Author : Maryam Majidadi Category : Tknovels
amma
beyi tunanin a yanzu zai kasa kwace hannunsa gareta ba,a tsawace yace"ki sakeni ko kuwa kiyi
ta ranki"Murmushi Shuzna tayi ta kallesa ido a ido tace"aeni Amaan tun daga ranar daka rabani
da iyayena,yar uwata,D'ana da Kuma Nanina from that very day u took my life,shiyasa yanzu
bana tsoron na mutu,amma sai naga bayan tantiri marar tsoran Allah irinka,saina tabbatar nice
ta k'arshe da zaku lalatawa rayuwa a duniya gaba d'aya".murd'eta yayi ta dur'usa k'asa,cikin
dabara ta samu ta d'ago ta zare hannunta daga jikinshi ta wanka masa maruka har biyu ta
kuma ingijesa yayi baya,juyawa tayi zata dauki waya ta Kira y'an sanda ,cikin sand'a ya daura
Mata bindiga a Kai yace"tabbas yau saikin mutu,haka sauran yaranki da tsohon mijinki da
Uwarki sai sun mutu kinga duk abunda kika mallaka nawa ne"motocin y'an sanda dana soji ne
suka shigo gidan,kafin kace me sun zagaye gidan ,daga ciki harda General Muslim da General
Ahaad,sai shugaban Shuzna kuma Wanda take jagorancin team dinsa a yanzu haka,parlon
suka shigo harda Aiban,"ku tsaya daga nan idan Kuma har kukayi wani abu marar kyau to
tabbas zata mutu yanzu",ganin da gaske yake yasa suka ja baya,kallonsu General Asam
yace"dole fa yanzu ayi zab'i na k'arshe ,sai an harbi Amaan"zaro ido Aiban yayi da sauri ya
k'arasa wurin Mamanshi tare da riketa jikinsa ta fad'a ta saki kuka tace"Aiban ya kashe mani
ita,ya kashe mani Islam,Islam ta tafi ta barni Aiban"juyar da fuska yayi yana share guntun
hawayen dake zubo masa rungumeta yayi yace"Hajiya kiyi hakuri,hakan Allah ya rubuta".kamar
daga sama sukaji k'arar halbi Wanda basu gani ba harsunyi saranda kowa daukarsa Shuzna ya
harba,ganin Ahaad da bindiga a hannu yasa kowa ya kalli inda yake Kallo,k'ara Amaan ya saki
ya dafe k'afarsa da Ahaad ya harba ya zube anan wurin,wani kukan Mummy ta Kuma saki
tace"Ahaad karka kashe d'an uwanka,dan Allah kabarmun yarona Ahaad"ta wuce gabansa zata
duk'a,da sauri ya riketa ya kawar da kansa gefe"daku kamani gara na kashe kaina,bazan tab'a
bari na mutu a hannunku ba"kanshi ya saita Mama tana kiran"a'a Amaan karkamun
haka".kallonta yayi hawaye na zubowa daga idonsa yace"ki yafemun Mummyna"kafin tayi
magana ya harbe kansa a take ya mutu a wurin ko shurawa beyi ba.y'an sanda suka kwashe su
sai office dinsu Fadila kam a sume aka kwasheta sai asibiti,har Dr Jamil an kamo tare aka
rufesu a office din y'an sanda.duk abunda sukeyi Daddy yana jinsu daga part dinshi be fitoba
,ya rasa meke masa dadi,kwakwaran motsi baya iyayi.cikin sati d'aya aka shirya komai aka Kai
,Mummy ,Hajiya Sadiya da Dr Jamil kotu,Shuhada da barista Abbas sune suka tsayawa
Shuzna,ba wani b'ata lokaci suka ansa laifukansu,kotu ta yankewa Mummy da Hajiya Sadiya
