HASASHE KO BURI BOOK COMPELET PDF BY PRETTY SK.txt

Author :  Pretty Sk Category :  Tknovels

Chapter   8 / 12

21K to 24K   out of 34.5K words

wajen yayan bababmu, karatu ne ya haɗa ni da Rahma, kuma ina yawan zuwa gidan nan amma ɓantaɓa ganin ka ba.” ta faɗa harda wani ranƙwaɗa murya.

“Eh ban wani zama, ban numberki zan nema magabatanki dan jin ta bakinsu." Take suka yi exchanging number.

“Ya sunan Hajiyar?.” Ukasha ya faɗa sai ta ɗan yi murmushi sannan ta ce.

“Zuby, wato zubaida.” sai ya yi saving da haka sannan ya bar ɗakin. Yana fita Umar ya ce.

“Ke da muka yi magana a sirri, ai da sai ki min magana, yanzu ji yadda kika ɓa ta komai."

“Uhmmm ai shike nan, ƙawata zo mu shiga ciki.”

“Yamma na yi yaushe za ki wuce?.” ya kuma tamabaya ganin ko shiryawa ba ta yi ba.

“Sai gobe zan wuce, Baba nake jira.” ta faɗa tana shigewa ɗakin tare da kulle ƙofar.



“Ƙawata ya kika ganshi?.”

“Gaskiya Guy ɗin ya yi, ƙawata ina godiya.”

“Kinfi ƙarfi haka a wajena, yanzu dai da biyu na zo Abuja, dole muje wajen Mai sittin goma kafin na wuce."

“Gaskiya kam, nima ko kwalli ya ban dan na janyo hankalinsa."

“Sosai ma kuwa, ai wani bura-uban sai bayan auren, duk ki yi waje da sauran ki mallesa kaman yadda na mallake Abubakar, kinsa tin daga wancan lokaci har yau bai sake waiwayen familynsa ba, kuma suna can cikin wahala.” tafawa suka yi, dan tin da Zuby ta shigo hirar da suke yi kenan akan Ukasha, balle yanzu da Zuby ta gansa sai ta yi ya yi mata 100%.....



*KADUNA*


_Muheey_

Yau a gidan su ta wuni, ta sha faɗa sosai wajen mahaifiyarta akan rashin leƙosu da ba ta yi, dan rabon da su haɗu da Mahaifinsu ta manta.

“An ce ana ganin kina fita a motar Hajiya (Mariya), haka ne?." Mama ta faɗa tana kafe Muhibbat da idanu, haɗe fuska ta yi tana faɗin.

“Mama ashe har gulmata ake kawo miki, to dan ta a ramin menene a ciki, har mijin na ta ya sani ai."

“Hmmm ina raba ki dai, bansan wannan halin wallahi, ka tsaya in da Allah ya ajeka ya fi, amma ke tin kina ƙara akwai son rayuwar ƙarya, gidan nan dai babu abin da muka rasa amma ke sam mafiyinsa kike so."

“Mama dan Allah ya ba ka bashi kenan ba ka nema ƙari da mafiyinsa." Ta faɗa tana miƙa wa, ɗakinsu ta koma, a lokacin duk ƙanenta na Islamiyya, dama ita ta yi sauka, to ci gaban ne ya gagara.


*Merry*

Kamar yadda ta yi tsammani sai da Abbas ya dawo mata da wannan kuɗin, murmushi ta yi dan ganin alert ɗin sannan ta yi accepting kiran da yake mata.

“Babyna me yasa in na maka alheri kake dawomin da shi?.” ta faɗa tana zama kan fridge dan shigarta kitchen kenan.

“Malamata kenan, ni ya dace na miki ba ke ba, yanzu dai ba wannan ba, kinci abinci kuwa?."

“Gani a Kitchen dai, zan haɗa custard ne."

“To shike nan, haɗa zan ta ya ki sha.” murmushi ta yi sannan ta sauka, kashe wayan ta yi sai bayan da ta gama haɗawa sannan ta koma room ɗin ta, video call ta kirasa, duk da ɗakin nasu da haske amma ya yi dishi-shishi dan haka ya koma waje dan ya fi haske, hira suka sha sosai. Ita dai tana zaune ne kan babban gadonta, ɗakin komai pink colour ne dan shine favourite ɗin ta.

