ”
“Habawa en matana😆Nine fa sheikh dinki...yanzu mama ta Baki har dubu ɗari bazaki tayani hidimar gida ba? Ai da kai da kaya duk mallakin wuya ne ko ba haka ba?"
Soror ta tsaya tana kallonsa cikin tsananin mamaki
Sake washe baki yayi ,sai yanzu ya samu sa'idan zuciya da yaga kudinsa basu tafi a banza ba ,cike da nishadi ya sauke hulan kansa ya ɗaura akan Centre table ,ya saki hamma gami da miƙa.
“Yawwa me kika girka mana?”
Wasu mugayen harara ta shiga tunkuda masa harda murguɗa baki .
Murmushin mugaye yayi irin na saman leɓen nan ,ya mike da sauri yana cire boturan wuyar rigarsa
“Uhm bari inje in duba da kaina tunda hajjajuna fushi take sani,bansan wa ya taɓo kan jirgin ba”
A yanda take tsaye ta rafka tagumi tana kallonsa ,ta zurfafa cikin tunanin yanda dubu ɗari zai ishi dogayen bills ɗin nan da ya faɗa har na shekara guda....kenan maimakon sauki kudin nan tsanani ya kara mata
To kodai in roƙesa ya bani account number ɗinsa ne in maida masa kudin sa in tsaya yanda Ubangiji ya ajiye Ni?
“Hmm ban Account Number dinka kawai in maida maka kudin ka cigaba da hidimarsa,kar ka saka Ni a ciki ma!”
Zuwa yayi ta bayanta ya riƙo cinyoyin hannunta ya ɗaura kansa a kafaɗarta
A kunne ya raɗa mata
“Habawa matar Sheikh ki barsu a wajenki atleast nasan wainnan budget din na gama dasu ko?"
***
Washekari Sheikh cikin ujila ya fita zuwa aiki ko 8 na safe ma bata ƙarasa ba ,saidai yana fitowa ya tuna yayi mantuwa da mukullan Office ɗin don haka da sauri ya faka motarsa a gaban gate din gidansa ya fito daga cikin motar zai juya cikin gidan da ƙafa
Adnan da fitowar sa kenan ya hango ya Sheikh da sauri ya ɗaga masa hannu
“Salamu Alaikum....salamu alaikum”
Cak ya Sheikh yaja ya tsaya yana tunanin wani taimako kuma za'a bukaci yayi a safen nan
“Wohoho Allah bacin tara gashin gemu kwarjini ne kuma Kayan samun ladane matsayina na Ahlus Sunnah ,wallahi da na ɗebe shi na aske nima ina rinƙa tsutsukewa ina shiga kamar ɗan iska ɗan iska haka nan dai...na tabbatar mutane ba zasu taso Ni a gaba da neman taimako ba...amma ynz ko nasa jeans da shirt gemun nan zaisa asan Ni Sheikh ne"
Da wannan zancen zucin da yakeyi har Adnan ya cin masa
Wani ƙamshin deaigners din turare yaji masu tashin kai da mugun tsada ,wow ga masu barnatar da dukiyar da ilahu ya basu nan😕
“Sannu ko?😃Na dade ina son mu hadu mu gaisa amma ku malamai ahlul ilm ,ba zama uzuri yayi maku yawa”
Jinjina kai yayi “Haza haƙƙun...(wannan gaskiya ne)”
“Sunana Dr Adnan sabon maƙocinka...”
Kurrrr yaji cikinsa ya yi kuka
Ohkoo shine makocin da Salima take mun gori a kansa ?
A kasalance ya miƙa masa hannu don su gaisa
“Sheikh miqdad inkinya Abu_sumayya”
Washe baki Adnan ya sakeyi ,yana jin hannunsa na masa raɗaɗi saboda yanda ya Sheikh ya matse masa hannu da ƙarfin tsiya kamar zai karyasu.....mugu yaji hannun butters da suka saba cin daɗi ,jiki duk madara😉😆
“Sannu Abu_sumayya ,wallahi kayi Sa'a Allah ya albarkaci ƴaƴanka da zasu zo da uwa ta gari....Plz ka cigaba da kyautata mata kaji Sheikh?”
