Author : Zainab Dahiru Wawo Category : Arewa Pen
daya ce Anwar pretend as you don't know. Ka nuna Sam baka sani ba..... Zanyi haka saboda Zan tayar ma Bilkisu da hankali.... Ai anyi shawarar ita a sanar da ita saboda ta kiyaye sharuddan Aure...... Ya dafe Kai tare da runtse ido to ni me yasa basa so na sani?????? ...... Saboda rawar kanka. Sadeeq ya fada Kai tsaye..... Zan basu mamaki sadeeq.... Wallahi Zan nuna masu how true I love 'yarsu........ Alhamdulillah sadeeq ya fada tare da janyo Shi ya rungume Shi..... Anwar wannan ba karamin gata akayi maku ba wallahi hakan da akayi ya faranta zukatan dangin ka..... Ina ka taba ganin anyi Haka? Ka tabbatar gida kamar na su Bilkisu ba za su taba hakan don kwadayi ..... Mtseww please I don't suspect that.
Ya tashi zaune sadeeq an dauran Aure da Bilkisu?????
Ya kara runtse ido yayi baya ya kwanta bisa gado har lokacin bai bude ido ba.... Sadeeq Ina son Bilkisu, wallahi duk abinda nakeyi ina sane am just testing her , Ina jaraba ta ne sadeeq Kuma yarinyar taci jarabawa ta, tana Sona sosai I knew it amma kullum tana kokari ta danne don ta tsira da mutuncin ta Ina son Mata Mai Hali irin nata *she's exactly the wife am praying for*........ Ka Basu mamaki Anwar..... Ya bude ido ya dago da sauri..... *I will* wallahi zasu Sha mamaki *trust me*
...... *How I wish ita ma su Kyaleta bazasu fada Mata ba?*
No, is better su fada Mata Anwar kasan Mata da wauta....... Yes ni Kuma ga kishi.... Duk sukayi dariya... Ya Mike tsaye ya buga wata Kara... Wuuuu *Mrs Bushara* wawwwwww!
Sadeeq ya bishi da dariya.
Ko su Hajiya baza su san na sani ba. Sadeeq Zan ba guys din nan mamaki..... Dan ubanka su daddyn ne guys.... Duk suka kwashe da dariya sadeeq yace *Yaro da kudi*...... Ya Kara sa da *Abokin tafiyar manya* suka tafa.
Ya zuki iska ya hurar *Honestly I can't believe we are now husband and wife*..... Kai zanje na kwanta I'm feeling sleepy. Sadeeq ya fada tare da mikewa..... Sadeeq Ina zamu je hado lefe?
Ya banka mishi harara sai Corona tayi sauki Dan ubanka....... Ya kyalkyace da dariya, Shi Kuma ya fice yaja mishi kofa.
Ya fada bisa gado..... Wai ni nake da rawar Kai, zasu karyata hakan da kansu lallai Basu San waye *Bushara* ba.
Ya dauko waya lemme call her idan sun fada Mata nasan she's awake now, idan Kuma basu fada ba tayi barci....
Taci kuka har ta bani tayi lamoo bisa gado, wayar ta Fara Kara a hankali...... Kamar kada ta dauka sai Kuma ta tuna da nasihar daddy cewar Yanzu duk abinda tayi mishi na rashin Jin dadi Allah zaiyi fushi da ita.
Hello.... Ta fada cikin dusasshiyar muryar da Tasha kuka...... *What are you crying for?*....... Gabanta yayi mummunan faduwa Taya akayi yasan kuka tayi?
Um? Ya Kara fada.
Tayi shiru kwallan suka shatato Mata.
Bilkisu? Ya kirata a hankali.
Gabanta ya Kara faduwa tsoron ta daya Anwar ya San ita matar sa Yanzu tasan kawai *Ta mutu* Yanzu ma ya ta Kare dashi bare yasan matar sa ce....... Bazakiyi magana ba?
Ba komi, ta fada a hankali.
*Is that because you missed me?*
Ta buga tsoki..... Ya kyalkyace da dariya to kukan na meye daddy ya dake ki?
Tayi shiru,
Ki jirani karfe takwas da safe Zan zo inji dalilin.....
Ba sai ka zo ba....
Ta fada kamar zata Kara rushewa da kuka.
Saboda me?
Huh?,
Sai da safe Ina son nayi barci.... Karya kikeyi ba Zaki iya barci ba yau..... Gabanta ya fadi.
Bazan iya barci yau ba?
Eh,
Me yasa?
Saboda na tafi na barki.... Ta buga tsoki ya kyalkyace da dariya.
Kilibabba Allah ya kamaki Ashe kullum nabarki sai kinyi kuka ko?
Wallahi a'a .
To kukan meye kikeyi?
Ba komai.
Na Jin dadi kenan?
Eh. Ta fada cikin tsawa ya Kara dariya..... Ko dai ni nayi laifin?
Ta ce hmmm,
Ya lumshe ido, kiyi hakuri toh.
