Author : Halima Abdullahi K Mashi Category : Tknovels
Cikin kiɗima Nafisa ta girgiza shi.
"Brother lafiya ka ke hawaye?"
Sam bai ma san yana hawaye ba.
Fatima ta fito da gudu daga banɗaki, tana cewa "Me ya faru na ji kin ce yana kuka?" Sadiya kam tana sallah, amma duk hankalinta na gurin,sai kawai gani suka yi ya juyo ya rungume Nafisa yana magana cikin rawar murya,tamkar kuka zai ƙwace mishi. Yana cewa, "Sister A'isha tana ɗauke da cikina!!"
Duk su ukun har da mai sallar suka furta cewa ciki? Ya yi ajiyar zuciya, ashe zan ga ɗan kaina? Murna suka shiga yi tare da yi wa Allah godiya. Nan suka shiga kiran iyayansu. Nafisa ce ta yi dacen kiran Hajiyarmu tana ɗagawa Nafisa ta ce Hajiyarmu A'isha na da ciki,Bros zai samu ɗa." Kalmar ta doki zuciyar Hajiyarmu, har ta kasa magana. Nafisa ta ce kin ji me na ce?" Hajiyarmu ta ce, "Allah ya inganta, ya bata lafiya." Ta ce,"Amin" Nafisa tana kashe wayar, Hajiyarmu ta miƙe ta ɗauro alwala ta zo ta soma nuna murnarta gurin Ubangiji, lokacin da take godiya ga Allah har da hawayen ta.
Uncle shi ne ya sanar da Alhajinmu wanda shima ya katse duk harkokin da yake yi a wannan lokacin ya sake nufo asibiti. Lokacin da ya iso, Uncle ya koma masallaci, inda ya zube cikin sujjada yana yi wa Allah godiya. Lokacin da ya dawo ɗakin su Alhajinmu, suna cikin ɗakin har da Likitan. Alhajinmu nan take ya yi wa Likitan ƙyautar mota, ya ce yaje gidan motocinsa da ke kan titin Isa Kaita ya zaɓi duk wadda yake ganin ta mishi. Kai yau kam duk wanda ke da dangantaka da su, sai da ya san A'isha na da ciki.
"Kai Nafisa, har da ƙawayanta ta ringa kira tana shaida musu, cikin ne da ita. Amma yanda suke murnar na A'isha abin da mamaki...
######
[12/15, 19:45] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 13*
Lokacin da Alhajinmu ya iso gida har lokacin Hajiyarmu tana zaune kan sallaya amma yanzun tana jan carbi ne, cikin tsokana ya ce ke ban ganki a asibiti ba, tunda na san dai kin samu labarin matar ɗan naki tana da ciki."
Ta sunkuyar da kai, "Me zan je in musu? Na san duk ƴan'uwanshi suna can." Ya zauna, "Naga fuskarki, ta nuna murnarki, tayi ɗan murmushi kana son jin ta bakina ne kawai,to na ce Allah ya inganta mishi, shikenan? Ya yi dariya na sani duk cikin ƴaƴaki kin fi son Abubakar,don haka yau babu wanda ya kai ki murna. Ta yi ɗan murmushi.
"Gaskiya ka faɗa." Ya sheƙe da dariya," Ashe dai kina son shi ki ke share shi? To yau zan gaya mishi ya daina min mita kan cewa shi baki son shi,shiru ta yi mishi.
Ku tambaye ni lokacin da ake wannan murnar ina su Hajiya Jummai da Hadiza suke? To sai in ce muku suna gida, labarin ya ishe Hadiza ne ta bakin mahaifiyarta wadda Alhaji Sunusi maigidanta wanda Alhajinmu ya yi mishi waya ya sanar dashi, cikin murna ya zo gidanshi ya sanar. Nan fa Hajiya Lanti ta ji tamkar labari mutuwarta ya zo mata dashi. Nan ta kira ƴarta tana son jin gaskiyar lamarin.
Haƙiƙa Hadiza ta ruɗe da jin wannan labarin, sai dai ta ce wa Hajiya Lantin tana shakka domin a saninta dai A'isha tana makaranta. Hajiya Lanti ta ce,an ce tana asibiti. Hadiza ta ce, zan dai bincika,nan take ta ɗauki waya ta kira maigidan.
"Assalamu alaikum,darling kana ina ne?" Ta tambaye shi.
Cikin murna ya ce, "muna asibiti da A'isha,na manta ban sanar da ku ba, A'isha tana nan asibiti."
