Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
zuciya da take yi, kai ba ka ce ba ɗan ta bane ba.
Adam ya numfasa ya ce "Ina ga mu tafi, rana na cigaba da yi".
"Ni dai ku je ku dawo, kan nan na ga sabir sosai".
Ammi ta ce "Rumaisa, ai zuwan naki ne, ke yake son gani, ki yi haƙuri in Allah ya yarda da kaina zan din ga sawa a kawo miki sabir kin ji".
Kallonsa ta cigaba da yi tana kuka, Adam kuwa ya taso, yazo kanta ya durƙusa zai ɗau sabir.
Riƙe shi ta yi gam tana kuka, ya saka hannu ya ɗauke sabir ɗin ya bar ta da towel.
Riƙe towel ɗin tayi ta cigaba da kuka, ammi gaba ɗaya ta rasa me zata cewa rumaisa, sai da a ranta ta ji tsoron kar su shiga hakkinta wani ciwon ya kamata saboda ƙwace yaron nan.
Haka nan sai ammi ta ji nauyin rumaisa, ta ma rasa me zata gaya mata ta rarrasheta.
Nusaiba kanta wani irin tausayin ruman ne ya kamata, ta tashi ta bi bayan Adam bedroom ɗin ammi.
Ya dubi nusaiba ya ce "Ku kula da kyau, kar a sake fito da shi, ina iman take?"
Jiki ba ƙwari Nusaiba ta ce "Ta sha maganin mura ne, tana ɗakinta tana bacci"
Ya miƙe mata sabir, sannan ya fito ya dubi usman ya ce "Mu je ko".
Ammi ta kasa cewa komai, sai riƙo hannun rumaisa, zuwa babban falo, ta ce "Rumaisa, ni dai ina kuma baki haƙuri, na san mu masu laifi ne a wurinki, amma ki yi haƙuri ki mayar da hankali a kan makaranta, in dai sabir ne bamu isa mu rabaki da shi ba, tunda ɗanki ne"
Baba Uwani ce riƙe da tsintsiya a hannunta, ta biyo bayan ammi, ta washe baki ta ce "Uwar ɗakina baƙi ki ka yi haka ne?"
Ammi ta waiwaya ta ce "Eh, dama ina nemanki" ta mayar da idonta kan rumaisa ta ce "Rumaisa, ki gaida mini da mamanki, akwai saƙonki a wurin takawa, ki yi haƙuri ki yi ta addu'a kin ji yarinyar kirki" rumaisa kawai jinjina kai ta kasa, ta bi bayansu takawa.
Usman har cikin ransa yake jin babu daɗi kukan da rumaisan ke yi, adam kuwa jinjinawa azababben ƙarfin halin rumaisa yake yi.
Ba wanda ya kuma juyowa tsakanin shi da usman, sai dai suka fita haraba wurin motar da za su hau, sannan suka waiwaya ba su ganta ba.
Usman ya ce "Kaii, ina yarinyar nan ta tsaya kuma?".
Adam ya ce "Bari na je na duba, ina zuwa "
Ya ja da baya ya koma in da suka biyo.
A zaune ya tarar da ita, bayan wasu bishiyu, ta cukuikuye a cikin hijjabinta, tana kuka mai ɗan sauti kaɗan.
"Ke!" Ya yi maganar cikin tsawa. Ta zabura ta ɗago ta kalleshi, da sauri ta tashi tsaye.
A ɗan ƙufule ya ce "Meye haka muna tafiya zaki ja ki tsaya? Sauri fa nake bani da lokaci".
Wani mugun kallo ta yi masa ta ce "To ina ruwana da rashin lokacinka, ni fa ba a son raina na zo ba in gaya maka, kuma wallahi babarku tana son bani sabir, kai ne ka dage ka ƙwace mini ɗa, kuma sai ka bani ɗana ko ba ka so, ko kuma ka ga matakin da zan ɗauka".
Adam ya ƙare mata kallo ya ce "Idan aka baki shi, gaya mini da me zaki shayar da shi? Kalleki fa".
"To ai dai na ga ba shayar da shi ake yi ba, madara ake bashi, kuma idan na girma na zama babba sosai zan dinga shayar da shi".