Sakaka ya saki hannunsa ba tareda ya karye masa yatsunba kamar yanda zuciyarsa ta sallaɗa masa mugunta .
“Bari inje ko? I'm off to work ,sai anjima” ya juya ya soma tafiya hannayensa suna soke a Aljihu yana bubbuɗawa irin tafiyar matasan nan masu fama da Giyar kuɗi.
Sakin baki yayi sakaka kamar sakarai har saida yaga shigansa mota ,kana yahau ɓaɓatun iska “Dallah ji sakaren nan,yenyenyen uwar yaranka mace ta gari ce ,ina ruwanci? Banza kawai !....mune za'a koya mana kula da mace ? Muda muke tafiyar da iyalan mu daidai da fiɗratul Islam !!!”
Oum Aphnan
#BAD BOYS
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki...*_
_*It's #500 Regular*_
_*09065990265*_
023
____________________
Yareema
Motar Yareema ita kaɗai tal ,take sharara gudu a biya kwaltar cikin garin ,ba motocin masu bashi tsaro yau fitan daga shi sai Amintaccen yaronsa Jabeer ,shine ma yake tuƙasa a motar shi yana ta baya ,idanuwarsa kar akan kwalta baya ko ƙiftawa,Kai daga ganinsa kasan yana cikin damuwa amma yanayin fuskarsa da fushin sa da baƙin halinsa na dindindin yasa mutane basu gano tashin hankalin da ya ke ciki ba.
***
“Waziri,wannan fa ba abu bane da zamuyi shiru mu ƙyale ya cigaba da faruwa ba,Yaron nan Yareema kowa tsoronsa ma yakeji ,kenan mu bazamu tsawata ba ,har sai ya zama yayi riƙan da ya ƙwace a ikon mu...?...bazai yiwu ba!”
Waziri kallon Galadima yayi da yafi kowa fusata a cikin taron manyan fadan,wanda suka taru a gidan wazirin a safen nan don tattauna matsalar Yareema da yake neman Gallazar kowa a gari.
“Galadima! Na fada maka Yareema fa baifi ƙarfin mu ba ,kawai muna bi ne a hankali ,saboda en gaza gani...kuma ma ai bamu isa muja da ikon Allah ba,in Allah yasa Yareema zai sarki babu ja...in Kuma baida rabon sarauta ,tijaransa da Izzarsa bai isa ya bashi ba”
Ciroma da sauri ya amshe maganar da cewa “Muma ai ba ja da ikon Allahn muke ba ,amma gasky ɗaya ce daga ƙinta kuma sai ɓata .....kowa yasan Yaron nan Yareema Asalinsa fa soja ne,kenan mulkinsa zai zama mai zafi,kowa yasan mulkin soja akwai tsanani talakawa nashan wuya....Shi yasa Ni ɗabiunsa basa bani mamaki ,yana da gautsi sam ! Baya mulki irin mulkin sarautan babanshi....In fa yana ran gadi ,da bindiga yake yawo!!! Waziri wlh! Idan Yaron nan ya zama sarki ba mutane ba mu kanmu kashinmu ya bushe...”
Galadima katse Ciroma yayi da cewa “Don Allah mu tsagaita maganar nan,ynz dai ina mafita? Kunsan cewa dai sauratar nan gadonshi akeyi tun iyaye da kakanni bawai zaɓe akeyi ba ,don haka Yareema shine kaɗai ya cancanci hawa gadon mulkin nan ,to mu tayaya zamu tunkuɗe faruwar hakan?...”
