RUHIN FANSA BOOK 2 COMPELET BY MARYAM MAJIDADI

Author :  Maryam Majidadi Category :  Tknovels

Chapter   5 / 6

12K to 15K   out of 16.5K words

tace"a'a sannunku da zuwa ,tun d'azu nake tsimayen
isowarku"ta k'arashe maganar tana mik'ewa ta nufosu,sun kai minti d'aya suna kallan Kallo
tsakanin Mummy da Shuzna sannan Shuzna ta wayence tare da rungume Mummy tace"barka
Mummyna".rungumta Mummyn tayi tace"lafiya qlau y'ata ,Allah yayi maki albarka sannu da
dawowa k'asar haihuwa".dariya Shuzna tayi sannan Mummy ta rike mata hannu suka zauna a
chair kafin kace me tuni an cika gaban Shuzna da abubuwa iri iri,Mummy sai rawar kai takeyi
tace"ki gama ku gaisa da Governor da kuma Hajiya Mama".
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail Majidadi*

Part 2 ,part 2 ,part 2

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
Page 41-45

Da fara'arsu suka k'arasa akan milisar da Mama ke zaune,kallonta Shuzna takeyi cike da
matuk'ar kewarta,Babu laifi Mama ta k'ara tsufa babu laifi,cikin d'oki Shuzna ta k'arasa gabanta
ta duk'a tare da rungumeta ta baya ta sark'o kanta dai dai wuyanta,da sauri Mama ta d'ago
fuska a hankali tace"Najma",da yake suna hayaniya babu Wanda yaji me tace sai ita
Shuznar,murmushi kawai tayi tace"Mama barka da hutawa".k'ara kura mata ido Mama tayi jin
muryar Shuzna sharewa tayi ganin ba fuskarta bace tace"yauwa yarinya"labari sukeyi amma
kab hankalin Mama yana kan Shuzna yarda takeyin abubuwa da matsa k'afa yasa take ganin
kamar Najma ce zaune a wurin,a b'oye sai share hawaye takeyi.shigowar Amaan yasa Shuzna
mik'ewa tsaye tana kallonsa,wani irin zaro ido yayi bakinsa na k'yarma ya d'aga hannu yana

