WAZAI FURTA BOOK COMPLETE BY ZAINAB DAHIRU WAWO.txt

Author :  Zainab Dahiru Wawo Category :  Arewa Pen

Chapter   8 / 30

21K to 24K   out of 89.4K words

me ya hana kizo ayi dake?
Ko Zaki hanani ne?
Sadeeq zai Kara magana ya nuna Shi da yatsa a hostel zamu hadu zanga ubanda ya tsaya maka kaima......duk suka zaro ido lallai fa da gaske yake. Sannan ya kalleta kada Allah yasa kiso ke Kika rasa........ Ya wuce fuuuuu ya fada wani class ya zauna Rai bace kamar zaiyi hauka idanun sa sunyi jawur.
Bilkisu ta rasa inda zata Sanya kanta, kuka zatayi ihu zatayi, itama nata idanun sukayi ja tare da kawo ruwa kamar zatayi kuka abin yazo kaina?
Hakan take ta nanatawa cikin zuciya.
Sadeeq ya kalleta hankali tashi, wallahi fada zamuyi dashi tunda Kika ji ya rantse....... Ta zaro ido fada?
Hmmmmm Baki San halin Anwar ba..... Sai akwai tabar Shi nan ta wuce class din da taga ya shiga....
Yana zaune ya hade Kai da table. Ta zauna kujerar gabansa, ta Kira sunan sa,
Anwar!..
Ya dago da sauri sai da gabanta ya Fadi ganin yanayinsa.
Ta daure ta Kura mishi ido zuciyarta kamar zata fito amma ta daure kada tayi sanadin raba abokai . Ta Fara magana a hankali.....
Ba ruwan sadeeq cikin maganar nan, kada laifina ya shafeshi duk abinda zakayi mishi kayi mun Amma kada ka Sanya Shi ciki kayi hakuri ka kyaleshi .......bazanyi hakurin ba. Ya fada kamar zai mareta.
Duk ajin akayi shiru ana kallonsu,
Ya daga murya, ke har Zaki ce na Bata lokaci Baki so na koya miki? Ni idan naje wurin malamai su koya mun korata sukeyi wani lokacin sai na kwashe fiye da awa daya sannan suce in tafi in Basu wuri, bana zuciya gobe sai na koma sai ke daga Yan mintoci Zaki nemi kiyi mun wulakanci cikin jama'a?...... Naji kayi hakuri,......
Bazanyi ba nace ki tashi ki bani wuri.....gabanta ya Fadi.
Ta daure ta hadiye kwallan dake son taruwa a idonta tace sadeeq nake nufi kayi....... Bazanyi hakurin ba ya Mike, idan ke bazaki tashi ba ni na tafi.....kawai yabarta wurin.
Na shiga uku ni Bilkisu ta fada.
Tashi tayi tabar class din don kwallar sun kasa tsaiduwa.
Ni Anwar zaiyi ma wannan wulakancin? Ni Anwar zai dizga?
Ni Anwar zaiyi ma gorin karatu?
Me yasa tun farko na bashi fuska?
Idan sai Anwar ya koya mun karatu zanci jarabawa billahil azim na hakura da degree har abada. Biji biji take ganin hanya....ba abinda kanta keyi sai sarawa, kaicho na ni Bilkisu na kyale Anwar har abada tallahi ko kallonsa bazan karayi ba.....ta bude daki ta fada bisa katifa sai kuka.........
Hankalin sa yafi nata tashi, kamar mahaukaci ya Isa daki Anas ne kwance ya fada bisa katifa Anas na shiga uku nayiwa Bilkisu wulakanci.
Ya zaro ido me ya faru.?
Yarinyar nan kureni tayi yau, na rasa ta inda Zan bullo mata.....naji me ya faru.
Ya Mike kamar mahaukaci.......laifinta ne nasan gobe zata Kara bani hakuri. Zamu shirya .....ya fice dakin.
