RUHIN FANSA BOOK 2 COMPELET BY MARYAM MAJIDADI

Author :  Maryam Majidadi Category :  Tknovels

Chapter   4 / 6

9K to 12K   out of 16.5K words

ta wuce training na tsawan wata shidda cikin ikon Allah tayi ta gama ta zama
cikakkiyar soja Kuma suka dauketa da Digree dinta dan sunan da tayi yasa bata wani wahala
ba ta fito a matsayin Captain.bayan samun horon soji da tayi,abubuwa da yawa sun faru a
lokacin.
*Note zakuga nan page din yawanci labarin yazo a gaggauce to ina so in shiga cikin aenahin
labarin ne,ina so na gama book din kafin azumi,na gode da soyayyarku gareni*

Allah ka gafartawa iyayenmu kayi manakyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail Majidadi*

Part 2 ,part 2 ,part 2

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

Page 31-35

Tafiya takeyi cikin nutsuwa sanye take da uniform na kakin soji tayi matuk'ar kyau a
cikinsu,gashin kanta a nannade ta rike cap din a hannu ba zaka tab'a cewa wai Shuzna tayi
aure ba ,bare Kuma kace ta haihi su Faida,babban wurin taron ta doso da d'an gudu gudunta ta
shigo wurin tabi layi cikin sabbin ma'ae katan da aka dauka sannan ta sanya hular dake
hannunta tayi,kamar yarda aka tsara taron yayi kyau sosai kuma anyi jawabai,manyan sojoji
aka gabatar ciki harda Ahaad Wanda yanzu yake rik'e matsayin General Muslim ma
haka,lokacin da aka gabatar da Shuzna a matsayin Captain ta gidan soji wasu irin zafafan
hawaye ne suka wanke fuskarta,ta d'aga kanta sama tayi magana a hankali tace"Allah na gode
maka,Ina nan zuwa gareku iyalan Kabir Bindawa,wasan yanzu aka fara",tana fitowa daga wurin
Nani ta rungume tace"y'ata Allah yayi albarka,wannan ma wani matakin nasara ne a
rayuwarki,na tayaki murna sosai y'ata"haka y'an gidan suka koma gida cike da farin ciki ga
Shuhada ta zama cikakkiyar lawyer itama ta cika burin nata.
"Ki tashi,ba lokacin baccinki bane wannan,lokaci yayi da zaki cika alk'awarin da kikawa Ruhina
,ki tashi Najma ,ki tashi". firgigit Shuzna ta farka daga baccin da ya d'an dauketa bakinta dauke
da addu'ar bacci,duk lokacin data kwanta bacci takanyi mafar amma na yau ya banbanta da ko
