WAZAI FURTA BOOK COMPLETE BY ZAINAB DAHIRU WAWO.txt

Author :  Zainab Dahiru Wawo Category :  Arewa Pen

Chapter   21 / 30

60K to 63K   out of 89.4K words

kitchen na hangen su..... Ta Kama dariya ita kadai....lallai Bilkisu tana da aiki.
Ta fito da doguwar hijab har kasa ta banka mishi harara muje..... Suka bi bayanta..
Ba sadeeq ba, Anwar kansa falon ya tafi da imanin sa, ya zauna bisa two sitter sadeeq Kuma ya zauna kujerar dake can karshe Shi kadai ya ma t.v kuriiiii ganin ana best film dinsa *mortal combat*
Ta zauna bisa three sitter tana facing sadeeq ta Kara gaishesu
Sadeeq ya kalleta Yana dariya sai Kika ganmu ko?
Tayi murmushi hmm,
Hakuri muka zo badawa..... Ke ki dawo Nan kin mun nisa... Ya fada Yana kallonta.
Tayi kamar Bata ji ba, sai kawai taga ya Mike tayi saurin kallonsa... Yana tasowa ya figo hannun ta Yana fadin ke wallahi wata bagidajiya kike wancen Dan iskan ba dashi zakiyi fira ba ni ne bakon...... Ta fizge hannunta... Akwai CCTV ta nuna mishi da hannu.... And then?
Ta zaro ido.... Kai Wai baka da tsoro?
Mtsew yaja guntun tsoki tare da figarta da karfi ya zaunar da ita kusa dashi, just sit down here.
Kaii Allah ya raba ka da rigima..... Allah ya rabaki da gardama kema.
Rahina ta shigo da tray cike da kayan marmari da lemuka masu sanyi ta Fara jerawa a dining table sannan ta fita tana kawo kuloli kala kala.....
Baza mu ci abinci ba fa saboda bamu sanar ba kada a takura ayi Mana.
Har an gama ai, idan baku ci ba mommy zataji babu dadi?
Me yasa Kika kashe wayar ki?
Tayi shiru tana murmushi.
Kinji?
Duk kin rame kinyi rashin lafiya ne?
Um, ta ce.
Ko dai tunani na ne?
Ta galla mishi harara , ya kyalkyace da dariya ni ma na rame ko?
Um, ta ce.
To ki tambayeni dalili Mana ...... Ta danyi murmushi kaiiiiiii Anwar.
Me yasa Kika koma da gudu bayan kin ganni?
Tayi Yar dariya....
Murna CE?
Ta Kara galla mishi harara.
Bacin wancen Dan iskan da Baki sako hijab din nan ba kayan sun Miki kyau kin San Haka?
Ta ce hmmm, kawai.
Gobe Zan dawo ni kadai kada ki Sanya hijab kinji ko?
Ta harareshi kammmm.
Yayi murmushi Dan Allah kisa irin gyalen dazun.... Bafa Zan saka ba dazun ma na manta ne..... Zan cireta idan Kika saka wallahi...... Anwar Nan fa gidan mu ne nidai ka rufa mun asiri. Ni Yanzu ka janyo mun anjima dole in amsa tambayoyi wurin daddy?
Na mene?
Dalilin zuwan ka ko?
Kice fada mukayi gashi kin kashe wayarki nazo bayar da hakuri...... Nidai Dan Allah da baka zo ba saboda zai...... Ya tsareta da ido. Tayi shiru.
Uhum, Ina jinki saboda zai ce meye?
Nidai shikenan.
Ya kalli sadeeq jeka ci abinci fa, okay ya Mike ya nufi wurin
....ke Kuma kawon nawa anan inci.
Saboda me?
Saboda bana son kimun nisa Kuma bazan yarda gani ga ki ga sadeeq a wuri daya ba muna ci...... Wai Kai meke damunka....????
Yayi dariya kawai.
Suleiman ya kiraki?
Gabanta ya Fadi, wace amsa zata bashi kada Kuma ya Kara hasala saboda ta lura tabbas baya kaunar Shi.
Bari kawai na fada mishi gaskiya..... Ya yi ta Kira Amma ban dauka ba wallahi...au haba?
Allah kuwa.
Ko shine dalilin da yasa Kika kashe wayarki?
A'a ba Shi bane.
