Taj ɗin bai ma san da maganar ba.” ya kai maganar yana mai jin babu daɗi.
“To yanzu menene abin yi?.” faɗin Shamo
“Karku damu, ba sai an ce muku ba kunsan waye I.B.” sai suka ɗaga mai kai, sun san tsab zai ji da komai.
*Ma'esh*
Bayan fitar Abdul, Ta koma cikin gida murna fal ranta, Maman Ruma ta samu zaune a babban falonsu sai ta ƙarasa tana faɗin.
“Ruma an samu na cin bisciut.” Ruma dake kwance kan cinyar Mamarta ta ɗago tana kallonta. 10k ne ya Abdul ya ba ta da ta bawa Ruma duk da ita ce ta tura mai 20k daren jiya.
“To Allah ya biya, ki ce ƙanwata kin ɗauko mana babban mutum, Ai Alhamdulillah, yana da ƙyau haka kuma ga alamun za mu huta da shi, Allah ya taimake sa da kun kammala karatun ya ta fi aikin a U.S.”
“Aunty ai aiki na ƙasa, takaddun suke jira kawai.” cike da alfahari da faɗa. Aunty ta yi murmushi, sannan ta kwashe kuɗin da Ruma ta ajiye a gefen Auntyn.
*Muheey*
Bayan ya wuce, tattare komai ta yi, sai a lokacin matar gidan ta fito wato Aunty Mariya.
“Na ganshi ta window lokaci da kuke shigowa, gaskiya ma sha Allah kawai.” murmushi ta ɗan yi sannan suka ɗan hau hira sama-sama.
*Merry*
Farin ciki fal ranta, domin yadda Abbas ya shiga parlour na su, ya dinga ɓoye-ɓoye akan kunya yake ji, haka suka gaisa da Hajiya da Babban yayanta kuma Alhamdulillah bayan ta fiyansu sun ce ya musu, sai dai za su bincika halinsa. Daga haka ta koma ɗakinta dan wani nishaɗi take yi saboda haka. Sannan awaran ɗazu ya mata daɗi. Wayarta ta ciro tare da tura mai kuɗi 20k amma ta san zai dawo mata dasu......
*KANO*
Washegari misalin 11:30am, yana shiga wani office in da ya tabbatar mutanen da ya umartar suna ciki, sai bayan da ya shiga suka gaisa da kowa sannan ya zauna, take aka buɗo ƙofa aka shigo, wani matashin saurayi ne da bai huce 26yrs ba, yana sanye ne da ƙananan kaya wanda suka ƙara bayyana jikinsa na ƙarfaffen namiji, hannunsa na ɗauke da system da kuma wayarsa sai wiyansa da ya ke ɗauke da igiyan da ya riƙe camera, yana duhun fata kaman baƙin balaraɓe, Allah ya mai ƙyau sosai. Faɗaɗa murmushi ya yi yana magana cike da dakewa, bayan sallaman da ya yi suka amsa.
“Sir Good morning, a min uzuri da arean mu ana gyaran titi, to motata ma ta maƙale na barta a can.” daga mai kai Abubakar ya yi yana mai kallan ƙofa, da aka kuma shigowa.
Ita ce ta shigo, kamar kullum haka yau ma shigan na ta, dogon hijabi dari blue, niƙaf ɗin ta ciki ta ɗaura haka kuma hannunta suna sanye da handglobe, ƙafanta kuwa ko hangensa ba ya'a yi balle a san me ta sanya amma daga gani shima a rufe yake. Kowa na ciki kallonta suke da mamaki ganin ta shigo hannu kawai ta ɗaga musu sannan ta zauna. Haidar dake tsaye jikinsa babu laka, dan daga ganinta zuciyarsa ta tsaya cak, take ya kuma tina ɗazu.