yaushe,lallai Najwa tana tunanin kamar ta manta da burin d'aukar Fansa dake cikin ranta
Wanda ko yaushe yake cin Ruhin ta,"a'a Shuzna lafiya dai ko?"Umti ta fad'a tana kallon yarda
Shuzna ta jik'e da zufa,da gudu Fayyad ya k'araso ya rumgumeta cikin kwarancinsa yace"Aunty
kice ya daina",Fayyam ne ya rugo wurin shima yana cewa"bani abuna"b'oye abun wasan
Fayyad yayi,kallonsa Shuzna tayi tace"my boy kaga Yayanka ne Fayyad ,ka daina binsa haka
da gudu sai kunje kun fad'i?".tsalle Fayyam ya daka tare da kwala ihu ya fad'i akan tayil yana
kururuwa,wata zuciya tazowa Shuzna ta fizgoshi ta dalla masa mari tare da sakar masa
dundu.bai fasa abunda yakeyi ba,cikin Sauri Ahaad ya safko daga bene yace"karki k'ara
dukanshi haka,yaron zaki wa duka kamar kina filin daga?,ke waye ya dakeki?". murgud'a baki
Shuzna tayi cikin zuciya tace"shi yaro ba'a da ikon masa magana?,Babu abunda ya ajiye sai
dukan y'an uwansa,nan jiya sai da ya fashewa Faida goshi yanzu kuma ya biyo Fayyad wallahi
bazan dauki wannan iskancin nashi ba"ta d'auki Fayyad tayi wucewarta,k'wafa Ahaad yayi ya
d'auki Fayyam yayi ciki dashi.
"Bazai yiwuba Muslim,wannan ba abunda zan iya yarda dashi bane,kayi hakuri bawa Shuzna
fuskar Zeenart ba shi yake nuna kazo kace kana sonta ba Kuma,Shuzna tana da miji Kuma
gidan uban y'ay'anta zata koma da yardar Allah"Umti ta fad'a.
Dafe kai Muslim yayi yace"Umti kada kiyi mun haka dan Allah,na tsaya tsawan shekaru ina
kallonta kamar Zeenat na bari ta haihu ne kafin na bayyana mata soyayyata,Umti ki taimaki
d'anki Wanda tsawan Shekara 5 kenan aka kashe masa masoyiya ya shiga tashin hankali har
yanzu ya kasa samun wacce zata maye gurbinta".d'aga masa hannu Umti tayi tace"ya isa haka
Muslim bawai bana tausayinka bane ko wani abu ba a'a ,kasan zanfi kowa san ganin farin
cikinka,amma kaddara bata zo da Shuzna gidan nan danka aureta ba,na gama magana Kuma
kada in k'ara jin kayi maganar da wani".duk'ar da kansa yayi cikin ladabi yace"to Umti insha
Allah zanyi kamar yarda kike so,amma ki sani babu ranar da zan iya yin aure ko naga wata da
kaina nace ina santa".yana gama fad'an haka ya tashi ya fice daga wurin.tashi Umti tayi ta wuce

