MUMMUNAN ZATO BOOK 1 COMPELET HAUSA NOVELS

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   4 / 10

9K to 12K   out of 29.7K words

ranar tafiya maguzawan, "To yaushe ne zuwan? Inji Hajiya Jummai,ta cigaba "Kuma sai dai mu je da direbanki, kamar kowane lokaci" "Eh,ai ina sane ba zamu bar wata kafa ko ya ya take wadda zata tona mana asiri ba,ke dai ki sha?i kuWi don bokan dutse yanzun idanunshi sun buWe da son kuWi,da, ko akan dubu biyar ma sai ya yi kisan rai." Jummai ta ce,"A sosai ma kuwa, Wan iska ni har yau ma ban sai mashi motar da yake naci ba". Hajiya Kari ta ce "ke dai bar Wan iska ko ina ruwan wanda ke cikin daji da mota?" Jummai ta ce,"nima shine na gani, shiyasa na share shi,rabo na da zuwa gun shi tun aikin ?arshe da ya yi mana,na matar ?arshe da Alhaji ya aura." Hajiya Kari ta ce, "?yale shi wannan karon sai ki sai masa ko ?ar starlet" Hajiya Jummai ta ce "hakan za mu yi" nan dai suka ci gaba da shirya ranar da zasu tafi.



Da gudu suka rungume juna suna murna.

*A'isha Mustapha kin Wan rame." Inji Suwaiba Ringim.

"Nayi rashin lafiya ne, Zainab K.T bata iso ba?"

Sam, A'isha ba tayi niyyar sanar da Aminan nata batun auren nata ba, saboda kunya take ji, duk cika bakin da takeyi na cewa ita karatu zatayi kamar ba gobe,don Doctor zata zama yanzun ma har Doctor Aisha suke ce mata,in ko suka ji ta san zata sha tsokana, sai dai su shafa su ji bata dawo ba, Zainab ma ta iso kuma sun du?ufa karatu babu wasa.



Alhaji Saddi? ya yaba da yanda Abba ya tsaya tsayin daka, aikin kamfanin ya kammalu. Guri ya yi ?yau duk mutane sun yaba,don haka shima bai yi wasa ba wurin kawo duk wani abu da kamfanin ke bu?ata don fara aiki.

Alhamdulillah,tuni kamfani ya soma aiki, Abba kuwa ya samu kujerar manaja, yanzu sunturi yake yi tsakanin Dutse da Jigawa, Alhaji Saddi? ya ce mishi ya nemi gida nan Jigawa sai a siya, sannan ya saya mishi ?ar mota,ba a jima ba suka samu gidan suka dawo Jigawa.

[12/1, 19:47] Ummi Tandama=??: ____________________________
*=???MUMMUNAN ZATO=???*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*?andano page 6*


Aisha tana makaranta ba ta san ana yi ba.

Gurin Abba Alhaji Saddi? ya ji cewa satin da zamu shiga ne visiting day Win su mutuniyar shi,ya ce "To Friend ka bari ni zan je mu da Nafisa" Abba ya ce,"shiyasa na sanar da kai don tasan cewa magana tana nan.

Waya ya yiwa Nafisa cewa,ta shirya zasu je visiting tana jin haka ta soma murna. Sun Wau hanya in da Yahaya direban shi yake jan su. Aikin shi yake yi a bayan mota cikin laptop, harkokin business Win shi yake ta yi. Nafisa ko sai dai kallon ?auyuka take yi, sai da suka isa garin Kano sannan suka tsaya bakin Sahad Store ya yi mata tsaraba mai ban mamaki, sannan suka Wauki hanyar Munjibir.

Da tambaya suka isa makarantar,Henesy ba?a wul tana ta she?i,ta Wauki hankalin da yawan ?an makarantar,gilashinta masu duhu ne,don haka suke ganin mutane. Ya dubi direbanshi ya ce "Yahaya fita ka samo mana ofis Win (PC) Win makarantar."

"To ranka ya daWe" inji Yahaya.

Jim kaWan ya dawo.

"Ranka ya daWe ga ofis Win can, har ma na yi mishi bayanin cewa maigidana yana son ganinshi,kuma ya ce mu shigo" "To ai shi kenan." Inji Alhaji Saddi?, tare da Nafisa suka fito. ?warjinin Alhajin ya sa ya zama abin kallo gurin Waliban tare da masu ziyara. Kai tsaye ofis Win (PC) Win suka nufa,suna shiga shima (PC) din ya mi?e tare da ba Alhaji Saddi? hannu,don daga ganin shi ya ji?e da Naira. Sun gaisa, sannan suka zauna kan wasu kujeru da ke gefe,ya nuna ma Nafisa wata kujera ya ce, "Bismilla Malama" shi ko Yahaya cewa ya yi,bari ya koma gurin mota.