To nine?
Tayi shiru.
Saboda me Kika ki daukar wayarsa?
Anwar ka daina kawo maganar Suleiman tunda ita ke kawo Mana sabani..... Dole ki canza layi..... Ta zaro ido dole fa kace .
Yasha mur tabbatas and I mean it.
Ta Mike kawai tana hararar sa, ya Kai hannu zai kamata tayi baya da sauri tana fadin Zan kawo ma abinci ne.... Sadeeq ya banka mishi harara kaidai wallahi bakayi ba..... Yayi murmushi ka Gama kazo ka bar Falon nan ka isheni haka Nan .... Babu inda zaije. Ta fada tana zuba mishi farfesun Koda da dankalin turawa....
Ki hanashi din ki janyo ma kanki Yanzu in ci ubansa anan har su daddy suji.... Gabanta ya Fadi tasan karamin aikin sa ne.
Ta kawo Masa ta Dan janyo stool ta ajiye ta koma ta dauko mishi juice exotic Mai sanyi na kwakwa da abarba.
Ke ce kikayi?
Ya kalleta lokacin da yayi lomar farko...... Mommy ce.
Yayi dadi amma gobe komeye za'ayi kiyi mun kinji ko?
Ta galla mishi harara kawaiyayi murmushi Ina dai Shan harara Ni Anwar.
In tambayeki???
Ya tsareta da ido.
Um,
Tsakanin ki da Allah kinji dadin zuwa na?
Tayi Yar dariya kawai..... Kinji?
Wai ya akayi kasan address din nan gidan?
Yayi murmushi sirri ne.
Ta Dan harareshi ka Sanya mun ido da yawa me yasa ka damu dani haka?
Saboda....... Yayi shiru Yana Yar dariya.
Ta tsareshi da ido, saboda me?
Saboda kawata ce ke my best friend.... Ta buga tsoki.... Ya kyalkyace da dariya. Yana ci gaba da Shan pepper soup din.
Sadeeq ya Mike Bilkisu bude mun kofar can naga exit ce ko?
Eh, amma ya zaka fita zaka biye maganar sa ne?
Yayi murmushi a'a Zan dawo ne shidin banza ya hanani Zama anan?
Ya bisu da kallo kawai Yana Shan lemu.
Tana budewa ta hango iyayen motoci da katti sai gewaye gewaye sukeyi suna mazurai..... Ta dawo da sauri, Wai Kaine kazo da waccen bataliyar?
Ta tsaya gabansa tare da rike kugu, ya daga ido Yana murmushi tsiwar ce ta tashi?
Anwar waye baban ka?...... Ya fesar da lemun bakin sa saboda dariya. Ta tsuke fuska, ya fizgo hijab dinta tayo kansa zata fada yayi saurin mayar da ita gefensa ta zauna..... Innalillahi, Kai Wai wane irin mutum ne?
Idan za 'ayi tambaya Zama akeyi ba tsayuwa ba bakauya.... Nice bakauya ? Eh ya fada Yana hararar ta,
Ka amsani ........ Maganar ta makale ganin ana shigowa da jikkuna set/set..... Ta zaro ido ko yazo neman auren ta ne?????
Ta kalleshi da sauri meye ake shigowa dashi kamar wani lefe?????? Ya kyalkyace da dariya lefe Kuma an fada Miki na Isa Aure ne?
Ta daka mishi tsawa to na menene?
Calm down ya fada a hankali ganin tana neman tayar da hankali...... Na kawo Miki tsaraba.... Tsaraba ta mecece?
Anwar wanene baban ka a Kano? ....Kai Ina son in San waye Kai ayau... Dai dai sun gama ajiye jakunkunan set hudu ta daka musu tsawa ku mayar dasu mota bazamu karbi kayan Nan Haka ba fa.... Sadeeq zaiyi magana ya daga mishi hannu yace jeka kawai Zan Mata bayani...... Anwar ko hakan zai Zama batawar mu ta har abada...... Ki dubi girman Allah ki daina janyo mun tashin hankali ki jira na amsa Miki duk wata tambaya da Kika rasa amsar ta.
Zan amsa Miki wanene baba na a Kano....
