Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
kwanta.
Ba ta tashi ba sai bayan azahar, ta tashi ta yi wanka, ta yi alwala ta yi sallar azahar, ta kuma neman wuri ta zauna a tsakar gida.
"Mutuniyar, wai ya aka yi ne? Zo ki sayo mana kifi mu ci Abinci, tun da na dawo nake cigiyarki" yayi maganar yana leƙa fuskarta.
Maimakon ta amsa masa kawai ya ga hawaye a fuskarta.
"Ke, menene mama ce?"
"Yaya Usy"
"Na'am rumaisa"
"Ni za a daka a hana kuka? Zuciyata zata fashe" tayi maganar tana sake fashewa da kuka.
Rarrashinta ya shiga yi, yadda ya ga tana neman ta shiɗe, idanunta duk suka yi ja.
Ya din ga lallaɓata ta gaya masa abin da ya faru.
Mama da take jin su ta ce "Allah ya ƙara miki, Allah ya sa yau da ki ka samu wadda ta zane ki, ba zaki sake dambe ba, dama ban da iskanci meye na zana uwar wani, idan ke aka zana taki uwar zaki ji daɗi?"
"Mama cewa fa ta yi babata tsohuwa"
"To sai me? Tsufa ai arziki ne, ruma ita duniya 'yar siyasa ce, ba komai ƙarfi yake baka ba, amma kin kasa gane hakan"
Wani irin kallo take yi wa mama, wato ita mama ko a jikinta kenan.
Usman ya kawar da fuskar ruma daga kallon mama. Abu ne mawuyaci ruma ta yi fushi, ko an ɓata mata rai sai dai ta yi kuka, idan ta gama kuma shikenan ya wuce sai a shirya, amma yadda idanunta suka yi yau ya tabattar masa da ta kai maƙura a ɓacin rai, ba a taɓa defeating ɗin ta ba sai yau. Irin zuciyar mai sunan baba ce da ita, idan rai ya ɓaci silently suke fushi, sai dai suna shiga mawuyacin hali, har gara shi Umar yana shouting wasu lokutan, amma ruma gaba ɗaya kasa komai take idan tana cikin matsanancin ɓacin rai. Wata irin ajiyar zuciya kawai take yi.
"Yaya ni raguwa ce ko? Aka zageni, a kan gaskiyata kuma aka hukunta ni, ni ko?"
Usman ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Ke ba raguwa ba ce, kowa shaida ne, kamar yadda nake gaya miki, ki fuskanci duk wani abin da yake baki tsoro, gaba da gaba na tsaya miki"
Ta ɗaga kai ta kalli Usman, ya jinjina mata kai alamar ƙwarin gwiwa, ta jinjina kai ta mayar da kai ta kwanta a jikinsa, tana cigaba da ajiyar zuciya.
Duk wanda ya shigo ya ga ruma a haka, sai ya tambayi ba'asin meyafaru, ko ba ta da lafiya ne?
Mama ta ce "Ina fa, lafiyarta ƙalau, yau bori ne ya kar boka, ta tsokano wadda ta fi ƙarfinta, aka naɗa mata duka, shi ne take nema ta suma ki cigaba kar ki fasa halinki"
Aliyu ya tsaya a kan ruma ya ce "Ke, ki na wani sokwancin ki ka yadda aka dake ki har ki ke wa mutane kuka?" Ruma ta yi shiru ba ta amsa ba.
"Ina fatan dai ba a gaban wadda ta dake kin ki ka yi kukan ba? Wallahi da ina gidan nan sai kin fita kin rama, dan ubanki yaushe ki ka koma shashasha har aka dakeki aka fitar miki da jini, 'yar uban waye da baki taka mini ita ba"
Buɗe baki mama ta yi, ta kalli Aliyu ta ce "Gadanga, maimakon ku tayani yi mata faɗa, ku ke mara mata baya? Ba sai ku ce Allah ya sa hakan ya zama silar shiriyarta ba"
Aliyu ya girgiza kai ya ce "A'a Addu'a ce kawai za ta shiryata, amma ba a daketa a waje ta tsaya tana kuka ba, babu rago a gidan nan, ko ɗan uban waye ta daka zamu bada haƙuri, amma wallahi aka kuma dukanki a waje, ki ka zo mana gida ki na kuka, sai na ƙara miki wallahi, idan mazane kawai ban yadda ki yi faɗa da maza ba, ki zo ki gaya mini, amma mace dai 'yar uwakki, ki tattaka mini kowacece"
Aikuwa mama ta haɗasu gaba ɗaya ta din ga faɗa kamar ta ari baki.