nuna Shuzna yace"ke..e..ke...Zee...na...t"da sauri ya dafe kanshi ya fice da gudu yana k'ok'arin
sakin ihu yana bubbuga kanshi yana so ya gane ko dai yana da hankali.Daddy suka gaisar
sannan suka isa gidansu Islam,anan da taga Shuzn yi tayi kamar bata Santa ba,anan suka
had'a kawancen yarda babu Wanda zai zargesu.sosai Hajiya Sadiya ta k'arbeta.ta jima sosai a
gidan kafin tayi masu bankwana tace su zauna zataje gida ga Driver dinta nan yazo,tun da suka
fita ,Amaan kam baya ya bisu dan yana so ya tabbatar da abunda ya gani,da sauri tasa Driver
ya taka burki daidai wani super market,har kusan Faduwa takeyi data fito tayi kan wata
kyakyawar mata dake shirin shiga mota hawaye suka wanke fuskarta
tace"Ummu,Ummu"juyowa matar tayi ta kalleta kawai ta shiga mota kafin Shuzna tayi wani
yunkuri tuni Driver din yaja motar yabar wurin,hawaye suka Kuma zubo mata da k'yar ta k'arasa
mota ta shiga,Amaan ko ihu ya saki a cikin motar yace"menene haka yake neman zautar
dani?,ni da hannuna na kashe Zeenart ,haka Ummu amma meya sa sukemun gizo a
idona?,wannan ba abunda zai tab'a yiwuwa bane"da gudu ya taka mota ganin tasu Shuzna tayi
masa nisa har suka iso bakin gate dinsu yaga gidan sannan ya koma gida a matuk'ar rude.
Har yanzu Shuzna hawaye sun kasa tsayawa akan idonta,ga k'afarta da takejin kamar bazata
dauketa ba tunda ta shigo parlon tayi wurki da Jakarta hannu tasa ta b'aro glasses din dake
wurin ta cusa hannuwanta cikin yalwatacciyar sumar gashin kanta ta zube a wurin.Ahaad shine
Wanda ya fara ganinta kafin Nani ta k'araso gareta shi harya iso da sauri ya rike hannunta dake
zubar jini yace"subhanallah,meye haka kikeyi,kin jiwa kanki ciwo"."meye yake samunki
y'ata?"Nani ta tambaya.kuka Faida ta saka tace"Aunty ki tashi please".rike hannun Ahaad
Shuzna tayi tace"naga Mamana,Allah itace na gani,kafin nayi wani abu ta b'ace ta barni"riketa
sosai Ahaad yayi ganin yaran sun rud'e yasa ya dauke Shuzna cak ya wuce sama da ita,Nani
kuma ta Kama su Faida zuwa d'akinsu.koda ya kaita d'akin gefen bed ya ajiyeta ya dauko first
aid box ya soma gyara mata hannun,duk zafin iodine a ciwo ko motsawa Shuzna batayi ba
,kanta k'asa kawai yake kallo idanuwanta sunyi jajawur.kallonta yayi yace"ki kwantar da
hankalinki,wannan ba shine mafita ba,kinsan kina da aeki a yau da dare nan,idan kika kuskure
kin fad'i daga amincewar da abokan aekina suka baki".ganin yarda yayi maganar a daure ya
koma mata tsab oganta a wurin aeki .mik'ewa tayi tare da Sara masa tace"insha Allah General
Ahaad".kallonta kawai Muslim keyi Wanda yake tsaye bakin k'ofa,da hanzari ya k'arasa shigowa
ya rike hannuwan Shuzna hawaye na silalowa daga fuskarshi yace"Ashe kece Najma
k'anwata,Ashe ke jinina ce?".a razane Najma take kallonsa tana son tuno abubuwan da suka
faru a baya,bakinta na rawa tace"tabbas kaine Yayana Wanda Mummy ta kashe d'aya kai Allah
yasa ka rayu,sai yau na gane dalilin da yasa nake matuk'ar son Daddy Ashe shine Uncle Bashir
dinmu,na dade ina ganin kamarsa da Ummuna amma na share hakan,Ashe a cikin Family dina
nayi rayuwa,Allah na gode maka".da gudu ta fad'a jikin Muslim tana sakin kuka,Nani ma kukan
takeyi had'e da dariya ,matsowa tayi tana shafa fuskarshi tace"munyi kewarka sosai Muslim,ka
yafe mana tabbas dani aka had'a kai aka rabaka da mahaifiyarka,amma munyi hakan ne dan
ceton rayuwarka"sunkuyar da kai Ahaad yayi yana jin wata matsananciyar kunya ta rufesa da
sauri yabar d'akin yana jin wani iri daban saboda halin Mummy.nan Nani ta basu labarin
komai,kwafa Shuzna tayi tace"nikam bazan tab'a iya yafewa wad'annan mutanan ba,ko yaushe
su suna kawo hari akan farin cikinane".dafata Muslim yayi yace"ko dan Hallaccin da Aiban yayi
maki bai isa ace kin gafartawa k'anwarsa da Ummansa ba?,duk da nasan Islam itace ta kawo
shawarar a zuba maki Acid Kuma ita ta siyo ta bawa Fadila kuma ita tasa Fadila tasa ayi maki

