Author : Maryam Majidadi Category : Tknovels
*RUHIN FANSA*
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Part 2 ,part 2 ,part 2
*AINUWA RITER'S✍*
*SSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Bismillahir rahmanur rahim
Page 1-5 part two (2)
Aiban yana fita da Najma kai tsaye hospital dinshi ya wuce da ita,fadin tsantsar tashin hankalin
da yake ciki ma b'ata lokaci ne,gaba d'aya ya rasa me yakeyi masa dadi a rayuwa ya rasa gane
shin sama yake ko k'asa,miyan bakinsa ya k'are bayajin zai iya furta ko da kalma d'aya karanto
duk wata addu'ar da tazo bakinsa yakeyi,ga kukan Nani da yakeji har cikin ranshi dan shikan
baya san kukan mace balle babbar mata irin Nani.ko daidaita parking beyi ba ya fito da sauri
tare da daukar Najma yayi ciki da sauri Nani na biye dashi kai tsaye Emergency ya wuce da
ita,nurses ne suka bisa baya tare da abokinsa Dr Auwal,d'aya daga cikinsu ne ta rike Nani
tace"kiyi hakuri malama bazaki iya shiga ba"janye k'ofar tayi tare da rufewa,wani kukanne ya
Kuma kwacewa Nani ta zauna a chair bakin wurin ta rasa abun yi,addu'arta kawai Najma ta
samu lafiya,dan idan ta rasa tasan tabbas bazata kumayin rayuwa mai dadi ba.
Duk'ufa Dr Aiban da Dr Auwal sukayi akan Najma amma ba wani labari,dafe kai Aiban yayi
yace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"dafasa Dr Auwal yayi yace"kayi hakuri abokina,ae munyo
sa'a da allurai bata gama cika kwanankinta ba kaga akwai yiwuwar bata gama shiga jikinta
ba,insha Allah zamu gwada wata hanyar yanzu"cikin sauri Aiban yace"Dr Naman,bara n Kira shi
yanzu"Dr Naman zaune yake a k'asar India,shine farkon malamin Aiban lokacin da yake k'asar
India yin karatun likitanci,babban likita ne da akeji dashi a k'asar,yana matuk'ar son Aiban
saboda maida hankalinshi da kuma kwazo a wurin karatu.bugu d'aya ya dauka tare da fara
magana cikin harshen turanci yace"Dr Aiban ya aeki da k'ok'ari?".shima cikin harshen turanci ya
ansa da "Alhmddlh sir,dama na kiraka ne akan wata matsala"natsuwa Dr Naman yayi kamar
Aiban na a gabanshi yace"ina jinka ".sosai Aiban yayi masa bayanin abunda ke faruwa da
Najma .jinjina kai Dr Naman yayi sannan yace"kada ka damu komai zaiyi daidai,ae anci sa'a da
allurar bata gama bin jikinta ba,zan fad'a maka alluran da zakayi mata zai tsaida gubar alluran
ne,ya zama dole ka taho da ita nan da zuwa gobe kada ka yarda a wuce goben,sai ka kula da
fuskar nata ,nasan kasan me zakayi"godiya yayiwa Dr Naman sannan sukayi sallama,cikin sauri
ya fita neman alluran balle wahala takeyi yasha wahala sosai sannan ya samota lokacin da
yazo Dr Auwal harya gama gyaran fuskar Najma ya rufeta da bandeji ruf baka ganin komai sai
farin abu.cikin ikon Allah sukayi mata alluran,sannan ya fita nema masu yarda za'ayi suyi tafiya
ba tare da b'ata lokaci ba.
A hankali Ahaad ya soma bud'e rinannun idanuwansa wanda suka sauya kala zuwa ja,bin
mutanan dake wurin yayi da kallo,sannu kawai su Mummy suke jera masa amma ya kasa
ansawa koda mutun d'aya a cikinsu,dafe kansa yayi da yake barazanar tarwatsewa,lumshe ido
yayi da k'yar Mama ta lallab'ashi yasha magani sannan ya koma barci,"daga ina kike ke
Kuma"Mummy ta jefawa Fadila tambaya.turo baki Fadila tayi tace"Wai Mummy ni kamar wata
k'aramar yarinya zaki sakani gaba da tambayar ina naje"share maganar Mummy tayi kawai
tace"Wai baki San meya faru da y'ar uwarki bane?"yatsina fuska Fadila tayi da nuna alamun
k'osawa da magana tace"naji waye a garin nan da Wanda ma baya cikinsa zaice be sani ba,an
tab'a yarinya mai tashe da dukiya daji da kyau,ae ko ina ya dauka an watsa mata acid an Kuma
kasheta an sace gawar,ni zanje ciki na huta".bata jira cewar Mummy ba tayi ciki abunta tana
kunshe dariyar muguntar da takeyi.