****Motarsa bayan ta maƙale, shine ya fita tare da canza hanya, napep ya samu ya ko hau, a ciki ya same ta zaune tana latsa wayanta. Sun ɗan jima suna tafiya sai ya buɗe baki ya ce.*
*“Baiwar Allah a ina za ki sauka?.” sai ta yi shuru, rufe idanunsa ya yi sannan ya buɗe, ya manta sharp ya fito babu kuɗi, kuma akwai wasu a mota shima ya manta da ya ɗau ko 5k ne, kuma mai Napep ya ce ya fi son cash, abin haushin har ATM ɗin na mota. Ƙara kallonta ya yi yana kuma ce wa.*
*“Zan iya miki transfer ki ban aron ₦500 naira.” shuru ta yi dan yau sam ba ta san rubutu da ta rubuta mai. Take mai nepep ya faka, ganin a dai-dai in da yake aikin ne yasa ya ce mai yana zuwa, ko bayan da ya dawo, sai mai nepep ɗin ya ce.*
*“Ai matar nan ta biya ma, dan ma kayanka na ciki ne da na wuce.” murmushi ya yi yana kuma bashi 1k ɗin ya ce.*
*“To ka ƙara Nagode.” cike da nishaɗi ya wuce, shima ya shige cikin station ɗin.******
Zama ya yi yana mai ayyana ta ya ya zai mata godiya, amma sam bai ji daɗin sharesa da ta yi ba, haka kuma yanzu ya ga tashigo amma ba ta yi magana ba.
“Ta burgeni sosai.” ya faɗa dan yana da yaƙinin ba matar aure ba ce. Take Sir Abubakar ya fara abin da ya haɗa su, duk motsi sai ya sata kallon, kuma har ga Allah wani yanayi na musamman yake ji akan ta. Bayan ya ɗau 20mnt yana bayanin sannan ya jero musu tambayoyi tare da ce wa kowa ya rubuta yanzu, take mutanen da ba za su ce 15 ba suka hau note, ciki har da ita. Bayan lokacin amsa ya yi ya amsa ya yi tare da ba Haidar daya duba dan shi bai yi ba saboda yadda yake da ƙwarewa sosai. A take ya duba sannan ya fitar ma kowa da marks, a na ƙarshe ya tsaya, ya rasa ganewa shin da rubutun da abin da aka rubuta wanne ya fi sanya sa mamaki, rubutu kaman zanen inji, haka kuma duk abin da yake tinani akan in da an ce ya rubuta to su zai rubuta to a wannan har da ƙari. Domin a abin da aka yi da wanda aka kalla za ka fitar da tambayoyi tare da amsa su. 100% ya sanya mata yana kallon sunan Ameeratulkhair. Kamar kar ya ba da dan ya shagala da kallon sai da ya ji murya Sir Abubakar.
“Are you done?.” sai ya miƙa mai. Take ya duk wanda ya kira sai ya bashi har aka kira Ameeratulkhair, cike da natsuwa ta miƙe ta isa gabansa amsa ta yi, ta koma ta zauna.
“Duk wanda ke da mark sama da 80% ya zauna sauran kuwa ku je zan nemeku anjima. Take duk aka watse sai ita kaɗai. Mamakine ya kamata dan ita ba ma komai ta rubuta ba amma wai ta ci 100%, ganin su uku suka rage sai Sir ya mata alama da ta dawo gaba, ba musu ga dawo set ɗin dake gefen na Haidar.
“Bara na ɗauko abu a office.” daga haka ya yi waje, ajiyan zuciya ta sauke tana ta karanto addu'oin dake kan leɓanta.
“Madam nagode da biya min kuɗin mota da ki ka yi.” sai ta ɗaga mai kai, ganin haka ya kama kansa, ko da Abubakar ya shigo, wani video ya kunna musu suka mai da hankali sosai. Bayan ya ƙare ya ce.
“Muna da gurare 8 na musamman wanda kuma in muka samu ɗaya a ciki to zamu iya cin wannan gasar, sai dai a yanzu wasu gidan tv sun diran ma wasu.” take ya ɗan basu labarin yadda tsarin yake.
“Hakane in babu damuwa zuwa gobe sai mu fara namu binciken.”
“Shike nan Haidar, Ameeratulkhair kin yi sa'a daga zuwanki za ki hau aiki, fatan a gida za'a barki?.” sai ga ɗaga mai kai.
