MUMMUNAN ZATO 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY K MASHI

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 35.5K words

to ya kasance shi ne zai sa waɗanda zuciyarshi ta yarda da su su dafa mata. Uncle ya ce shikenan. Likitan ya ce ko gidan mahaifiyarka kawai ya fi dacewa a dinga kawo mata duk me zata ci,ya ce ƙwarai kuwa na gode insha Allah zan kiyaye.

Hadiza kuwa suna tattaunawa da mahaifiyarta kan cewa, duk wannan Nafisar ce ta ɓata musu shiri, Hajiya Lanti ta ce,ni ba wannan ne matsalata ba, damuwa ta kuɗin da na kashe gurin amso wannan maganin. Kai ina ma wannan cikin jikinki yake,kinga tun cikin asibitin nan sai mun ƙwashi kuɗi. Hadiza ta ce,ke dai bari, Hajiya yanzun ya ya zamu yi da wannan abin? Lanti ta ce wa? Ai tunda ranta na so sai ta ci shi, gobe zan ɗinɗima tunda yau ne aka ce kada ta ci saboda ana mata ƙarin ruwa, gobe da sassafe in zaki taho ki biyo ki amsa. Ki zo mata dashi,sai ki ce wani ne ki kayi. Ta ce, to shi yasa ai na ce su bari na tafi da shi tunda ba zasu ci, tunda ba nice nazo dashi ba,na su zaton ke ce ki ka dafa. Haka ne inji Hadiza, zan biyo, suka yi sallama,ta dawo Hajiya Lanti kuma ta hau mota.


**** *****. ****

Goma dai-dai Uncle ya kula Nafisa tana hamma, A'isha tuni ta yi bacci,don haka ya miƙe ya je bakin A'isha ya tsugunna ya sumbaci kumatunta, sannan ya zo gurin Nafisa ya ce "Sister tashi ki je ki ƙwanta kema sai da safe." Hadiza ma tayi musu sai da safe, sannan suka fita.

A cikin mota take ce mishi "Darling amma ran A'isha ya biya da naman nan ko in yo mata wani gobe tunda tana so? Gashi ance mace mai ciki in ta buƙaci abu a bata in dai da shi kada ta haifi ɗanta da tabo." Ya yi ɗan murmushi, "inji hadisin hausawa ko?" Hadiza ta ce, "Allah gaske ne." Ya ce,to ki kawo mata, amma fa ba lallai ba ne ta ci tunda Likitan bai ce da safe zata ci wani abu,kai ko dai ki barshi kawai ma." Hadiza ta ce, a'a zan mata ko bata ci ba na san mutanan gurin za su ci, ya ce shikenan.

Ranar ƙwana Uncle ya yi yana sallah, ya kasa bacci. Washegari tunda Asubahi ya kira Abbanta. Bayan sun gaisa, Abba ya tambaya ko lafiya? Uncle ya ce, A'isha ce bata jin daɗi ba, tana asibiti. Abba ya ce, "assha gado aka bata kenan?" Uncle ya ce wallahi, amma da sauƙi ba sai kun zo ba. Sannan ka taya ni addu'ar Allah ya sauke ta lafiya. Abba ya ce,ashe? Lallai nayi murna Friend, Allah ya bamu masu albarka. Uncle ya ce Amin. Daga nan ya nufi asibitin don yaga yanda suka ƙwana. Zaune ya same ta tana sallah, gaskiya yaji daɗi sosai,ya zauna har ta idar ta juyo ta dube shi, ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby ya ya jiki? Ta sunkuyar da kai ta ce,da sauƙi. Ya ce ina Nafisa? Ta ce ta shiga wanka. Ya ce,to daƙyau,kema kin yi ne? Ta ce eh, nayi shi ne na ji ɗan ƙarfi. Ya ce su Abba suna gaishe ki,ta ce gaya musu ka yi bani da lafiya? Ya ce eh mana, har ma nace musu kina da ciki." Ta saka kanta a gwiwarta tare da faɗin haba dai don Allah. Ya ce to mene ne? Ta ce,ni ina jin kunya yanzun su Hajiyarmu sun ji? Ya yi murmushi.

"Sun ji mana,tun lokacin da Likitan ya sanar damu."