Duk duniya Yanzu Babu Wanda takejin tsanar say ranta irin Anwar ko sunan sa Bata so a fada ta fita batunsa Amma kullum cikin kuka take.
Kwananta biyu daki kwance ta kasa zuwa lecture saboda Bata kaunar Kara ganin sa.
Shi Kuma jira kawai yakeyi tazo ta Kara bashi hakuri su dai dai gashi Yana ganin ya zubda ma kanshi class matukar ya kirata a waya, abinda bai sani ba har ta goge no. Sa cikin wayarta.
Abu kamar wasa kusan sati Bata zo school ba, sai dai kullum tabi dakuna ta karbi note tayi.
Ranar laraba ta Kama kwananta tara rabonta da school Shima tazo ne dole saboda za'ayi C.A Kuma course din da tafi tsoro.
Dadi ya kamashi yasan dole yau ta nemeshi.
Yana zaune Yana koya masu Helen ta shigo gabansa ya Fadi ganin irin ramar da tayi though Shima ya Dan fada.
Layin da yake Bata kalla ba ta Isa can baya, Damian please help me here ta fada a hankali..... Ashe bai iya uwar komai ba nan da Nan hankalin Anwar ya tashi ganin ana koya Mata wrong.
Helen ta zungureshi ga fa Bilkisu..... Eh na ganta, tana fushi dani ne Kinga taje Damian na koya Mata hauka. Mtsew ya buga tsoki.
Ya kasa ci gaba da koya ma Helen din.
Damian na gamawa tabar class din sai lokacin test ta dawo.
Tana shigowa ta hango sadeeq ta Isa wurin Shi....... Alhamdulillah dama Ina ta addu'ar kada a riga ni.
Yayi murmushi kawai, tare suka zauna ya Bata ta kwashe hankalin Anwar na kansu kamar zai haukace.
Tana gamawa taje tayi submitting tayi tafiyarta daki Koda Anwar din ya fito bai ganta ba ya Kara hasala....... Sadeeq na fitowa ya Fara surma mishi Zaki har Yana yunkurin dukansa Wai ya zauna tare da Bilkisu test.......🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Tirkashi.

Ayi hakuri da kadan...✍🏼. Zainab wowo ce💖😄
Juma@ mubarak don't forget to receive suratul kahfi👏🏼
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: 🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
0⃣7⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ina alfahari daku kawayen yarinta:*
*Rakiya Amadu m/bread da badiyya Amadu m/bread*

***************

*Federal University dutsinma*
Aisha, sumayya da khausar sune kawayen Bilkisu na kut da kut!, Tare suka zo makarantar secondary school daya sukayi watan federal Bakori dake shiyyar funtua ta jihar katsina.
Aisha da sumayya political science sukeyi, khausar na micro biology sai ita Bilkisu dake Economics.
Su ukun dakin su daya, Bilkisu kadai ke nata dakin.
Mafi yawa su ne suka fi zuwa dakinta ko a secondary ana tare Amma ita komai nata daban ne.
Tana yawan yin girki baka raba ta da ko miya ce Shi yasa Mafi yawa sune ke zuwa wurinta neman abincin musamman irin lokacin da semester ta raba tsakiya komai yayi zafi.
Khausar na bala'in son Anwar Amma tun lokacin da ya dizga ta daga magana taji ya fita ranta.
Aisha ce ta shigo dakin tana ta kokarin yanka carrot da zata Sanya cikin farar hinkafar Daman tun safe kafin ta fita tayi miyar kifinta.
Ke yunwa fa nakeji har bana gani.
Tayi murmushi to gashi Bata karasa tsanewa ba ko zakiyi tsame yau ma?
Mtsew tayi guntun tsoki, tare da kwanciya bisa lumtsetsiyar katifarta, wannan uwar shinkafar Kuma fa ko yau kin tabbatar zamu zo kwaraka ne?