Aiban kam be koma gida ba sai wurin 11 sai da ya tabbatar ya had'a komai na tafiya,Kuma be
wani sha wahala ba kasancewar da marar lafiya za'a bar k'asar,da shi da Nani da Dr Auwal ya
tsara tafiyan,yana shigowa Hajiya Sadiya ta jefo masa tambayar da yasa y'an cikinsa
juyawa"ina fatan bakai ka dauke Najma ba?,bazan tab'a yarda wata alak'a ta kullu tsakaninka
da wannan shed'aniyar ba"Hajiya ta Kuma maimaita tambayan,a tsarinshi baya yiwa Hajiya
k'arya komai yana k'ok'arin fad'a mata Amma wannan karon saiya tsinci kanshi da fadin "ko
kusa Ummana,ni tun da mukaje da Shuhada d'azu gidan to ban sake komawa ba ae,Allah ya
tsare gaba ae naji abunda ya faru"tab'e baki Hajiya tayi tare da wucewa d'akinta bata bashi
amsa ba.shafa kanshi yayi ya mike tare da nufar part din shi a hanya ya had'u da Muslin ,kallon
Muslin yayi fuskarsa dauke da damuwa ,"wai lafiya kuwa?,me yake damunka ne?"Aiban ya
tambayi Muslim,had'iye yawu Muslim yayi yace"bari bro ina cikin tashin hankali,shi wancan
uban zuciyar yayi saki cikin fushi,gashi yanzu Kuma yazo ya damu da acid din da aka zubawa
yarinyar abun d'aga hankalin shine ko gawarta ba'a gani ba,Kuma babu wanda yasan Wanda
yayi mata haka,ga Shuhada can na rasa ya zanyi da ita,ni kaina inajin babu dad'i dan inajin
Najma tamkar yarda nakejin su Islam a raina"."Allah sarki sai hakuri kayi k'ok'arin shawo kan
Ahaad insha Allah zan kula da Shuhada ita Kuma Kuma Najma Allah ya bayyana mana ita,nima
dauriya kawai nakeyi.yana tura k'ofar d'akinshi ya hango Shuhada zaune ta had'a kai da
gwaiwa sai rafsar kuka takeyi,da sauri ya k'arasa ciki yace"haba haba mana my sweet sis,meye
abun kukan Kuma?,ina Ahaad din ya saki matar da aka daura masa a gabanki ?meye Kuma na
kuka irin haka?"Aiban ya fad'a,cikin muryar kuka tace"haba Yaya ni yanzu bata wannan nakeyi
ba,kaji zalincin da aka aekatawa Najma amma kai kamar baka wani damu ba,nu ina Santa har'a
Raina ina jinta kamar ya yarda nake jinku ,duk yarda akayi wannan bak'in zslincin nasan makirci
ne"."ya isa haka bana sonji,kiyi hakuri kiyi mata addu'a insha Allah komai zaiyi daidai bana son
kuka irin haka"da irin wannan kalaman Aiban ya kwantarwa da Shuhada hankali har ya samu ta
daina kuka Kuma ta tafi ta kwanta.
Tunda asubar fari Aiban yayi sallama k'ofar d'akin Hajiya,ansawa tayi tana fadin"shigo mana
Muhammad aena tashi",shiga yayi samunta yayi zaune a bakin bed tana sanye da hijab da
alamaun sallah ta gama,duk'awa yayi har k'asa yace"Hajiya ina kwana?,an tashi lafiya?".cikin
sakin fuska da tsananin soyayyar d'an nata tace"lafiya qlau Muhammad,lafiya na ganka da
sassafen nan?".sun kuyar da kai yayi cikin jinjina maganan da yakeson yi mata can k'asan
mak'oshi yace"Hajiya zan tafi wani aeki India yanzu da safen nan"."Muhammad yanzu kuwa
,tafiya har India ba shiryawa tafiya"."Hajiya tun jiya nasan da tafiyar to ganin ban dawo da wuri
ba shiyasa ban sanar maki ba,aekin na gaggawa ne,kuma munyi magana da Abba a masallaci
yanzu ,zanyi kusan sati biyu a can"jinjina kai Hajiya tayi tace"to shikenan ae da yake sha'anin
aekin ceton rai ne,Allah ya bada sa'a ya kuma tsare"da Ameen kawai yake ansawa sannan ya
taso ya fito domin shiryawa.zuwa k'arfe takwas ya gama shiri har breakfast yayi dan Hajiya
tsareshi tayi,sallama yayi da mutan gidan sannan ya fita,adaidaita yahau ta k'arasa dashi
asibitin,kai tsaye Emergency ya wuce ya samu Najma tana nan yarda ya barta sai dai an
shiryata shi kawai ake jira su wuce airport,shafa kan Najma yayi cike da matuk'ar tausayi yayi
magana a hankali yace"Allah ya baki lafiya Khadija,Allah Kuma yasa fitarki k'asarnan ya zama
warakar dukkanin wani abu dake damunki,Allah yasa ki samu sabuwar rayuwa ki mance da
burikan daukar fansa dake ranki dan ba'a gyara b'arna da b'arna".guntun hawayen dake idonsa
ya goge aka tura gadon da take aka sakata a motar asibiti sannan suka dauki hanyar
airport,lokacin da suka isa kusan jirginsu na haramar tashi dan haka basu wani b'ata lokaci ba
suka shiga cikin mintoci jirgin nasu ya lula cikin sararin samaniya suka doshi k'asar India.