"Me ya same ta?"
"Ciki ne." Ya bata amsa a taƙaice.
Ya kira layin Jummai lokacin tana lissafa kuɗin da zata kai ma wasu malamai guda biyu, ɗayan yana mata aiki kan Hadiza, ɗaya kuma kan A'isha. Ta ɗaga wayar cikin raha ta ce, "Maigidana na kaina." Ya ce, "Jummai yau dai Allah ya amshi addu'armu." Ta ce, "Ta me fa?" Ya ce,"A'isha tana da ciki." Da sauri ta miƙe tsaye, "Ci me?" Ya ce,"Ciki." Ta yi ƙoƙari ta saisaita numfashinta,"kai Allah mun gode maka,kuna asibitin ne? Ya ce eh,ta ce gani nan zuwa,ya ce dama na sani Jummai za ki yi murna,ta ce ai faɗa ma ɓata baki. Ya kashe wayar.
Jikinta har rawa yake wajen neman number Hajiya Karima,daƙyer ta samu taga number saboda fita hayyacinta da ta yi,tana ɗauka ta fashe mata da kuka "Na shiga uku!, Shikenan tawa ta same ni,ni nasan tawa ta ƙare."
Hajiya Kari ta ce,"Sakinki aka yi? Ta ce,wane saki ba gara a sake ni ɗin ba da wannan takaici! A'isha fa ke da ciki." "Ciki?" Inji Kari, Hajiya Jummai ta ce "Ciki kuwa," Hajiya Kari ta ce, to share hawayenki,ba sai mun barshi ba, sannan zai zo duniya,tankaɗar da ɗan iska zamu yi ya bi sokawe kawai,ai haka zai zauna yanda baki haihu ba babu shegiyar da zata haifa. Ki shirya zama guri ɗaya a tsautsayine. Hajiya Jummai ta ce, to sai na ganki Aminiya ta, mai maganin kuka na."
Suna gama wayar,ta zabga tagumi a yanzun babu abinda ya fi dacewa face ta bar batun fitarsu, ta koma kan batun cikin nan. Don haka ta soma tattara kuɗin guri ɗaya,tana yi tana magana ita kaɗai cewa take yo in ma ta fitar da ita alhali ga ciki ai nayi ta banza, tunda ɗan shi da ita zai zo duniya. Kaji masu ja da ikon Allah.
A'isha sai da tayi baccin wajen awa biyu sannan ta farka,Uncle dake zaune kujerar gefen gadon ya yi tagumi yana kallon ta,jin hannunta a riƙe ne yasa ta buɗe ido ta kalli ko ina, sannan ta kai dubanta ga Uncle ɗinta wanda ya ke kallonta cike da murmushi, ta ce har yanzun muna asibitin? Ya ce,eh muna asibiti, ta ce Uncle baka je Ofis ba? Ya ce, Ofis sai da lafiya ai Beby. Ta kalli ƙarin ruwan suna min ƙarin ruwa ne? Ya ce eh,ta ce gashi ina son inyi sallah. Ya ce za kiyi Beby,bari ki ɗan ƙara jin ƙarfi. Ta ce to. Ya ƙara matsowa kusa da ita,"kin san ciwon da ke damunki? Ta ce, a'a ya saka hannunshi cikin tafin hannunta ya ce "Beby ashe ɗana ne nake ta neman inda zan saka na sha wuya, Allah ya dube ni da rahamarshi ya sa ni na ɗauko ki tun daga makaranta na saka cikin mahaifarki. Beby don murna yau ji nake tamkar yau aka haife ni, nima zan zama uba,kina ɗauke da cikina ƙwana goma sha baƙwai." Ta juyar da fuskarta gefe don kunya.
Ya miƙe tsaye "Beby kina jin kunya ne? Yana magana yana ƙoƙarin leƙa fuskarta. Tasa hannu ta rufe fuskar, ya ce a'a Beby kada ki cuci ɗanmu,kada ki mishi yanda Hajiyarmu ta yi mini har yau na kasa yarda cewa tana sona kin ji? Ta ɗaga kai alamar eh, amma kanta na ta can gefen, ya ce to gaya min ki yi murna? Ta kuma ɗaga kai,kina son Bebyn? Ta kuma ɗaga kanta, ya ce na gode. Bari na ce ma Likita kin farka,bai ce dasu Nafisa ta farka ba,ya nufi gurin Likitan tare suka shigo da Likitan ya duba ta tare da tambayar inda ke yi mata ciwo,ta ce babu, sai dai jikinta Duk a gajiye,sannan bakinta babu daɗi, kuma tana jin yinwa sai dai ta san in ta ci zata yi amai ne.