Ta dan tabe baki Anwar ne Mana da rigimar sa nace zanyi girki Wai zaici na tafin mishi dashi class 4 idan zamuyi tutorial.
Hmmm, kawai tace.
Ta Dan waigo Fadi kada ta kasheki.
Ta kyalkyace da dariya keji Kama Kai ai bandai *furta* ba ko?
Murmushi tayi kawai,
Daga Nan Bata kara mata magana ba.
Yar madaidaiciyar cooler ta samu ta zuba mishi miyar Kuma tayi amfani da Yar roba Mai marfi.
Saboda kurewar lokaci a daki tayi sallah tun kafin ta sallame yayi mata missed call biyu.
A gurguje ta shirya ta fito.
A bakin gate ta kirawo shi, bugu daya ya dauka.
Malama kinfa shanyani,
Ya hankuri gani na shigo school kana Ina?
Lecture room 2, ya fada.
Okay I'm coming......ta kashe wayar.
Sanye take da doguwar riga ta lace coffee brown, hijqbinta kalar flowers lace din maroon.
Tana saka kafa wayar ta na Kara *Daddy ne ke mata video call* ta karasa da sauri tana murmushi.
Ya hangota Amma sai yayi kaman bai ganta ba har ta zauna kusa dashi dai dai kuma lokacin da ta ajiye mishi ledar abincin sannan ta latsa wayar.....Hello daddy. Ta fada tare da fadada murmushinta zuwa Yar dariya.
Yabi fuskar ta ta da kallo Yana masifar son tayi dariya Shi kadai yake ganin abinda yake gani.
Bilkisu ya kike?
Kina class ne?
Eh daddy kaga nazo karatu ne wurin Anwar ta kanga fuskar wayar saitin Anwar din.
Yayi saurin sunkuyar da Kai...... yarinyar nan nada hankali kuwa?
Anwar?.......ya dago ido da sauri....barka da wuni Daddy ya fada da sauri tare da rusunawa Yana Dan murmushi.
Dariya yayi ......Kaine Anwar? Yau ba'ayi fadan ba kenan?
Ya zaro ido kadan kunya ta baibayeshi yayi saurin kallon Bilkisu atuhumce.
Ta janye wayar.....mun shirya daddy yaban hakuri ta fada tana dariya.
To yayi kyau. Allah ya taimaka a kula dai kada amanta Allah Yana tare da kowa a zahiri ko badini.
Na sani daddy.
Ta zaro ido Wai daddy kana sokoto ne???
Eh mun zo nida mommy bikin saifullahi ko?
Ta zumburo Baki daddy......ke sai anjima kuyi karatu kada lokaci ya shige......
Daddy zakuzo din ko?
Eh in shaa Allah zamu shigo jibi......yeeeeeee ta fasa Kara yayi saurin latse wayar Yana dariya.
Ta kalli Anwar su daddy zasu zo jibi......ya dalla mata harara. Ya akayi yasan muna fada?
Ta danyi guntun tsoki.... Ai sun Sanka Ina Basu labarinka sosai.....kina cewa me?
Tayi murmushi.
Kinji?
Hmmm kawai tace.
Magana zakiyi meye kike fada ne?
Ka gane sun San wajen ka nake daukar karatu to ya kirane yace yau bamuje karatu ba nace munyi fada dakai shine........yaushe mukayi fada?
Me yasa zakiyi karya? Sai kice fushi nakeyi dashi ba kice muna fada ba.......naji sorry oya muje ta bude littafin.
Ko sai kaci abincin zamuyi?
No, Zan tafi dashi hostel ne.
Okay.
Lafiya lau sukeyi tana ganewa sosai, yana magana tana satar kallonsa idan taga ya maida hankali ga littafin sai ta daddage kuwa ta Kura mishi ido.