Tunda ya tashi ya soma had'a kayanshi a akwati ,duk wani abunda yake buk'ata sai da ya
had'ashi sannan ya dauki wayarsa daketa faman ruri murya can ciki yace"ya akayi ne?",lumshe
ido Muslim yayi yace"haba Sulaiman yanzu bazaka d'aga tafiyar nan ba?,ka duba jikinka ko
kwari babu Kuma bamu k'arasa abunda ya kawo mu ba"."kaga malan idan zaka je ka shirya in
Kuma baka zuwa ni yanzu zan Kama hanya"be jira ansar Muslim ba ya kashe
wayarshi,akwatinshi ya janyo daidai na matafiya ya fito yakoyi sa'a duk suna dining suna break
,ciki ciki ya gaishesu sai kuma yayi shiru daga duken da yake,Mummy tasan y'an mishkilancin
suna saman kai idan za'a shekara a haka bazai ce komai ba shiyasa tace masa"Ahaad tafiya
zakayi ne?"kai kawai ya iya d'aga mata alamar eh,"haba ka zauna ka idasa warkewa
mana"girgiza mata kai yayi alamar a'a ya mik'e tare da d'aga masu hannu yasa kai ya
fice,yaransa suka karb'i kayan dake hannunsa ,sannan suka jera motocinsu suka fice a hanya
suka d'auki Muslim dan haka suka dau hanyar Niger Delta".
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe.
Kamar kullun majidadi ta dawo,ina fatan yarda muka fara lafiya Allah yasa mu gama
lafiya,sannan Kuma inji ruwan comments kamar yarda aka saba mu farantawa juna rai.
Stylish star
Jorderh majidadi
Page 6-10
*RUHIN FANSA*
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Part 2 ,part 2 ,part 2
*AINUWA RITER'S✍*
*SSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Ga mai neman bayani akan sabon book dina*DIKKO AHMAD* mai fita gobe ya tuntubi
07033636337
Birnin India
Jirginsu ya sauka a garin Mumbai ,juye juye yakeyi yaga ta ina zai hango Umti motar asibiti ta
k'araso lokacin da ake fitowa da bed din da Najma take kwance tamkar gawa,can ya hango Dr
Naman da Umti,murmushi Umti ta sakar masa sannan sukayo inda yake,rungumeta yayi tare da
sakin ajiyar zuciya cikin muryar dake son sakin kuka yace"Umti kinga yarda suka mayarmun da
ita ko?"bubbuga bayansa tayi tace"ni dai Aiban dina jarumi ne,dan Allah ya daure komai zaiyi
daidai insha Allah"(Umti itace Aunty Maryam k'anwar Aunty Sadiya ,Kuma mahaifiya ga
Shuhada da Muslim).risinawa yayi tare da gaishe da Dr Naman shima murmushi yayi sanann ya
rungumo Aiban zuwa jikinshi,Umti gaisawa sukayi da Nani ta Kuma jajanta mata,tun a nan Nani
ta gazgata tsananin kirkin Aunty Maryam,mota suka shiga tare dabin bayan motar asibitin ,kai
tsaye asibitin Dr Naman aka kaita Wanda suke had'in gwaine da Aunty Maryam,d'aki na
musamman aka kai Najma cikinsa duk injina da na'urori na gwaje gwaje.office din Umti aka kai
Nani ,sannan su Kuma suka duk'ufa akan Najma da take k'afa d'aya duniya d'aya lahira,sosai
manya manyan likitoci suka duk'ufa a kanta dan ceto ranta,ajiyar zuciya Umti ta sauke
tace"Alhmdllh,nasara ta farko da muka samu shine allurar ko kad'an bata tab'a cikin dake jikinta
ba"gyad'a kai kawai Aiban yayi yace "Umti what about her?",dafa kafad'arsa wani baturen Dr
yayi yace "soon komai zaiyi daidai"wannan maganar da sukeyi duk a harshen turanci ne.wata