Alhaji Saddi? ya ce,"mun zo ziyarar yarinya ne."

"Ya ya sunanta?" Inji P.C.

"A'isha Mustapha, daga Gumel ta jihar Jigawa."

P.C ya ce,(S.S) take ko JS?"

"S.S one." Inji Alhaji Saddi?.

"Ok" ya mi?e yana fita ya kira shugabar Walibai ya aike ta neman A'isha,ya dawo ya ce bari a kira ta.

Alhaji Saddi? ya ce,"Ba komai" ya zauna tare da cewa, "Ranka shi daWe ?ar ka ce?" Alhaji Saddi? ya amsa da cewa "Eh,?ar abokina ce", wayarshi ta shiga ruri,ya Wauka yana magana.

Shugabar ta gano A'isha ne tare da ?awayanta Zainab da Suwaiba,in da Yayan Zainab ya kawo mata ziyara daga Katsina, ta ce kece A'isha Mustapha ko?" Ta amsa da "eh,ni ce."

"To ki zo inji P.C"

A tsorace ta ce,"lafiya?"

Nima ban sani ba" ta ce "Ina jiran ku" ta nufi ofis Win shugabar ce ta shiga,ga ta nan Sir,ya ce ta shigo, nagode miki ta fita sannan ta ce A'isha ta shiga, ita kuma ta tafi. Tana shiga ta ji hancinta ya sha?i daddaWan ?amshin turaren Uncle,gabanta ya faWi amma ta daure ta shiga,sanye take da wando da riga haWe da gyalen su, kayan mutanen Pakistan masu kalar sararin samaniya, kai tsaye teburin P.C Win ta nufa, inda ta gaishe shi cikin harshen Turanci, sannan ta ce gata,ya nuna mata Alhaji Saddi? da ke waya.

"Ga masu visiting na ki." Ya mi?e "Bari na barku, ku gaisa ko?" Ya fita.

Duk sai taji kunya ta rufe ta, har ma ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskarta. Ta dubi Nafisa,ga zatonta matarshi ce. Cike da dariya Nafisa ta ce, "zo mu gaisa A'isha." Ta isa gurinta ta zauna, sannan ta ce "Ina yini? Ya ya hanya?" Nafisa ta ce "lafiya lau,hope kema kina lafiya?" A'isha kanta a ?asa ta ce "lafiya ?alau." Nafisa ta ce "Hajiyarmu da Alhajinmu sun ce mu gaishe ki" A'isha ta ce, "ina amsawa, na gode."

Dai-dai sannan Alhaji Saddi? ya gama waya ta Wan saci kallonshi da gefen ido. Wata ji?a??iyar shadda ya saka kalar ?asa,ya yi ?yau sosai ta zamo daga kan kujera don ta gaishe shi.

"Ina yini Uncle?"

"Bana cin mi?e A'isha, daga nan za ki gaishe ni?".

Ta saka gyale ta rufe fuskarta, sannan ta mi?e taje gefenshi ta tsugunna,muryarta ?asa-?asa ta sake gaishe shi. Ya amsa yana dariya.

Nafisa ma dariya take yi, sannan kunyar A'isha ta burge ta, A'ishan ta mata ?yau,sai dai yarinya ce ?warai, ya ce "Nafisa yau dai ga ki ga A'isha" Ya dubi A'isha ya ce, "Ga ?anwata Nafisa." Ta kuma duban Nafisan.

"Sannu da hanya"

"Yauwa," Nafisa ta amsa da fara'a.

A'isha ta mi?e tana kallon Nafisa, "Bari na kira ?awayena." Har za ta fita, ya ce "Zo" Ta dawo ta tsugunna.

"Wa zaki ce musu ya zo?"

Ta rufe fuska,tana Wan murmushi. Ya ce, "Umh,wa zaki ce musu? Ko har kin basu labarina ne?" Ta girgiza kai, sannan ta ce, "Ce musu zan yi Uncle Wina ne." Ta mi?e ta fita da sauri. Dariya Nafisa ke musu, ta ce "Yaya Saddi? duk da A'isha yarinya ce kun matu?ar dacewa, Allah dai ya yi mana jagora tare kuma da shige mana kan matsalarmu." Ya ce "Amin sister."