Yana da kyau, natsuwa da Kuma kamala problem dinsa kawai miskilanci.....da yazo zai kalleta sai tayi saurin kawar da ido....haka..haka....sunyi nisa sosai sai taji an kwada mishi Kira ```ANWAR```.....
Dukkansu suka kalli wajen... Mufeeda ce.
Gaban Bilkisu yayi mummunan faduwa.
Saboda, mufeeda ana raderadin budurwar Anwar ce physics department take yarinyar ta hadu karshe saboda iya daukar wanka, Bata fi Bilkisu kyau ba Amma saboda iya gayun ta yasa idan tana wajen baza'a taba ganin kyan Bilkisu ba da kullum cikin hijabi.
Sanye take da wani material dinkin Riga da skirt, tayi kyau matuka fuskarta sanye da kwamemen glass ya mata kyau sosai.
......... Ta tsaya daga jikin taga alamar ganinsa take sonyi.
Kawayen ta Kuma na gefe suna jiranta.
Ya kalli Bilkisu please Ina zuwa, ya mike.
Wani abu ya taso mata ya tokare a makogoro tunda ta yi kasa da Kai bata dago ba.
Tana ta latsa waya ta ma kasa gane inane take shiga tana fita.
Agogo kawai take dubawa.
Mufeeda nada daukar hankali, kafin kace me.....Anwar ya fara shafa'a.
Ai nayi tunanin bazaka taso ba tunda ance tsoron ta kake ji.
Yayi murmushi sai kuma na taso Kika gane hakan ba gaskiya bane ko?
Wai meye tsakanin ka da yarinyar can da kullum baka tashi koya mata sai da marece Kuma ku biyu kawai?.
Yanzu dai gani. Ya fada Yana murmushi.....
Ta dalla mishi harara minti nawa ta baka ne?
Ni kamar baka cikin natsuwa ma wallahi. Baka daukar waya baka amsa gayyata idan ma an iske ka..... Ikon Allah mufeeda ki Bari zamuyi waya anjima Kinga Babu dadi......babu dadi ka barota kazo wurina?
Bai San lokacin da ya kyalkyace da dariya ba ......dai dai lokacin da Bilkisu ta dago Kai, kutumar bala'i....
Yana mamakin yanda yanmata ke tuhumar Shi akan Bilkisu.
Mikewa tayi ta hada litattafan sannan ta dauki ledar abincin kawai ta fito......
Ba karamin razana yayi ba don yasan kwanan zancen..... *Bilkisu*.......... *Bilkisu*.... *Bilkisu*!!!....... Amma Ina! Ko waige....
Duka yaushe ya samu suka daidaita, mtseww.
Please zamuyi waya ya fada tare da Dan rugawa *Bilkisu*.......
Sauri takeyi sosai, ya cimmata da kyar...Dan Allah kiyi hakuri.
KO kallonsa batayi ba.
Wallahi ban manta dake ba Ina cikin kwatanta mata naga kin fito......... Nace ka manta Dani ne? Ko kaji nace nayi fushi ne? Kaje ka gama da ita ni lokacin da kake free Zan dawo tunda nice nake nema a wurinka......kiyi hakuri Dan Allah.
Ta tsaya cak tare da kallonsa..... Banyi fushi ba, kamar yanda ba haushi naji ba, ai kana da damar ka ko?
Wannan bin da kakeyi mun Shi zai hasalani don haka ka koma ka kyaleni.......ya daga hannuwa sama, naji Amma kiban abincin Mana......wallahi bazaka ci Shi ba. Ta fada tare da wurga mishi kallon da yafi komai tsana sannan ta tafi tabar Shi tsaye.
Wai me yasa bazai kyale yarinyar nan ba?
Duk Yan mata na shakkar sa me yasa ita bata tsoron yi mishi gadara?
Ko ya ayyana zaiyi fushi da ita Shima me yasa baya iyawa?
Yaja wani dogon tsoki....... Ya wuce a fusace.