Ta ce, "Shi kenan ba zan kuma zuwa gidan ba" ya ce "Don me?" Ta dube shi, yanzun kowa ya san abinda na yi na samu cikin kuma? Ya yi dariya, sannan ya ce, a'a ba wanda zai sani,ke da ki ke makaranta, wasu za su ce a ruwa ki ka sha." Ta ɗan yi murmushi don ganin ya maida ita doluwa,ta ce "Ai na san ba'a sha a ruwa." Yasa dariya.

Nafisa ta shigo tana cewa "Bros ka zo kenan?" Ya ce, "wallahi ya ya kuka kwana?" Ina ta tunanin dare? Nafisa ta ce bacci sosai mu ka yi kaga gashi har ta yi wanka,ta yi sallah. Ya ce aiko naga da sauƙi yanzun me zaku ci inje gidan Hajiyarmu in sa ayo muku? Nafisa ta ce,Mama two me zamu ci? Ta ɓata rai Anty Nafisa bana so, Uncle ka ce ta bari fa, cikin murmushi ya ce , Sister bama so gaskiya, ya dubi A'isha ƙyale ta Beby gaya min me zaki ci? Ta ce,da zan samu waina ko irin ɗan waken nan? Ya ce zaki samu ya miƙe, har ya fita. Ya dawo zaki ci farfesun irin na jiyan a zo miki da shi? Ta ce a'a, ya ce shi kenan.

Hadiza ta zo lokacin suna karyawa. Hadiza ta aje mata kular a gaba gashi kin ji ƴar'uwa na yi miki wani ne. A'isha ta ce na gode, yanzun kam na ƙoshi amma anjima zan ci. Ta miƙa ma Nafisa ta ce Anty Nafisa gashi ki sa can gefe kada ku ci min fa. Nafisa ta ce, to A'isha Hadiza kam daɗi ne ya rufe ta.

Hajiya Jummai kam an bazama nema,an nemo kuma an samo,ana kan aiwatar wa. Satin A'isha ɗaya a asibiti, ta samu sauƙin aman. Sai dai kasala tare da tsirfa iri-iri har yau abinci in ba daga gidan Hajiyarmu ba ne bata ci. Hajiyarmu kuwa ko yaushe mai aikin ta tana kicin tana dafa duk abinda A'isha ta buƙata, sannan addu'o'i ko yaushe tana nan tana tofa mata su cikin ruwa tana sha. In za'a kawo abinci sai an kawo, shi kam Uncle shi ne mai jinya, duk wadda yake ɗakinta zai je ya bata haƙƙinta in ya kintsa jikinshi zai dawo gurin A'isha.

Ya lura da ita, musamman saboda dare Hajiya Jummai ce ta so ta nuna rashin amincewarta ya ce haba Jummai,in kin lura A'isha tana buƙatar kula,ba fa wai ta samu sauƙi ba ne, dole sai da mai kula in kuma da wanda ya dace ya kula da ita,to ni ne. Ta dai ƙyale shi ne kawai.

Kullum sai Ummanta da Abbanta sun kira ta sun tambayi jikin umma ta kan bata shawarwari masu kyau game da rainon ciki. A daddafe cikin ya yi wata biyu, suka yi waya da Samira inda Samira take cewa wannan satin ne za'a koma makaranta, ta ce, ina sane ni da nasha ciwo kamar ba zan tashi ba tun daga wannan dai ciwon? Samira ta ce ayya amma me yasa ba a samun wayarki? Ta ce,ke dai bari,ni da tunanina manta da batun wata waya, sai dai mun haɗu a makaranta. Samira ta ce to shikenan, Allah ya sawwaƙe, A'isha ta ce Amin.

Koda Uncle ya dawo ta ce mishi an koma makaranta, sai ya ce mata wace makaranta? Beby gaskiya ba zaki koma makaranta da ciki ba." Ta dube shi cikin rashin walwala ta ce, Uncle kana nufin ba zan zana (S.S.C.E) ba? Ya ce haba Beby,ke sai ma ance miki,kina ganin yanzun ban bari ki yi nisa da ni? Ta ce, gaskiya ba zan so haka ba, wata uku fa kawai ya rage min in gama duka,don Allah Uncle ka daina wannan maganar." Ya ɗaure fuska wata shekarar kin zana, ganin yanda ya ɗaure fuska, abin da bai taɓa mata ba,sai ta yi shiru ta kifa kanta kan filo, shi kuma ya fita abinshi. Kuka ta ringa yi wiwi,na ta ganin Uncle bai mata adalci ba, ita a nata son ran ta koma makaranta tunda ba wanda ya san tana da ciki, har ta gama.