"Kaf cikinku babu wanda na sha wahalr rainonsa kamar ruma, amma kuna zigata ta ɗauko magana, rainonta dai-dai yake da rainon fitinannun yara maza huɗu, maimakon ku tayani dawo da ita hanya, amma ku ke ingizata"
Gaba daya suka yi wa mama shiru, ta yi ta banbaminta ta yi ta gama.
*****
Karkarwa jikinsa yake yi, tamkar zai hau bori, jikinsa sai wani ƙaƙƙamewa yake yi, tamkar ba jikin ɗan Adam ba.
Wata matashiyar mace ce zaune a kan gadon, tana kallonsa, ido fal hawaye, ya yin da shi kuma ya cigaba da tunkararta.
Girgiza masa kai take yi, amma ta kasa motsawa balle ta gudu.
Yana zuwa ya zauna a gabanta ya tsura mata ido, ya miƙa hannunsa kan cikinta, take jikinta ya hau rawa ta rintse idanuwanta, tana zubar da hawaye. Sautin muryarta ne ya dakatar da shi ga aikata abin da yake ƙoƙarin yi
*Sarki ka ganni, ya na ga sarki da ƙananan kaya, sarki ka kalleni* tamkar a zahiri haka yake jin muryartata a cikin kunnuwansa, a hankali ya buɗe ido ya na ƙarewa ɗakinsa kallo. Sai a lokacin ya gane mafarki yake yi, ba zahiri bane.
A hankali ya tashi ya zauna, ya yaye bargon da ya rufa da shi, ya kalli agogon da ke kafe a jikin bangon ɗakin. Ƙarfe tara da rabi.
Ɗan guntun tsaki ya ja, me yasa yake yawan jin muryarta ne? Anya ba aljana ba ce ita ma?. Gabansa ne ya faɗi da yayi wannan tunanin, da kuma tuna matsalar da yake ciki, yake ta neman mafita a kanta.
Saurin girgiza kai ya yi, ya sauka daga kan gadon, ya wuce banɗaki.
****
Cikin matsanancin razani ta ƙwala ihu "Wayyo Allah mama" a gigice mama tayi kanta tana faɗin "Ke lafiyar ki kuwa?"
Tashi ta yi zaune ta na rarraba ido, tana kallon ɗakin.
"Lafiya menene?"
"Mafarki na yi na tsorata"
Mama ta ja tsaki ta ce "Ba dole ki dinga mafarki kina tsorata ba, tun da ba kya Addu'a kwanciya bacci".
"Wallahi mama na yi"
"Ke ki ka sani dai, ko a garin neman maganar ki ruma, kya tsokano abin da zai dinga tsorata ki, ya hana ki bacci tashi ki je ki yo alwala, yanzu za a kira sallar asuba.
Haka nan jiki babu ƙwari, ta tashi ta yi alwala ta gabatar da raka'atanul fajr, sannan ta yi sallar asuba.
Jikinta duk yayi sanyi da mafarkin da ta yi, amma ta kasa tuna me ta gani a mafarkin ya tsorata ta.
Babu wanda Ruma ta kula a ajinsu, ta nemi wuri ta yi zamanta ta yi shiru, tana ta takura ƙwaƙwalwarta, ta tuna mafarkin da ta yi ya bata tsoro, amma ta kasa har aka kusa tashi, hankalinta baya tare da ita.
Asiya ce ta zo kan ruma ta tsaya, ta riƙe ƙugu ta ce "Ki je ki wanke banɗakin da aka saka ki, ko na je na faɗa" tamkar ruma na jin tsoron Asiya, haka ta tashi jiki na rawa zata fita daga ajin, sai dai ta yi burki a gaban allo, ta ɗaukko chalk a aljihun rigarta, ta sake zana wata shirgegiyar matar, wadda tafi ta jiya, ta yi labelling ɗin ta.
Ta waiwayo kuma tana kallon Asiya, tare da jiran ko ta kwana.
Aikuwa kamar ruma ta san a rina, Asiya ta kuma nufo ruma, tana zuba ashar, kan ta ƙaraso ruma ta yi ciki da ita, suka faɗa kan wasu ɗalibai.
Hannun Asiya ɗaya ta samu, ta din ga duka kamar ta samu ɓarawo, sai da ta tabattar da ba zata iya kai duka da hannun ba, sannan ta koma fuskarta.
An kai ruwa rana kan a ƙwaci Asiya daga hannun ruma, sai a lokacin ruma ta ji hankalinta ya kwanta, baƙin cikin da ya tokare mata zuciya ya sauka.
Babu wata-wata, malamin su ruma ya saka su kneeldown a rana, ba tare da ya tsaya ya ji ba'asin ma meyafaru ba.
Tun a lokacin Asiya ta ji ba ta iya motsa hannun da ruma ta din ga jibga, ta din ga jin kamar ba a jikinta yake ba.
