MUMMUNAN ZATO BOOK 1 COMPELET HAUSA NOVELS

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   8 / 10

21K to 24K   out of 29.7K words

ku zo muje in kai ku masaukin ba?i,in ya so sai amaryar da ?awayanta su ?wana a nan. Suka ce to, suka mi?e suka bi ta sai sa'anninta uku aka bari.

Ita dai tana zaune kan sallaya,Wakin ba?in yana da girma ga ?aton gado sannan ga wasu manyan katifu guda biyu an baje duk sun sha shinfiWa. T.V na bango ne a Wakin kamar dai na falon sai dai shi ?arami ne,ga (AC) ga kuma bayi. Ta buWe wordrobe ta ciro musu manyan barguna kasancewar lokaci ne na sanyi, sannan ta ciro parnpas ta ce, masu yara gashi nan suyi musu nafkin,ta kunna musu T.V tashar da ake yin wasan Hausa,wato fim Win Hausa. Ta ce,in zaku yi bacci sai ku cire soket Win, kada ku manta da yiwa yara addu'a kun ji ko? Ku karanta musu ?ulhuwallahu,fala?i da Nasi ?afa uku-uku, da kuma ayatul kursiyu duk ku shafe jikinku da shi dana ?a?anku, suka ce to mungode fa Hajiya, Allah ya saka miki da alkhairi,ta ce haba ba komai sai da safenku,ku huta gajiya suka ce to Allah ya bamu alkhairi,ta fita ta ja musu ?ofa,su kuwa suna ta yabonta da cewa Allah ya saka mata tana da kirki,lallai A'isha ta yi dacen dangin miji da kishiya,ita kuwa fita ta yi tana cewa ?an iska ba zaku gane ba ne sai kun zo zaman makoki.

Ita ko A'isha tana nan zaune kan sallaya ta zuba tagumi, yayin da su Naja suka yi Wai-Wai kan gado har sun soma bacci saboda gajiya zuciyarta ta nata neman dalilin da yasa Wazun da Hajiya Jummai ta zo musu sannu da zuwa gabanta ya yi mugun faWuwa, yanzun ma haka. Tana sallama ta ji gabanta ya faWi,in ko haka zata ci gaba da ji lallai zata bani tunda guri Waya suke. Ta soma tambayar kanta da cewa menene ma na jin tsoron ta ko faWuwar gaba dan ta ganta? Mace mai karamci da mutunci.

?wan?wasa ?ofar tare da buWewa ne ya katse ta,a hankali ya yi sallama tamkar yana ciwon baki,ko kuma baya son ya tashi ?aramin yaro. Kanta na ?asa ta amsa, amma bata Wago kai ba,ya tako har gabanta ya tsugunna,sam bata ma san ya iso ba, sai dai ta ji yace Beby (a hankali) ta Wago idanu ta zuba mishi. Yana sanye da wandon jeans ba?i da rigar sanyi tafkekiya ta sa?ar ba?in zare da fari, sai ta ganshi tamkar Wan matashin saurayi,ko kusa ba ya kama shekarunsa,?yawun fuskarshi ya sake fitowa saboda ?ar rama da ya yi,ta sauke idanunta ?asa, hancinta yana ci gaba da sha?ar ?amshinsa,ya yi Wan murmushi yanda Bebyn tasa ke dubansa, cikin yanayin damuwa ya ce Beby baki ci abinci ba, saboda me? Ta gyara zama bana jin yunwa ne Uncle, ya ce Nafisa ta ce min kina cikin damuwa ko ruwa ba ki sha ba,why Beby? Kina fargaba ko? Ta ce ba haka ba ne Uncle, ya ce to gaya min ya ya ne? Ta rasa me zata ce, ya ce ok,kina tunanin cewa in kinci wani abu na gidan nan shi ne zaki mutu ko? Da sauri ta dube shi, Uncle ba na nufin haka, ya ce to in ba ?ya nufin haka ki ci wani abu in gani, ta ce to,ya ce me ranki yake so a kawo miki shi yanzun? Ta ce komai ma zan ci ba sai na daban ba, maimakon tsugunnon da yake sai ya zame ya zauna sannan ya kira wayar Uche. Ya ce ka kawo min kaza mai zafi in kuna dashi a kitchen da maltina ko fresh milk ya kashe wayar ya dubi gefe,su Naja ?awayan naki sun yi bacci da sun taya ki ci ko? Itama ta dube su,sun gaji ne, ya ce dole su gaji don da nisa. Uche ya ?wan?wasa ?ofa, ya mi?e yaje ya amso tiren ya dire a gabanta sannan ya zauna, "ci in gani" nauyinshi take ji don haka sai ya kauda kanshi gefe ya ciro wayar shi ya soma neman wani layi, aka Wauka suka ci gaba da hirar kasuwancinsu.ita ko nan ta soma cin kazar nan wadda ta ji haWi ta kuma gasu, ta ci sosai ta sha maltina kaWan sai ruwa. Ya dube ta har kin ?oshi? Ta ce,eh ya ce yauwa to tashi kije ki ?wanta zuwa ?arfe uku in gajiyar mota ta barki sai ki tashi kiyi alwala ki yi nafila ki tsananta ro?on Allah ya albarkaci aurenmu, ta ce to, kanta na ?asa ta tashi ta hau gado ta kwanta tsakiyar su Naja ya ce sai da safe,kizo ki rufe muku ?ofa kiyi addu'a fa,ta ce to. Bayan ta karanta ?ulhuwallahu,fala?i da Nasi,ta tofa cikin tafukan hannayanta sannan ta shafa tun daga kanta da fuskarta har da sauran gaSobin jikinta,ta yi haka har sai uku ta karanta Ayatul kursiyu.....