A fisace Fagaci ya katse shi “Ban yarda da maganarka ba Galadima ,mu ne masu naɗa sarki ,mu muke da damar ɗaura sarki ,in muka soke mu din nan ta soku...don haka Yareema bazai zama sarki ba da wannan ɗabi'un nashi gwara ma ku sauya tunani”
Ciroma ɗaga ma Fagaci hannu yayi “Yi hakuri Fagaci nasan kana da zafi,Amma ga mafita"
Kowa gyara zama yayi yana kallon Ciroma
“Tunda dai mu ba ƙwace masa sarautarsa muke son muyi ta ƙarfi ba...ina ga me zai hana mu haɗa kan mutane suje su sameshi su tattauna a masa nasiha ya daina abunda yakeyi ba”
“Ehen kaji batu mai kyau,naji dadi da kuka gane ba abu mai sauki bane mu tunɓuke Yareema a kujeran ubansa ba......to tunda Ciroma ka kawo wannan shawara mai haske ina ganin abunda za ayi mu tsaida ranar da zaka shugabanci mutane kamar bakwai ,aje wajen Yareeman ayi masa magana gemu da gemu” cewar waziri
Yaƙe Ciroma ya soma yi “Wannan abu yayi kyau sosai wlh....saidai wani hanzari ba gudu ba ,kasan dai Ni matafiyi ne ,zai iya yuwuwa ranar da za'a yi meeting din bana nan,kawai dai waziri kaine shugaba inaga kawai ka jagoranci zaman dole ya saurareka”
“Haba meye haka ? Aini ba tsaranshi bane ,saidai tsohon sarki da yana da lafiya tabbas shine zan sama kai tsaye amma yanzu da tsufana sai aga naje Ina ma Yaron nan magana haba ai baiyi ba...duk gakunan,Fagaci,Ciroma ,Turaki ga galadima ,a cikinku za'a fidda wanda zai jagoranci zaman dole!....” tsuru tsuru sukayi da ido kowa yaƙi magana. Wannan yasa waziri harzuka
“Shiknn a matsayina na waziri na zartar Galadima yaje ya magana da Yareema ,tunda dai shine mai ilimin fada kuma akwai baki,tunda ai ɗan jarida ne ,nasan muna da kyakyawar wakili....”
“Yawwa haka ne kuwa mai girma waziri” duk sauran suka amsa
Girgiza kai Galadima ya shigayi ,yana karkaɗa ƙafa daga kan kujeran da yake yana faman hura hanci har saida yaji sun natsa da Hayaniya sannan yayi gyaran murya
“Hmm kazaɓo wanda zai iya cin zarafin Yareema kuwa....amma kasan sai Ni Galadima ina da mugun fushi ai ko?ta yaya zakace inje in samu yaran nan da bashi da kunya bayan kasan ina da fushi...?So kake Yaron nan ya fada mun magana in Yi fushi in kakkarya shi? Wallahi in yanemi mun rashin kunya ɓaɓɓalashi zanyi ,sai na kashe shi a ƙarshe ace Galadima ya kashe magajin masarautarku...” kallon juna sukeyi suna caɓe baki irin tabi ta farkon kunni ta fita a ta hagu
“Waye yariman ? Yariman banza da wofi... Ni ba sai in kashe banza ba..”
“Kai don Allah ka dame mu da barazana ,Dukkan mu tsoro ke ɗawainiya damu,kowa sai....sai...sai....” kasa ƙarasa maganarsa yayi saboda hango motar yarima da yayi ta shigo harabar gidan wazirin
Yanda bakinsa ya kama rawa yasa kowa waigawa yana kallon ƙofa....Tsit sukayi tamkar ruwa ya cinyesu ,Turaki kam hannu yasa ya kanƙame kujeran da yake kai ,sai maimaita duk addu'ar da yazo bakinsa yake yi a zuciya ,wani irin gumi yake tsatsofa masa....tsoronsa ɗaya kar yarima yaji maganarsa sanda yake masifa n Nan
Jabeer yana faka motar ya fita da gudu yaje ya buɗe Boot ya kinkimo dankareriyar kujeran royal Amma mara nauyi an masa adon gwal. Ya taho gaban tsofaffin ,ba tare da yayi masu magana ba ,ya kafe kujeran a gabansu
Sannan ya sake runtumawa da gudu ya bude gidan baya,cikin tafiyar ƙasaita ya shiga takowa inda suke yana tafe alkyabbarsa na sharar ƙasa.