Fyad'e".murmushi Shuzna tayi tace"Kuma Mamanta harda hadin kanta aka yimun allurar
mutuwa ko?,Kuma Islam itace wacce ta gayawa Ahaad nice Shuzna bayan daya saka aka
kamo masa ita".zaro ido yayi yace"a ina kika San wannan?"."ina tare daku a India amma ruhina
yana nan Babu wasu bincikena da ban gama ba,abunda ya rage shine sora d'aukar hukunci". Da dare ta shirya cikin Uniform dinta na kalan Soji tayi matuk'ar kyau sosai ,sai dai har yanzu
idonta akwai alamar ja ja a jiki,sai fidda kamshi takeyi,da gudu Fayyad ya shigo d'akin tare da
rungumeta yace"Ummu kije dani bana son Zama anan",k'arasa daure igiyar takalminta tayi
tace"haba Super hero ,kasan bazan dad'e ba kuma Ummanku na tare daku,aeki ne na
gaggawa yazo mun"ta k'arashe maganar tana janyo hannunsa suka sauko daga bene ,har a
ranta tana matuk'ar son Fayyad saboda Shima yarda yake tsananin sonta da nuna kula
gareta,a kusa da Nani ta zauna ta rungumota tace"Nani zan tafi"."kai kinyi matuk'ar kyau
y'ata,bara muyi photo a tare"wayarta ta d'akko take hotonsu da Shuzna ya bayyana tun bata
girma sosai ba,camera ta shiga ta soma daukarsu tare,d'aya ta rungumeta,d'aya ta Mata kiss a
kumatu,d'aya Kuma sukayi duka harda yara,mik'ewa tayi ta sumbancesu su duka ta nufi hanyar
fita da gudu Fayyad ya k'araso ya rike hannunta Cuo din madara ya bata yace"kinyi mantuwa
baki sha madarar ki ba"duk'awa tayi murmushi dauke fuskarta Tasha madaran sannan ta shafa
kanshi tace"na gode".kanne Mata ido d'aya yayi tare da sakin murmushi yace"Allah ya tsare,ya
Kuma karemun ke Ummina,ki kulamun da kanki,ko yaushe ina alfahari dake,kedin garkuwace ta
gari garemu,ko yaushe zaki kasance a zuciyar Fayyad Aiban"sak fuskar Ahaad ya koma
mata,duk wani abu nasu yayi kala d'aya,rungume yaron tayi tare da saka masa albarka hannu
ya d'aga mata yace"masoyiya am gonna miss u"dariya duka suka saka a parlon,sannan duka
yaran sukayi mata Allah ya tsare sannan ta fita daga gidan, Driver yaja motarta zuwa babban
barikin soji a katsina,da d'an gudu gudu ta shiga d'akin taron,k'amewa tayi tare da sarawa
manyanta irinsu General Ahaad, General Muslim,General Akiyy da dai sauransu duk manyansu
sun hallara ,ansa Mata sukayi kafin ta k'arasa jikin wani k'aton allo Wanda Computer ke ajiye a
gefansa bisa tebir ta soma masu bayani tiryen tiryen akan yarda akayi aka kwashe kud'in matai
Makin shugabansu,sannan ta Kuma fad'a hanyoyin da za'abi a kawar da irin wannan b'annar
tasha wahala sosai kafin ta gano Wanda sukayi aekin dan da gani Shima k'warone a computer.
Tafa mata sukayi tare da Mata jinjina dan tabbas sun jiniinawa k'ok'arinta ba kad'an ba,hakan ya
k'ara Mata kima a wurin aekinta,gabanta ne yayi mugun fad'uwa da sauri ta soma karanto
addu'a ta samu taji daidai sannan taci gaba da godiyar kyaututtukan da take samu.ba su suka
Kama hanyar gida ba sai bayan sallar asuba,Muslim yaja Ahaad yace"muje idan an ajiye
Captain Shuzna gida sai driver dinta ya mikamu kaga Amaan bai bada motar an kawo ba"ba
yarda ya iya haka suka shiga motar sai faman had'e rai yakeyi,yayinda Shuzna keta jan siririn
tsaki dasun had'a ido ta b'allah masa harara.murmushi kawai yayi ya kawar da kansa yana
Mata akamar zaki gane kuranki.
Daidai k'ofar layin sukaga motar Ahaad fitowa sukayi tun a nan,Ahaad yace"to Kuma waya
kawo motar anan?".jinjina kai Muslim yayi yace"nima ina zan sani".ko kulasu Shuzna batayi ba
ta wuce tare da tura k'ofar parlon tanajin gabanta yana dukan ukku ukku kamar zuciyarta zata
bud'e kirjinta ya fito,ganin duhu yasa ta matsa wurin makunnin kwan fitilar ta kunna,a hankali ta
soma juyowa kamar mai tsoron d'akin baya tayi tana jin jiri na neman kwasarta ,murza idonta
tayi ganin kamar dishi dishi take gani,lallai ba mafarki bane,wani irin zananniyar k'ara ta saka
wacce ta karad'e duka illahirin gida ta Kuma kwala wata k'arar tace"Nani,Fayyad"jin motsin