######
[12/5, 20:22] Ummi Tandama=??: *=???Page 13*


Amanar rasulu, sannan ta karanta da sunanka ya Ubangijina na ?wanta kuma da izininka ne nake tashi in ka ri?e raina da (mutuwa) to ka ji ?anta in ka sake ta ya Allah ka kiyayeta da abinda ka ke kiyaye bayinka salihai da shi, sannan ta ce:--

Allahumma innaka kala?ta nafsi wa'anta tawaffaha naka mamatuha,wama hayaha in ahyetaha,fahfadha wa'in amattaha,fagfirlaha. Allahumma inna as'alukal afiya,tana koyi da Manzon Allah (S.A.W) in tazo ?wanciya sai tasa hannunta na dama ?ar?ashin kuncinta ta ce:--

Allahumma ?iyni,azabaka yauma tab'asu ibadaka. Sau uku, sannan ta ce bismikallahumma a mutu wa'ahaya. Lokacin ta soma hamma sosai don haka sai ta tsaya nan gurin ta kuma ?wanta.

Shigar Alhaji Saddi? Wakin da fitarshi kai har zuwan Uche duk a kan idanunta ne. Hajiya Jummai ta yi ?wafa sannan ta ce lallai ban da yarinyar nan mutuwa zata yi ?ila da na ?unshi takaici gidannan,dubi yanda mutumin nan ke ta faman sintiri a Wakin yarinyar nan tun ba?i na nan,ta ciji yatsa tare da cewa kash, da na sani da har ?awayan nata na ce su je can shi ko nasan da nan zai ?wana ba kuma zai bar ta ba,in ya so tana mutuwa suyi zaman makokinsu gaba Waya an huta,su koma Jigawa su dawo, amma tunda an riga an yi haka shi kenan,sun dawo Win tunda ya kama su ne.

Washegari tuni tasa Uche a dama koko ga ?osai. Rahina mai aiki tana ta suya. Sai ga ?an aikin Hajiyarmu tare da Nafisa Wauke da ruwan zafi gwangwanayan madara milo suga da kuma ?atuwar kula mai Wauke da soyayyan dankali da kuma ?wai. Sanda su Sofy da Suby suka shigo Wakin babu ko sallama suka aje bokitin koko sun same su suna ta wada?arsu da shayi sororo suka tsaya sannan suka fita suka koma gurin Jummai in da take ce ma Rahina rage ?osai ?an ?auyan banza shiyasa na ce ayi musu koko tunda shi suka sani, Suby ta ce Hajiya ai ba zasu sha koko nan ba, domin tea da ?wai suke ta bikin sha.

