Author : Hassana Bamalli Oum Aphanan Category : Read Hausa Novels
,abun na bashi haushi amma baya iya daurewa.....”
“Mun gode Adnan ,Ina maka fatan samun mace ta gari kwatankwacin Salima ta ”
Ta juya da sauri ta dauki hanyar gidan Salima ba tareda ta sake waigawa ta kalli Adnan ba ,tabbas ta tausaya masa ,rashin masoyi ba daɗi ,soyayya da matar aure ai masifa ne
A sarari take cewa “Bari Saliman ta warke zan ja mata layi akan wannan makocin nasu ,tunda dai bayi da matar da zasuyi zumunci to ta kiyaye masa , musulunci bai yarda da zumunta tsakanin mace da namiji ba ba”.
Oum Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki...*_
_*It's #500 Regular*_
_*09065990265*_
034
___________________
2 weeks Later.
3pm
Ya sheikh daga office suka dawo gida tare da Ambassador ,bisa Matsawar Ambassador lallai dole sai yazo yaci girkin Salima ,bayi da zaɓi sai ya kawo shi ko ya yarda ƙwallon mangoro ya huta da ƙuda .
Salima ta ƙuƙe a kichin tana girki ,Adnan yazo gaban ƙofar ya fara knocking a jere Mazan suka amsa da “Yes come in” dararas ! Gaban Adnan ya faɗi Amma bazai iya juyawa ba don haka ya murza handle ya shiga hannunsa niƙi niƙi da kaya .
A ɗarare ya masu sallama, Ambassador da be waye shi ba ya amsa with a broad smile “Zo ga waje ” ya nuna masa kujera ,shikam Ya Sheikh yanda kasan an aiko masa da saƙon mutuwa haka yayi kicin kicin da rai .
Washe baki yayi yana ƙaƙalo dariyar yaƙe “Weldon bros ,ya aiki ya gida”
“Lafiya kalou ”
Sosa ƙeya yayi kamar maijin kunya kana ya maze “Plz Ina Salima...” kafin ya karasa magana Ya Sheikh ya kwatse shi da hargagi da tashin Hankali
“Gata nan a bayana ” Adnan ba hausa ,baisan baƙar magana ba ,sai muskutawa yayi yana leƙen bayan ya Sheikh
Ya Sheikh dukan gadon bayansa ya shigayi da tafin hannunsa “Kasan yarinyar goye ne zo ka cireta...naji mun bala'i uban me kake nema a wajen ta ,eyyeh jarababbe?”
Ƙiƙƙifta idanuwa Adnan ya shigayi ,shidai yasan masifa yake amma bafa ya fahimta ,sai ma Ambassador ne yake bashi baki haba Now,daga zuwa neman matarka sai zagi? Ina laifin wanda ya damu da naka?.."
“Sharaff...”
“Food is readyy...” Salima ta fito tana faɗa cikin barkwanci tayi gayunta da ɗaya daga cikin kayan da Adnan ya Bata ,tana ganin Adnan zaune da manyan jakuna a gabansa tasan ba lafiya a sanyaye ta cigaba da sakkowa,daga matakalen benen
“Dr kaine ? Amma ynz ka shigo ko?” ta masa magana da larabci a sanyaye kamar tasan ana tsaka da cin masa mutuncine.
Gyada mata kai yayi fuskarsa kadaham kadaham
Miƙewa yayi ya cicciɓi madaidaicin jakan gabansa ,ya miƙa mata
“Happy wedding anniversary...Allah ya ƙaro zaman lafiya a aurenku ya baku zuriya masu Albarka these are the little gift I can offer...” ya nuna mata tarin kayan da ya zo dasu bayan ɗan madaidaiciyar jakar da ya bata
Cusa kanta tayi ta leƙa ,agogone na mace da namiji iri ɗaya sai wani box ɗin ɗan kunni da yarin gold”
Ihun murna ta fashe dashi “Yeeeeh ta runtuma gaban Sheikh tana nuna masa gift din da aka basu tare dukda sauran masu nauyin batasan ko menene ba amma basu wuce sutura ,don shine abinda Salima take ƙaranci.
Ba kunya ya Sheikh ya washe baki “Kamfanin Rolex ne ko me? Kai wanann agogo da ɗaukan ido yake ,ya akayi kasan yau ne ma ranar....” buge masa hannu ambassador yayi ,wanann yasa ya Sheikh shiru yana zare ido .