d'akin Shuzna samunta tayi kwance tayi rubda ciki ,jin an bud'e kofa yasa Shuzna juyowa ganin
Umti yasa ta tashi tace"a'a Umti aeda kin aeko sai nazo basai kin taso da kanki ba"kallon Faida
tayi yarinyar kyakyawar gaske gata fara tas tace"kije wurin Ummanku(Nani)Ina zuwa kinji".da
gudu Faida ta gice daga d'akin.gefan gado Umti ta zauna tace"Shuzna yau zan sauke
alk'awarin dana dauka kanki,kinga komawarki nan Nigeria ina tsoronsa sai dai babu yarda zanyi
tunda aeki ya kaiki can(zataje yin wani aeki Nigeria),Kuma ko ba aeki nasan tabbas zaki koma
gida,wannan fuskar dana baki Wanda nasan kinsan fuskar Zeenart ne y'ar aminiyata,Kuma
itace wacce D'ana Muslim zai aura,wannan fuskar bata cancanta a badata ga kowa ba,saboda
ba kalar kowa bace,lokacin da aka kawoki,duk da kina a sume amma naga idanuwanki suna
fitar da hawaye,naga kina da San k'ara rayuwa,baki da wani muradi daya wuce wannan,shine
dalilin da yasa na dage wajen neman mafita a kanki cikin yardar Allah kuma muka samu
nasara,Ina so ki sani Zeenart kasheta akayi ba mutuwa tayi ba,yankan rago akayi mata saboda
sanin wani sirri da tayi,zan gaya maki Wanda yayi mata haka,amma ko da wasa kiyi mun
alk'awarin bazaki tab'a fad'awa kowa ba".jinjina Kai Shuzna tayi tace"Umti basai kin rok'eni
ba,zan iyayin komai a kanki". murmushi Umti tayi taci gaba da cewa"Amaan shine Wanda ya
kashe Zeenart"a matuk'ar firgice Shuzna ta kalli Umti baki na rawa tace"dama ya santa
ne?"."dalilin mutuwarta ne yasa ta gitta a rayuwarsa,tabbas zaki fuskanci k'alubalan da yawa
daga wurin Amaan,amma insha Allah zaki tsallake Kuma duk wani sirrin da yasa ya kasheta
Zeenart ta gama bayyanamun komai insha Allah idan lokaci yayi zan baki,ke dai ki kula da
kanki".Umti bata jira cewarta ba tayi waje abunta.jujuya Kai Shuzna takeyi a tsawace yace"Wai
kai wanne irin mutunne Amaan?,tabbas ka kasance azzalumi mai rusa farin cikin kowa,tabbas
ka shirya ina zuwa gareka,ba Kuma zan tab'a tunanin kai D'an uwana bane".wayarta data soma
ruri ta dauka ganin Barista Abbas yasa ta dauka da sauri tace"Ina zuwa yanzu"kashe wayar tayi
bata jira komai ba tayo waje kawai,masu tsaronta suka taso tare da bud'e mata mota ta shiga
,kamar kullun da mota biyu suka fita .ba wani nisan tafiya sukayi ba ta k'arasa inda zasu had'u
da Barista Abbas zama tayi a d'ayar kujerar dake kusa dashi tace"barka da zuwa Barista, harka
huta daka fito haka da wuri?". murmushi yayi yace"ae dole nayi abunda ya kawoni
k'asarnan,balle Kuma aeki daku manya ranki ya dade,nasan zaki shiga rud'ani dajin abunda
zan fad'a maki amma karki wani damu kaddara ne yazo da haka,Fadila itace wacce tayi niyar
sakawa ayi maki Fyad'e a Kuma ranar da Dr Jamil yayi maki wannan allurar,ta ajiye lemu a firij
dinki shine Ahaad ya taka sawun b'arawo ko ince Allah yana sanki ya kub'utar dake daga tarkon
Fadila,Ahaad yasha lemun da Fadila ta ajiyene kuma shine Wanda yayi maki Fyad'e a wancan
lokacin a tak'aice dai shine uban y'ay'anki".jefar da glass Cup din hannunta tayi a matuk'ar
razane ta mik'e tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,ni ,ni Shuzna Ahaad shine Wanda yamun
wannan abun?"take kalamansa da yake kiranta da Dabba,mazinaciya,dak'ik'iya suka soma
dawo mata radau a kunne kamar yanzu yake fad'a mata haka,ihu ta saki Allah ya taimaka wurin
rufe yake da glass Babu Wanda zai iyajin sautin muryarta,hannu tasa ta dod'e kunnuwanta
tace"a'a,a'a hakan Sam bazai yiwuba,na tsane shi,na tsane shi,meyasa duk wani farin cikina
Ahalina suke k'ok'arin rabani dashi".dafata Aiban yayi yace"meye haka kikeyi?sai kace wata
warda aka fad'awa mutuwa?meye da Ahaad din?Wanda yanzu zaki godewa Allah kin haifi
yaranki da aurene,ba shegu bane da ubansu".lokaci d'aya fuskarta tayi jawur harda k'asan
idonta had'e fuska tayi kamar an saukar mata da mutu ta kalli Aiban da idanuwanta Wanda suka
firfito waje alamun tsananin b'acin rai cikin kausashiyar murya tace"na tsane shi,na tsane

