Author : Halima Abdullahi K Mashi Category : Tknovels
nan sannu kin ji, A'isha ta ɗago kai ta ce ko zaki yi wanka ne? A'isha ta girgiza kai alamun a'a, sannan ta ce bacci nake ji,ta ce to yi ƙwanciyarki nan bari in ɗauko miki filo. Luba mai aiki ta shigo tana cewa Hajiya an gama a kawo?, Hajiyarmu ta ce, a'a bari su Alhajin su shigo,je ki kawo mata filo, kafin ka ce haka tuni bacci ya yi gaba da ita. Uncle sai da Hajiyarmu ta matsa mishi sannan ya tafi gida.
Su Jummai rai fal murna, addu'a take Allah yasa rai ya yi halinsa,lallai zata koma gurin wannan makamin don za'a dashi,tashin farko aiki ya soma ƙyau? Hadiza ma tana baje kan gado suna waya da Hajiya Lanti tana cewa,ai gaskiya malamin nan ya yi ne, ina ga aljannu ma ya haɗa ta da su,fatana dai Allah yasa cikin ya zube,tunda kinga damben da suka sha da maigidan? Yanzun dai ya fita da ita. Hajiya Lanti ta ce, Allah yasa asibiti suka je,kin san Aljani yana son a yi gabas shi yana yamma, ana maganin asibiti shi yana nan yana ɓanna. Suka sheƙe da dariya. WANDA YA YI NISA BA YA JIN KIRA.
Lokacin da Alhaji Saddiƙ ya shigo gidanshi, abinda bai taɓa gani ba wai yau Jummai da Hadiza ne zaune suke hira. Hakan ya yi mishi daɗi,ga nashi zaton jikin A'isha ne ya sa su zubar da komai, domin ya lura sun tausaya ma A'isha.tare suka miƙe suka nufo shi, suna cewa ya ya me jikin? Ya ce,jiki da sauƙi, Hadiza ta ce, wane asibiti aka kaita? Ya ce, tana gidan Hajiyarmu, ta dawo cikin hankalinta ma, yanzun na barta tana bacci. Jummai ta ce Alhamdulillah, amma Alhaji babu abinda ya samu cikin ko? Ya ce bana zaton ya samu matsala, ta ce amma mun gode Allah,ni dama damuwata kenan. Hadiza ta ƙara da cewa mun yi arziƙi, Allah dai ya kar lafiya,ya nufi ɗakinshi su kuma kowacce ta shige ɗakinta ba haka suka so ba,jikin A'isha yana yin sauƙi sosai ɗakin Hajiyarmu take ƙwana,zuciyar A'isha na matuƙar son Hajiyarmu,duk sanda ta farka kan sallaya take ganin wannan baiwar Allah, gashi suna jin nauyin juna balle ta tambaye ta cewa tana bacci kuwa? Sai dai duk lokacin da ta farka ta ga Hajiyarmu tana ibada, itama sai ta tashi ta hau yi. Wannan abin yasa itama Hajiyarmu jin A'isha a ranta. Ta yarda yanzun wannan yaron ya samu mata, irin matar da ta ringa mishi addu'a tun yana yaro.
A'isha na da kunya da son addini, tana jin nauyin surukanta, sai dai hakan ba ya hana ta zo ta zauna kusa da Hajiyarmun,in ko Uncle ɗin ta yazo ba ta iya yi mishi magana gaban Hajiyarmu, kuma takan miƙe da kanta ta shiga kitchen ta kawo mishi ruwa mai sanyi,ta bashi cikin girmamawa. In ko ya ce Beby ban ci abinci ba yau ta kan je ta kawo mishi ba tasa me aiki hakan yana yi wa Hajiyarmu daɗi, ba kamar Jummai ba duk da tana ƴar uwarta, ko ruwan gidan su bata sha, sannan gabansu zata yi ta yiwa mijinta yatsine-yatsine,bata la'akari da cewa su iyayan shi ne.