Waigawa Salima tayi ya kalli Adnan “Ya akayi kasan yau anniversary dinmu?”
“A IG Naga post din hotunan bikinku” girgiza kai tayi cikin jimami yana tuno mata da memories.
Kauda kai yayi “Bari inje ko?🤨”
“Aah no abincinmu a table tare zamuci duka” Ambassador ya karɓe da sauri.
Ya Sheikh ji yayi kamar ya kashe Ambassador don haushi ,zaija a cinye masa abincin da yayi budgeting zasu ɗumama da safe,in yayi ragowa.
“No Yanzu na dawo daga Office inaso inje inyi wanka"
“Aah kaga ka dawo da empty stomach kenan ma...” ambassador ya cigaba da insisting
Da sauri ya Sheikh yasa hannu a gefen cinyar ambassador ya manna masa mintsini wanda yasa Ambassador zabura
Sarai Adnan da Salima duk sun lura da halin da ya Sheikh ya shiga ,don Adnan ya gama gane Sheikh ba ƙaramin zumbuli bane ƙarewar rowa.
“Bari inje inyi wankan zan dawo” Ya amsa tayin Ambassador da gayya ,yau saidai in yaci abincin Ya Sheikh ya hadiyi zuciya ya mutu.
Oum Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki...*_
_*It's #500 Regular*_
_*09065990265*_
035
___________________
Yana fita Salima ma ta juya cikin ɓacin rai ,ta rasa wanann wani irin rowa Allah ya jarrabi mijinta dashi,mutum ya kashe maka maƙudan kudi ya kawo maka kyauta kai da matarka amma kai bazaka iya bashi dama yaci lomar abinci a gidanka ba? Allah yayi mana tsari!
Ƙumewa tayi a bedroom Taki fitowa ,sai hawayen nadama take ɓulɓulo mata ,ada tana ma ya Sheikh tunanin shiriya amma wanann yasha mata hankali.
***
Ambassador waigawa yayi ya kalli ya Sheikh
“Amma kaidai bakayi ba wallahi bakayi ba...ka kwafsa!”
”Ban gane ba, kuma me nayi ?”
“Wai date ɗin bikinku ma ka manta sai wani bare yazo ya taya ka celebrating ,ka zageshi yabaka abu ba kunya ka karɓe,Kuma still kana so ka hanashi abincin gidanka ,anya nima kuwa ba cika maka ido nayi ba ,kan dole zaka barni inci?”
“Ji wani magana dai? Inda banso kaci abincin sai kuma in ɗauko ka da kaina?...kawai bana sonsa ne,jinin mu baizo daya ba ,banason yanda yike shishige ma Salima ,ka kalli yanda duk ta wani damu ,ko baka lura fushi ba tayi ta barmu? Shiknn yau ya siya mata kaya gobe sarka gaba-daya yana nema yasa Matana ta fanɗare mun ”
“Ohoo kace ga inda ɓarakar ta taso kenan...to yanzu shawarar da zan baka maza muci abinci muje kayo mata shopping da ya ninka kudin nasa sau uku,ka haɗa mana kayattaccen party anjima da dare ka gayyato shi da matarshi yazo ayi danashan Arziki ,na tabbatar zaka burge Salima ,shima kuma zai gane ka damu da matarka kuma kana farinciki da rayuwar auren ku”
Tunda yake magana ya saki baki galala yana kallonsa ,har yakai karshe
“Gaskiya ban taɓa sanin ƙwaƙwalwarka bata ja ba sai yau! ,Kawai saboda kar a zargeni sai in asaran kusan miliyan guda takan Salima?! Haba...haba ba gunma in buɗe mata shago ba ma”
***
Ya Sheikh knock yayi a bedroom dinta ya shiga da kaya niƙi² a manyan baƙaƙen leda masu zanen fari ,ciccike da ɗinkakkun Atamfofi da lesuka .
Sayyida a hankali ta amsa sallamarsa ciki² ,sbd har ynz bata huce abinda yayi mata ba.
“Matata sayyida...bazaki iya zuwa ki amshi mijinki ba?”
Miƙewa tayi fuskarta ba yabo ba fallasa taje ta amshe ledan hannunsa ta ajiye akan gado ,masu kirtanin laces irin na matan zumuntan da da ake masu ɗinkin riga da zani(Ciki da alaku) ta ga set ɗaya ya faɗo
“Meye wanann kayan waye?”