“Yauwa, to Haidar ka ƙara mata explain akan yadda tafiyan yake.” sai ta ɗaga hannu, kallonta suka yi dukkansu.
“Kina da magana?.” ta kuma ɗaga kai. Whiteboard ɗin dake gefe ta nufa tana ɗaukan maka ta fara rubutu.
“Na yi bincike akan gasar nan, kar mu tsaya a iya wa'innan saboda kowa da su suka dogara, gurare 8 ne, kuma abubuwan wajen suna kamanceceniya dan haka a ciki akwai masu ɗaukan iri ɗaya, ina babu damuwa a nema a wani waje na daban wanda hankalin mutane ba zai kai wannan ba, kuma na wannan gidan Tvn zai zama na daban thanks." Daga haka ta koma ta zauna. Abu ne ya ishe Haidar kuma shi baya ɓoye duk abin da ke ransa.
“Baƙya magana ne?.” ta ɗaga mai kai, sai suka kalla juna amma ko kaɗan ba ya ganin idanunta.
“Haidar bebiya ce ita.” Abubakar ya faɗa yana ɗan jin wani abu a ransa.
“Ayya shi yasa na miki magana ɗazu baki kulani ba kenan.” ta kuma ɗaga mai kai, lumshe idanunsa ya yi yana mai jin wani yanayi na daban. Abubakar kuma waya ya ɗaga yana faɗin.
“Alhamdulillah Darling, ya gidan?.” basu ji mai a ke ce ba sai dai take fuskarsa ya sauya sannan ya ce.
“Shike nan sai kin dawo?.” ya kashe kiran wai ace sai da ta isa Abuja take kiransa akan ta je gidansu..........
END.
> Hmmmm soyayya, toh fa da alamun Haidar ya kamu, kuma shima Sir Abubakar ya harbul..... Ko yaya tafiyar za ta kasance oho......
> I.B sannu da ƙokari. hmmm wato ke Maman Ruma, Abdul ya muku za ku huta 👍🤗.. Mai kunya kai ma sannau *Abbas* . Sai ku ma sauran sannunku. Jama'a akwai ƙura muje zuwa....... By PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️.
🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕
https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t
*_HASASHE KO BURI_*
_SADAUKARWA_
*🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).*
You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪
🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!
PAGE1️⃣7️⃣⏩1️⃣8️⃣
*ABUJA*
Ukasha yau cikin farin yake sosai, domin kuwa Baba am ya amince da shi, sai dai bai san ko ita Fillo za ta yadda da burin sa ba, ya ji daɗin yadda yaga Baba am ya sakar mai fuska, sai dai yasha tambayoyi sosai, kuma dukka ya amsa. Parking ɗin da Umar ya yi yane yasa ya kalla Umar ɗin ya ce.
“Ya mun iso ne?.”
“A'a, a yanzu idan na samo wacce ta yi, to sai ka fara ganinta, to na samu wata Yaruba, dan haka zuwa za ka yi ka ganta, na yi bincike akan ta sosai, sunan ta Ashake amma na ainiyi, Bilkisu, shekarunta 21, ta kammala HND wanna shekaran, ana suke sai da abinci sannna gidansu na farkon layin dake bayan namu." Sai Ukasha ya jinjina kai.
“Ka yi aiki me ƙyau, bara na ganta, akwai tuƙwicin da zan ba ka." Numfashi Umar ya sauke dan shi har ga Allah komai da yake ma Ukasha tsakani da Allah ne. Sauka Ukasha ya yi yana mai isa wajen da ake siyar da abinci, kafin ya isa ƙamshin fatan wake ya cika sa, sai a lokacin ya tina bai san ma mai suke siyarwa ba. Yana isa wajen ya yi sallama, sai wata wacce ke gefe ta amsa tana miƙe wa daga gaban murhu, a kallo ɗaya yasan ba ita ba ce Asheka dan wannan za ta girmesa ma.
“Alhaji, mi za ki siya ne." Ta faɗa da hausarta mara ma'ana.
“Wake da bread.” sai ta ɗaga mai kai.