shi,har abada bazan tab'a sassautawa wani daga cikinsu ba,sun tarwatsamun rayuwata"."duka
abunda aka yi maki ke shaidace Babu saka hannun Ahaad a ciki,wannan ma kaddara ce
kawai,Ina so ki sani zafin kiyayyah baya canza komai Shuzna"."haka zalika bazan tab'a bari
suyi nasa a kaina ba wannan karon,yanzu ne zan fuskancesu,meye amfanin rayuwa idan har
za'a rayu babu martaba?,zalinci kawai suka saka gaba,suyi farin ciki yau Baba Kabir ya zama
Governor a garin katsina ,dan zuwa gobe tunaninsu zai hargitse ne gaba d'aya"files din da
Barista Abbas ya ajiye mata ta dauka ta fice daga wurin suka bita da ido.
Tunda ta shiga mota take kuka harta k'arasa gida,goge fuskarta tayi ta fito cikin izza tana tafiya
shan gabanta yayi yace"Najma daga Ina kike?".a hassale tace"daga inda ka aekeni
malan".sosai ran Ahaad ya b'aci da ansar data bashi ya daure fuska ya nunata da hannu"yake
ki kiyayeni,niba tsaranki bane da zakina fad'amun duk abunda yazo bakinki,sake maki da
nakeyi baya nufin ki rainani kuma,ki rika shiga yarda kike so kina fita Kuma ki dawo lokacin da
kike so". murmushi tayi tace"kasan Dabba abunda yazo kanta kawai takeyi ,yawan kasuwancin
Dana saba na tafi".ji kakeyi tas tas tas ya daiketa da kyawawan maruka.ko gezau batayi ba
bare Kuma ta nuna masa Marin ya shigeta ta nunashi da hannu tace"wannan ya zama na
k'arshe da wannan k'azamin hannun naka zai sake tab'a wani b'angare na jikina,bazanyi
mamaki ba tunda gadon zalinci kayi,Ahaad na tsaneka ,na tsaneka ,na tsaneka bana son sake
ganin fuskarka ina Dana sanin kasancewa a cikin zuri'arku"wata irin zuciyace kecin Ahaad ya
rud'e gaba d'aya tunda yake a rayuwa ba'a tab'a gaya masa ba'a sanshi ba,ko wacce macce
burinta ya kulata,amma yau shi ake gayawa haka,dandanan idonsa ya canxa yace"ni kike
gayawa haka"."ka sani bazan tab'a yafe maka kusantata da kayi ba,ni yarana ba yaranka
bane,kada ka k'ara nuna wata alak'a a tsakaninku,ka fita daga rayuwata dan Allah".
7years later
Allah ka gafartawa iyayenmu kasa muyi kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail Majidadi*