Likitan ya ce, yanzun dai faɗa mana me ki ke marmari? Ta yi shiru tana tunani,can ta ce tuwo da miyar kuɓewa,tuwon garin masara. Uncle ya ce,to bari na sanar da Nafisa ta je tayo miki yanzun kin ji? Ta ɗaga kai. Likitan ya ce ya kamata dai ta sha ko ruwan tea ne haka saboda cikinta ya warware.
A'isha ta girgiza kai, tare da cewa,ba zan sha ba,in na sha tea bakina tsami yake yi, Likitan ya ce za ki jira har a kawo tuwon? Ta ce eh, Uncle suka fito da Likita. Lokacin ne ya ce musu ta farka suka shigo.
Nafisa tana cewa,"Maman biyu, Maman biyu" A'isha ta rufe fuska, Uncle ya shiga ya dubi Nafisa "Sister ki je ki yo mata tuwon garin masara da miyar kuɓewa,ya dubi Beby ɗin ya ce, wace irin kuɓewa? Ta ce ɗanye. Nafisa ta suri jakarta,ta ce bari naje na cika aikin Bebynmu. Ta fita tana cewa, sai na bi ta gidan Hajiyarmu na amshi garin,don ba ni dashi a gidana.
***. **** ****
Hajiya Jummai suka yi sallama ita da Hajiya Kari,ɗakin cike da dangin maigidan nata aka amsa musu. Ta shigo tana cewa, sannunku, sannunku fa. Ina A'ishan? Suka ce ga ta nan a ƙwance. Hajiya Kari ta ce sannu kin ji, Allah ya inganta miki. Hajiya Jummai ta ɗora hannunta a goshin A'isha tana cewa Allah mun gode maka, ashe mu ma zamu ga ɗanmu? A'isha ko jin hannun ta yi tamkar an ɗora mata dutse, ita tun fil'azal in dai Hajiya Jumman nan ta zo inda take gabanta sai ya yi ta faɗuwa,don haka yanzun ma addu'a take yi cikin ranta.
Hajiya Jummai kuwa saboda tsabar makirci sai ta kama kuka tana faɗin, ni ƴa su wannan yarinya kin share mana hawaye, shekaru sha baƙwai! Babu ɗa cikin gidanmu." Anty Sadiya ta ce, Jummai ki daina kuka, insha Allah sai kun samu dozin.
A ran Jummai ta ce,tir da maganarki tsinanniya amma a fili sai ta ce,amin Sadiya. Karima ta ce,ƙya koka Aminiya,kukan farin ciki ne" Fatima ta ce, "Nafisa ta daɗe ko in kira ta ne?" Anty Sadiya ta ce,ai Bros ya bita. Rufe bakinta ke da wuya sai gashi da sauri yana ɗauke da cooler, Nafisa tana biye dashi, itama ɗauke da ƙwando da su plate, Jabiru ya shigo ɗauke da ƙwalayan ruwan (EVER) da kalolin juice,ya ajiye ya koma ya shigo da manyan ledoji cike da tarkace
Hajiya Jummai dai suna gefe suna kallon ikon Allah,suna taɓa baki tare da girgiza kai ƙunci cikin zuciya kuwa ba a magana, shi ko maigidan sam bai ma kula da su ba.
Ya ja kujera ya zauna gaban gadon, ya ciro waya ya kira Likitan yana shaida mishi sun kawo mata abincin, Likitan ya ce, gashi nan zuwa. Ya shigo Nurse's ke biye da shi ɗauke da ƙwanonin silver, Likitan ya dube ta da murmushi ya ce, sannu Madam. A'isha dai hannunta na kare a fuskarta,ya ce da Nurse's ɗin bata ta wanke bakinta,ta shi ko? Ta yunƙura kafin ta ankara tuni Uncle ɗin ta ya ɗagata zaune yasa filo ya jingina ta, kunya duk ta rufe ta. Ya amshi ƙwanan daga hannun Nurse ɗin ya ce Nafisa bani ruwa ɗaya a can cikin ƙwalin,ta miƙo mishi ya ajiye ƙwanon kan cinyarta ya buɗe ruwan,ta ce kawo zan iya da kaina. Likitan ya cire mata ruwan da ake ƙara mata. Ta kuskure bakinta, Nafisa ta miƙo mata tuwon nama ya yi wa tuwon zube, Uncle ya amsa ya ajiye mata a cinyarta,ta taɓa baki ta ce,a cire naman,ya ce to Nafisa cire mata naman. Aka cire ta kuma cewa a rage tuwon. Ya ce,ki ci iya cinki, in kuma ba zaki iya ba, bari na baki ko? Ta ce, a'a zan iya sai dariya su Nafisa suke mata.