Ta tsareshi da ido, ya yi Yar dariya.
Baba na ya rassu Ni maraya ne...... Jikinta yayi mugun sanyi.
Tayi saurin kallon sa kamar zatayi kuka...kayi hakuri Anwar ban San Haka ba.
Ta Fara magana a hankali Allah ya jikansa da rahama yasa mutuwa hutu ce, yayi murmushi cike da Jin dadi Amin ya Rabbi.
Sai kuma me?
Waye Kai? Ko Kuma wanene marikin ka?
Yayi Yar dariya nine *Hamza bushara*..... Ta dago Kai da sauri taja baya ta koma karshen kujera kamar wacce taga abin tsoro....
Ya Kara Yar dariya.... Bilkisu nine *Bushara* Wanda Kika ji ana fada a *Nigeria*.... Na shiga uku ta fada da karfi.... Ke kwantar da hanka... Ta Mike da sauri shima yayi saurin mikewa...... Idan Kika gudu Zan biki har gaban mommy wallahi.... Dan Allah me kake nema wurina Anwar?.... Na shiga uku. Ta Kara fada duk jikinta ya tsinke da rawa...... Zauna in Baki amsa ta Kara ja baya....
Ka kwashi kayan can kabar gidan nan tun kafin ma..... Ke Wai ya akayi ne ya daka Mata tsawa.
..... Ta daga hannuwa kayi hakuri na tuba *Bushara* ta Kara maimaitawa a hankali..... Ya buga tsoki ke bana son gidadanci zo Nan ya Mika hannu..ta ja baya .
Ya fiddo ido...ke me yasa kin cika kawo matsala? Yasha mur kina son in kamaki ko?
A'a, ta fada tana girgiza Kai, oya come and sit down let's sort out where the problem is...... Ta zauna a dosane..... Ya kyalkyace da dariya ji yanda Kika canza lokaci daya..... Kin taba ganina a TV?
Ta ce a'a.
Jarida fa?
Ban gani ba.
To Kuma.
Kika sani ko Ina zolayar ki ne?
Ta Dan kalleshi.
Yayi murmushi eh Mana .
To ko da wasan kakeyi?
Ya kyalkyace da dariya kawai.
Ta bishi da kallo.
Ke Ina Kika San *Bushara*?
Ta harareshi a Nigeria waye bai San wadannan sunayen guda biyu ba *Dan gote da Bushara*?
Ya Kara yin dariya..... Yayi saurin matsawa kusa da ita ya chafki hannuwanta.... Yawwa ya fada Yana murmushi....nine *Bushara* ki kwantar da hankalin ki nothing will happen sai alheri...... Kwallah suka shatato Mata ita kanta Bata San ko na menene ba...... Kuka again?
Ke bakya da wahalar kuka?
Bana son kayan can daddy zai tambayeni na menene Kuma zai mun tambayoyi akanka......Yanzu kukan na menen ciki? Kayan ko kuwa sanin da kikayi nidin waye?
Kai nidai gaskiya ka kyaleni.... In kyaleki? Kin Kara maimaita wannan kalmar Dana fi komai tsana ko?
Ta kalleshi Anwar me yasa ka mun waccen hidimar?
Ya saketa tare da watsa hannuwa kawai I feel to..... Ba yiwuwa ka fada mun me yasa kake wannan over acting din?
Na ce Miki kawai na siyo miki tsaraba ne bana son zuwa hannu biyu..... Ta Mike bazan karba ba ka mayar dasu gida idan ka Isa Aure ka hada wa matarka..... Ya Mike ta nemi kwasawa da gudu ya yi saurin rike hijab dinta.
Wallahi sai ka sakeni haka kawai daga muna course mate zaka jibgo irin wannan hidimar ka kawo mun..... Kawai ne Bilkisu?
Ya fada Yana matsawa kusa da ita.... Kawai ne wallahi, I don't value friends lemme tell you.
Kina son ki kunyata ni ne?
Ta galla mishi harara Ni ma ai kunyata ni zakayi idan daddy ya tambayeni sai kawai ince abokai..... Kice *INA SON KI* ne.... Ta zaro ido jiri ya nemi daukar ta.........✍🏼
*Zainab wowo ce*