Ya girgiza kai ya ce "An daina ba shi madara yanzu ai, ni nake shayar da shi, tunda na san nesa ba kusa ba, na fiki abun bashi, tashi ki wuce mu tafi".
AYSHERCOOL.
08081012143
paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*
Shiru ta yi ta bishi da ido, tana nazarin maganarsa, ta yaya namiji zai shayar da jariri ita tun da take ba ta taɓa gani ba, ko dai raina mini hankali yake?' ta tambayi kanta.
"Ki tashi mu tafi ina magana kina kallona" ta ji maganar sa cikin tsawa, da sauri ta tashi ta yi gaba ta wuce shi, ba tare da ta waiwayo in da yake ba ta miƙa ta tafi hanyar harabar gidan.
Usman na ganinta ya ce "Ke kuma ina ki ka tsaya, sai da ki ka saka a koma nemanki, wato dai ba ki ji abun da mama ta gaya miki ba ko?" Ta girgiza kai alamar a'a.
"Ba ki ji ba mana, idan muka koma gida sai na gaya mata" ita dai ta yi shiru ba ta ce uffan ba.
Adam ya ƙaraso ya nufo motar, rumaiss kallonsa take ta ga ƙirjinsa a cike yake yadda zai shayar da yaro, amma ta kasa gane komai, kasancewar dogayen kayane a jikinsa.
Adam ya shiga ya kunna motar, usman ya buɗewa ruma baya ya ce ta shiga, amma ya ga ta tsaya cak, ta zubawa gate ɗin gidan ido.
"Wuce mu je" usman yayi maganar yana tunkuɗata cikin motar.
Cikin motar wani irin sanyi da ƙamshin turaren Adam suka cika mata hanci, sai dai ta din ga jikinta wani iri, kamar wani mara daɗi na tunkaro in da suke.
Adam ya kunna motar, ya nufi gate, sai ga motar Jabir ta shigo, jabir ya tsaya dai-dai in da motar adam take ya ce "Yaa ina zaka kuma? Daga gidanka nake".
"Eh wani muhimmin abu ne ya taso mini"
Samha ta ce "Barka da rana yaya" ɗaga mata kai kawai yayi ba tare da ya amsa ba, ya ce wa jabir "Ka jirani da daddare, zan nemeka in sha Allah"
"Ok, dama na je na kuma yi wa turaki gaisuwa, Samha ta ce idan nan zan taho zata zo ta sake yi maka gaisuwa".
"Na gode, zan je na dawo yanzu in sha Allah".
Tun da samha ta sanya idonta a na rumaisa, ta ji wata mummunar faɗuwar gaba da fargaba, kamar ta san idon rumaisa amma ta manta a ina ta santa, gashi ruman ta rufe fuskarta da facemask, ita kanta ruma ba ta san yadda aka yi ta tsare samha da ido ba, ko ƙiftawa ba ta yi, kamar wani abu mai muhimmanci take son ganowa a tattare da Samhan, amma ta kasa gano ko me take son ganowar. A haka Adam ya ja motar suka bar gidan.
Tun da suka fara tafiya, rumaisa ba ta iya cewa komai ba, ras ba ta manta samha ba, sun taɓa haɗuwa, kenan 'yar uwar su takawa ce ko kuwa oho?.
Har suka ƙarasa gidan turaki, kasancewa tafiyar ba wata ta azo a gani bace, ruma zancen zuci kawai take yi.
Ko da aka buɗe gate ɗin gidan suka shiga, kamar wadda ta farka daga bacci ruma ta ce "Kai, ai na san wannan gidan".
Usman ya ce "A ina?"
"Ni da hauwwaliya muka taɓa zuwa gidan, wai akwai ƙawarta ana bikin ƙanin babarsu, wata fiddausi sunanta ko jannatu na manta, har na ga waccan da muka gani a motar ɗazu mai bluen kaya, tana ta hantarar mutane ba ta da mutunci, har muka yi faɗa da ita".