Hajiya Jummai ta dube su,a ina suka same shi? Sofy ta ce,oho ?ila daga gidan waWancan tsegumammun ne, gidan su Hajiyarmu. Hajiya Jummai ta suri ?wanon ?osai ta nufi Wakin ba?in,tana shiga sai ta saki fara'a sannunku da tashi ba?i, suka ce yauwa ina ?wananmu? Bayan sun gama gaisawa sai ta ce, to ga ?osai nan da koko in zaku ?ara dashi, domin naga abin marmari ne na ce ayi muku, suka ce to mun gode, sai dai gashi duk mun ?oshi gara ma ?osan ma Wan taSa, Allah dai ya baku zaman lafiya.

Hajiya Jummai ta fita tana faWin amin a baki, amma a cikin zuciyarta tsine musu take yi.

A ranar ne aka yi buWar kai suka gyara mata Waki sosai, sannan suka shirya ta suka kaita gidan Hajiya Babba inda suka dan?a amanarta gurin Hajiyan, sannan suka dawo in da dangin nashi suka tara mata kuWi daga nan aka kaita gurin Hajiya Jummai wadda ke hakimce tare da ?awayanta, itama ance ga amana nan ta kuma ce ta amsa tare da cewa Allah ya taya ta ri?o,wata cikin ?awayan nata ta ce ba a karSar amanar kishiya fa Jummai. Hajiya Jummai ta ce ke daina gaya min wannan zancan,ai jahilan mata ne suke wannan abin yarinyar nan na Wauke ta ?ar'uwa Allah yasa ki haifa mana ?an dagwai-dagwai a gidan nan, suka ce amin,ta mi?o rafar ?an Wari bibbiyu to gashi ?anwata. Nan aka shiga godiya kowa yana yabonta cikin dangin amarya.suka maida ita Wakin ta,nan suka ?ara yi mata nasihar ta bi mijinta da matarsa, sannan ta bi danginshi ga dai shi ta gani kowa sonta yake yi. Suka shiga shirya kayansu,nan fa A'isha ta soma kuka suna ta lallashinta.

Hajiya Jummai ta fito da tiraman zannuwa goma sha huWu ta basu wai suyi tsaraba, nunawa ta yi itace ta basu alhalin Alhajin ne ya bada kuWin da zannuwan,tirmi ishirin, sannan ya bada ne kan Naira dubu uku uku ta siya ?an dubu da Wari bibbiyu,su dai suna ta godiya. Lokacin da suke shiga motoci ne a harabar gida motarshi ta shigo, kusa da su ya ce direban ya tsaya ya fito,yana cewa ina ce sai gobe ko jibi zaku tafi? Suka ce an gama komai Alhaji gara mu je gida dama ?wana Wai-Wai muka ce zamu yi,ya ce to Allah ya kaimu da alkhairi, kuma ya sauke ku lafiya. Ya dubi direbanshi bani kuWi nan in da na zauna,shi kan shi bai san ko nawa bane ya dai san ?an dubu Wai-Wai ne. Suka ce har da wahala haka? Dama ka barshi gashi ma Hajiya ta bamu zannuwa, ya ce ku ?ara, suka ce to mungode Allah ya sa muzo suna haka, ya ce amin. Nan dai suka Wau hanyar Jigawa suna yabon waWannan mutanan.

Shi ko Wakin amarya ya nufa domin ya san yanzun tana cikin damuwa,hakan ce kuwa ya taradda tana ?wance tana ta shirga kuka na fitar hankali. Da sauri ya isa gaban gadon,ya zauna a bakin gadon, tashi mana Beby ta so ki gaya min zaki bisu ne? Tashi inji" ta tashi zaune,ya ce kina son ki bisu ne? ?aga kai ta yi alamar eh, yace"to taso ki Wakko hijabinki" ta share hawayenta,ta zauna tana ajiyar zuciya. Ta kasa tashi,ya ce "to muje Beby kada su tafi," ta ce "Abba zai min faWa har da Umma" ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce to kiyi shiru,in naga kin kwantar da hankalinki zan Wauke ki muje in kaiki,in da ni ne zasuyi miki faWa? Ta ce a'a ta sake yin ajiyar zuciya sannan ta ce in dai ba zaka ce musu ina kuka ba,to baza su yi min faWa ba,ya ce ai kafin muje ma kin daina kukan ko baki daina ba? Cikin shashshekar kuka ta ce na daina, wasu hawayen suka sake zubowa,ya ce a'a to gashi kina yi kuma? Ta ce to na daina, ya ce wai ba ki son gidan ne? Ko kina ganin za ki mutu Win ne? Ta ce ba haka bane, ina tuno su Umma ne da su Jafar.