“Ashake Ṣe o fi ounjẹ sí (Zuba mai abincin)." Take wata budurwa ta miƙa daga zaunen da take, hannuta na ɗauke da huƙa alaman yankan wani abu take yi. Kallon tsab Ukasha ya shiga mata, daga in da take tsaye ya kimanata tsayinta, dai-dai wadaida take, ba ta haske sai dai colour ɗin ta mai sheƙi ne, sannan tana da jiki ba laifi. Tabur dake wajen ta buga, sai ya dawo duniyar nan yabar kallon ta.
“ To, bani take away. (Ó dájú, fún mi ní take away).” ta fa ɗa cikin yaren, matar ta miƙa mata.
“Sir, for how much?.” sai ya sosai kai sanna ya ce.
“Beans for 1k than 1 bread." Zuba mai ta yi a babban take away sanna ta kalla shi tace.
“Sir, which bread? Choose one?." Sai ya ɗauka Jovard bread.
“₦220." Sai ya ciro a pocket ɗin sa. 3k ya ba ta sannan ya ce.
“Please can i have your digit." Ɗago idanunwa ta yi ta wurga mai kallo, sannan ta miƙa mai canjin sa.
“Please." Ya kuma faɗa yana rage murya.
“Sorry Sir, me za ki yi da shi?." Sai ya yi murmushi.
“I want."
“See you next time." Ta faɗa tana zama bayan ta aje mai canjin kan table. Wucewa ya yi, yana shiga mota ya kalla Umar ya ce.
“Insha Allah, Burina yana gab da cika, ta yi min sosai, amma ba ta ban number ta ba."
“Zuwa dare zan samo maka domin nasan yayanta." Rumgumesa ya yi yana cewa.
“Kai Umar ka biya ni, gaskiya nima zan taimaka maka akan wannan number, zamu samo ta insha Allah." Da mamaki yake kallon Ukasha dan bai faɗa mai ba sam.
“Hmmm, an faɗa ma kai kaɗai ne kasan ni sosai, nima nasan naka kuma nasan irin gwagwarmayar da kake yi akan ta." Sai Umar ya yi murmushi suna barin layin.
**** “Gakiya yaron ya yi, me yasa ba ki ba shi ba number ba?, (Ọmọkùnrin náà ti pe, kí ló dé tí o kò dáhùn nùmbà rẹ?).”
“Uhmmm Hausa ba abin yadda bane. (Uhmmm, èdè Hausa kò rọrùn.)” Sai matar ta yi murmushi tana cewa.
“Wannan ne bahaushe? Ai da Balarabe yake kama. (Ṣé èyí ni Bahaushe? Ó dàbí Bàláràbì gan-an.)” ta ɓe baki Ashake ta yi tana canza hirar.
“Ni dai barni, aramin wayarki. (Èmi, jẹ́ kí n gba fóònù rẹ.).”
“Amsa. (Dáhùn.).” ta miƙa mata, amsa ta yi, tana zama tare da ci gaba aikin da take yi tana kallo a wayar matar Yayanta, ita wayanta ya ɗauke......✍️
*KANO*
Driver ya ɗauke ta har zuwa Abuja, gidansu ta shiga, wanda ta kwana biyu ba ta zo ba, ba ƙarya gidan ya ƙara jan kuɗi, fitowa ta yi tana mai gyara vail ɗin kimono wanda ta sanya, ta yi ƙyau sosai, dan gida ta zo shi yasa ta yi wannan shigar amma har ta gaji da shi, shiga baban parlourn ta yi wanda ya ƙawatu sosai kaman ba ɗakin iyayen ta ba.
“Aunty Aisha, kin iso ashe?.” sai ta ɗaga mata kai, kusa da ita ga zo ta zauna tana faɗin.
“Ya hanya?.”
“Lafiya lau, ina Boy yake?.”