Suna Kneeldown ruma ta riƙe ƙugu ta ce "Ke kin isa ki dakeni na ƙyaleki, hmm baki sanni bane, kuma wallahi ban huce ba, zaki ga abin da zan yi miki, ki dakeni ki zageni, sannan ki zaci kin ci bulus, ai faɗa ni da ke daga yau har ranar busa ƙaho, ba dai uwata ce tsohuwar banza ba sai ka ce babata sa'arki ce ba? Ai ki yi mini komai ban da taɓa uwata, ban taɓa zagin uwar wani ba, kema babarki jibgegiyar bayerabiya masu kashi a leda"
Gigicewa Asiya ta yi, tana kuka tana son kaiwa ruma duka, amma ta kasa sarrafa hannunta ga ciwon da jikinta yake yi mata.
Ruma ta durƙusa ta dinga dumbuzar ƙasa hannu bibbiyu tana watsawa Asiya a fuska. Ban da kuka babu abin da Asiya take yi.
Ranar ma sai da aka tashi sannan aka sallame su, aka ce gobe da safe za su cigaba da punishment.
Rumaisa ta riga Asiya tafiya, ta je ta samu hanya, ta tattara duwatsu, ta tara su a cikin jakarta. Ta kuma datsar Asiya a hanya, ta dinga kabbara tana jifanta. "Sheɗaniya gara na jefeki na huta, na ga haka ake yi idan an je makka a jefi sheiɗan, gobe ko cewa aka yi ki kalleni, ba zaki sake ba balle ki dakeni"
Sai da ruma ta gama abin da Allah ya nufeta da yi, sannan ta wuce gida. Yau kam bakinta har kunne, jin ta take wasai ba ta da wata damuwa ko banza ta rama abin da aka yi mata har da riba, malamai kuwa ko zasu kwaɗata su cinye bai dameta ba.
Abdallah ne yake ta shiri, ruma sai tambayarsa take ina zashi?.
"Ke wai kin aikeni ne?"
"A'a, amma dan Allah ka gaya mini"
"Cikin gari zani ziyara"
Ta haɗa hannayenta biyu ta ce "Dan annabin rahama ka tafi da ni" hararta ya yi ya cigaba da shirinsa.
Ta dinga bin sa tana lallaɓa shi, har ya amince zai tafi da ita.
Mama ta ce "Hmm in dai ruma ce zata baka kunya, Allah ya sa kar ta ɗauko maka magana"
"Ta ɗauko ma, dakuwa zata yi wallahi"
Ruma ba ƙaramin daɗi ta ji ba, ganin ta a cikin gari cikin 'yan uwa, akwai 'yan uwan mama sosai a cikin gari, sai dai mama ba ta zuwa da ita, saboda ta din ga neman magana da dukan 'ya'yan mutane kenan.
Akwai wata 'yar cousin ɗin mama, da rashin jin su ya kusa zuwa ɗaya da na ruma, duk da ruma ta fita. Ta ce "Ruma, zo mu je yakasai, akwai ƙawata a gidan Turakin Kano, jikarsa ce biki ake a gidan, kuma za ayi kilisa, kan Abdallah ya dawo mun je mun dawo, mu je mu ciyo banza"
Ruma ta ce "yauwwa hauwwaliya, yi sauri ki shirya mu tafi kan ya dawo ya hana ni zuwa"
"Ke har da babbar leda zan ɗauko, idan mun ci mu ƙullo sauran"
Haka suka shirya, suka yi sallama a kan zasu je biki su dawo.
Suna tafe a hanya suka sai masara, suna tafe suna ci suna hira.
Tabbas idan ka ji wane ba ƙarya ba, gidan ya tsaru yayi kyau sosai da sosai, gini ne na sarauta da aka ƙawata da kayan alatu, ruma sai rarraba ido take yi.
Ƙawar hawwaliya ta din ga murna da ta gansu, ta kai su wani falo suka zauna.
Ruma kuwa hankalinta na kan wata mata, da ta sha ado sai kai wa take tana komowa tana wani hura hanci, tana dakawa mutane tsawa.
Ruma ta ce "Taɓ, wai wacece waccan?"
Yarinyar ta kalli wadda Ruma ta nuna ta ce "Laa Anty Samha ce, ƙanwar mama ce, ba mata bace ba ta da aure".
Ruma ta ce "too na ganta wata gwabjejiya, sai masifa take yiwa mutane, ni na zaci matar sarki ce ma, yakamata a samu mai kwaɗeta ya zata din ga hantarar mutane?"