“Ustaz ɗina, yanzu da mun kammala karatu sai ka bar ƙasar nan! Gaskiya banso.” sai ya yi murmushi.

“Aikin ba tabbas domin wani Alhaji ne ya yi mana alƙawari, balle ni a gaskiya na fasa zuwa, insha Allah zuwa lokacin aikin hannuna ya yi ƙwari kuma ina samu, zai fimin da barin county.”

“Haka ne, domin a can ɗin bakusan wani aiki za ku yi ba."

“Aikin company ne."

“Okh, ni da kana son aikin soja dana neman maka."

“Soja a'a, nafison aikin hannu, amma Malamata in shi ɗin nasamu zanyi.."

“Zan ma hanya."

“Na gode, ki barshi kawa.”

“Baka so na ko kaɗan, komai na ce kai bai maka ba, shike nan sai da safe." Kafin ya ce komai ta kashe kiran, take yi offline, kiran wayan ya yi _witch up_ sai ya yi murmushi sannna ya koma cikin ɗakin na su.

“Ɗan soyaya an gama ƙonewar kenan?.” Shamo ya faɗa da sigar tsokana.

“Na lura kaf cikin mu babu wanda ya kai Abbas iya soyayya, mu na mu duk wasan yara ne."

“In na fika (I.B) iya soyayya ai sai an bugani a jarida, ni Bara na matso mu yi sirri, dan kuwa ina so ka ƙara koyamin kalamai sosai, na lura Ma'esh sai da haka." Abdul ya kai maganar yana dariya, sai a lokacin Abbas ya ɗan dafa kafaɗar Abdul yana faɗin.

“Hmmm Allah ya shirye ku, yauwa shamo ya maganar mu ne?." Sai Shamo ya ce.

“Don't worry mutumina, zamu ja maka attendance."

“Gobe hala akwai aiki sosai ne a gareji?.”

“Eh Abdul, akwai motar da za mu kai Kano, da asuba zan fita." Hira suka sha kamar kullum, wani suyi dariya wani kuwa su yi hayani akai, haka har suka yi barci.......✍️
END.

> Hmmmmm na yi shuru kawai.

🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚


✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕




💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!


PAGE2️⃣5️⃣⏩2️⃣6️⃣.


*KANO*


_Abubkar_
Yana kammala cin abinci sai ya tattara komai sannan ya koma ɗakinsa, kwanciya ya yi sannan ya ɗauki wayan nasa ya dasa karatun, shafin gaba ya shiga tare da ganin *FARIN CIKINA*

“Uwata ita ce farin ciki ta, idan har mutum na son faranta min to ya so ta, murmushin ta shine ƙwanciyar hankali na, sai dai kash, ƴan uwan na, na jini sun ruguza wannan farin cikin dake zuciyar Mahaifiyarta, sai dai ina fatan Allah ya isar mana tin a nan duniyar ba sai munje can ba, ya saka mana, da gatanmu amma muke rayuwa a wahale, amma muna cikin farin ciki sosai da sosai.......” daga haka ya ƙare sai ya sauke a jiyan zuciya yana mai ci gaba da duba na gaba.......



_Ameeratulkhairi_

Shuru parlour ya ratsa na tsawon lokaci mai yawa, sai a lokacin Mahaifiyarta ta saki wani ajiyan zuciya mai ɗauke da manufofi, kallo Ameeratulkhair ta yi sannan ta mata magana da hannu.

“Shike nan, amma ki kula sosai, ni dai banso daga fara aikin ki, ki bar gida ba, amma wannan ne burin ki ba zan shiga haƙƙin ki ba.” hawaye suka idanun Ameeratulkhair, sai ta rungumeta, take ita ma mahaifiyar ta fara kuka, sun jima a haka, daga bisani suka tsagaita sannan Ameeratulkhair ta wuce ɗakinta dan fara shiryawa...........


_Haidar_

Sallah magrib da Isha ne kawai suka fitar da shi daga gida, sai misalin 9:20pm ya fito daga ɗakin dan gaishe da Abban Haidar dan ya ji dawowarsa. A babban parlour ta riske Abban Haidar ya zauna yana shan ruwan da Maman Sumayya ta ba shi, bayan ya musu sallama ya zauna daga ƙasa yana faɗin.

“Abbana an dawo lafiya?.” sai ya yi murmushi Abban Haidar har haƙorin makansa na bayyana.