mutum ta bayanta yana niyar shak'areta yasa ta juya da sauri zaro idonta tayi cikin muryar kuka
tace"sai kayi dana sani,sai kayi nadamar zuwanka duniya,Amaan ka tabka babban kuskuren
k'ara kashemun farin cikina"duka ya kai Mata a fuska ta goce ta kai masa wani duka a
wuya,k'ara ya saki ya nemi hanyar fita,yaransa guda biyu suka rufa masa baya,cikin zafin nama
ta rufa masu baya ta zare bindigar dake jikin wandonta ta soma harbi ta ko ina ,da gudu Muslim
da Ahaad sukayo cikin gidan jin ihun Shuzna,bangajesu Amaan yayi sukayi waje,itama turesu
tayi ta rufa masu baya,cikin sa'a ta harbi Amaan a k'afa,sai yaronsa d'aya akan cinya ,kafin ta
k'arasa garesu suka shige mota suka ja da gudu.dafe kai Ahaad yayi yana Kiran"Innalillahi
wa'inna ilaihir raju'un"Nani da Fayyam ne kwance cikin jini anyi masu yankan rago,gaba d'aya
parlon ya b'aci da jini,da gudu Ahaad ya k'arasa ya d'ago gawar Fayyam sai yaji hawaye nabin
kuncinsa,yau d'ansa ne a hannunsa Kuma wai k'anensa ya masa yankan rago ya kashesa.jin
muryar su Ahaad yasa Faida da Fayyam fitowa da sauri,mak'alk'ale Muslim Faida tayi
tace"Uncle suka kashesu ,suka yankasu muna kallo,Uncle a idona,wani ne mai Kama da
Papa,muma suna nemanmu Fayyam ne ya buga masa katako a kai ya janyeni ya b'oyeni a
bayan k'ofa"nuna gawar su Fayyad kawai takeyi a take ta sulale jikin Muslim
sumammiya,shikam Fayyam jikin Ahaad ya kwanta ya kasa cewa komai .girgiza Faida Muslim
yakeyi amma shiru,ruwan sanyi ya zuba mata amma ko motsawa batayi ba,sai yanzu tunanin
Ahaad yazo masa akan Shuzna janye yaran yayi daga jikinsa ya fito da gudu yana kiranta duk
da ji yakeyi kansa tamkar zai tsage,Shuzna kam fad'uwa tayi akan gwaiwowinta tana sakin kuka
,da gudu Aiban ya fito daga mota ya k'araso ya rumgumeta yace"kiyi hakuri,kada ki d'auki doka
a hannunki,nayi maki alk'arin zanbi hakkin D'ana a ko wanne yanayi".ganin hakan yasa Ahaad
sunkuyar da kai ya koma ciki tare da jingina da bango ya dafe kansa.Aiban yanayin tozali da
hawar su Nani,besan ya soma hawaye ba.ruwa da yawa Fayyam ya ebo ya watsawa Faida ya
girgizata da k'arfi yace"kema tafiya zakiyi ki barni?,ki tashi kada ku barni ni kad'ai ina sanku
sosai"ya k'are maganar tare da sakin kuka mai karfi,wani dogon numfashi Faida ta saki itama
tana sakin kuka,ba arziki aka Kira Dr yayiwa yaran allurar bacci su duka biyu dan nema sukayi
su zare masu.
Cikin awanni kad'an aka gama shirya gawar Nani data Fayyad,Shuzna kam ta koma kurma ko
motsi batayi ha daga inda take,har aka fita da gawarsu.ganin Shuhada ta shigo a rude yasa
Shuzna sakin kuka ta rungume Shuhada suka saki kuka a tare. Kamar daga sama sukaji
magana"yanzu ba lokacin kuka bane,ki Zama jaruma ki share hawayen kije ki gama da
makiyanki,ki kawar dasu daga datsewa duk wani bawa farin ciki,ina so yau ki Zama ta k'arshe
wacce zasu tarwatsa wa rayuwa Najma"jin muryar Ummu yasa suka juyo da sauri su duka.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.

Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail Majidadi*

Part 2 ,part 2 ,part 2

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

End

A kallon Ummu kawai Shuzna takeyi sannan ta fad'a jikinta cikin dishewar murya tace"Ummuna
Ashe zan k'ara ganinki?".
Shafa fuskarta Ummu tayi tace"kwarai kuwa y'ata,komai kike ciki ina sani,ina jiran lokaci kawai
yayi kafin nazo gareki,saiki godewa Yayanki Kuma Baban yaranki danshi ya dauke maki
Ummarki ya kula da ita duk tsawon wannan shekarun yana bata tsaro"sunkuyar da kai Shuzna
tayi ta kasa cewa komai,sai dai tana jin dadin yarda Ahaad ya kula da Ummanta duk da Shima
tashi ce ita ta rainesa,rasa kalmar da zatayi amfani tayi.matsawa kusa da Ahaad Ummu tayi ta
Kama duka hannuwansa ,kansa a k'asa yace"Ummu dan Allah kuyi hakuri,nasan Familyna sun
cuta maku da yawa"rufe masa baki Ummu tayi tace"nima Family dina ne ae,kayi hakuri bana
nufin Shuzna ta cutar dasu,sai dai ina San a d'auki matakin da irin haka ba zata k'ara faruwa
ba".murmushin k'arfin hali yayi cike da kunya amma bece komai ba,shi kanshi tsiyar dasu
Amaan suke aekatawa ya ishesu haka.cikin k'an k'anin lokaci ta sauya kayan dake jikinta ta fice
daga gidan.
Da matuk'ar gudu ya shiga gidan tsaye yayi turus ganin Daddy yana balbale Mummy da bala'i
yace"kinyi abunda kika iya,amma ki sani bazanyi maki baki ba,sai dai yau iyalan y'an uwana
zasu dawo gida,kin cutar dani Bilkisu,bansan iya wanne abubuwa kika saka na aekata ba,bazan
tab'a yafewa kaina ba"ya k'are maganar yana fita daga parlon. Hannu Mummy ta saka a Kai tace"Amaan aekin komai ya bud'e,mun shiga ukku idan Alhaji ya
juya mana baya".
K'arasowa yayi cikin d'akin yace"ae wannan bakiga komai ba akan abunda ke dosomu,Ummu
Sha'awa tana raye Ashe Yaya Ahaad shine Wanda ya dauke Ummu,Shuzna k'awar Fadila
Kuma itace Najma"dafe zuciya Mummy tayi tace"Amaan karkasa zuciyana ta buga,na mutu ka
huta".sallamar Hajiya Sadiya da Islam ya mai da hankalinsu garesu,fuska daure Hajiya Sadiya
ta shigo a hassale ta nuna Mummy tace"Ashe ke baki da mutunci?,yanzu mijin nawa kike
tunanin zaki iya sakawa a ture daga Gwamnati?,to wlh kinyi kad'an ke baki kaiba,duk wani
abunki bayana kika biyo"."Kai Kai Wai meye kukeyi haka ?,yanzu ya kamata mu nemi mafitar
tsiratar da kanmu ne,duk abunda muka dade muna shiryawa zai rushe rana d'aya".murgud'a
baki Islam tayi ta soma zagaye Amaan cikin d'aga murya tace"naku dai ya tarwatse maciya