Uncle in zai je Ofis zaya biyo haka in ya dawo, waya kuwa sai ya kira ta fiye da sau goma a rana. Ita dai kullum zancan ta ya barta gidan Hajiyarmu,ta fi jin daɗi. Shi kuma sai ya ce a'a,ko hirarta ba ya samu sosai, ballantana ya ɗan shasshafa jikinta ya ji daɗi, sai ta ce duk me ya ke so zai mata ai gidansu Hajiyarmu ma gida ne, ya ce abinda in nazo sai ki zauna kusa da Hajiyarmu,ko magana da ƙyar ki ke amsa min, ta ce to in ban da abinka Uncle,da so ka ke inyi ya ya? Ya ce ka ji Beby da wani zance,ke baki da irin wayon nan ne naku na mata? Sai ki shige ɗaki ki zauna ni kuma na biyo ki, ta ce kai. Cikin mamaki ni dai ina jin nauyi, ya ce to ko irin rakiya ɗin nan cikin mota? Ta t, Uncle kenan,ni dai ina jin kunya, ya ce to ba zan iya barinki ba kenan ki zauna,nan da ƴan ƙwanaki zamu koma gida." Cikin shagwaɓa ta ce, kai don Allah Uncle ɗina. Ya ce Allah Bebyna. Ta ce, to in ka zo in baka ganni a falo ba ba sai ka shigo ɗakin ba. Ya ce,kin ga ina shigar ma Hajiyarmu ɗaki ne,bare ma in miki wani abu ciki? Ta ce to to ai dai haka kakeyi ba? Ya ce,in ba mutane ba, amma in da mutane sai ta ce min in fito mata daga ɗakinta tun ina ƙarami fa. Ina ga Hajiyarmu ba ta sona shi yasa nake tausayin kaina, gashi ban dace da matar da zata rungume ni ba.
A'isha ta tausaya mishi, sannan ta ce haba Uncle, ya ya zaka ce haka bayan ga ka da mata uku? Ya ce, duk ba ku damu da ni ba. Hajiya Jummai bata ma zauna ba, ballantana ta san matsalolina. Hadiza ko son abin duniyarta yasa na kasa sakin jiki da ita,ke ko Beby kunyarki ta yi yawa, ta ce to zan rage yace to na gode.
Satinta biyu gidan Uncle ya ce ma Alhajinmu tunda ta samu sauƙi yana so ta koma. Ranar da A'isha zata tafi har da kukanta,wai ita tafi son gidan Hajiyarmu, Hajiyarmu ɗin ce ta bata baki kan cewa ta ɗaure ta koma ɗakinta. Ta yi mata nasiha kan cewa ta ƙara dagewa gurin addu'a.
Su Jummai sun zo duba ta sau ɗaya, ganinta cikin hayyacinta yasa su cikin baƙin ciki, duk da suna ɓoyewa junansu mugun halinsu, ma'ana babu wadda ta nuna ma ƴar uwarta cewa tana shiga gurin bokaye, sai dai duk suna zargin junansu. Daga nan ko basu ƙara zuwa ba har kau da ta dawo gida. Sun dai shigo ɗakin sun yi mata Sannu, A'isha ta amsa tare da yi musu godiya.
*📗📗Page 16*
Wani lamari na Allah, A'isha sai ta samu sauƙi sosai, Uncle ya kai ta gurin Likita,ya duba ta ya kuma tabbatar musu ciki yana nan lafiya lau. Ya keɓe da Likitan ya tambaye shi ko zaya iya saduwa da ita babu matsala? Likitan ya ce babu wata matsala,don haka ranar suna dawowa daga asibitin misalin ƙarfe huɗu na yamma,nan ko ya sa ma ƙofa key, ya kuma shiga yi mata wasanni, duk da tana fargaban wuyar da ta sha, kuma tana tunanin ita zata ƙara sha,bai sa ta nuna fargaba ba. Sai gashi itama bata sha wuyar da tayi tunani ba,haka nan tun daga ranar itama ta shiga sahun matan gida, sannan yanzun ne ta san me ake yi wa kishin?.
Don haka ta ƙara yarda zata ƙyautata mishi,duk ranar da ita ce da shi ta kan shiga kitchen ta yi mishi girki da kanta,ga zoɓo mai sanyi, sannan duk lokacin da ya buƙace ta ba ta ɓata rai,ko jan aji tana ba shi dukkan goyon bayan da ya dace, shi yasa ta ƙara ɗaukaka cikin ranshi, ta kuma zarce duk matan nashi, har ya dinga Allah-Allah girkin ya zagayo kanta, haka nan duk abinda ta ce yanzun nan za'ayi shi,ko da ta yi mishi batun makaranta ta ce tuni an wuce ta a karatu, sai ya ce za ya samu (P.C) ɗinsu ya ga me zasu yi, koda ya samu (P.C) da batun cewa bata da lafiya ga jarabawa yana son su yi mishi taimako kullum za a ringa kawo ta ko kuma in suna da abu mai mahimmanci (P.C) ya yarda. duk da ba hakan ya taso ba,taji daɗin samun hakan,nan ko ta shiga zuwa makaranta.