Tayi shiru....
Kinji?
Um,
Ba um Zaki ce ba toh ake cewa, ko inzo nan mu kwana....... Kamm, ta fada tare da latse wayar..... Ya Kama kyalkyatar dariya Yana mirgina bisa gado, dukkan su babu Wanda ya samu yayi barci, Shi Murna ita zullumi.
Yana gama sallar asubah barci Mai bauyi ya daukeshi, sai Sha biyu ya tashi,
Ita kuwa ta tashi idanu kumbure saboda kuka, karfe Sha daya mommy ta tafi airport, daddy Kuma ya na gida saboda hutun Corona virus.
Karfe biyu ya karaso, Rahina ta shigo Aunty ga Uncle Anwar....... Gabanta ya Fadi.
Daman tayi wanka ta Dan gyara fuskar ta har lokacin ana gane tayi kuka.
Yauma da kananan kaya, ya mayar da facing cap din gefe ya rufe idanun sa da bakin goggle.
Jiki ba kwari ta shigo ya kura Mata ido har ta zauna sai kawai ta bashi tausayi.
Ina kwana...... Wuni dai ko?
Yanzu Kika tashi barci ne?
Yana maganar a dake,
Tayi shiru.
Kin dafa mun abinci?
Ta girgiza Kai,
Saboda me?
Yanzu meye zanci toh?
Tayi shiru,
Ke me Kika ci?
Nan ma tayi shiru.
Jeki kawo mun abinda Zan karya..... Ta Mike sim sim....ya bita da kallo.
Ya zuki iska ya fesar tare da Dan zamewa ya kwantar da bayansa a kujera.
Wayoyi kawai yake amsawa har ta shigo da tray a hannu.....kawo nan bazan hau ba table ba.... Okay Zan Kira anjima kaci gaba da lissafi ka turon brake down...
Ya ajiye wayar Yana Mai saukowa bisa carpet.
Indomie da kwai ta kawo mishi da oat.
Ya hada oat din da kansa ya cika Madara yasa sugar kadan ya tura Mata bowl din wallahi tallahi sai kin shanye duka ni zanci indomie din....... Ya Sha mur,.
Zatayi magana ya harareta Zan hada Miki da indomie din Kuma itama nayi rantsuwa... Ai yamun yawa... Ba abinda ya dameni ko zakiyi amai sai kin shanye.
Yaci gaba da cin indomie din yanayi Yana satar kallonta, tana tsakura, tana tsakura har ta daga bowl din ta kafa Kai.... Da kyar ta shanye.
Ya mike zanje Kano anjima sai next week Zan dawo kinji ko?
Toh,
Ya kalleta kinyi zaune ba rakiya ko cikin ya cika da yawa?... Ya karasa maganar Yana dariya..... Ta banka mishi harara ta mike.
Yana tafiya ta koma daki, ashe hada yunwa ta hanata barci ko mintuna 3 batayi ba barcin yayi awon gaba da ita.
....... Kwana biyu ta warware, kullum basa yin waya sai cikin dare.
Hankalinta ya Fara kwanciya saboda sam da alama bai San an daura masu auren ba.
Hajiya ta kasa boye farin cikin ta Koda yaushe maganar ta Bilkisu.....
Ja'iri ashe mace kabi Shi yasa ka dage Kai anan zakayi karatu.... Ya yi dariya Wai waye ya fada miki mace nabi?
Coincidence ne ya hada mu, amma ni ba ita nabi ba.....yaki nuna ma kowa yasan wainar da ake toyawa.
Har suka je sokoto suka dawo bai nemeta a waya ba. Hakan ya Bata mamaki, ta Fara tunani ko daman rashin sanin inda alakar su ta dosa yasa yake yawan takura Mata Yanzu da ya tabbatar magana taje ga iyaye yasa ya Sami natsuwa?.
Har iyayen nata sai da suka fahimci hakan.
Shi kuwa yayi amfani da wannan Dan hutun ya Fara zirga zirgan nemar Mata transfer zuwa University of Abuja. Ko sadeeq bai fadawa ba yasa aka had a mishi transcript dinta cikin sati biyu ya kammala komai. Hatta kayan ta kafff yasa an balle dakin an kwashe sannan ya gyra kofar ya rufe.
Yana jira akoma ya Mata registration......
Ranar da aka koma, ya aika da komai washe gari yazo da takardun gidan su.
Tana ta shiryen komawa, bai Mata waya zai zo ba sai dai suka ganshi kwatsam, ta gama kulewa fushi sosai takeyi dashi saboda kusan sati daya kenan basuyi waya ba.
Yanayinta kawai ya kalla yasan fushi takeyi.
Yana zaune bisa hannun kujera alamar kamar sauri sauri yakeyi, ta Kara daure fuska..... Wai fushin na menene?
Ta mishi banza.
Yayi Yar dariya, kiyi hakuri abubuwa sun mun yawa ne, bana zaune..... Kuma shine baka da lokacin kirana???