Adam bai ko nuna ya san mai rumaisa take cewa ba, usman ya juyo, yayi mata inkiyar ta yi shiru, amma ina kamar ya tunzurata "Wasu mutanen dai yan uwansu kaɗan ne masu kirki, duk masifaffu ne, ta din ga yi wa mutane tsawa, na fito kawai muka yi karo da ita, wai ke ba kya gani ne, nace eh bana gani, yo ni za ta yi wa gatse, bana son in ga ana wulaƙanta mutane"
"Ke ya isa rufewa mutane baki" usman ya yi mata maganar cikin tsawa, jan facemask ɗin ta ta yi, ta buɗe motar ta fita, kasancewar tuni adam yayi parking.
Hadimai na ta risunawa, suna gaishe shi, yana ɗaga musu hannu maimakonsa ya amsa, hakan ya ƙara sanya rumaisa jin haushin takawa, tare da ganin yana wulaƙanta mutane.
Adam ya yi musu jagora, har cikin babban falon gidan, nan ma rumaisa ta sha kallo, gidan ya so yayi shige da na su Adam, sai dai na su ya fi kyau sosai a kan nan.
Adam ya ce wa usman "Ina zuwa, bari na shiga na sanar masa da zuwanmu".
Usman ya ce "To shikenan"
Adam na barin wurin, ya matsa kusa da rumaisa ya riƙe kunnneta ya yi ƙasa da murya ya ce "Dan ubanki me aka gaya miki a gida, wato ke ba a isa a faɗa miki ki ji ba ko? Ki ke ta zuba kina surutu, kina cewa wata ba ta da mutunci ke mutuncin ne da ke?"
Riƙe kunnen ta yi ta fa ƙoƙarin fara kuka, wata mata ta fito ta ce musu "Bisimillah, an yi muku iznin shiga"
Suka tashi suka bi bayan matar. Subhanallah wani irin ƙaton falo ne, ko ina ya sha kilisai da lallausan carfet, sai ƙamshi yake yi.
Daga nesa ta hango dattijon jawurr da shi a zaune, sanye cikin kayansa masu sauƙin nauyi, sai rawani sai dai ya sauke takunkumin fuskarsa.
Maimakon rumaisa ta nutsu, sai ta yi ta kalle-kalle tana kallon abubuwan gidan sarauta da ba ta taɓa gani ba.
Usman ya ce wa dattijon "Barka da wannan lokaci, fatan mun same ku lafiya?".
Turaki ya jinjina kai ya ce "Alhamdilillah".
Usman ya sake duƙawa ya ce "Ya ƙarin haƙuri na wannan rashi, Ubangiji Allah ya jiƙanta da rahama, ya bada haƙurin jure rashin"
Turaki ya amsa da "Amin 'yan samari, madalla Allah ya yi albarka"
Rumaisa ya kalla da take ta kalle-kalle, usman ya zungureta tayi maza ta kalli turaki ta ce "Ina wuni?" Yayi ƙuri yana kallonta, amma bai amsa ba.
Kallonsa tayi, ta kalli adam sannan ta kalli usman, ta kuma cewa ina wuni.
Adam ya risuna ya ce "Tuba take, ba ta san kan gaisuwar gidan sarauta ba, kamar yadda na yi maka bayani a baya, wannan ita ce wadda ta zo da jaririn wurin marigayiya". Adam ya ƙarasa maganar yana yi mata alamar ta sauke facemask ɗin ta.
Harar Adam ta yi, ta sake jan facemask ɗin ta, ta rufe fuskarta.
Turaki ya yi mata ƙuri da ido, tsananin kwarjininsa ya sanyata sunkuyar da kai, ta ji kamar jikinta zai hau rawa, saboda kwarjininsa, sun fi mintuna biyar bai ce komai ba.
Adam ya kuma yi mata nuni da ta sauke facemask ɗin ta, amma taƙi sai da usman ya kalleta, sannan ta cire.
Turaki ya cigaba da kallonta sannan ya ce "Iko, sai Allah yanzu wannan ƙaramar yarinyar ce ta ceto yaron wurin fulani"
"Eh Allah ya baka nasara, ita ta zo da shi"
Ruma a ranta ta ce "Taɓ, wanna wace irin wahala ce, da ban cire facemask ɗin ba, kenan haka zamu yi ta zama ba zai yi magana ba?'.