*Assalamu alaikum*
Masoyana Ina alfahari daku.

Nazo da wata tsaraba, hausawa na cewa kula da Kaya.......

1. Ina wacce ke fama da karancin ni'ima?
2. Wacce ke fama da budewa tana son jinta a matse da ni'ima sosai?
3. Ko kinsan yawan zubar da ruwa wani lokacin matsala ne? Wacece keson taji ta adai adai?
4. Wacece mijinta baya gamsar da ita?
5. Suwa ke fama da infection?
6. Akwai matan da har yau Basu San dadin Aure ba sam Basu Jin sha'awa ko kin San dalili?
7. Wacece keson ta gyara nonon ta da jikinta yayi luwai luwai?
8. Ina wadanda mijinsu baya gamsuwa dasu?
9. Wacece kullum sai tayi amfani da lubricant saboda karancin ni'ima?
10. Ina wadanda miji ke musu gani gani da hargagi kullum?
Akwai supplement masu kyau na dukkannin matsalolin aure daga zainab wowo, direct order ne muna turawa ko wane gari Amma Kano, Abuja da katsina zaku sameshi free delivery in shaa Allah. Masu bukata su tuntube Ni. Darajar annabi da alqur'ani serious buyer nake bukata Dan girman Allah na rokeku. Ga number ta 08089973394 in shaa Allah.
[3/23, 8:01 AM] +234 706 188 4461: 🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐
2⃣2⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’• *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜.


*Wannan page din na sadaukar dashi ga dukkan masoyan wazai furta*πŸ’žπŸ’—
Shi yasa yau na saki biyu don kuji dadi farincikin ku shine nawa wallahi.😭😭 Ina son ku😍😘πŸ₯° kullum sai nayi kukan dadi.

**************
*ABUJA NIGERIA*

........ Ya tallabo bayanta ta dawo ta tsaya dai dai Amma ta kasa yarda su hada ido, *INA SON KI BILKISU* Yau na *FURTA* Abinda kike son ji..... Ta Kara kasa da Kai jikinta har lokacin bai daina kyarma ba....Wai mafarki takeyi ko kuwa da gaske ne?
Ya rungumota ta sunne Kai jikinsa.... Ya Kara Rada Mata... *ina son ki* tsikar jikinta ta tashi Yarrrr..... Duk wannan haukan da Kika ga inayi sonki nakeyi, Shi yasa na kasa boye kishina gareki...... Nasan kin fahimta Yanzu Kuma kin Sami amsar fadawa su daddy ko?
Ya dago fuskarta....ta koma da sauri.... Ya kyalkyace da dariya yau Kuma jikina ake son Hawa?
Kin wahalar damu da yawa, kina kawo rigima kullum because you want me to say it.... Ni nasan kina Sona I knew it...Kuma ko Baki furta ba nasan kina Sona wallahi....... Ki daga ni na tafi... Ya fada Yana dariya.
Kinga duk laifin ki ne, da kinsan zakiji kunya da hakuri kikayi muka tafi a Haka bakiji komai ba..... Ta zame a hankali ya mayar da ita da sauri, kafin ki gudu Dan Allah gobe kada ki Sanya mun hijab din nan kuma kiyi mun girki da kanki Zan zo around 10:00am kinji ko?
Ki ce b lefe na kawo ba, hasafi ne saboda Ina son ki.... Ta zame yayi saurin rike hannun ta ki jira na Baki kudin dinki Mana ..... Ka barshi nidai... Bakya so?
Ta daga Kai..... Da gaske bakya so?
Um, tace a hankali.
Yayi Yar dariya kudin ke Baki so ko Ni?
Kudin ta fada tana sim sim da Kai.
Yayi murmushi Ni kina Sona Kenan?
Ta yi alamar fizge hannunta.... Ya rike gamm. Kice inji Mana kina Sona?
Ta yi kasa da Kai ji takeyi kamar ta bude kasa ta shige ta huta.. ...ya Kara dariya sosai ohh ni Anwar Ashe akwai ranar da bakin nan zai mutu?
Ai Dana San wannan kalmar ce zata sa in Sami saukin tsiwa da tuni na Gaya Miki saboda na Dade Ina dakonta.......
Idan daddy ya Baki zabin auren mu kice kinfi so ayi kafin mu Gama school....... Lokacin ne ta banka mishi harara da sauri ta kawar da Kai.
Ya Kama dariya ya figi hannunta zo kiyi mun rakiya naga alamar nema kikeyi ki gudu ciki ko?
Ta biyoshi a hankali yasa hannu ya fiddo rafar kudi ya ajiye hannun kujera idan kin shigo ki wuce dasu na dinki ne....na gode. Ta fada a hankali. Tayi murmushi ya ce my pleasure dear.
Ta Dan harareshi ya tuntsure da dariya shin na Riga na *FURTA* ai to boye boye name?.
Suka fito tayi saurin fizge hannunta ya Kama murmushi Yana fadin ke dai Yar kauye ce...... Allah yayi?
Sadeeq ya taresu.
Allah yayi sadeeq yau kwana ta saka ni sai da na *FURTA* Ina son ta...... Sadeeq ya you firgigi ya ce waoooh *Anzo wurin kenan*.... Duk suka bushe da dariya ita ko sai murmushi takeyi kasa kasa...... Munafuki ai duk Kaine tun farko kayi ta wahalar da ita... Shin ai nadai FURTA gobe Zan dawo *Zance* ya bangajeta da kafada ko Bilkisu???
Ta galla mishi harara suka kwashe da dariya.....
Kiyi mun tuwo goben.... Ya shiga mota tana tsaye har suka fice gate din....
Wai da gaske ka furta kana sonta?
Wallahi kuwa, sadeeq rigimar Bilkisu bana iya daukar ta, ta tsareni lallai sai tasan wanene Ni...... Saboda me zaka boye Mata Wai?
Ai na fada.... Amma fadar sai ta tsorata Kuma. Na rasa me take so, Kuma Wai ita ya zata fada a gida wace amsa zata bawa su daddy....na ce kice *Ina son ki* saura kadan tayi penting .....suka bushe da dariya...... Amma ka Mata gatsal! To ya zanyi da ita? Kaga yanda ta nemi ta firgice mun?
Banza finally ka furta dai.
Yayi dariya *Anwar ya furta* naji tsoro yarinyar Ina son ta saboda class wallahi.....gidan sa dake *Minister's hill* suka nufa.
Mommy..... Mommy ta Fara kwada Mata Kira tana Hawa sama.
Tana faman shirya jaka ta shigo dakin, mommy Anwar fa ya kawo Kaya da yawa ..... Wane irin Kaya?
Ina daddy?
Sunje sallah kasa.
Wane irin Kaya ne ya kawo.
Jikunkuna ne set hudu.... Ta kalleta da sauri jakunkuna? Na menene????
Ta sunkuyar da Kai ta sunga Mata kudi Kinga Wai su Kuma nayi dinki...... Duk Akan me?
Ta Kara kasa da Kai, ya ce tsaraba ce ya kawo mun.... Saboda???...... Ta Kara katseta da sauri.
Ya ce Yana Sona ne???
Muje naga kayan, bazaki ce mishi daddyn ki ya hana karbar kaya ba?
Wallahi duk abinda na kokari in sanar dashi bai yarda mommy.
Wohohoho ta fada tare da rabka salati...... Amma kin San daddyn ki zaiyi fada ko?
Mommy Anwar Shi ne *Hamza bushara*..... Mun sani. Ta ce a takaice ta zaro ido Kun sani mommy?
Yes, ta fada tare da wucewa tana fadin jekiyi sallah nasan fada ne yau duk sai mun Sha ni da ke.....
Ta falon ya shigo Yana ganin kayan ya kwala ma Bilkisu Kira.
Ta fito da gudu gudu.....