Ya ce,ba ki ce da Abdulrahman ya gaida su ba ne? Ta ce na gaya mishi,ya ce to ki daina kukan kin ji ko? Da ?yar dai ya shawo kanta ta yi shiru kusan awa Waya da rabi yana lallashi, lokacin ne aka yi kiran magriba sannan ya fito bayan tayo alwalla,sai da aka yi issha sannan ya dawo lokacin ma yayo wanka yana sanye da jallabiya mai ruwan toka mai gajeren hannu.

Yana ri?e da jakar laptop da wayoyi ya shigo Wakin da sallama,tana zaune kan sallaya kanta yana ?asa kewar gida ce ta cika ta har ma hawayenta suke zuba. Jin sallamarshi ta mi?e da sauri tare da share hawayenta. Ya tsura mata idanu, sai ta sunkuyar da kai ya isa kujerar da ke gefen gadon ya aje kayan hannunshi sannan ya zo kusa da ita. Beby! Beby! Har yanzu dai kukan ne? Ta ce a'a ai na daina,ya kama hannunta ya zaunar da ita bakin gado, sannan ya ce sanar dani me ke saka ki kuka ne? Ta ce, tunanin gida kawai nake yi,ya ciro waya bari na kira Abban,bata san lokacin ta ri?e hannunshi da sauri ba,ta ce Uncle don Allah yi ha?uri kada ka kira shi zai min faWa,ya ce to shikenan kin ci abinci? Ta ce na ?oshi ne. Nan dai ya yi wa Uche waya ya ce kada ya shirya mishi abinci a dinning,ya kawo mishi Wakin amarya,nan yasa ta shinfiWa mishi babbar darduma.

Uche yana kawo abincin ya shirya mishi a kai ba tare da neman izini ba,ya ce zo nan muci abinci,ta kalleshi ganin fuskarshi Winke sai ta je,ya jawo plet ta amsa cikin natsuwa ta buWe kulolin,tuwan shinkafa ne da miyar agushi, sai dafadukan taliya mai haWe da kayan lambu.

Ta Wago ta dube shi, kafin ta yi magana ya duk wanda ki ka ga ya yi miki a ranki sa mun. In to bashi ranka ke so ba fa? Ka ci dai duka, cikin natsuwa ta ke maganar ya ce Waya zan ci kuma ke ce zaki zaSar min da abinda ya dace in ci matsayin abincin dare, ba ta kuma cewa komai ba ta janyo plet Win ta saka tuwo da miya sannan ta saka cokali ta aje mishi a gabanshi. Ta tsiyaya mishi ruwa da jus,itama kaWan tasa tuwon tana yin loma Waya sai ta ji babu wani WanWano duk da ?amshin da ya cika Wakin amma haka ta daure tana Wan tsakura. Amma shi yana ta cin abinsa da alamu ya saba da shi, wayoyinsa suka soma ringing lokaci Waya ta mi?e ta Webo mishi su, sannan ta koma gefe ta sha ruwa ta zauna tare da tsura ma guri Waya idanu da alamun ta faWa cikin tunanin nata,kusan minti talatin yana amsa wayoyi, sannan ya kira Uche ya kwashe kayan ya dubi A'isha, "Beby tunanin ko?" Ta sunkuyar da kai ya mi?e ya isa gurin T.V wanda ke manne a jikin bango ya kunna sannan ya shiga neman tasha,MBC 3 yasa sannan ya dube ta ga irin naku ko Beby? Ta kalla Cartoons suke yi na Tom & Jerry tana son cartoon,sai dai ta kula shi Uncle ya maidata wata ?ar mitsitsiyar Yarinya. Nan ko ta gyara zama ta shiga kallonta, shi ko ya jawo laptop Win shi ya shiga al'amuranshi na kasuwanci daga bisani ta ji bacci yana fizgarta,don haka ta hau gado bayan tayo alwala ta zauna ta jero addu'o'inta sannan ta kwanta bacci kuwa ya yi gaba da ita,sam bata tare da fargaba irin na amaren nan game da angwayensu, uku dai-dai ta farka har lokacin yana gaban laptop alwalla tayo ta zo ta soma na filfilu, hankalinshi ya yi nisa sai daga baya ne ya ji motsinta, nan shima ya yo alwalla.