Tana nuna masa kayan tana caɓe baki kamar zatayi amai
“Naki ne mana,set biyar na shiga gwanjo na siyo maki ,kinsan gwanjon Kayan atamfofin nan da lesukan nan sirri ne dasu ,kayan matan masu kudine sai suyi dinki susa sau daya biyu su ajiye mu kuma a kawo mana nan a farashi mai arha....ya kike gani in kika sa? Wow nasan zai maki kyau ,kuma za'a rantse da tsada kika cire kudi kika siya....”
Ƙuuurrr ta kafeshi da ido Saiga ƙwalla na Shirin zubowa
“Yanzu talaucina ,fatarana ,da rashin suturana ya kaima ka siyo mun gwanjon mama ta mutu!!!? Kayan da ake fitarwa na matattun mata shine zaka bani Ni Salima in sa?”
“Haba ke baki da wayo wallahi ,kaima tailor zakiyi ya rage maki carasras Zaki fito tas da ke ,duk wanda yace maki kayan mamata ake saidawa ƙaryane...bari fa ki gansu ƙila don A leda ne kike masu kallon tsofaffi tas suke da ƙwarinsu ”
Ya fara zazzago mata su a kan gado
Wani ihu tayi ta yi tsalle tasa hannu tana tunkuɗesu suna zubewa a ƙasa
”Aah karka zuba mun a kan gado”
“Meye haka sai kace kinga najasa! Suturune fa masu ƙwari da kyau”
“To Ni bana so ,ko ana dole ne ? Kai ka sa mana..Abu sai zuba wari yakeyi ,Ni har kaina ma ya fara mun ciwo ka fitar mun dashi!!” tayi magana da ƙarfi
Ɗaukan ɗankwalin atamfar yayi ya kanga a hanci “Wainnan kayan ne zakice da warrriiii” jan sunan warin yayi saboda yanda warin gwanjo ya daki hancinsa a take yaji ƙwaƙwalwarsa ta hautsina ,da sauri ya sauke a kusa da hancinsa.
“Aah maida dai ai bakaji komai ba shaƙa da kyau..” marairaice fuska yayi kamar zai rusa Ihu.
“Ai naji ...hummm hummm..na shinshina Ni banji komai ba ,rainuwa ne dai irin na matan zamani a ƙi maku kuyi ƙorafi. Ai maku kuma ku raina,Salima kin sauya wannan ba itace salimar da na aura ba”
“ya Sheikh Nagode ba sai ka fada mun ka gaji dani ba nima na gaji da wannan Auren ,da gatana ka ganni da Suturu na ,bazan zauna yunwa da rashin walwala ya zama ajalina ba kai daidai da kwanciyar aure bayi kake ba ,so kake ka jefani a halin zina?? Wani hakkin aure daya da Ubangiji ya baka kake iya saukewa fully ya sheikh ehmm ,a hakan ma fa ban fara ajiye ƴaƴa bane ba ,tun azo biyar kudin makaranta ya Sheikh inajin saidai su ƙare a public school,to zuwa yanzu mu haƙura ,Kar in cutar da kaina in cutar da yarana ,Suna da hakkin tarbiyya da ilimi a wajena , kawai aja layi daga nan kafin in fara maka kallon kaskanci mu haƙura da auran nan”
Maimakon ya nuna kakabi sai ma yayi Murmushi “Duk fushin nan saboda na siyo maki gwanjo? Lallai kina da high teste siyama ,bari in tattare kayana in maida a bani kudina"
“No ba don kaya bane Sheikh kawai na gaji ne, jiba ɗazu wai anniversary dinmu Saida Adnan yazo ya tuna muna...Sheikh wai auren dole akayi maka dani ne? Fadamun don Allah ko kuwa auren sadaka ne ,an maka talla na...to in ma haka ne yau na gaji zan bar maka gidan ka ka huta da ciyarwa daga kai sai cikin ka ,don na lura sarai tun da ka aureni rama kake yi ,saboda abincin da kake ci a da ,kamar shi dai kake bamu muke ci mu biyu saboda tattali da tsoron kar arzikinka ya kare”
Fuuuuu ta fice ,ta ɓamo ƙofar ɗakin
“Salima!
Salima!!”
0um Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki...*_
_*It's #500 Regular*_
_*09065990265*_
036
___________________
A Guje ta gangara zata fice daga gidan shikuma Ambassador ya shigo yana tsaye a gaban motarsa hannunsa riƙe da bottled water ya ɗan harɗe ƙafarsa yana waya cike da nishaɗi yana rausayar dakai yana shaƙar iskar wajen a hankali...Nikuwa oum Aphnan ɗinku nace hmm kaji masoya , ana ta baiwa Fulawa ruwa.