Part 2 ,part 2 ,part 2

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
Page 36-40

7 years later

Jirgin ne ya sauka babban filin jirgi a Kano,cikin takun k'asaita ta safko ,sanye take da kakin soji
ba kad'an kayan sukayi mata kyau ba,lumshe idonta tayi tana jin wani sanyin dad'i na shigarta
ga iskar garinta dake ratsata,lallai yau dole ta godewa Allah,tsawan shekara goma bata garin
amma yau gashi ta dawo mahaifarta,bayanta Nani ce da Shuhada sai y'aranta Wanda suka
gama Zama samari Faida an Zama y'an mata ko wanne cikinsu fuskarsa dauke da
murmushi,cikin yaran dake k'ark'ashinta ne suka zo daukarsu saukar safiya sukayi dan haka
suka d'auki hanyar katsina dan nan ne zatayi aekin nata a k'asarta Kuma a garinta,titi kawai
take Kallo tana tuna rayuwarta ta baya har suka iso tank'amemen gidanta na katsina batace da
kowa komai ba.Fayyam kam sai yatsine fuska yakeyi yace"Ni Mamie ki mayar dani wurin Umti
bana son zama garin nan".dafa kafad'arsa tayi tace"Son nan ne fa garinka na asali ,nan ne
garin kowa naka".zaro daradaran idonsa yayi yace"Mamie kina nufin su Daddy dinmu nan ne
garinsu?"dariya kawai tayi tace"kuje ku huta anjima kayi tambayar naka"Mai aekinsu ta jasu
zuwa d'akinsu,sai Nani ta ja Faida dan tayi mata wanka.
Da gudu yaran ke riga rigan fitowa jin Muryan Aeban,kowa so yakeyi ya fara
rungumeshi,duk'awa yayi ya ware duka hannuwansa ya tungumesu gaba d'aya,dingure kan
Faida Fayyad yayi yace"harda wani saurin riga na fitowa".wani mugun Kallo Fayyam ya wurga
masa Wanda yake fitowa yanzu cikin takun izza yace"wallahi idan ka k'ara ture mun k'anwa
saina karya maka hannun gobe inga da wanne zakayi".ya samu Chair ya zauna sai huci
yakeyi,"k'anwarka ce kai kad'ai malan?ko nakaga wasa mukeyi bane ,Fayyam ka fiye neman
tsokana"Fayyad ya fad'a.glass cup din dake kusa dashi ya dauka yayi jifa dashi amma ya kasa
furta komai da sauri Shuzna ta safko daga sama tana fad'in"subhanallah lafiya?"tsaye tayi turus
tana kallon ikon Allah,sakin Fayyad Aiban yayi ya k'arasa ya Kama Faddam yace"haba son
kullun ina gaya maka ka daina fad'a da y'an uwanka baka bari,kai kullun sai kayiwa wani
duka".cikin d'aga murya yace"to Daddy ae laifinka ne,kaine ka bari Fayyad da Faida suka fara
rungumarka kafin inzo,Ni bana son sai wani yayi abu sannan in yi".murmushi kawai Shuzna tayi
ta k'arasa shigowa parlon tace"Fayyam ka cika rigima da yawa ,to su ba Yayanka da k'anwarka
bace".alama Aiban yayi mata da tayi shiru ya rungumo Fayyam jikinsa yace"am sorry
son".Shima Fayyam din rungume Aiban yayi saboda yana matuk'ar sonshi.
Bayan sati d'aya da sukayi a Nigeria ,komai ya daidaita Aiban ya saka yaran makaranta boko
da islamiyyah makarantu masu kyau ya Kuma d'aukar masu mai lesson komai yana tafiya yarda
suke so,yaune kuma plan din Shuzna zai fara aeki dan ta gama shirya komai ,musamman
yanzu da Abba(Kabir)ya Zama Governor na garin Katsina.bayan yara sun tafi scul, Shuhada ta
yafi wurin aeki tayi wanka ta shirya cikin dogon riga Purple colour sosai tayi mata kyau ta dauko
k'aramin bak'in veil ta daure kanta dashi,hand bag ta dauka bak'a sai hills shoe dinta ma
bak'ak'e sai fitar da sihirtaccen kamshi takeyi tana fitowa ta rungumi Nani tace"saina fawo
Nani,ki kula da kanki".shafa kanta Nani tayi tace"Allah ya tsare hanya y'ata,kinyi matuk'ar kyau
sosai".Shuzna tana fitowa masu tsaronta suka taso da mota biyu suka fita kai tsaye wurin