Ta je gurin su Suwaiba ta kira su, ce musu ta yi Uncle Winta ne daga Katsina, suka shigo suka gaishe shi,ya tambayi sunayen su suka gaya mishi,ya ce "Har da ?ar garinmu? To sannuku,ku dage da karatu ko?" Suka ce, "To mungode" ya ce "nima na gode." Suka fita suna mamakin dama A'isha tana da Uncle a katsina, Amma ba ta taSa gaya musu ba? Zainab kam so take ta tuna inda ta san shi.

Nafisa ta mi?e, "A'isha bari na bi ?awayenki na Wan mi?e ?afa," A'isha ma ta mi?e ta fito, kira ta ?walawa su Zainab.

"Ga ba?uwa ko zaku je school shop."

Suka ce, "To" ta dawo ofis Win ta zauna, ya dube ta "Ya ya bayan rabuwa?" Ta ce "Da godiya, shi Abbana ba zai zo ba?" Ya ce,in gaishe ki ba zai samu zuwa ba, saboda aikin shi ya koma Jigawa. Kuma yanzun Jigawan ku ke" ta dube shi, "Mun tashi daga Dutse?" Ya ce "Haka ne,to yanzu yaushe ne zakuyi hutu?" Ta ce, "Nan da sati biyar zuwa shida." Ya ce, "To so nake a shirya komai kafin kuyi hutu, cikin hutunku za'a Waura aure tare da bikin." Gyale taja ta rufe fuskarta. Ya ce, "Me kika ce?" Ta ce, "Duk yadda ku ka yi,ni dai karatuna na fi ji" Ya ce, "wannan babu komai, sai makarantar da ki ke so ita zan kai ki" ta ce "Bari na samo maka wani abu." Ya ce, "No,bar shi am ok." Ya dubi agogo bari muyi sallah mu zo mu tafi." Ta ce, "To."

Bayan sun yi Sallah,ya dawo ya yi ma P.C alkhairi mai yawa,P.C ya rako shi har gun motarsa. A'isha taje ta kira su Zainab su yi sallama,har ma ta ce ma Sani Yayan Zainab,ya zo ya bi su Uncle Win ta mana tunda suma Katsina za su je.

Sanda suka iso gurin motar Yahaya,yana ta aikin jibge ?walaye a ?asa daga boat Win motar,Sani yaja baya ya tsaya yana mamakin ganin Alhaji Saddi? K.T. mutumin da ya yi kuWi da jinin mutane, yanzu kuma dabarar da ya sake kenan? Ta shigowa makarantu yana son shan jinin ?an makaranta? Sun gama sauke kayan suka shiga mota.

Alhaji Saddi? ya mi?a ma Nafisa bandir Win kuWi yace ba ?awayan nata. A'isha ta le?o tana cewa, "Nafisa ku sauka lafiya,ku gaida ?an garin." Ya ce, "Ni fa ko Nafisa kaWai ki ka sani?" Nafisa ta ce, "yauwa ga Yayan Zainab shima Katsina zai je". Alhaji Saddi? ya ce, "To ya shiga mu je." Ta zo gurin su, ina Sanin?" Yana daga bayansu ya ce,"A'a su tafi ni dama sai gobe ina da aboki nan cikin Munjibir,ta je tace su tafi su Zainab ma suka je sukayi godiya.

Suna tafiya sai ya zo gurin su ya nuna A'isha, "wannan mutumin ne Uncle Win ki?

Zainab ta ce, "Ka san shi ne? Nima ina ta mishi kallon sani."

"Sani ya ce, "kin san shi mana, Alhaji Saddi? Usman K.T Win ne baki sani ba."

Zainab ta dafa ?irji da ?arfi.

"Kana nufin me kuWin jini?" Ya ce "shi ne mana."

A'isha ta zaro ido,me kuWin jini kuma?" Sani ya ce, "tabWi,ke da baki san halin Uncle Win na ki ba? Koda yake ai basa cin na gida sai bare."

Jikin A'isha ya soma rawa, cikin matsanancin tsoro ta ce, "Don Allah ku gaya min gaske ne?" Zainab ta ce, "kada ki damu zan baki labari,ku zo mu ?washe kayan nan." Ta ce, "ai ni bazan Wauki wani abu ba har sai naji labarin Uncle." Suwaiba da Zainab har ma da Sani suka shiga ?washe kayan. Zama tayi bakin gado tana tunanin ba?on al'amarin, har suka raka Sani suka dawo.