Wadannan kayan fa? Ta sunkuyar da Kai, Anwar ne ya kawo su daddy.
Na menene?
Ya ce tsaraba ce kada yazo hannu biyu....
Saboda me?
Tayi jimmmmm kafin ta ce *Wai Yana Sona ne* yanayin yanda ta Fadi maganar kamar Yar koyo mommy ta shigo ya kalleta Kinga Kaya?
Hada kudi....
Ya kalli Bilkisu ke kina sonsa?
Tayi shiruuuu kinji mamana kina son sa?
Tayi kasa da Kai kawai.... Yayi murmushi kina son sa kenan.
Ki mayar mishi da su kice bana karbar irin wannan kyautar idan har da gaske yakeyi ya turo iyayensa.... Ta dora hannu saman Kai.... Daddy bayar Dani zakayi haka da wuri ta kurma ihu tana kuka.
Ya yi Yar dariya, to tunda kin Sami Wanda kike so me ake jira..... Nidai kada a turo...ke bama son rashin wayo.
Turowar an fada Miki Yana nufin za'ayi Aure?
Hakan zai nuna idan da gaske yakeyi sai a ajiye magana.
Ta danyi shiru alamar ta gamsu.
Ya wuce Yana girgiza Kai Yana murmushi,
Mommy ta kalleta tana hararar ta, wannan koke koken ba komai zai janyo Miki ba sai raini wurin Miji. Komai ke sai ki bare Baki saboda kina ruwa ruwa.... Mtsew ta ja tsoki.
Wannan rawar Kan da Anwar keyi inba auren ba meye zai kamance ku?.... Mommy..
Yi min shiru, Ina

21 / 30