Su ko su Jummai, sai suka shiga cewa don yaga tana da ciki shi yasa ƙarara ya ke nuna tafi kowa kuma ko gaban wane ne. Don haka kowacce ta tsaya ɗacin ran ba ya sonta, ta shiga fushi, tare da shiga faɗi tashin neman asiri. Hakan da suka yi na yin watsi da shi ya bashi damar more amarcin shi da A'isha, wanda bai yi a baya ba.
Duk ran girkin ta ya kan makara Ofis kuma ya dawo da wuri. In ya kalli madubi sai ya ce Beby kin sani na yi ƙyau fa,ko ba ki lura ba ne? Sai ta ce ai kai Uncle kullum mai ƙyau ne, komai naka yana da ƙyau. Ya ce har da ƴar Bebyna? Ta ce ai ni ba'a saka ni cikin jerin masu ƙyau, ya ce inji wa? Kina kallon madubi kuwa? Ai Beby har yau ni ban ga me ƙyanki ba, cikin haka suka soma jarabawa, dole ta zauna a ɗakinsu na cikin makaranta saboda suna karatu ita da su Samira,su Samira sun dame ta wai wane irin ciwo ne wannan da ya sakata yin shegen ƙyau haka? Ga wasu (hips) da ta yi,ƙirji kuma ya ƙara cika ta ce zaman gida ne kawai,ai ba za'a haɗa zaman gida da makaranta ba,sai dai cikin ranta ta saka duk ranar da suka yi banƙwana zata sanar da su cewa ita matar Uncle ce, haka suka ci gaba da jarabawa har suka gama. Ranar da aka yaye su,sun yi hotuna tare da canja lambobin waya,su da ƴan ajinsu, lokacin da za su rabu, Uncle ya zo tafiya da ita. Samira Suka ce in za ta yi aure ta faɗi musu,sai ta ce musu sai dai in zata haihu. Ta gaya musu cewa dama ta ɗauki alƙawarin yau zata sanar da su cewa Uncle mijinta ne. Dukkansu baki suka saki cike da mamaki. Ta ce musu yanzun haka ma ina ɗauke da ciki wata uku, zan sanar da ku in na haihu,ku kuma ina jiran bikinku don Allah da zarar ya zo in sani,nan suka yi banƙwana suna kewar juna.
Ta dawo gida suka ci gaba da zama da mijinta lafiya. Uncle na kula da ita sosai, sannan ba ta damuwa da lamarin su Hajiya Jummai, musamman da suka haɗe kai da Hadiza. Sun haɗa kansu, sai su zauna falo suna zuba mata habaici tare da su Suwaiba, musamman ranar da ya kasance ita ce da girki,nan fa za su yi ta surutunsu na cewa salon banza ana yi wa miji girki alhalin ga mai girki sai wannan ta ce ba dole ba ke ko abar wani ya yi ana son a zuba asirin mallaka duk da dai ba ta kula su kuma bata taɓa gaya mishi ba, cikin wannan halin ne wata ranar Litinin yana ɗakinta misalin ƙarfe ɗaya da rabi, haka kawai ya bar komai ya zo wai ya ganta da yaronshi, tana ƙwance kanta na kan cinyarshi, ya shafi cikin ta ya ce, Beby naga cikin ya ƙi ya yi girma ya fito ki dinga tafiya da ƙyar da ƙyar,na ƙosa in ga lokacin. Ta ce Uncle to cikin ƙwata-ƙwata watan shi uku fa, ya ɗaga rigarta mararta a shafe tamkar ba ta da komai, ya ce ni dai wannan cikin naki wane iri ne? Bai ƙara komai ba Beby? Kafin ta ba shi amsa sai ga Hajiya Jummai ta banko ƙofa babu ko sallama, ta ce ashe gaske ne,dama an ce kana zuwa kana cin amanar mu, tunda ai naga yau ba ita ce da kai ba, kuma yanzun ba lokacin dawowarka ba ne ka sato jiki ka dawo. Kallonta kawai yake yi sai da ta kai aya sannan ya dube ta ya ce,haba Jummai,me zai sa ki tsaya kina zubar da girmanki a gurin wannan ƴar yarinyar,ya kamata ace yanda take baki girmanki ki riƙe shi ni a zatona kece mace ta farko da za ki kula min da A'isha,da halin da take ciki,in na tuna yanda a baya ki ka fi ni son ki ga na samu ɗa, sai naga akasin haka, maimakon haka ma sai ki ka yi watsi dani da lamarina, kuma ki ka nuna tamkar kina faɗa da Ubangijinki, saboda ya bani ƙyauta, shawarar da zan baki,ki sake hali ki rabu da mugayen ƙawaye za su kai ki su baro. Ta soma kuka,ai ni yanzu komai ya zo bakin ka gaya min zakayi tunda mahaifata ba zata iya ɗaukar cikinka ba.