allura Dr Naman yayi mata suka tsaya jiran tsammani tare da mak'ala mata wata na'u'ra mai
danjoji,addu'a Aiban ya somayi yana a matuk'ar tsorace dan wannan ne lokaci na k'arshe in
bata farka ba sai dai ayi hak'uri da ita.ganin danjar jikin na'u'rar zata kawo yayi saurin rintse
idonsa ya rike Umti sosai yana karanto duk addu'ar da tazo ransa dan nesan wacce kala ce
zata kawo ba,dit dit haka na'u'rar ke k'ara tare da halba tsanwar danja,"Alhmdllh ya
Allah,Alhmdllh"abunda Umti ta fad'a kenan,godews Allah Aiban yaci gaba dayi cikin tsananin
farin ciki da jin dad'i,ganin Najma ta farfad'o har k'afarta na motsawa.sosai Drs din sukaji dadin
nasarar da suka samu,kula ta musamman suka bata sannan aka saka Nurses kula da ita office
din Dr Naman sukaje hannu ya bawa Aiban yace"congratulations,na tayaka murnar dawowar
y'ar uwarka,insha Allah nan da kwana biyu za'a iya bud'e mata fuska Kuma allurar barcin da
aka mata zata saketa,sanann Kuma sai muga wacce hanya zamu b'ullowa fuskar tata"godiya
sosai Aiban yayi sanann yayi transfer din kudin da ake buk'ata na aekin yau dan yacewa Umti
baya son komai a kyauta ayi mashi kamar kowa.Nani da taji labarin tashin Najma saida ta taka
rawar murna,taita zubawa Drs din godiya ,ansha daga da ita sannan aka jata zuwa gida.
Tun daga waje Nani ke kallon gidan dukda ba yau bane rana ta farko da ta fara fita waje ba da
Kuma zuwa gidaje irin wa'annan,amma ta jinjina kyawu da tsari na gidan,babban gida ne sosai
komai a tsare yake kwanin ban sha'awa ko ina ga filawoyi suna kad'awa.tunda suka shiga
takebin wani makeken pic da kallo a parlon na wani Dattijo mai tsananin kyau,amma sam ta
rasa ina ta tab'a ganin wannan fuskar sai kawai ta share ta wuce d'akin da masu aekin suka
nuna mata,wanka ta shiga lokacin da ta fito har an jera mata abinci a madaidaicin table na
d'akinta dan haka taci ta kwanta danta d'an huta.
Har k'asa Aiban ya d'uka tare da gaishe da Abba,cikin sakin fuska Abba ya ansa yace"watanni
da yawa malan Muhammad,sai yau har nayi cigiya na gaji"sunkuyar da kai Aiban yayi
yace"Abba ayyukane keyin yawa"."to Allah ya taimaka,naji abunda ya faru Allah ya bata lafiya
ya kuma tsare gaba,jibi zanje na dubata insha Allah"Abba ya fad'a,godiya sosai Aiban yayi
masa sannan ya wuce d'akinsa ya shirya ya koma asibitin,haka Aiban yaketa d'awainiya da
Najma ba dare babu rana ko yaushe yana hanyar asibiti da Kuma kashe mata kud'ad'e.
3days later
A hankali Dr Naman yake warware bandage din dake rufe da fuskarta,yayinda take zaune ko
hadiye miyau ta kasayi sai fargaba da tsoro,Aiban kam kasa shigowa d'akin yayi,zaro ido Umti
tayi tare dayin baya tasa hannu ta rufe bakinta,a hankali Najma ta d'aga idanuwanta Wanda
suka zama kalar ja,ta kalli mirror din dake gefenta k'arami,zaro ido tayi tasa hannu a hankali ta
shafi gefen hagun fuskarta,wata irin razana tayi ta fasa wata irin razananniyar k'ara ta zube
k'asa akan gwaiwowinta,ta fitar da sautin kuka mecin rai.