*******************
*KADUNA RIGASA*
Wannan ba shawara bace, kasan su mata shaidanin su babba ne, Basu da hankali ko kadan.
Idan nayi haka mun Zama daya dasu kenan.
Abinda nake gani ka dawo gobe da safe kawai Bari na shiga masallaci na kwanta.
Amma yarinyar nan akwai Yar iska..... Ya dafa kafadar idanun sa kamar garwashi kada ka damu, mu zauna da safen...... shikenan Zan taho dasu hajia......noooo kada ka Kira kowa please.
Dole ya hakura ya tafi ba don ya so hakan ba ..... Abin Babu dadi hakan yake ta nanatawa a cikin Rai domin yasan kawaici ne yakeyi mishi saboda kada abotar su tayi rauni.
Ya girgiza Kai......zata ci ubanta goben.
Ina Kai Yara school 7:30 gidan Zan yi ma tsinke.
Hakan kuwa akayi,
Kamar kullum karfe bakwai Yara suka fito Yana hangosu ya fito masallacin saboda Babu Wanda ya gane a can ya kwana daga cikin masu aikin gidan sai Mai gadi.
Ya ce Ahmad je ka karbo mun mukullin motar mamar ka.
Da gudu ya juya, tana kitchen tana gyaggyara inda tayi aikin kayan break din yaran domin ( Amira tana da masifar tsafta Sam da yawa Bata jiran masu aiki musamman bangaren da ya shafi dahuwar abinci).....Kai lafiya ko jakar ce ka manta?
Abba yace ki bashi makullin mota.
Ta kalleshi sosai Ina Abban?
Gashi can ya fito daga masallaci....gabanta ya Fadi. Kamar zata Kuma tambayar Shi sai ta fasa ta tafi daki don dauko mishi.
Ya kura ma kofar ido ya kalli agogon wayar sa har da kwata tayi Yana mamakin dadewar da Ahmad din yayi sai gashi ya fito da gudu.
Ya Dan saki ajiyar zuciya har Almustapha ya Dan kalleshi abinka ga yaro bai hasaso komai ba saboda Babu kwalwar tunanin.
Duk abin nan tana tsaye jikin taga tana kallon su, Yana fita da motar ko layin bai shanye ba ta fito da sauri don komawa bangarenta, maimakon tabi ta hanyar baya kamar kullum sai ta fito ta kofar gaba, abinka ga babban gida kuwa tana mikewa zata Sha kwana Yana shigowa da mota.
Gabanta yayi mummunan faduwa ta tsorata ainun sim...sim ...sim ...zata wuce ya fito. Wurinki nazo daman.
Ta yi zuru zuru da ido alamar rashin gaskiya Yaya Ina kwana ta Dan rusuna, ya wuce gaba muje daga ciki.......
Mai aikinta har tazo tana ta goge goge, saboda tana da nata makullin.
Yana shiga yace ke fita ki jira a waje..... Tayi saurin ajiye mop kuwa.
Tana bayan sa zugum tayi tsuru tsuru tsaye....waigowar nan da zaiyi kuwa sai kauuuuu ya wanka mata Mari ta gigice kafin ta saka hannu ya Kara wanka mata......sai kawai ta zukunne don girman Allah Yaya na tuba......ta fada cikin karaji tana kuka....
Dan ubanki kina tunanin kin wuce duka har Yanzu? Ke har Zaki rufe ma miji kofa Kuma nazo nayi magana kinji muryata saboda ki nuna bamu Baki tarbiyya ba shine Kika yi shiru. Ya daga hannu zai Kara Kai mata bugu yaji an rike hannun........Kana da hankali zaka Dakar mun Mata?....... Ya fincike hannun cikin bacin Rai....Dan ubanta ta wuce a dake ta ne?