Da wani irin Almighty murya ya ke masu magana a daidai sanda yake tunkaro inda suke zaune.
“Duk na fahimci dalilin taruwarku a nan wajen....Sbd Ni ne ...Ni...Ni sarkin ku” ya kare magana yana zama a kan kujeran gabansu jirim kamar namijin zaki.
Yanda ya zauna jirim da ƙarfin Allah saida kaf gabansu ya fadi ras!
Oum Aphnan
#BAD BOYS
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki...*_
_*It's #500 Regular*_
_*09065990265*_
024
____________________
Turaki mutsirtsuke ido yayi cikin jan rai yace “Eh sabda kaine! Yareema mufa iyayenka ne,Amma ada garinmu na zaune lafiya sanda kake wajen aikin sojanka a ƙasar waje shekaru uku baya amma tunda ka dawo komai yayi tsanani ..... Adon haka Bazai yiwu mu zuba ido muna ganin abunda ke faruwa ba,mutane daga wasu daulolin suna zagin masarautarmu sbd kai tun asali,to bare kuma ace masu kaine Sarkin...”
Komawa yayi luu ya kwanta akan kujerar mulkinsa ,kana ya lumshe ido cike da ɗagawa ,ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya
Da wani sassanyar murya mara Hayaniya yace “Hmm haka ne kuma fa🤗Saidai zaɓi biyu Gareku ,kodai ku zaɓeni a matsayin sarkin ku ,ko ku soke Ni a matsayin sarkinku....” still idanuwarsa suna lumshe ba tare da ya buɗe ba har ya gama maganar
Waziri sassauta murya yayi “Yarona ba maganar zama sarki shine matsalar ba ,ka sauya halinka mu shine damuwar mu,bakajin abinda Turaki yace ne? Mutane na kuka da baƙin halinka...muma iyayenka bamajin daɗi wannan zubar kimarmu ne”
Ai yanayin shiru suka soma gungaguni dake nuna duk sunji daɗin yanda waziri ya gaya masa magana kai tsaye.
Yareema da idonsa ke kulle ,Gwale idanuwar yayi , yana kallon sararin samaniya ,yana sauraron gunaguninsu da baka iya fahimta ,
kana ya gyara zamansa da sauri , gamida ɗaure fuska tamkar bai taɓa dariya which defect Jeopardy
“Uhumm” yayi wani gurnani kamar naman daji
“Jabeer !!”
Ya Kira sunan yaronsa
Ɗan rusunawa Jabeer yayi “Allah yaja zamanin yarima”👍🏼
“Dakkomun Littafin Mutuwa!!!😡”
“Ok yarima na” ya falla da gudu ,zuwa wajen mota.
Diddilo idanuwa duk sukayi ,cikin whispering Galadima yake tambayar Ciroma ,meye littafin mutuwa kuma? Ciroma da yaji yana jin zawo ,watsa hannunsa a cinya yayi ma'ana bai sani ba ...duk haka suka cigaba da kallon kallo.
Har jabeer ya dawo hannun sa ɗauke da ƴar stool Kamar na ajiye cofee ,ya ɗauko wani fankacecen littafi Mai Kamar album ɗin hotuna ya ajiye akan ƴar stool din ,Saida ya saka handgloves sannan ya buɗe tsakiyar littafin.
Kyakyawar bindiga ne er ficila ,duk sukayi tozali dashi a cikin littafin an ɗaura bindigar a saman farin ƙyalle.
Sa hannu Yareema yayi ya ɗauki bindigar yasa tsinin