zaman gidan yari na shekara biyar da tarar dubu d'ari bibiyu,sannan su mayarwa Najma da
dukiyarta.Fadila kam Shuzna bata yarda an kaita kotu ba,yarda taga tanata faman kuka da
rokon Shuzna gafara ,ga tausayina Nasirah da Shuzna keji yarinyar bata da damuwa,tun kafin
ayi wannan rigimar dama aka dauke Mama da Nasirah aka had'asu dasu Ummu dasu
Faida.cikin sati biyu aka sallami Fadila suka dawo gidan Shuzna,ga Umti da Daddy Bashir
sunzo Family ya hadu sai tattauna sukeyi da sanin abubuwan da suka faru a da.da gudu
Shuzna ta shigo rike da wasu takardu ."a'a har yanzu kina nan da wannan shiriritar taki
?"Ummu ta tambaya, murmushi Shuzna tayi ta rungume Mama tace"Hajiya Mama yau jikarki ta
koma da sunanta Najma Jafar Bindawa,Komai nawa ya koma da sunansa na da".Alhmdllh Umti
ta fad'a ta dafa kafadar Shuzna tace"y'ata Najma kiyi hakuri da rasa fuskarki"rungume Umti
Najma tayi tace"ba komai Mamana".tureta Muslim yayi yace"dallah malama tashi anan,zaki
karyamun Mama".rigiman hakan suka fara Ummu ta janyoshi tace"barsu suje Sojana ae nima
ga y'ata nan"ta fad'a tana janyo Shuhada jikinta ta had'asu ta rungumeta,hannuwansu ta had'a
wuri d'aya tace"nima ga ma'auratana na had'a,zanyiwa Muslim da Shuhada aure"kowa dariya
ya saka ,Shuhada ta boye fuskarta jikin Ummu,janyo hannunta yayi yace"haba masoyiya
kunyata kikeji ne?".dungure masa Kai Mama tayi tace"gaba d'aya baku da kunya Kai da
wancan labcecen bayahuden"harara Ahaad ya maka Mata wanda tunda ya zauna saika dauka
baya d'akin.shigowar Aiban d'akin yasa suka takaita dariyar sai da ya gaishe da kowa sannan
ya zauna kusa da Mama,"kaga yaron kirki mai tarbiya ,sannu da zuwa Aibanu".danna k'afar
Mama ya farayi sannan yace"Mamana nazo neman aure fa"."yi sauri gayamun wace mai sa'ar
ce?,gaskiya na gaji da zamanku hakanan dama".sunkuyar da kansa yayi alamar kunya sannan
ya rad'a Mata a kunne,"Alhmdllh,Alhmdllh,Allah na gode maka,Aiban Allah yayi maka albarka
Kuma na maka alk'arin baka abunda kake so Koda hakan zai Zama abu na k'arshe da
zanyi,Allah ya shiga lamuranka,na baka Najma duniya da lahira".wani irin bugawa da k'arfi
zuciyar Ahaad yayi ,"toshi Papa waye zaku bashi ya aura?"Fayyam ya tambaya."baba ko
ubanwa,aeshi wannan fad'in ran nashi bazai barshi yayi aure ba".turo baki Fayyam yayi yaja
hannun Nasirah yace"sai kiyi dama ae halinkine"tunda Nasirah ta dawo gidan Fayyam yake
kula da ita,baya yarda kowa ya tab'a ko da wasa,"tsohon marar kunya Wanda yayi gadon
ubanshi".
Bayan sati biyu
Ko wanne b'angare Shirin biki sukeyi ba k'akkautawa, yayin da Ahaad tun ciwo yana cinsa a
tsaye har yakai gaya kwantar dashi ko fita bayayi kullun yana kwance kawai.ko kad'an Mama ta
hana kowa ya kulashi tace a barshi can shiya sani.