Ta soma ɗan ci loma ta uku ta ajiye ta ce ta ƙoshi,ya ce, haba Beby ɗan ƙara mana,ta ci kaɗan nan fa zuciyarta ta soma tashi. Da sauri ta miƙa mishi ƙwanan kafin ta ce wani abu tuni ta soma sheƙo amai. Kai kawai ya riƙe yana kallonta,kowa sai sannu ya ke mata,su Hajiya Jummai dai ana ta kallon ikon Allah,da ƙyar aman ya tsaya.
Nurse suka shiga gyara wurin. Ya ba Nafisa makullin ɗakin A'isha ya ce, "Ki ɗauki mata kaya ta cire wannan Uniform ɗin ta amsa ta fita.
Bayan an gama gyara komai, dole sai dai ruwan aka maida mata,jim kaɗan bacci ya ɗauke ta don ya yi mata allurar bacci, cikin ruwan.
Koda aka kira sallar magriba, Uncle ya ce to duk su koma gidajensu. Nafisa ta ce wa zai zauna da ita? Ya ce, shi ne suka sa dariya, tare da cewa, "haba dai" ya ce Allah kuwa. Nafisa ta yi wa mijinta waya ya ce gashi nan ma cikin asibitin. Shigowarshi Katsina kenan daga Kaduna,ko gida bai je ba.
Bayan sun gaisa ya taya abokinshi murnar samun ƙaruwa. Nafisa ta nemi iznin zama da A'isha, jin cewa Alhaji Saddiƙ ne zai zauna, Alhaji Bello ya ce, ya yarda Nafisa ta zauna tunda su Fatima duk suna da yara.
Hajiya Karima ta kira Jummai gefe ta ce,sakarya ki zauna da ita mana in yaso na amso magani sai mu kaɗar da shegen cikin tun daga nan. Hajiya Jummai ta ce,jinina zai iya hawa ba zan baki a ɓoye ba, matsawar zan cigaba da kallon yarinyar da kuma rawar jikin da Alhaji ke yi kanta,wai baki ga dauriyata ba ne wannan zuwan da nayi ma? Ni dai gobe mu shirya mu bazama."
Ƙarfe taƙwas daidai su Hadiza da Hajiya Lanti suka shigo,su da shirinsu ma suka shigo. Hadiza tana ɗauke da kula anyo farfesun kayan ciki wanda ya ji haɗin magungunan salwantar da ciki. Cikin raha Hadiza ta shigo, ina A'ishan ƴar'uwa rabin jiki, lokacin ta farka tana ƙwance.
Nafisa kuma tana sallar Isha'i, shima Uncle yana masallaci. Hajiya Lanti ta ce sannu ƴar nan,kin ji Allah ya raba ki lafiya. Mun yi murna mun yi farin ciki." Nafisa ta idar suka gaisa ta ce, Nafisa ke ce gurinta? Nafisa ta ce,eh, Hajiya Lanti cikin makirci ta ce,haba dai ga ƴar'uwarta ba sai ta zauna ba? Kema sai ki koma gidanki,ki ji da kanki" Hadiza ta ce,ai kam ki tafi kawai". Nafisa ta ce, a'a ai babu komai maigidana ne ya ce in zauna. Hajiya Lanti ta ce, to shikenan.
Hadiza ta buɗe kular hannunta, ta ce ga farfesu na ɗan yo miki ko za kiji daɗin bakin ki." Ƙamshin shi ya doki hancinta, ta ce to na gode." Nafisa ta taso tana cewa,anya za ta ci? Komai ta ci fa sai amai. Hajiya Lanti ta ce "Wayyo, amma kuma kin san ciki sai ki ga in ta ci wani abin ya zauna,in tana so a barta ta ɗan taɓa" Nafisa ta ce to." Ta kalli A'isha za ki ci ne? Ta ce eh, Hajiya Lanti da Hadiza suka kalli juna, suka yi murmushi. Nafisa ta lura da hakan da suka yi don ta gani,don haka sai ta tsargu da wannan girkin,don haka sai ta ce to bari Uncle ɗin yazo ya kira Likitan don ya ce duk abinda ta ce zata ci sai yazo tukunna.