“Yarona lafiya lau lau, yana ga kaman ka rame?.” dan dattijon mai cike da haiba da kamala ya kuma faɗin haka, sai Haidar ya yi murmushi.

“Abbana ƙi ba ma na yi fa.” kafin ya ce komai sai ga wasu ƴam mata sun iso cikin parlour, sai wani yauƙi suke yi, akan kujera suka zauna suna gaida Abban Haidar.

“Abban Haidar an dawo lafiya?.” Take fuskar ɗan dattijon nan ya haɗe, sam su Safna ba su da tarbiyya shi yana sama suma haka. Safna da Sumayya taunar cwing gum suke yi. su dai suna kama a fizge amma ba da Abban Haidar suke kama ba, haka kuma shima Haidar ɗin sam ba sa yanayi, sai dai Haidar ya fi kowa na gidan ƙyau, daga shi sai Mahaifiyarsa.

“Uban wa kuke gaisarwa daga a gadarance?.” Haidar ya daka musu tsawa, dama sun sa ba basa zama inuwa ɗaya da shi. Miƙa wa suka yi maimakon su zauna a ƙara sai suka bar parlour suna ƙunƙunai.

“Abban Haidar (Haka ya yi umarnin kowa ya dinga kiransa.) ka ja ma wannan yaron ka mai kama da baƙin balaraɓe kunne, ya dena koran mana yara, sun zo su ji dubin mahaifinsu amma sai ya koresu." Maman Sumayya ta faɗa tana ɗan jijjiga.

“Ke ba ki ga abin da suka yi ba.” Abban Haidar ya faɗa, tsaki ta ja tabar parlour, sai ya girgiza kansa sannan ya ce.

“Yaro na, gobe ne tafiyan ko?.”

“Eh." Ya faɗa yana jin zafin tsakin da ta ja ma Abbansa.

“Shike nan, ka je ka huta, da safe kafin ka tafi kazo na ganka, sannan na turo maka da wasu kuɗaɗe, salan ka dawomin da shi, dan mai kai sam baka ɗaukan shaware ne da aikin companynka ka dawo yi, ka bar wannan aiki.”

“Abbana ai nama alƙawarin zan amsa sai bayan wannan aikin, Aikin jarida buri na ne, sannan aikin da kake magana akai wannan burin Abban na ne, kuma duk zan cika."

“Shi yasa nake alfahari da kai, yanzu kar na jaka da magana, je ka kwanta." Rabuwa suka yi kowanne cike da soyayyar juna. Yana shiga ɗakinsa ya kwanta akan babban gadonsa, Company haɗa motoci na H - Halal Company na Abbansa ne wanda a zahiri Abban ya mallaka mai, zai fara zuwa soon, dan sanya Abban Haidar farin ciki. Amma kafin ya fara ya so a nemo mai abokin aiki amintacce sosai.

“Gobe zan ma Abba magana insha Allah.” ya faɗa dan ya tina ya so ya faɗa mai amma yake mantawa..........✍️





*ABUJA*

_Ukasha_

Washegari weekend babu office, dan haka da misalin 4:30pm ya nufi gidan su Fillo, yau shi kaɗai ne dan Umar ya fita zuwa kasuwa. Bayan ya aika wani ya kirata, ba ta ɓa ta lokaci sosai ba, ta fito sanya take cikin hijabi har kasa ɗan kaɗan ake iya hango zanin amatamfar da ke jikinta, baƙi ne hijab ɗin sai ya ƙara haska fatar da sosai, fuskar ta ba ta bayyana ba sosai saboda ta jawo hijab ya rufa rabin fuskar, bayan ta yi sallama ya amsa sannan cikin yaran fullancin ta fara gaishe da shi sai kuma ta sauya harshen ta dawo hausa amma hausar a gurbaci take.

“Ina yini?.” sai dai bai amsa ba, kawai kallonta yake yi, a karo na farko ya ji wani iri dangane da ita, shi bai ta ɓa jin irin wannan yanayin da game da mace sai yau, kuma ya ji zuciyar sa ta buga, karo na farko kenan a rayuwarsa da ya ji mace ta shiga ransa, ba wai dan cika burin sa ba, sai da ya ɗan ja lokaci kafin ya ce.

“Ina lafiya lau. Ke fa?.”