Kaya Muslim ya ajiye masa yace"ka tashi ka shirya mu tafi,lokaci yana kurewa".Jan pillow yayi
ya rufe fuska cikin dishewar murya yace"kuje kawai bazan iya fita ba".sai da Ummu tayi da
gaske sannan Ahaad ya shirya cikin blue din shadda suka saka mai matuk'ar tsada sai black din
huda da black din takalmi sai fitar da sihirtaccen kamshi sukeyi.haka suka tafi daurin auren.wuri
ya cika makil da mutane na nesa dana kusa,baka iya banbance wurinwa wane yazo,dafe Kai
Ahaad yayi da yaji yana barazanar tarwatsewa juyawa yayi yaga babu mai kallonshi ya samu ya
fito daga cikin masallacin can baya ya koma ya zauna tare da had'e Kai da gwaiwa yana jin
jiri,jin hawaye masu dumi yayi suna bin fuskarsa..kamar daga sama yaji ana cewa an daura
auren Muslim da Shuhada,Aiban da Fadila sai Ahaad da Najma akan sadaki naira dubu d'ari.a
firgice ya d'ago yana jin tabbas mai shelar nan bejiwa kunnensa daidai ba.murmushi Aiban yayi
masa lokacin da suka had'a ido yazo ya kamashi ya d'auki babbar rigarsa daya cukurkude ya
ajiye a k'asa"ace ango ya b'ata kwalliyarsa haka?,kakkabe rigar yayi ya saka masa ya Kama
hannuwansa yace"Congratulations angon Najma Allah ya bada zaman lafiya".tangare k'eyarsa
Muslim yayi yace"raggon maza,ashe kasan kana Santa ka saketa"kasa furta komai Ahaad yayi
sai murmushi kawai da godewa Allah da yakeyi a ranshi,"kada ka damu,ni bazan raba zuciya
biyu ba,ina tabbatar maka itama Najma tana sanka ".Jan hannunsa sukayi zuwa cikin mutane
fara'a kawai yakeyi yana gaisawa da mutane haka har suka samu damar komawa gida bayan
hotunan da suka sha sunyi kyau kamar y'an ukku.koda suka shiga gidan an tsara wurin sosai
anayin y'ar dinner,kujerune ukku inda su Najma suka zauna komai nasu iri d'aya fuskarsu a rufe
sunyi masifar kyau.rike hannun Ahaad Umti tayi tace"yarona muje ka fara zab'ar matarka a
can"binta kawai yayi a wurin ta tsakiya ya tsaya inda Shuhada take kenan,har zai budeta Kuma
ya fasa ya tsaya yana k'are masu Kallo su duk'a,matsawa yayi can hannun dama sannan yasa
hannu ya yaye lullubin take fuskar Najma ta bud'e Tasha kwalli,ihu mutanan wurin suka dauka
tare da tabi ana masu ruwan nera da turare,sosai abun ya k'ayatar.
5years later.
Yarinya kyakyawa ke gudu ta fad'a jikin Ahaad tace Daddy "kacewa Ammi ta kyaleni ni bazan
koma gida ba"Farna ta fad'a tana fad'awa jikin Aiban,dariya Ahaad yayi yace"Captain kibar
yarinyar nan wurin Babanta,bazata bimu bafa"dariya sukayi Najma tace to"nima zan tafi da little
Najma kuwa"ihu Farna ta saka ita bazata yarda ba,fuska Fayyam ya yatsina yace"u idiot keep
queit mai bakin parrot kawai"ba musu ta hadiye ihun da takeyi tasan yanzu sai tasha dukan
tsiya..
A yanzu Fadila yaranta biyu Little Najma da Mahamud,sai Nasirah da take wurinta, Shuhada
kuwa ukku dan Muslim yace saiya ta taddosu yara,Islam itace babba sai Afnan sannan Salim
shine auta,Najma kam Faida da Fayyam sai Farna kawai data k'ara.sosai suke kaunar junansu
suna zaman lafiya komai ya koma lafiya suna sada zumunci,a cikin satinne Kuma aka saki
Hajiya Sadiya da Mama,shikam Jamil shekara Goma zaiyi dan haka yanzu yayi rabi,sosai
Mama da Hajiya Sadiya suka canza zaman lafiya sukeyi suna Kuma San jikokinsu da iyakansu
gaba d'aya suma ko wacce ta koma d'akin mijinta,Ummu ce kawai taki yarda ta sake aure take
zauna da tsohuwa Mama Wanda tsufa ya fara kamata.
Fadin irin soyayyar da Najma da Ahaad sukewa junansu b'ata lokacine yanzu kam Babu
abunda ke rabasu zaman lafiya sukeyi da nunawa juna matuk'ar soyayyah.
*alhmdllh, Alhmdllh,Allah na gode maka daka bani ikon kammala k'arshen littafin nan,Allah ka
yafe mana kurakuren dake ciki,Allah kasa kuma a amfana da abunda ke cikinsa*
*Sakon godiyata ga masoya Ruhin Fansa,na gode kwarai da nuna kauna a agareni,sanso
fisabilillah,wannan littafi sadaukar ne ga masoya labarin Ruhin Fansa*
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.
Stylish star
Jorderh majidadi