Yanda ta fito a hargitse tana wuri wuri tana Neman Hanyar barin gidan yasa ya bita da sauri
“Hey wassup”
Waigowa tayi ta kalleshi cikin dacin rai . A duniya ta tsani abokin miji mai damun mutane da yawan zuwa ,to shi wanann kuma mai ya dawo dashi ? Shikenan su basu da sukuni kenan?
Ɗan sakin dariyar yaƙe tayi “Ambassador kaine again?”
“Nine wlh ...humm ya na ganki kamar a firgice ? Saƙone zaki amsa?”
Kafin ta bashi amsa ya jiyo Muryar ya Sheikh yana takowa da sauri yana kiran sunanta .
Wurrrr ta falla da gudu tayi hanyar back yard ɗin gidan ,tabar Ambassador a tsaye ,yau ta ƙudiri aniyar sai ta bar gidansa kuma in ta tafi bata dawowa har abadan.
Mamaki abin ya baiwa Ambassador ,lallai ba lafiya ! Shima kafin Ya Sheikh ya gansa ya wulƙa yayi hanyar da yaga tabi .
Yana shiga wajen ya ga ta jingina bayarta da bishiyar barankace,tana bulbular da hawaye kanta a sama.
“Salimart menene?” in a speed motion like a twinkle of an eye ta sa hannu ta goge hawayen fuskar ta ,ta kuma daura da washe baki .
Kallonta yayi ga hawaye ga dariya “Humm kina da matsala...”
“Ban dashi”
Da Karfi ya amsa ta irin na mazajen nan masu bada Authority
“No kina da matsala”
“Yes ina dashi and it's your friend Kuma yau ko zaku kasheni sai gawata ta bar gidan miqdad ! Bazan sake zama dashi ko na sekwand guda ba”
“Is that what makes you to be running like a foolish rat? Calm down ok? I'll help you solve the problem ,you knw here too might not be secured to you ,as you know is his house ,iyaye zai kira maki su Baki baki,and dole ki hakura bayan an muku sulhu...” Zaro ido tayi
“What is the solution ?” kafeta da ido yayi yasa haƙorinsa yana jan leɓensa na ƙasa yana tsotsewa.
Cikin ƙaraji da ƙosawa tace “Plz what is the way forward ,I need to move desperately ,oh like.....” kawai sai ta dafe kai hawaye na sharara mata
Ɗaura hannunsa yayi a kafaɗarta ya ɗan cakumi naman kafadarta yana murzawa a hankali
“Sorry ok? Zaki bar gidan Sheikh kina da dukkan makamanki , yanzu zan saka ki a motana inja tint in ya gama karakaina up and down sai in tuƙaki mu tafi”
Kallonsa tayi kamar bata yarda ba sai kuma ta murguɗa masa Baki cikeda tsiwa “To ɗan bar kama mun kafaɗa”
“An bari sarauniya,wa ya isa ya bata ma tsaleliyar mace kamar ki rai sai maras rabo”
“Ban gane ba?”
“Eh mana ,Nifa na daɗe ina gaya ma Miqdad ya sauya zamansa dake in Kuma Bai iyawa to wallahi muna gefe kamar kuraye yana sakaci kika fito ,caraf zamu cafe...”
Dariya tayi saboda yanda yayi magana
“You funny hahahaha”
“No I'm not,Gwara in fara shigar da ƙoƙon barata ,tun yanzu kafin manema su Kunno Kai a manta da ɗan bawan Allah ambassador ,tunda na lura dramar nan naki da ya Sheikh yana dab da karewa to na ajiye appointment Zan dawo inyi spilling ,Dama muna ciki tun a wancan karon ,ya Sheikh ne ya riga mu....”