Hauwwaliya ta daki cinyar ruma ta ce "Ke, ƙanwar mamanta cefa"
Yarinyar ta yi murmushin yaƙe ta ce "Bari a kawo muku Abinci, sai mu je wurin kiɗan ƙwarya da kilisa"
Ruma ta miƙe ta ce "Hauwwaliya, ni dai zan je wurin da na ga an ɗaure dokuna na kallesu, idan an kawo Abincin ki ƙulle mini nawa a ledar da ki ka zo da ita" buɗe baki Hauwwaliya ta yi, da jin hansfreen da ruma ta yi musu.
Kai tsaye ruma ta fito tana cigaba da kallon gidan, da yadda manyan mata ke shiga suna fita, da shiga kala-kala.
"Ke ba kya gani ne, meye haka?" Ruma ta ɗaga kai ta kalli wadda ta daka mata tsawar. Matar da take ta hantarar mutane ce.
"Eh bana gani, sandata na fito nema, ke da ki ke gani meya hana ki kauce?" Ruma ta yi maganar tana tsare Samha da ido.
Wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Samha, da ta yi tozali da idanun ruma, ga ta ƙarama amma wani abu mai kaifi ne a idanun ruma.
Ruma ta raɓata ta wuce abinta. Da sauri Samha ta bi bayan ruma, amma ta nemeta ta rasa.
Kai tsaye burgar dawakin da suka wuce ta je ta tsaya. Ta tarar da wani dogari yana basu Abinci.
"Sannu da aiki"
Ya kalli ruma ya ce "Yauwwa sannunki"
"Dan Allah ina dokin sarki a nan?" Yayi murmushi ya ce "Nan babu dokin sarki, na 'ya'yan sarki da manyan Hakiman fada ne"
"Dan Allah ka cewa sarki ya bani doki ɗaya"
Yayi dariya ya ce "Ke idan aka baki doki ya zaki yi da shi?"
"Hawa zan din ga yi mana" ruma ta din ga yiwa dogarin nan surutu, sai da ya gaji sannan ya ce "To ai Shikenan, yanzu dai fita za ayi da su, za ayi kilisar angwaye"
Ta jinjina masa kai, ta koma gefe ta tsaya, tana kallo aka shirya dawakan, aka yi musu kwalliya sannan aka fita da su.
Hauwwaliya ce ta fito ita da ƙawar ta ta tana faɗin "Ke ruma, tun ɗazu jira nake ki dawo, amma ki ka ƙi komawa"
"Ke ƙyaleni, kallon dokuna nake"
Ƙawar hawwaliya wadda suke da Turaki, ta ce "Mu je to, sai mu kalli kilisar"
Suka fita daga cikin gidan gaba ɗayansu, kan barandar wani gida suka je suka tsaya, suna tsumayin a fara kilisar.
Abin yana burge ruma sosai da sosai, duk wanda ya zo wucewa sai ta ɗaga masa hannu tana tsalle.Tun da suke wucewa babu wanda ta kira sarki, sai da ya zo wucewa tare da ango.
"Sarki mai koriyar alkyabba, a dawo lafiya, dan Allah ka bani kyautar doki, ko kuma ka ɗanani a kan dokinka!!!"
(Wannan 'ya ni kaina tana bani ciwon kai 😒 in kun ji ni shiru ku dinga yi mini addu'a, Allah ya ƙara mini lafiya 🙏)
Mai nema daga farko, ya duba watpad Please 🙏
Ayshercool
08081012143
[21/07, 10:53 am] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*
*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
*Ina yiwa 'yan uwa musulmi barka da shigowar, sabuwar shekara musulunci, Ubangiji Allah ya sada mu da alkhairan da yake cikinta, akasin haka kuma Allah ya iya mana*
P 15
Gaba ɗaya aka juyo ana kallon ruma, mutanen wurin suka hau dariya.
Shi kansa Jamil da yake ango, da sauri ya ƙara rufe fuksarsa da rawani yana murmushi, dan saura ƙiris dariya ta ƙwace masa.
Adam kuwa sake tsare gida yayi, kasancewar dama can ba mai yawan fara'a bane ba, jin muryar ruman yake a wani abu daban, anya mutum ce?. Kamar zai juya domin ganin fuskarta, sai kuma ya fasa ya sake rufe fuskarsa da rawaninsa, yayi gaba.
Ƙawar Hauwwaliya kuwa ɗan zaro ido ta yi ta ce "Ke kin san waye wannan kuwa?"
Ruma ta ce "Ba shine sarki ba?"
"Ba sarki bane ba ai, ɗan gidan marigayi Galadima ne da ya rasu, sunan sarki ne da shi, Takawa ake ce masa, wallahi ki ka bari ya kamo ki, sai kin gayawa mutanen garinku, ba ki san yadda muke jin tsoronsa ko a family ba, hmmm su Ummanmu sun girme shi amma tsoronsa suke ji, ba ya wasa da mutane"
Bayan gama jin jawabin da aka yi mat, ta taɓe baki