amana,koka manta yanzu Kai kaje ka kwanto wata rigimar?,Kaine kaiwa yaran Najma yankan
rago,ka kuma kashe Mata Naninta ,bayan a baya kayiwa y'ar uwarta Fyad'e ka kasheta,Kuma
ka kashe Mata Babanta,kayi hari akan Ummanta sai dai ita bata mutuba,Zeenart kam daka
kashe ta mutu sai dai fuskarta aka bawa mak'iyiyarka,Kuma Najma tasan komai akan abunda
ka aekatawa zeenart,abun farin ciki da zan gaya maku shine Muslim shine yaron Umma da
Kuka kashe Mata y'an biyu to D'an uwanta Bashir yaji komai Kuma shiya dauke Muslim ya
renesa,yana nan zuwa gareku".Mari Fadila ta katsawa Islam tace "ke marar mutunci yanzu
Iyayen nawa kike gayawa haka?,ae duk abunda ake k'ullawa da Uwarki Sadiya aka
yishi,hasalima itace mai kawo shawara,banzaye masu bak'ar zuciya kawai"shak'e Fadila Islam
tayi tana kiran"ke harkin isa?,wallahi ko uwarki Bilki bata kaini tasha ba balle ke tsohuwar
guzuma jaka dake".jin an banko k'ofa da k'arfi yasa suka juyo da sauri,Shuzna ce cikin shigar
Uniform dinta na soji,sai yaranta su hudu suma duk a shigar Uniform.ko wannensu rike da
bindiga k'arasa shigowa tayi cikin d'akin tana kallonsu da tsantsar tsana tabbas wa'annan
mutanan sun cuta mata da yawa bata ma san meye zata iya aekatawa akansu ba inhar ta
biyewa zuciyarta.jin an fasa k'ara yasa suka juyo da sauri ganin Fadila na niyar faduwa yasa
Shuzna ta k'arasa da sauri ta fad'o a hannunta Islam ce ta caka mata wuk'a a gefen
cikinta,girgizata Shuzna keyi tace"Fadila ki tashi" hannu Mummy ta daura saman Kai
tace"wallahi yau saina kasheki kema,baza'a tab'a d'aukar gawar y'ata ita kad'ai ba,hakan bazai
tab'a yiwuwa ba"kan Islam tayi gadan gadan Hajiya Sadiya ma tayi kanta nan suka had'e kamar
mahaukata suna kokuwa da juna,fizgo hannun Islam Amaan yayi ya wanke ta da maruka har
hudu ya soma jibgarta,da sauri yaran Shuzna sukayi kansu,hannu ta d'aga masu tace"stay out
of this"Shima k'ok'arin jaka masa wuk'ar takeyi tana zage zage,ganin da gaske shima zata
illatashi cikin bak'ar zuciya ya saita bindigar dake hannunsa akan Islam ya danna kunamar
,wata irin ihu Hajiya Sadiya ta saki tayo kan Islam ,Islam ta fad'o a saman hannunta ga jini yana
zubowa daga kanta,ko shurawa batayi ba ta mutu a wurin.innalillahi wa'inna ilaihir raju'un
kalmar da Hajiya Sadiya ke maimaitawa kawai kenan hawaye na wanke fuskarta yaranta biyu
Islam da Aiban Kuma kowa yasan Islam itace rayuwarta yau ga gawar Islam a gabanta ,wani
kukan ta kuma rushewa dashi,k'ara kad'an Shuzna ta saki lokacin da Amaan ya janyo
yalwataccen gashin kanta take ribom din ya zare gashin ya watsu a fuskarta da bayanta,saurin
sakin Fadila tayi ta mik'e ta samu ta kwace kanta tace"kada ka kuskura k'azamin hannunka ya
k'ara tab'ani".dariya ya fashe dashi yace"Babu Wanda zaiyi rai a nan daga Ni sai Mummyna
Babu wani sarki sai ni a wurin nan"halbi ya soma saki kota ko ina cikin zarin nama Shuzna ta
goce ta koma bayansa,rike hannun da keda bindigar tayi suka soma kokowa ,yayi mamakin
yarda Shuzna tayi k'arfi haka duk da yasan ko a da can tana da k'arfi ba ragguwa bace

5 / 6