“Ya tafi makarantar.” a kallo ɗaya za ka ga suna kama sosai, sai dai akwai shekaru a tsakanin su, Aunty Aisha ita ce babba a ɗakin sai ƙanin Umar sai ƙaramar su Rahma, sam Rahma ta fita zakka a cikin su, domin kuwa tana da wani irin halaye marasa ƙyau, A'isha ita ce kaɗai tasan halayen ta na ɓoye, da fari zargi take amma a yanzu ta yadda. Rahma tun lokacin da ta kammala karatu ta haɗu da Abubakar, shike nan duk ta haukace musu, cikin ikon Allah kuma ya aure ta sai dai me Rahma ta rabasa da kowa, shi kansa yanzu ya mance su waye dangin sa, rayuwa yake duk yadda ta juyasa kaman motar da ake control, a haka ma auren dududu shekara ɗaya ne da ɗan watanni.
“Rahma kin iso." Su ka ji muryan Hajja, da sauri ta miƙe tana isa kusa Hajja sannan ta rungume ta.
“Hajja ya kike?.”
“Lau, ya Baba? Ya fita ne?.”
“Eh.” daga haka suka dawo cikin parlourn, gaisawa suka kuma yi sosai, hmmmm karkuso kuga yadda Rahma ke ƙanƙan da kai, tamakar ba Rahma mai isa da fariya ba. Jikinta ya mutu dan tana tunanin Aunty Aisha za ta tona mata asiri ne, sai dai a'a, amma cikin hikima ta isar ma Hajja da cewan sam Rahma ba ta jan ƴan uwan mijinta a jiki.
“Rahma, a wanna duniyar dangi sune komai, muddin mutum ya yi wasa da su to tamkar ya yi wasa wani babban dama ce da Allah ya bashi, ki riƙe dangin mijinki kaman naki, ki so su, ki ƙauna ce.”
“Insha Allah Hajja.” daga haka ta ƙara mata nasiha sosai sai dai me yana shiga ne ya fita dan ko ɗaya ba ɗauka ba. Bayan Hajja ta gama sai Rahma ta shiga ɗakin ta na da, tana shiga ta kira number ƙawarta.
“Ke Ina Abuja, zuwa anjima ki shigo mana.”
“Ai dole na leƙo, zan shigo, fatan kin zo min da tsaraban."
“Sosai ma kuwa ƙawata, ki zo sannan ki sha ado, domin kuwa a yau insha Allah za ki yi kasuwa, wani matashi uhmmmn ki dai zo." Ta faɗa tana kallon Aunty Aisha da ta shigo.
“Ba dai Zuby ce za ta zo ba?.”
“Aunty ita ce, ni fa dan Allah ki dena shiga rayuwata please.” sam A'isha ba tai mamakin jin haka daga bakin Rahma ba sai ta ce.
“Insha Allah, bazan kuma shiga abin da ya shafe ki ba, amma a duk lokacin da ƙwaɓarki ta yi ruwa karki nuna kin sanni." Daga haka ta juya ta fita.
“Khairan insha Allah.” ta faɗa har da murguɗa baki......✍️
END.
> Hmmmmmm lalle kam Rahma kina ruwa, kin raba mutum da danginsa, ke wai a haka soyayya ce. Fatan sa'a Ukasha
🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕
PAGE 1️⃣9️⃣⏩2️⃣0️⃣
*KADUNA*
Washegarin ranar, tare suka shiga makaranta, yau suna da lecture, bayan an tashi, a haraban da suke zama suka zauna su uku, dan I.B yana can class suna magana da Mymoon.
“Baby a ina shi yake Taj ɗin?.”
“Yanzu yana Dubai ne, tamkar yaro haka Dad ya ɗaukesa, marayane, yaron abokin sa ne."
“Hmmm har na harbo jirkin.” I.B ya faɗa yana ɗan murmushi.
“Me ka gane.” ta faɗa tana ƙare mai kallo, ya yi ƙyau sosai, yana sanye ne da ƙananun kaya sun mai ƙyau sosai, ba ƙyarya Ibrahim ƙyakkwane.
“So yake ya aure ki, ya mallaka duk abin da yake na ki, wasa yake so ya yi da hankalin ki da na Dad, shin idan kun haɗu yana sake miki sosai.”
“Ina