“Alhamdulillah." daga haka bai ƙara cewa komai ba ita ma haka, karantar natsuwar ta ya ke yi sosai kuma ya fahimta tana dashi, can sai ta ce.

“To zan koma gida ka gaida su Mama.” da sauri ya ce.

“To shike nan na gode da lokacin ki amma kin amince za ki aure ni a haka?.” sai ta dago take fuskanta ya bayyana sosai, ƙandarewa ya yi da kallon fuskarta, wani murmushi ta ɗan sakar mai, sannan ta nufi cikin gida har da haɗawa da sauri-sauri, sai ya saki murmushi dan ya lura kunya ce ta mata yawa, motan ya shiga sa'annan ya nufa hanyar gidan su ƴar yarbawa dan a jikinsa yake jin watan aurensa ya matso.

Tana shiga ta ga Dada am na wanki da sauri ta amsa tana ce wa.
“Laa ba na faɗa maka zan dinga yi ba.” ta kai maganar ta zama daga gefe tare da ɗaukan sabulu ta fara.

“Ya kun sasanta? (On waɗi laawol?).” Dada am fa tambaye ta. Sai ta yi murmushi.

“To masha Allah, Allah ya nuna mana lafiya? (Masha Allah, Alla hokki no fayde e jam?).” da sauri Fillo ta miƙa tana shigewa ɗakin, girgiza kai Dada am ya yi tana faɗin.

“Ameen, yaro sai kunya, kai Fillo fito nan mu yi magana." Tasan ba ma za ta fito ba sai anjima kuwa.


*****Bayan ya sauka a mota nan ma aka mai sallama da Ashake, ya jima a tsaye kafin ta fito, ta haɗe fuska sosai, dan wani zani ma ta yafa, kun dai san yaruba, Allah ya so dan ta gama wanki da ba za ta fito ba. Sallama ya mata ta amsa tana ɗan sakin fuskarta.

“My name is Ukasa. I came because I love you. Please… will you accept my love? (Suna na Ukasa ne. Na zo ne saboda ina sonki. Don Allah, za ki amince da soyayyata?).” sai ta ɗan yi murmushi, ta yi soyayya da maza uku hausawa kuma duk sun yaudareta.

“Sir, I don’t even know you. And honestly, I can’t marry a Hausa man — you people have attitude. (Ranka ya daɗe, ban san ka ba. Kuma gaskiya ni ba zan iya auren Bahaushe ba — ba ku da hali).”

“But I’m not Hausa. (Amma ni ba Bahaushe bane.)." Sai ta kallesa tabbas bai yi kama da bahaushe ba.

“Oh really? Then who are you? (Da gaske? To, kai wane ne?).”

“I’m Djerma."

“Hmm, okay… I’ve heard you. I’ll think about it. (Hmm, to shikenan… na ji. Zan yi tunani).” sai ya ji daɗi a ransa sannan ya kuma faɗin.

“Uhmm, but there’s just one thing — something small I need to say first. (Uhmm, amma akwai ƙaramin abu guda da nake so in faɗa.).” ya faɗa yana mai jin da ƙar ta yadda.

“ Alright, I’m listening. (To, ina sauraronka).” sai da ya sauke ajiyan zuciya sannan ya ce.

“I believe in marrying four wives. May Allah make it easy. But I’m telling you the truth — if that’s a problem for you, I understand. (Ni ina da burin auren mata huɗu. Allah ya sauƙaƙa. Amma na faɗa miki gaskiya — idan hakan zai yi miki wahala, zan fahimta.” zaro idanuwa ta yi tana cewa.

“Four wives?! Hmm... May God guide you. Honestly, go find someone else. I’m the jealous type — I can’t handle that. (Mata huɗu?! Hmm… Allah ya shiryar da kai. Gaskiya, ka nema wata. Ina da kishi — ba zan iya ba.)” sai ya marairaice fuska.

“Please, My Ashake, help me reconsider. (Don Allah Ashake, ki taimaka ki sake tunani).” furzar da iskan bakinta ta yi ta ce.

“Okay… I accept. But just to be clear, the other things — no hidden issues, right? (To… na amince. Amma fa dai sauran abubuwan babu wata matsala, ko?)

“No, everything is fine. A’a, komai lafiya.)"

“ Then go and speak to my uncle. Bye. (To, ka je ka yi magana da ƙanwata/uncle ɗina. Sai an jima.)" Wani nishaɗi ya ji sannan ya ce.