Turaki ya ce "Bamu labari, ya aka yi aka haɗu da fulani, har aka zo mana da jaririnta?"
Rumaisa ta ɗan waiwaya ta ce "Wace fulani kuma?"
"Aisha" Adam ya bata amsa.
Sai ta yi turus, ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Usman ya ce "Ki yi magana mana"
Ta yi shiru ta shiga wasa da ƙasan rigarta.
Turaki ya ƙura mata ido ya ce "Ke muke sauraro yarinyar kirki" ɗaga idonta ta yi tana kallon adam, da ya murtuke fuska saboda ƙuluwa da ya fara yi, da iskancin da rumaisa ke yi.
"Ko su bamu wuri ne?" Turaki yayi maganar yana nuna su adam.
Ta jinjina masa kai alamar eh, ya ce "To babu laifi, takawa a bamu wuri, kar a damu a bamu wuri mu tattauna".
Takawa bai taɓa zaton iskancin rumaisa ya kai haka ba, ƙin yarda da shi ta yi masa bayanin abun da ya faru, ya sanya yayi zaton a gaban turaki za ta yi bayani, amma mirsisi taƙi magana sai sai ya fita.
Ganin yadda adam ya harzuƙa, ya sanya turaki yi masa alama da ya kwantar da hankalinsa.
Sai dai ba iya adam ɗin ne ya ƙulu ba, har usman ya ƙule da abun da rumaisan ta yi.
Haka suka tashi suka bar falon.
Turaki ya mayar da kallonsa ga rumaisa ya ce "Matso kusa da ni nan ki yi mini bayani"
Rumaisa ta ɗan ƙara matsawa daf da shi, ta hango hoton aisha a bayansa, ta ƙurawa hoton ido, da har sai da turaki ya waiwaya ya kalli hoton.
Ya ɗauko hoton a hannunsa, ya shafa shi ya ce "Kin ganta nan, a cikin 'ya'ya na kusan goma sha rayayyu da wanda suka rasu, babu wadda nake jin daɗinta nake zartar da hukunci komai ɗacinsa ta karɓa sai Aisha. Na tafka babban rashin da ba zan iya maye gurbinsa ba, Allahn da ya bani ya fi ni son ta, ban so ta mutu a wulaƙance haka ba, sai dai ba zan zargi sirikina ba, ɗana ne shima, kuma ba zai cutara da aisha ba"
Rumaisa da hawaye ya fara zubo mata ta ce "Tabbas anty aisha tana da kirki, kowa cewa yake yi bana jin magana, amma ita ta fara cewa rashin ji na yana burgeta. A makaranta bana gan karatu, amma ta ce mini mai kaifin basira ce ni, ta yi ta kula da ni a hannun 'yan bindiga kan ta rasu, amma mijinta ne ba shi da kirki ko kaɗan, shiyasa naƙi magana a gabansa".
Turaki ya yi murmushi ya ce "Tabbas takawa yana da zafin rai, amma mutumin kirki ne sosai".
"Na san a ƙule yake da ni, yanzu ba dan kai ba tsaf sai ya zaneni a wurin nan, ita rayuwa idan mutum yana son ya ci ribar abu ba haƙuri ake a bishi a sannu ba? Idan haka zai din ga yi komai ya tunkara sai ya faɗi. Kuma dai naga ɗan sanda ne shi, mai ya hana ya kai mana agaji lokacin muna hannun 'yan bindigar, da bakinsu fa suka ce jami'an tsaro ne suke basu gudunmawa, to yanzu kuma dan Allah me zai yi bayan mai faruwa ta faru".
Zuba mata ido kawai turaki yayi, yadda take zaro magana, tana arranging ɗin ta, tamakar tana karantowa, kuma ba zaka taɓa cewa yarinya ce mai kamar shekarunta take faɗa ba.
Ya gyara zamansa ya ce "Haka ne, kema kin yi magana mai kyau, amma yanzu dai ina jin ki".