Da daddare ko da ya shigo ta bashi ruwa, sai dai ba ta cikin walwala,ya amsa yana sha yana kallon fuskarta, wadda ta kumbura ta yi dam. Ya aje kofin da sauri,me ya samu fuskarki Beby? Ta sunkuyar da kai babu komai, ya ce ban yarda ba kin yi kuka ko? Ta ɗago ta ce mishi, a'a sai hawayen da take maƙalewa suka zubo ya kama hannunta suka zauna, yanzu saboda na ce ba ki komawa makaranta ba shi ne ki ke kuka? Beby na fiki son karatun ki domin alƙawari na ɗauka cewa zan tsaya har sai kin ji da kanki cewa kin gaji da karatu, amma yanzu koda ba ciki duka-duka yaushe aka sallamo ki daga asibiti? Ba ki gama murmurewa ba" Ta ce, Uncle ko a makaranta fa zan kula da kaina." Ya yi shiru yana kallonta,sam baya so ko kaɗan ya ga yarinyar cikin damuwa, ya ce to daina kuka za ki koma, amma sai kin ƙara murmurewa, sannan in naga kina cin abinci. Ta ce, to Uncle zan dinga ci. Nan fa A'isha ta dinga ƙarfafa jikinta don kawai ta samu ta koma makaranta, sai dai duk da haka cikin nata mai saka laulayi ne da tsirfar zan ci kaza ba zan ci kaza ba,ga saurin fishi. Wata rana tunda safe ta ce da Uncle idan zai dawo ya zo mata da agwaluma, ya ce ni kam ina zan ga wata agwaluma? Ba na zaton cewa duk Katsina za'a samu agwaluma, amma zan sa a duba. Yinin ranar neman agwaluma gurin mutum huɗu ya baza,neman agwaluma. Ita kuma tana ta yi mishi waya a ƙarshe washegari a Kano aka siyo cikin baƙar leda ya tashi Jabiru ya dawo gida lokacin ƙarfe uku na rana ya same ta tana shan ƙanƙara ta fiya wota, ya ce Beby me yasa kike shan ƙanƙara? Kada in sake gani ta ce, to da ya aje mata ledar agwaluma komawa ya yi gefe yana kallonta, da gudu ta tashi ta ɗauko ruwa a firij ta wanke ta soma sha hannu baka hannu ƙwarya. Tausayinta ya cika shi, ya ce Beby bana son wannan gudun da ki ke yi,kin ga cikin ki bai yi ƙwari ba,ta ce na daina.

Washegari kuma ta ce zogala, gidansu Hajiyarmu ya yi waya aka kawo mata shi da yawa,ta yini ci. Irin waɗannan abubuwan suke sa Uncle tunanin yanda zata zauna a makaranta,ba za'a bari a zo kullum ba,week end ɗin da yake zuwa sun gaya mishi don shi ne, sannan ita abin tattalin shi ce,a yanzun saboda mutane da yawa suna bashi shawara kan cewa ya kula da ita sosai, saboda maƙiya ko ɓarayi masu yin garkuwa da mutum don su amshi kuɗi irin waɗannan abubuwan suna sa shi tunanin barin ta ta koma, amma ya san makarantar su akwai tsaro, sannan albarkacin addu'ar da yake yi ko yaushe Allah zai kare mishi ɗan shi.




######
[12/17, 11:31] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 15*



Cikin wannan halin wata rana A'isha tana ƙwance da daddare, Uncle yana ɗakinshi,yau Hadiza ce da girki,tasan komai dare zai dawo ɗakinta,don haka ba ta murɗa key ba. Shiru-shiru har ɗaya ta wuce, ita ko bacci na cin ta, don haka ta rufe ƙofarta,ta ƙwanta tana karanta addu'ar bacci ta gama bata gama ba oho bacci ya yi awon gaba da ita. Can cikin baccinta sai wata ƙatuwar mage ta nufo ta, nan suka soma gabza dambe ta nayi tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta,mage ƙoƙari take ta cafko mata cibiya, Allah bai bata Sa'a ba, suka yi wa juna kaca-kaca duk ta yayyaƙushe A'isha, itama ta ji ma magen ciwo. A tsorace ta farka da addu'a, sai me,magen ta gani a kan durowar gefen gadon ta murtukekiya. Ta yi wani tashi ta nufo ta,da matsanancin tsoro ta ƙwala ihu tare da kai ma magen nan duka da filo,ta miƙe tana waige-waige saboda bata san in da magen ta shige ba,ta nufi ƙofa da gudu tana salati, tana buɗe ƙofa Uncle yana fitowa, shima da gudu saboda duk wanda ke gidan ba zai ce bai ji ihunta ba.