#######
[12/16, 08:36] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 14*
Hajiya Lanti ta ce,ke rabu da su, waɗannan likitocin masu tsirfar tsiya,ba ni plate nan ki gani in bata. Nafisa ta ce,ki dai yi haƙuri mu bi dokarsu kada ta ci ta kuma yin aman su ce sun faɗa mun ƙi ji. Hadiza ta ce, haka ne kuma a bari ɗin. Tana magana tana taɓa Hajiyar alamun ta bari.
Uncle ɗin ne ya yi sallama ya shigo da sauri Hajiya Lanti ta ja baya tana faɗin sannu da shigowa Alhaji, ya amsa da cewa yauwa sannu da zuwa. Suka gaisa har tana durƙusawa. Ta ce,ya ya me jiki? To Allah ya inganta mana yasa a sauka lafiya, ya ce Amin nagode. Hadiza ma cike da fara'a ta gaishe shi, tare da yi mishi murna. Ta ƙara da cewa, insha Allahu ƴan biyu zata haifa,sai a bata ɗaya. Ya ce, Allah ya bi bakinki Hadiza. Hajiya Lanti tana dariya tana cewa,kai waɗannan yara.
Ita dai A'isha tana ƙwance tana jin su. Ya matso kusa da gadon ya duƙa ya ce "Sannu Beby" a hankali ta ce,zan ci naman da su Hadiza suka kawo,da hanzari ya ce Nafisa zuba mata,me su Hadiza suka zo dashi? Wai zata ci. Nafisa ta ce, sai in Likitan ya zo,ɗazun ya ce kada ta kuma cin wani abu sai in yazo. Hajiya Lanti ta ce,ni dai na ce da kun bata,ba lallai ne tayi aman ba. Nafisa ta ce bari dai in kira Likitan.
Uncle ɗin ya tashi, bari in kirashi ta ce zauna kawai Bros,bari na kirashi,ta fita. Ko da ta samu Likitan cikin Office ɗin shi, suka gaisa ta ce mishi,ta zo ne don Allah ya yi ma yayansu magana ba kowa ba ne zai kawo abinci ta ringa ci, saboda yanda ya daɗe babu haihuwa, wasu za su yi baƙin ciki,da samun cikin musamman kishiyoyinta,don haka ya zo yanzun ma an kawo wani nama wai zata ci, kuma ita bata yarda da naman ba,don haka tana son ya hana ta ci. Da hanzari Likitan ya miƙe tare da cewa, Madam nima nayi wannan tunanin,ba zan so wata matsala ta faru ba,na gode da wannan taimakon da ki kai min."
Likitan ya shigo suka gaisa da Uncle ɗin,ta hanyar riƙe hannu. Ya ce,ka ce inzo? Uncle ya ce eh, wani nama ne aka kawo shine take son ci. Likitan ya ce, "Yallaɓai ba zata ci komai ba yanzun ba sai zuwa da safe, saboda wannan ruwan da muke ƙara mata yana tare da abinci,ba ma buƙatar ta ci komai yanzui."
Fuskar su Hajiya Lanti Nafisa ta kalla, sai ko taga sun kalli juna da ɓacin rai. Likitan ya fita tare da cewa,in ka fito ina Ofis,ya ce to Doctor nagode."
Hajiya Lanti ta ce, to ni zan tafi ke zaki jira mijinki ne? Ta ce , to. Tana dubanshi ya ce to jira sai muje ɗin. Hajiya Lanti ta ce to bani cooler in tafi da ita mu ma ci can ko? Hadiza ta ce to ko Nafisa tana so? Nafisa ta ce a'a nagode." Ta ɗauki kular,wai bari ta rakata ta hau mota. Nafisa ta ce , to.
Suna fita shima ya nufi gurin Likita, Nafisa ta koma kusa da A'isha ta ce,ke wace irin wawiya ce zaki ce za ki ci? So kike ɗan cikin muna murna kisa ayi watsi dashi? Baki san su Lanti ba ko? Kar su kuma kawo wani abu ki ce za kici kin ji ko? Ta ce,to. Shima Uncle ɗin naki yasan komai don dai su maza ba su cika ɗaukan irin waɗannan abubuwan da mahimmanci ba ne, likita ya ce baya son kowa ya kawo abu ace ki ci, ya yi taka tsantsan, duk abinda tace tana so ta ci