“Thank you so much for your time. (Na gode sosai da lokacinki.)." Hannu kawai ta ɗaga mai tana shigewa gidan nasu, saboda murna har buga jikin motarsa ya yi, yanzu mace ɗaya ta rage Bahaushiya, kuma yana fatan ya yi dace, domin kuwa watan gobe insha Allah zai auresu dukkan. Mota ya data yana mai barin layin......✍️
END.

> Ukasha Fatan nasara, saura Bahaushiya hmmm akwai bura-uba, ga dukkan alamu Asheka ƴar Yoruba akwia masifa, Fillo bafullatana akwia kunya, ita kuma Zuby Kanuri 🥺 bin Boka,hmmmm ko wacece bahaushiyar oho?.
> Haidar kai kuma haka gidan naku yake, toh Allah ya ƙyauta wasu dai akwai hassada.

> Abubakar sannunfa Darling ba ta gida ka zamu yadda kake so, amma fa Darling ba ta ƙyauta maka. Mu dai zuwa. Daga littafin *HASASHE KO BURI* by PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️.

🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚


✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕







PAGE2️⃣7️⃣⏩2️⃣8️⃣

*KADUNA*

_Abbas_

Abbas da ogansu suka nufi Kano dan kai wata mota, tin asuba suka fita saboda mai motar na jira, dan Alhajin ya shigo Kaduna ne motar ta samu matsala, sun isa da wuri dan kuwa motar lafiyayya ce sosai. Da isarsu gidan Alhajin, aka umarci su jira yana zuwa, a dai-dai lokacin Haidar ya fito daga part ɗin sa cikin shigar manyan kaya ya yi ƙyau sosai, sannan ya ɗauko trolley wanda ya zuba abubuwan da zai buƙata. Har ƙasa suka gaishe da Haidar sai ya yi murmushi yana dafa su da faɗin.

“Injin miya (Haka yake kiran Ogan Abbas) ban so, ko Abbana bason wannan gaisauwar yake ba, ya Kaduna?”

“Alhamdullilah.”

“Sir good Morning." Abbas ya faɗa sai Haidar ya miƙa mai hannu suka gaisa.

“Morning, kai ma Injin miya ne koh?.” sai ya yi murmushi ya ce.

“Eh muna ta ɓa wa.”

“Allah ya ƙara jagora, bara na shiga zan fito da Abbana ɗin.” daga haka ya yi ciki, su kuma suka bishi da idanu.

“Kasan waye me wannan gidan?.” Ogan Abbas ya faɗa.

“A'a Oga.”

“Kasan H - Halal Nigeria Motors?.”

“Oga waye bai san wannan Company ba, ai yawancin daga can ake kawo mana kayan aiki.”

“Haka ne, to wanda muka zo wajensa shine mai wajen, wannan kuma da ya wuce shine babban ɗan sa, kuma ma'anar H- Haidar Halal Motors.” zaro idanunwa ya yi, yana ƙare ma gidan kallo, tabbas tin shogowanshi ya san mai gidan nan ya tara sosai, dan motocin dake gidan baya iya ƙirgawa.

“Ashe yau zanga wannan Attajirin."

“Aikuwa, shi yasa na tawo da kai, na aminta da kai sosai, kuma na yadda da kai, shi Alhajin yana neman na turo mai yaron aiki na guda 1 tak, amma bansan dalili ba, sai dai kai na za ɓa, duk da ba komai ka iya ba, amma hazaƙanka ya na min sosai.”

“Ogaaaaa na gode.” Abbas ya faɗa yana rungume Ogan sa.

“Kai sake ni, ka bari ya fito dai, tare zamu koma sai bayan wata biyu zaka dawo domin zuwa lokacin ka kammala karatun ka.”

“Haka ne, dan yanzu shirye-shiryen exam muke yi." Tare suka fito suna tafiya a tare cike da nishaɗi, yadda kasan wasu abokai, haka suka jero har wajensu.

“Ina kwana Alhaji.” suka haɗa baki wajen gaisasa, da murmushi ya amsa.

“Har kun kawo kenan, da yake wani zan ba mota kuma yau yake so, shi yasa na ta doku."

“Allah sarki, yanzu dai mota ta gyaru sosai.”

“Yauwa haka ake so, ina ɗayan maganar na mu?.”

“Alhaji gashi nan, sunnan

8 / 12