Ya janye Shi, malam ba haka ake sasanci ba....Ni kiranka nayi ka sasanta ni da matata ba ka rikita man ita ba........ Sasanci? Kishin nata na hauka shine zaisa a sasanta ku? Sai dai in Mata rauni in karairayata Dan ubanta...kizo ki iske Shi da matar Shi da yaranshi ki nuna Baki kaunar su don Kina mahaukaciya har kiyi tunanin zakiyi daraja da kima?
Duk suka zauna lokaci guda...... Saurara malam.
Matsalar Ummi daya tsageranchi da wannan mugun kishin na kwatanta Mata Amira Bata da matsala......ko tana da matsala ba dole tayi hakuri ba tunda ta Aure Mata miji don ubanta.....
Dan Allah ka daina hargitsa lamarin nan.
Ummi koma can ki zauna.....ya nuna Mata kujera...ba gardama ta tashi fuskar har tayi fushi.
Wallahi tallahi ban auri Ummi don in mayar da ita zawara ba. Amma Ina Mai tabbatar maka da cewa muddin ta Kara kuskuren da tayi jiya na rantse da Allah sai na rabu da ita Koda zata kawo karshen alakar mu......saboda tun farko ita ce ta hada mu?
Noooo....
Then, what do you mean, wannan idiot din ta Isa ta rabamu ne? Daga alfarmar Dan ubanta?......Dan Allah ya Isa.
Ummi .....Ummi...ummi.
Ya Kira sunanta sau uku.
Ga Dan uwanki zan maki magana ta karshe daga yau.
Kina son Zama Dani?
Tayi shiruuuuuuuuu,
Ki bude Baki kiyi magana yau zanyi wa tubkar hanci.
Kin shirya Zama Dani?
Da kyar ta daga Kai alamar eh.
Good, to saurara.
Muddin kina son Zama dani sai kinbi wadannan dokokin wallahi tallahi inba haka ba Zan sawwake Miki Yanzu matukar kikaji sunyi Miki tsauri.
Idan kuwa Zaki iya to ki sani Koda wasa Kika kuskure Nan gaba daga gone har shekara dari Nan gaba kada ki taba tunanin ban iya rabuwa da mace don na haihu da ita ba wallahi ko duniyar Kika safke mun sai na sallameki.
Na farko Amira wacce ta zame Miki damuwa tun kafin ki shigo gidan Nan. Matukar kina son Zama Dani sai kin Mata biyayya da kyautatawa, na biyu maganar abinci ya Zama wajibi kiba kowa hakkin sa lokacin da kike da dama. Na karshe Yan aikin gidan nan ki sani ba bauta suka zo ba neman abinci suka zo yi to ya Zama wajibi a kyautata ma nemansa ta ko wace hanya. Cin fuska ,izza da gadara bazan Kara dauka ba.
Allah ya gani naso in biki ta ruwan sanyi to maganar gaskiya yau na kafa shaida da yayanki akan kadan daga cikin wautar da kikeyi gidan Nan. Maganar iyaye na Kuma ko na Amira kice ma Baki sansu ba wannan kanki kikayi mawa domin duk Wanda ya kashe uwarshi to Shima baza 'a mishi kani ba.....
Wannan kenan shawara Kuma Yanzu ta rage daga wurin ki.............
*************
*Federal University dutsinma*

Idanun sa jawur kamar garwashi ....dakin a cike Amma ana ganin yanayin sa kowa ya Fara zarewa one by one. Ko takalmi bai cire ba ya fada bisa katifa ruf da ciki.
Anas ma fita yayi sadeeq kadai ya rage.
Anwar......ya Kira sunan sa.
Bai amsa ba Amma ya dago Kai.
Lafiya dai ko?
Kamar jira yakeyi...... sadeeq bana tsoron yarinyar nan wannan Zan biye Mata fa.
Bilkisu?
Ya buga tsoki who else?
Me Kuma ya hada ku?
Simply useless girl din nan mufeeda tazo muna karatu she couldn't even understand abinda nake undergoing a wurin yarinyar nan ta fito a

8 / 30