Hanyar fita ta nufa ya yi sauri ya riƙo ta, ta sake ƙwala wani ihun tana ƙoƙarin fizgewa. Abinda ya bashi mamaki, wani mugun ƙarfi ya ji ta yi. Ta ƙwace zata fita, ya kuma damƙo ta da ƙyar,ya kai ta ƙasa ya danne ƙafafunta da hannuwanta. Nan ya shiga tofa mata addu'o'i, sai ta yi laƙwas. Ya ɗauke ta zuwa ɗakin yana shiga ta soma ihu da sauri ya fito da ita kan kujera ya ƙwantar da ita yana tofa mata addu'o'i.

Hajiya Jummai tana leƙensu ta window, haka Hadiza daga falonshi ta leƙen su. Hajiya Jummai ta fito da sauri tana cewa, "Lafiya Alhaji?" Ya ce, wallahi nima ihunta na ji. Ta zo ta tsugunna tana cewa, A'isha me ya faru ne? Ina, A'isha sai wani gunjin kuka take yi. Addu'a dai yake ta tofa mata, Hadiza ma ta fito suka zauna cirko-cirko. Jummai tana ɗan mutsu-mutsunta da baki tana tofa mata amma a zukatan su farin ciki suke yi, kowacce tana zaton nata asirin ne ya ci, kafin safe ta yi wani sharaf ta daina gunjin kuma bata ko motsi.

Tun cikin daren ya kira Alhajinmu ya sanar mishi, ya ce mishi ko su wuce asibiti? Alhajinmu ya ce, a'a ya bari sai zuwa da safe. Suna idar da sallar Asubahi sai ga Alhajinmu,ba za ya iya tuna zuwanshi na ƙarshe gidan ba sai ko yau.

Lokacin da ya iso su Uncle ɗin suma fitowar su kenan daga Masallacin. Duk ya yi zuru-zuru yana sanye da farar jallabiya. Alhajinmu ya zuba ma A'isha idanu, inda take ƙwance kaman ruwa. Ya dubi ɗan nashi ya ce, Abubakar wai ya ya abin ya faru ne? Uncle ya ce , nima ban sani ba, ihunta kawai na ji na fito, da na kamata ma zan maida ita cikin ɗakinta sai ta fara ihu.

Hajiya Jummai ta ce,ko mafarki ta yi ne,ni ƴasu?. Uncle ya ce in kaga yanda muka dinga cin dambe da ƙyar na kai ta ƙasa, na soma karanta mata addu'o'i. Alhajinmu ya nufi hanyar fita, Uncle ya bishi.

Bayan sun fito suka tsaya a harabar gidan, ya dube shi.

"A gaskiya Abubakar al'amarin yarinyar nan ba na zaton na asibiti ne, Malamai zamu samu. Uncle ya ce , to yanzu ya ya za'ayi? Alhajinmu ya ce, yanda za'ayi shi ne,a saka ta a mota mu tafi da ita can gidanmu, Allah ya yi mana jagora.

Haka Uncle ya ɗebo ta yaraf,ya ƙwantar bayan mota. Hajiya Jummai ta ce, asibitin za'a ko? Ya ce, a'a bai tsaya wani dogon bayani ba ya wuce ya shiga mota, don hankalinshi ya tashi na ƙarshe. Jummai da Hadiza suka tsaya jikin motar suna to Allah ya sawwaƙa. Alhajinmu ya shiga gaban motar, direba ya ja suna cewa Allah ya sauwaƙe." Alhajinmu ne ya ce,ku koma gida kun ji? Kada ku damu, Allah zai kawo sauƙi.