Zainab ta zauna kusa da ita, A'isha dama baki sani ba,shan jini suke yi,An ce aure-aure ya ke yi, duk wadda ya aura ba ta sati biyu take mutuwa,aurenshi goma, uwargidan ce kaWai bai cinye ba, ke yanzu fa ba a bin layin gidan shi,don ance kana cikin tafiya a layin wani abu zai ja ka zuuu sai dai ka ganka a cikin wani Waki a gidan,ke kina ganin gidan kin san ana cin mutane a cikinshi, ko ba ki san gidan ba?"

A'isha cikin tsananin tsoro ta ce "ban taSa zuwa ba".

Suwaiba ta ce, "Tab! Amma ya yi ?yan banza." Zainab ta ce "kinga gidan ne wani mahaukacin gida ga bishiyoyi."

A'isha sai kuka,lallai Allah ya so ta tana zuwa gida zata sanar da Abbanta. Duk kayan da ya kawo ta ce bata so,ta ma fita hayyacinta cikin ?wana uku ta ?wanta ciwo,?wananta biyu ta Wan samu sau?i. Amma duk ta rame su Zainab sun yi ta matsa mata da son jin gaskiyar lamarin ta da Alhaji Saddi? don sun ga yanda ta Wauki abin da zafi ?warai. Ta gaji ta gaya musu cewa Babanta ya riga ya bashi ita,sun jajanta mata tare da kuma bata shawarar ta tashi tsaye da addu'a, Allah ya shiga tsakaninta da sharrinshi. Sun ce suma za su taya ta.

A daddafe dai suka yi jarabawa, Abba da Abdulrahman ne suka zo Waukanta, Abba ya dube ta, "A'isha ciwo ki ka yi haka? Na ganki ne babu ko ?yan gani?" Hawaye ya soma zubo mata, cikin sanyi murya ta ce "Abba nayi ciwo ne sosai."

Sun isa Jigawa misalin ?arfe biyar na yamma,suna tsayawa A'isha ta fito tana kallon sabon gidansu,ga dai gida mai kyau amma ta kasa jin farin ciki, kuma ta yarda cewa iyayenta suna cin kuWin ?arsu ne. Nan take hawaye ya soma zubo mata,ta shiga ciki.


#######
[12/2, 08:00] Ummi Tandama=??: ____________________________
*=???MUMMUNAN ZATO=???*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*?andano page 7*


Abdulrahman yana biye da ita da kaya, cikin wani tsararren kitchen ta hangi Umma, Umma tana juyowa ta yi arba da ?arta, da sauri ta fito tana cewa ga ?an makaranta ga ?an makaranta." A'isha ta faWa jikin Umma tana kuka.

Ramarta ta tsorata Umma, ta ce, "A'isha kin yi ciwo ne?" Dai-dai nan Abba da Abdulrahman suka shigo, Abba ya ce, "?awallin taki ta bani tsoro, Ummansu kin ga yanda ta ?are?" Umma ta ce "Shine ai,wane ciwo ki kayi haka?" Cikin kuka A'isha ta ce, "Nima ban san ciwon ba,ni dai duk jikina ne bana jin daWin shi. Suka shiga falo kan kujera ta ?wanta tana ?ara kallon yanda aka tsara falon da kuWin jini, duk sai ta samu kanta da ?yan?yamin komai na gidan. Umma ta zubo mata abinci ta tasa shi ta kasa ci, har dare Umma ta yi tayi A'isha, amma ta ?i cin komai. Hankalin Iyayen ya tashi, cikin dare zazzaSi ya rufe ta saboda tsananin damuwa da kuka, dole da safe suka nufi asibiti, duk binciken likitan bai gano komai ba, sai damuwa. Don haka yasa mata ruwa tare da allurai don ta samu bacci.

?wananta biyu aka sallame ta, tunda ta dawo ko yaushe jugum ba ta magana. Umma ta matsa mata da tambayar abinda ke damunta,don likitan ya ce tabbas akwai abinda ke damunta. A'isha tana son sanar da Umma amma tana tsoron kar ta gaya wa Abba, shi kuma ya yi faWa. Ko ma ya yi fushi da ita,don haka ta yi shiru.