A'isha ta ce, to kiyi haƙuri Hajiya, Uncle ka koma Ofis shi kenan. Jummai ta daka mata tsawa ke makira, yi min shiru ba ke ce sanadin canza min halin miji ba,an je makaranta an roro ciki an zo an manna mishi, shi kuma da yake yana neman haihuwa ido rufe ya amsa jiki na ɓari,in da ka iya cikin me zai hana Hadiza kai mata in ni ba zan haihu ba.....ya katse ta da tsawa mai tsanani. Jummai kina hauka ne? Wace magana ki ke yi haka? Ya kama hannun A'isha wannan yarinyar ƙaramar yarinya ta fi min duka manyan matan da na aura, wannan yarinyar ita ce mace mai daraja ta farko a idanuna ni nan nine na yi mata ciki tunda kin tono bari in sanar da ke. A ranar da na kauda budurcinta a ranar cikina ya shiga jikinta, dan haka ki kama bakinki Jummai.
Ta fita tana masifar cewa eh dole ka ce kai,ni dai ban yafe satar min ƙwana da ake yi ba.
A'isha tana zaune ta zabga tagumi mamaki take yi wannan kuma wanne irin sharri ne? Hawaye suna zubowa daga idanunta,ya zo yana bata baki ta ce ka tafi Uncle ba komai. Ya ce, Beby ki zama mai haƙuri, ina nufin ki ƙara kan naki, ta share hawayenta tana murmushi ka koma Ofis Uncle, ya dinga bata haƙuri har sai da ta tabbatar mishi da cewa ita fa hayaniyar da suka yi ne wato sa'in'sar da suka yi ne yasa ta hawaye, nan ya fita yana shi mata albarka, A'isha ko ta maida ƙofa ta rufe.
Bayan sallar la'asar Wani bacci A'isha ta ringa ji,ta ƙi ƙwanciya saboda ta san cewa baccin la'asar ba shi da ƙyau,ko a musulunce, ta zauna tana kallo wai don kada baccin ya ɗauke ta. Da yake an ce gwanin sata ne baccin, sai ko ya sace ta har ma bata san lokacin da ta ƙwanta ba.
Can cikin baccin sai take jin numfashinta yana yin sama, ta soma kokowa da numfashinta, buɗe idanunta ke da wuya sai taga hayaƙi ta kowanne bangon ɗakin,nan ta shiga salati da ƙarfi tare da ihu, amma muryarta ba ta fita. Nan fa hayaƙin ya cika ɗaki, ya toshe mata numfashi.
Biyar dai-dai Uncle ya shigo gidan, ya nufi ɗakin Beby domin zuciyarshi ta kasa nutsuwa,yana shiga ya same ta kan gado tana ta mutsu-mutsu, numfashinta yana wuya ko sauka ƙirjinta ba ya yi, bakinta na ta motsi. Amma ba a jin me take cewa, sannan shi bai ga hayaƙin ba, ya ɗauke ta yana jijjiga ta,yana cewa Beby! Beby!! Ai ina ta daina ma motsin ta yi lagaf ƙasan zaninta kuma wata laima ya ji mai ɗumi,tana sauka a hannunshi, da sauri ya duba kun san me ya gani? Jini. Da ƙarfi ya furta jini?.
Tabbas jini ne, sai mun haɗu cikin kashi na uku don jin shin cikin da ake nema shekara da shekaru a ka sha wuya kanshi,ya zube? Asirin Hajiya Jummai zai tonu? Da sauran wasu abubuwan. Daga taku har kullum Halima K/Mashi.
Na gode