Hajiyarmu tana zaune cike da zullumin wane hali ƴar mutane take ciki? Jiran dawowar maigidanta kawai take yi,ta ji labarin jikin, sai ga su sun yi sallama. Uncle ɗin yana rungume da ita, tamkar babu rai, ta miƙe cike da sallallami, tana cewa,ya ya haka? Uncle ya zube ta kan kujera. Hajiyarmu ta isa gurinta tana tofa mata addu'a, Alhajinmu ya ce ina ganin lamarin kamar na jinnu, shi yasa na ce mu yi nan da ita. Yanzu zan je gurin Malam Yakubu ne yazo ya duba mana ita, suka ce to. Uncle ya zauna yana gaida mahaifiyarshi, Hajiyarmu ta amsa cike da jimami, sannan ta ce ya ya akayi haka? Nan ya shaida mata duk yanda ya sani, ta tausaya sosai. Ta kuma ci gaba da addu'a, Alhajinmu ya shigo shi da malam Yakubu,da kuma wani Malam Sufi,suka zauna suna tofa mata addu'a, tana nan dai yanda take can Malam Sufi ya soma karanto alƙur'ani mai girma cikin Suratul Baƙara,nan ta soma motsi ya matso kusa da ita yana yi cikin ɗaga murya, sai kuma ta soma gunjin kuka cikin wata irin murya. Malam Yakubu shima ya amsa. Ai tuni ta soma fizge-fizge, suka ba da umurnin a riƙe ta, Uncle ya riƙe ta gam,tana fizge-fizge. Suka ce wane ne? Wata ƙatuwar murya ta soma magana,ni ne. Kai ne wa? Ni ne umm! Umm! Suka ce kayi magana kaine wa? Ya ce sunana Sulaiman, suka ce me ya kawo ka jikinta? Ya yi shiru,nan Malam Sufi ya ci gaba da karatu, shi kuma Malam Yakubu yana mishi tambaya,ba za kayi magana ba? Ya ce,kuna ƙona ni fa zan fita, to faɗa mana me kazo yi jikin wannan baiwar Allah? Ya ce turo ni aka yi,an umarce ni ne da inzo in sakar mata jini in fitar da cikin ta. Suka ce kai Musulmi ne? Ya ce eh,ka yarda da Allah da ranar tashin alƙiyama? Ya ce eh, na yarda,to me yasa kazo ka cutar da ita? Ya ce,an sani ne. To wa ya saka? Ya ce Ubangijina,shi Malami ne ni da mahaifana muna ƙarƙashin ikon shi ne. Suka ce to yanzu zaka fita ne ko mu ci gaba da karatu? Ya ce,zan fita. Suka ce to fita ta baki ko ta hanci,sannan ka ji tsoron ranar tsayuwa a gaban Ubangiji ko da ba jinsin ku ɗaya da ita ba, akwai hisabi tsakaninku ko? Ya ce,eh, suka ce to maza ka fita. Nan take ta yi atishawa mai ƙarfi sau biyu. Jim kaɗan ta buɗe idanu, ta tsura ma silin ɗin ba. Uncle ya ce, A'isha? Jin muryar Uncle ɗin ta, sai ta yunƙura,ya riƙe ta ya tada ita zaune ta ringa kallonsu cikin mamaki. Ta dubi Uncle, me ya faru Uncle? Ya ce ba komai,sai sannu suke mata. Alhajinmu mamaki yake tamkar tatsuniya. Hajiyarmu kam har da hawaye don tausayi,nata ganin ba su yi mishi adalci ba,ko waye ya turo su? Yaro shekara da shekaru sai yanzun ya samu rabo amma har ya tsole ma wani idanu, Uncle kam burinshi ta tashi,shi dai lamarin shi ya bar wa Allah, addu'a yake yi kullum Allah ya shige mishi gaba, kuma ya kai ƙararshi gurin Allah duk wanda ya ke son ganin bayan ƙwanshi a duniya.

Sun bada magunguna irin su habbatus sauda, zaitun, sai garin itacen magarya,sun ce ta ringa yin azkar safe da yamma, sannan ta zama mai yawan jin alƙur'ani.

Alhajinmu da Uncle sun musu rakiya tare da godiya gami kuma da yi musu alkhairi mai yawa. Hajiyarmu ta matso kusa da A'isha wadda ta jingina da kujera duk gaɓoɓin jikinta ciwo suke mata,ta so ta san yaushe ta zo gidan su Hajiyarmu? Ta ce,ƴan

11 / 12