Wani irin zabura Ahaad yayi amma ya kasa furta komai,zuciyarsa sai ambaton sunan Najma
takeyi amma saboda tsabar mishkilanci ya kasa furta koda kalma d'aya.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"shine kawai abunda Najma ke maimaitawa tana sake hararo
yarda taga fuskarta gaba d'aya rabin fuskarta ya toye ya jagule ya lalace ta tashi daga Najmarta
kyakyawar budurwa,hawayene suka soma zarya a kuncinta,daga Window Aiban yana hangen
komai beyi aune ba saijin siraran hawaye nabin fuskarshi yaji.
Stylish star
Jorderh majidadi
*RUHIN FANSA*
Na
*Maryam ismail Majidadi*
Part 2 ,part 2 ,part 2
*AINUWA RITER'S✍*
*SSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 11-15
Shigowar Daddy mijin Aunty Maryam yasa Najma saurin mik'ewa wani irin bugawa k'irjinta yayi
da k'arfi ta tsare mutumin da ido,shima ba k'aramar fad'uwa gabansa yayi ba,kallon yadda aka
b'ata fuskar yarinyar yakeyi,k'arasowa yayi inda take yace"kefa musulma ce,kiyi hak'uri ki
rungumi kaddararki ki zauna kinji ko"ji tayi wani irin nauyin mutumin takeji da ganin girmansa
dan haka babu musu ta zauna,tare da sunkuyar da kanta k'asa.d'agowa yayi yace"Dr yanzu
meye abunyi game da fuskar nata?"nisawa Dr Naman yayi ya kalli y'an uwan Drs y'an uwansa
dake wurin Dr Ishani ne yace"fuskan ya b'aci da yawa bama da wata mafita daya wuce a canza
mata fuska"wani irin razana Najma tayi ta d'ago tace"yanzu hazan dawo da kamanni na na asali
ba?"gyad'a mata kai yayi alamar eh, innalillahi wa'inna ilaihir raju'un shine abunda take
maimaita hawaye na Kuma wanke mata fuska,da sauri Aiban ya shigo d'akin ya Kama
hannuwanta yana girgizata ganin tana neman fita hayyacinta sai da yaga tad'an dawo daidai
yace"ki kalleni"d'ago idanuwanta tayi ta zuba mashi su,goge mata hawayen fuskarta yayi
yace"ki daina wannan kukan,ur d must strongest women I have ever seen,so karki bani
kunya,wannan ma wani matakin nasaran ne,ki bari ayi maki aekin nan,cikin kwanaki kad'an zaki
warke,ina so kiyi karatu sosai ki dogara da kanki ki haife abunda ke cikin ki,sannan kiyi k'ok'arin
had'a kan Family dinki,ki sani ba'a rama cuta da cuta"shiru tayi can tace"to kayimun alk'awari
zaka barni na cika mafarkina ina so in zama soja"girgiza kai yayi tare da shafa gefen fuskarta
yace"ga iyayena su zama shaida bazan tab'a hanaki cikar burin ki ba".murmushi ta saki tana
zancen zuci."to Alhmdllh hakan yayi kyau,ni Kuma na dauki nauyin karatunta da aekin canjin
fuskar da za'ayi mata"Daddy ya fad'a.har k'asa Najma ta d'uko tana zubawa Daddy
godiya,hannuwa yasa ya d'ago kafadunta yace"kada ki damu,abunda nake so dai karki bani
kunya,ki mai da komai ba komai ba kiyi rayuwa kamar kowa,ki dauka mun zama iyayenki karkiyi
fargaba a kanmu"har cikin ransa yakejin kaunar yarinyar kallo d'aya da Daddy yayi mata yaji ta
gama zama wani b'are na jikinsa,kallon Dr Naman yayi yace"a fara shirya kayan aekin".gyad'a
Kai Dr yayi yace"to wanne suna za'a saka mata a rasid'in da takardunta?".kafin kowa yayi
magana Najma tace"yarda Kama ya canza dole komai ya canza,ka samun SHUZNA BASHIR"ta
fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.shafa kanta Daddy yayi yace "na gode kwarai da kara
Shuzna,kinga yanzu y'an matana biyu Shuzna da Shuhada"dariya Umti tayi tace "baban y'an
biyu kenan.
Duk yarda Nani taso ganin fuskar Najma hanata sukayi sunsan ba k'aramin tashin hankali zata
shiga ba,dan haka sai dai suka ce mata za'a canza saboda wani b'are ya toye sosai,Nani tasha
kuka marar misaltuwa amma haka dai ta hak'ura ta zubawa sarautar Allah ido.
After 3 days
Sanye aka fito da ita da kayan aeki a jikinta