Abba yana zaune yana cin abinci, ya tasa ta gaba wai itama sai ta ci nata. Umma ma ta shigo Wakin na A'isha, wanda ya ji uwar katifa sai (T.V) ance ba za'a cika Waki da kaya bane tunda cikin hutun nan ne za'ayi bikinta, Umma ta zauna tana cewa,ka ce kana nan na fito ban ganka ba,ya ce "eh, ina nan gurin A'isha so nake ta ci abincin a gabana in gani," Umma ta ce "to nima dama na zo ne in tsare ta, yarinya duk tasa kanta a uku" ta dubi A'isha wadda take ta ?o?arin ganin ta ci abincin,ko don hankalin iyayenta ya ?wanta, ta ce, "To ko saboda aurenki da Alhaji Saddi? ne?" Da sauri ta kalli Abba, wanda ya tsura mata ido, sannan ta girgiza kai, "Ba haka ba ne Abba" ya ce "ai bani ne na tambaye ki ba, Ummanki za ki bawa amsa, tunda ni dai ai mun gama magana,jiya ma nake sanar da shi dawowarki, sai dai ban sanar dashi ciwon ki ba, saboda zai ce zai bar aikinshi ya zo,ya ce dai zai zo kafin su kawo kaya."

Umma ta ce "bari na saka mata wayarta ma a caji, saboda ?ila zai neme ta. A'isha ta yi ajiyar zuciya,lallai ya kamata ta sanar da Umma, domin dai ba su san komai kan Uncle ba. Sai da Abba ya fita sannan A'isha ta dubi Umma, ta ce "Umma zan gaya miki abinda ke damuna, amma sai kin yi min al?awarin ba zaki sanar da Abbanmu ba" cikin fargaba Umma ta ce, "Sanar dani,ba zan gaya mishi ba." Ta soma hawaye, "Umma ashe Uncle Wan yankan kai ne? Ashe duk kuWin shi na jini ne?" Umma ta daburce tare da cewa "Wane Uncle Win?" A'isha ta ce, "na Katsina, kinsan ?awata ?ar Katsina ce nan dai ta koro ma Ummanta labarin da ta ji game da Uncle Win nata, Umma ta shiga damuwa,zufa ta shiga keto mata duk da cewar da takeyi anya kuwa A'isha zancan nan gaskiya ne? Duk suka yi shiru kowa yana tunaninshi, can dai Umma ta yi ?arfin hali ta ce "A'isha wannan zancan ba na shiru ba ne, dole Abbanki ya ji, domin dai duniya yanzu babu gaskiya, kuWi suna kai mutane cikin halaka, sannan kai ka yarda da mutum shi ko yana da nashi burin a kanka".

A'isha ta soma kuka tana faWin, "Don Allah Ummata kada ki sanar da Abba,ba zai taSa yarda ba saboda ya yarda da Uncle ni dai na ha?ura zan auri Uncle Win tunda dai dama na san ?arshena mutuwa zan yi."

Abba da ke ?o?arin shigowa Wakin tun Wazun,ya ji A'isha tana sanar da Ummanta A ranshi ya ce, "shikenan sun ji zancan da ya ke Soye musu,ya zama dole ya shiga ya sanar da su gaskiyar lamarin domin ya yarda Alhaji Saddi? ba zai mishi ?arya ba,ba zai cuce shi ba,ba zai ci amanar shi ba, kuma ba zai kasance Waya daga cikin masu shan jini ba.

Da sallama ya shiga duk da baya da kuzari amma ya yi ?arfin halin cewa "kuna hira ne? Umma cikin damuwa ta ce "wane hira Abbansu zauna ka ji". Ya zauna tare da faWin "lafiya dai ko? Umma ta ce "da sau?i dai,dama Abbansu dama ashe irin sana'ar da yake yi kenan?" Abba ya ce "wa?" Ta ce "Alhaji Saddi? mana ta shiga jero mishi bayani yanda A'isha ta sanar da ita. A'isha dake ?wance jikin Ummanta tana kuka,ta ce "Abba ka min afuwa na sani ranka ba zai so ba, amma duk da haka zan aure shi.

Abba ya ce "ku kwantar da hankalinku ni kaina na san wannan labarin kuma shi da kansa ya yi min bayanin zargin da jama'a suke masa. Tabbas tun daga kan Hajiya Jummai duk Mata da ya aura mutuwa take yi, gaske ne ya yi aure kusan tara ko goma ne? Duk

4 / 10