"Baba"
Ya ce "Na'am yarinyar kirki"
"Amanatun amana, zan gaya maka komai, gani ake ni Yarinya ce amma ina da wayona, ta ƙarfin tsiya fa ya ƙwace mini ɗa, ko tausayina ba ya ji alhalin anty aisha ta ce ta bar mini shi halak malak. Zan gaya maka komai, amma shi ba zan gaya masa ba, kuma wallahi na san abubuwan da shi bai sani ba".
Duk girman turaki, ruma ta iya kallonsa ta ce masa amanatun amana, tare da yi masa kashedin, kar ya gaya wa kowa abun da za ta gaya masa.
Ƙwarin gwiwar ta, da rashin tsoronta a ƙananun shekarunta ne ya fi bashi mamaki, kuma tsara zancenta da kaifin basirarta ya burge shi.
Ya ce "Kar ki damu, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai ke sai Allah".
Nan rumaisa ta gyara zama ta fara yi masa bayanin abubuwan da suka faru, duk a hirarta ta ya fuskanci ba komai ta gaya masa ba, amma a hakan ta yi ƙoƙarin yi masa duk wasu bayanai da yakamata ya sani, sai dai kan ta kammala, hawaye ya wanke mata fuska, sai gogewa take da hijjabinta.
Shi kansa turaki kasa jurewa yayi, cikin dabara ya goge hawayen da yake shirin zubo masa, yana jin labarin wai-wai a kafafen watsa labarai, bai taɓa zaton masifa da tashin hankalin ya kai haka ba, kuma ta bakin rumaisa ne idan aka fara haɗawa da 'ya'yan masu faɗa a ji ana sacewa wataƙila a mayar da hankali a kan maganin abun, kuma abun kunya ne ga jami'an tsaro, ace an sace matar jami'in tsaro kuma an kasa ceto ta har ta rasa ranta.
Uwa uba azabar da rumaisa ta sha kan ta fito da jaririn, shi kansa ya isa abun tausayi duba da ƙananan shekarunta, gashi sai nanatawa take ita fa aisha ta bar mata ɗa, amma adam ya ƙwace mata.
Ya duba gefen sa, ya ɗauko wani handkerchief mai matuƙar kyau da taushi, sai ƙamshi yake yi, ya miƙawa rumaisa ya ce "karɓi nan ki goge hawayenki, kukan ya isa haka".
Karɓa ta yi, amma ta kasa gogewar, saboda kukan da ya ci ƙarfinta.
Usman kuwa ba ƙaramar mita yayi ba, a kan abun da rumaisa ta yi, tun da suka fito yake mita.
"Ban taɓa ganin yarinya mai azababben taurin kai, na tashin hankali kamar rumaisa ba, gaba ɗaya yarinya kamar wata majanuniya, ita duk wata hanya ta masalaha ba ta santa ba, idan ta akasin masalahar ma aka biyo mata ta fi misbehaving, ba a gane gabanta da bayanta kamar ɗan wake".
Adam kam azabar takaici, bai bari ya iya tankawa ba, gani yake gaba ɗaya yarinyar ta gama raina masa hankali.
A nutse turaki ya din ga rarrashin rumaisa, yana yi mata nasiha, har sai da ya sanya ta ɗan yi murmushi ta ce "Baba ka iya magana a nutse wallahi, ni yadda kake magana ma daɗi yake yi mini"
Abun da ta faɗa ɗin sai da shi ma ya sanya shi murmushi, ta kai handkerchief ɗin da ya bata fuskarta,
Ta lumshe idonta ta ce "Wayyo ƙamshi, baba ban taɓa jin turare mai daɗin wannan ba, kamar na suma dan daɗi".
Jan rawaninsa yayi ya rufe fuskarsa, dan dariya rumaisa take neman ta saka shi.
Hadimai ne suka yi sallama, suka shigo masa da kwanukan abinci a kuloli da kuma akushi, aka zo aka jere su a gabansa.
Rumaisa ta dinga kallon fulasai na alfarma.
Turaki ya ce "Ga abinci nan, buɗe a ciki ki zaɓi wanda ki ke so ki ci".
"A'a na ƙoshi, mama ta hanani cin abinci a waje".
"To ai nan gidanku ne, ki ci duk abun da ki ke so".
Ta nuna masa