Hajiya Jummai tana da tabbacin ango ya kwana Wakin amarya fatan ta dai Allah yasa sun sadu .

Da safe har Waki A'isha taje ta gaida Hajiya Jummai ta same ta tare da su Sofy, cikin fara'a ta amsa ma A'isha, sannan ta ce dasu Sofy ba za ku gaida Antyn taku ba? Har suna haWa baki gurin jan tsaki, haka da A'ishan ta gani yasa ta gaishe su ba su amsa ba, A'isha ta fito tana tunanin su kuma waWannan su wanene? Tana shiga Wakinta ta soma gyaran gado,ta gyara ko'ina sannan ta shiga toilet tana wankewa ya shigo cikin shirin fita motsin da ya ji a bayin ya sa shi tsayawa ya san tana ciki,jim kaWan ta fito. Ya ce na zaci wanka ki ke yi? Ta ce a'a ina wanke bayin ne. Ta dur?usa ina ?wana? Ranshi ya yi fari sannan ya ce lafiya lau tashi na gode. Ya ci gaba ni zan fita ne don Allah kada ki yi kuka ko tunani sannan ki ci abinci kuma wannan aikin da ki kayi yanzu akwai masu gyaran Wakunanku. Zan sanar da ke komai sai in na dawo yau da yamma zan haWa ku da Jummai, ta ce to, har ya soma tafiya ta ce Uncle ka....sai kuma ta yi shiru,ya dawo har kusa da ita, nayi me? Sanar da ni mana. Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta sannan ta ce ina nufin kayi break fast ne? Ya yi murmushi, abinda Hajiya Jummai ba ta taSa damun kanta a kan ya yi ba kenan, haka gaisuwar da A'isha ta yi mishi ya sa shi jin cewa shi Win maigida ne. Ya ce A'isha bana yin break a gida saboda ba?wa karyawa da wuri ni ko bana son mutane su yi ta jirana a Ofis," ta ce "to acan ana saida abu ne? Ya ce zan sha copee a Ofis da rana kuma muna kusa da gidan cin abinci," ta ce "to sai ka dawo Allah ya bada Sa'a" ya ce amin Bebyna,na gode miki kiyi kallonki kin ji? Zan kira ki" ta ce to,ya fita ta bishi da kallo. A zuciyarta tana tunanin duk in da Abbansu za shi komai sauri sai Ummanta, ta mishi Abinda koda ba zai ci ba saboda sauri zai ri?e.



######
[12/6, 07:59] Ummi Tandama=??: *=??? Page 14*


Shi ko ya fito ne yana jin daWin yanda A'isha ta nuna kulawarta kanshi, ?aramar yarinya kenan. Sai sha Waya sannan aka kawo mata abin kari tea kawai ta iya sha domin hatta dankalin WanWanonsa bai mata ba.

Misalin ?arfe Waya da rabi tana zaune kan abin sallah tana karatun Alkur'ani tun bayan da ta idar da sallar azahar, Hajiya Jummai ta shigo tare da ?awarta Karima, ta mi?e tana musu sannu duk cikin fara'a suka amsa. Karima ta ce wayyo ashe ma yarinya ce ?arama.

Ita dai A'isha kanta yana ?asa. Jummai ta ce eh, yarinya ce,sai wayar Jummai ta soma ringing sai ta fita ina zuwa bari in yi magana Alhaji ne ya kira ni ku gaisa ina zuwa,tana fita Karima ta matso kusa da A'isha, "yarinya ni dai zan miki nasiha ne ki ri?e mijinki ki mishi biyayya, kada ki zama cikin irin matan nan masu gudun miji,kin ga haihuwa yake so kiyi maza ki cika mishi gidan da ?a?a kin ji?" Zancan ya yi ma A'isha nauyi,don haka ta kasa Wago kai, sai dai ta kaWa kai alamun to. Ta ?ara ?asa da murya,kin ga dai kishiyarki aminiyatace ko? To wannan ba zai sa

8 / 10