shak'atawar da yasan kamar yanzu zata samu Wanda take nema ta nufa,Koda suka isa da aka
bud'e mata mota bata fito ba sai da ta tabbar ta hango Wanda take nema,murmushi ta saki
sannan ta ziro k'afarta fari tas ta jima kafin ta idasa fitowa gaba d'aya,Masha Allah shine
mutanan dake wurin suke fad'a saboda tsananin kyan halittar Shuzna da suka gani.kallon Islam
Fadila tayi tace"Islam waccan ba itace wacce taci gasar nan a k'asar India ba?".kallon Shuzna
Islam tayi sosai tace"Masha Allah itace ko,a filima tafi kyau akan a hoto"tsura mata ido
sukayi,ita Kuma kai tsaye ta wuce daidai inda suke cikin wata murya mai dadin sauraro
tace"zan iya zama?,bana son side dincan".har had'a baki sukeyi wurin fad'in"sure madam".
murmushi ta sakar masu ta zauna,order tayi masu na kayan ciye ciye kala kala kafin kace me
an cika teburin gabansu,ruwa kawai Shuzna ta kurb'a ta soma aekin latsa waya,amma a bad'ini
tana nazartar su ne,cikin felek'e Fadila tace"sis bazakici komai bane?".gyad'a kai Shuzna tayi
tace"am owk don't worry".bata dad'e a wurin zaune ba ta mik'e tace"na gode zan wuce"ATM
dinta ta mik'a wa d'aya daga cikin yaranta tace"ka biya bill din".cikin girmamawa ya k'arb'a yace
"owk Madam".cikin sauri Fadila ta mik'a mata hannu tace"am Fadila Kabir bindawa y'ar
Governor ta nan garin".sakin fuska Shuzna tayi ta bata hannu tace"nice to meet u am Shuzna
Bashir".Islam ma hannu ta bata tace"Islam Sadeeq,ko zamu iya zama friends".hannu ta bata
itama tace"why not?,sure".Jakarta ta bud'e ta fiddo card dinta ta basu ta d'aga masu hannu ta
wuce.
Da gudu Fadila ta k'arasa shiga parlon Hajiya Sadiya tsakiyar su Mummy ta fad'a
tace"albishirinku".da goro Hajiya Sadiya ta ansa tace"yau Kuma wanne kamun y'an matana
suka yomun?"washe baki Islam tayi tace"Umma yau babban kamu mukayu,Ina Shuzna Bashir
yarinyar nan da taci gasa a k'asar India ta computer?".cikin sauri Mummy tace"eh,eh meya
faru?".carab Islam ta ansa da cewa"wallahi yanzu muka rabu da ita,kunga katinta data bamu
mun Zama k'awaye".gud'a Hajiya Sadiya ta saki tace"lallai yau babban kamu,kuyi kokari ku
janyota jikinku mu dangwali dukiya mu barga inda take,ae ba abun wasa bane wannan".kafin
kace me harsun gama tsara yarda zasu janyo hankalin Shuzna zuwa ciki su"."ae insha Allah
Mummy kada kuji komai ae mun janyota mun gama kawai".sun dade a gidan kafin Mummy da
masu tsaronta suka daukesu tare da Fadila zuwa gida.
Cikin k'ank'anin lokaci Shuzna dasu Islam sun gama jonewa kowa k'ok'arisa ya fara janyota
cikinsu,yayinda take cike da matuk'ar farin ciki tasan ba zata wani sha wahala ba wurin cinma
burinsu,tunda suka had'u ko wacce ke kwakwar Shuzna taje gidansu amma bata maida hankali
ba,yau ta kasance babbar rana a wurin Shuzna dan yaune Nani Fammah ta k'arb'i muslunci ta
koma da suna Fatima,zaune suke cikin babban Parlonta zaune suke Shuzna ,Islam sai Fadila
fira kawai sukeyi,duk tsawon zuwansu gidan ko kad'an basu gane Nani ba dan ta k'ara kyau ta
murje bare yanzu da takeyin shigar hausawa duk daukarsu Su Faida kannen Shuzna ne,"ya
kamata yau dai ki cika alk'awarin ki Shuzna,yau kikace zakije gidanmu,daga nan mu wuce
gidansu Islam"."yes of course ina sane fa,zanje na shirya yanzu".tayi matuk'ar kyau cikin shigar
farin wando da blue din riga yau toms ta saka ta ja jakarta wurin Nani taje tayi mata sallama tare
da yaranta sannan ta fito yau bata fita da masu tsaronta ba,ita ke driving sai Fadila a front seat
sai Islam a baya,fira kawai sukeyi har suka isa k'ofar gidan su Fadila , Shuzna ta fara danna
Horn aka bud'e suka shiga,kallon get man din tayi shine dai tun nasu na da,sai dai yanzu a
gidan akwai tsaro sosai saboda gidan gwamna ne,basu da wani nisa tsakanin gidan Shuzna da
gidansu Fadila,jin komai takeyi kamar a mafarki Wai yau itace a cikin Family dinta bayan tsawan

shekara goma,a hankali ta fito da k'afarta suka wuce cikin tankak'amemen gidan,a ranta tace
lallai Mummy ta samu abunda take so,tunda suka shiga Fadila ke kwallah Kiran "Mummy
Mummy Ina kika shige?",part din Mummy suka shiga ,zaune a chair suka sameta tasha wanka
ga jikinta duk zinarai,fad'ad'a fara'arta tayi

4 / 6