“Are You serious? Kallon da kake ma matar abokinka dama haka ne? To ko kai ka hanamu zaman lafiya dama can ? I already knw abokan miji a yawan lokaci su suke hardasa rashin jin daɗin zaman ma'aurata,in kuwa har so kake in fito don ka aureni ,to na gunmaci in cigaba da zama da Ya Sheikh ko banza zai feeding Dina da ƙira'ar ƙur'aninshi,in bai bani abinci na ƙoshi ba ...... unlike youuuuuu idonka akan mata .move jhorrr” ta hankaɗe masa kai ta fito
“Salima wait...wait...ki tsaya mana ,let me clear my self to you ”
Ko kallonsa batayi ba ,kawai ta juya cikin gidan ,wata zuciyar na gaya mata “Salima kafin ki tona sirrin zamanku da mijinki a duniya sit with him at first ,kiji meke damunsa ,me yasa yake da maƙo? Maƙonsa ya zarce na lafiya ya zama ciwo,me yasa baya sauke haƙƙinsa na aure a kanki....make some promises indai har yayi alƙawarin sauyawa a aikace gwara ki daidaita da mijinki da ki fito ƴaƴan mage suna farautarki (Ambassador and co. ) Saboda auren ki dai shine ƙololuwar mutuncinki”
Da wannan shawarin zuciyar nata ta koma cikin gidan ta ,saidai Ya Sheikh tuni ya fice ya banzama nemanta a gidajen en uwa da abokan arziki
Da gidan Dr Adnan ya soma ,ya fara dukan ƙofar na hauka
“Alhaji fito mun da ita”
Adnan da ya farka daga barci murtsuke ido yayi da ƙyar yana kallonsa muryarsa a doshe irin na masu barci yace “Ita wa?”
Tsawa ya doka masa “Kaiiiii ! ,Dont tell me rubbish . enough is enough fa,wlh in baka fito mun da matata ba hukuma ce zata rabani dakai ....banza baƙo kawai,kazo garinmu ka shiga cikin gidana kayi kane ²
Warass idonsa ya buɗe
“Dont tell me Salimart ta Kara ɓacewa for the second time?
Nunashi yayi da ɗan yatsa yana gargaɗinsa
“Wallahi summa tallahi,a wannan karon idan har Salimart ɓata tayi ,to kai zansa a kamaka kuma in tona asirinka akan halin ƙuntata mata da kakeyi,wallahi sai kayi gidan yari,adadin kwanakin da zata ɗauka ba'a ganta ba kai harma da surplus , shashasha kawai wanda bai san darajar matarsa ba ,ka tara gemu biya² ,dashi za'a jaka zuwa jahannama in bakayi wasa ba....banza illiterate”
Yanda Dr Adnan ya saki jiki yana ɗura ma Ya Sheikh magana ya tabbatar masa da Salima ma bata tare dashi ,don haka bai tsaya bi ta kansa ba ya kwasa da gudu ya bar gidan ya banzama gidan sister ta ,inda take sauka in tazo Nigeria.
Dafe ƙirjinsa Adnan yayi da sauri saboda yanda wani abu mai ƙarfi yazo ya sokar masa ƙirji kamar icce
“Shikenann zan rasa ta,Plz karki gujeni bazan iya jurewa ba Salima ,gwara inta ganinki a daga nesa matsayin matar Sheikh ,it will ease my pain ,akan ki haramta mun ganinki for life....oh goshh”
Ya zube a varendar dinsa cikin mawuyacin hali .
Oum Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki...*_
_*It's #500 Regular*_
_*09065990265*_
037
___________________
Ambassador kasa bin ta cikin gidan yayi saboda ko rufeshi tayi da duka dai shi ya siya,don haka ya gangara ya shige motarsa ya kame ,alkawari ya daukarwa kansa yau sai yaga abinda ya ture ma buzu naɗi
Ya Sheikh a uzzure ya shige gidan Anty tana zaune tana baiwa yarinyarsa cerelac ya shigo ɗakin yana haki yana wuwwurga ido
Dam! Gabanta ya faɗi ta ajiye bowl ɗin cerelac ta miƙe tsaye “Bro Lafiya?”
“Bata zo ba?”
“Wacce kenan?”
Kafin ya bata amsa wayarsa ta fara ringing ,Sunan salimatu yaga na yawo akan screen ɗinsa .
Dama haka yayi saving number Salima dashi .
Da sauri ya ɗauka “He..Hello Salamu alaikum ...kina ina?”
A sanyaye tace “Kai zance kana ina? Na bincike ko'ina nagidan ,You no where in sight ”
“Humm! Gani nan dawowa” Yana kashe wayar ya juya zai fita.
“Aah Bro, dakata wai meke faruwa ne?”
“Laaa bakomai😃Dama Dama wai mun rabu zata zo nan ne shine nazo in ɗauketa ,Kinga gashima tace mun ta dawo gida ,To sai anjima”
“Miqdad!” ras ! Gabansa ya faɗi
“There is something fishy a cikin gidan ka,I need to knw what is it”
“To fa🤔Ita