Ya Dan yi murmushi to ke ba sai ki Kira ba?
Ko laifi ne Mata ta Kira mijinta..........dammmm gabanta ya Fadi ta kalleshi da sauri yayi murmushi yes tunda na Aiko gidan ku ai kin Zama matata ko wani ya Isa ya shigo Yanzu neman aurenki?
Ta Dan saki ajiyar zuciya, ya kusa sakin dariya..... Nayi missing dinki sosai Bilkisu, Ina ma ciki amma nasan komai na Dan lokaci ne daga ranar da aka mikon ke nasan komai ya Zama labari....... Gobe Zan koma school. Ta fada a hankali.
Keda waye Zaki koma?
Ban sani ba daddy yace na Fara sanar dakai tukun.
Da banzo yau Kuma fa?
Zan maka text.
Saboda me bakya son kirana?
Tayi shiru,
Ya kamata ki rage kunyar nan fa.
Tunda na Aiko gidan nan Bilkisu duk kin canza kinyi sukuku Anya kina Sona?
Ko baki son kiyi rayuwa Dani?
Baki magana?
Kina damuwa ne akan rabuwa dasu mommy??...... Sai kwallah suka zubo mata sharrrr...... Ya Salam ya tashi yaso gabanta , tunanin ta zai kamata kamar yanda ya Saba sai taga ya zauna gabanta ya harde kafa.......
Kinga ki kwantar da hankalinki wallahi Bilkisu bazakiyi dana sanin Aure na ba, bazan taba Bari ki tozarta ba.
Ke shaida ce, duk kudi na da commitment nawa bai hana na baki time din kanki ba, Ina son kula Shi yasa Nima nake kulawa dake, Ina son ki fiye da dukiya ta, wallahi tallahi ko Yanzu da Kika ga na Dan kaurace Miki I wanted to prove your parents how good I am, and how I truly loved you.
Kin San cewar nasan an daura Mana Aure?........ Ta Mike tsaye ta zaro ido, ya Kara Yar dariya yes I knew it and I promised my self I'll never touch you again, tunda an ce *Ina da rawar Kai*
Ta Kara kallon sa da sauri, ya Kara dariya.
Ya Mika Mata takarda ga Shi gobe gobe Zaki je kiga registration officer na nan University of Abuja akwai abinda Zaki karasa, ta Kara zaro ido.
Me kake nufi?
Ya Dan Sha mur, Ina nufin na mayar da ke can anan Zaki gama.... Kai kuma fa?
Ni Zan karasa a dutsinma..... Wallahi ban yarda ba ta Mike tsaye.... Shima ya Mike, wannan shine umurnin da na Baki Kuma abinda na zartar a matsayina na mijinki....... Akan meye zakayi haka?
Saboda na nunawa kowa cewar ba sha'awar ki nake ba sonki nakeyi saboda Allah......Anwar.... Bilkisu kada Kija maganar nan, kada kuma ki sanar wa iyayen ki cewar nasan an daura Mana Aure kawai Ina son ke ki amince da *Ni Anwar son da nake Miki na Aure ne ba na sha'awa ba*.............πβπΌ
*Zainab wowo maman Abdallah*π
Masu kirana waya kuyi hakuri ku aiko da sako ta whatsappππΌππΌππΌ
[3/24, 8:50 PM] +234 706 188 4461: π€ *WA ZAI FURTA?*π€
2β£5β£
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
ππΌπππ *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*π₯°ππ.
******************
*ABUJA NIGERIA*
.... Na rantse da Allah ban aminta ba, sai dai kaima ka dawo nan mu gama tare .... What do you take me for?
Bilkisu...... Da su mufeeda a school Zan Barka acan bana nan?.... Ya zaro ido...
Ta rike kugu billahil azim tare zamu koma FUDMA.... Abinda nake so ki fahimta..... I'll never understand you, amma ka mayar dani shashasha.... Wallahi bazan aminta ba,
Ya harde hannuwa a kirji ji yakeyi kamar ya kamota ya rungume....
Ta banka mishi harara, yanda kake da kishi nima haka nake dashi, dole ka zaba ko nan ko dutsinma Amma kafa ta kafarka....... Ya kyalkyace da dariya...
Ikon Allah Bilkisu ta dawo..... Ta banka mishi harara, Shi yasa ka daina kula ni ka kaurace mun?
Kana son proving meye?, Wannan ne prove? Ai prove shine gani ga ka ba Ina can kana can ba..... Naji maida wukar yanzu zauna ya kike so madam.....
Ta galla mishi harara kaje ka yo cancelling din komai mu koma FUDMA.... Ya maganar Sanya nikaf???? Wannan ce damuwar ka?
Zan saka...... Ya kura mata ido.... Sai Kuma kunya ta kamata ta sunkuyar da Kai..... Ya yi murmushi yace *Akwai chakwakiya*.......
Tayi shiru..... Watau kina son gani gaki ko?
Ni Zaki kure Bilkisu????
Kome zakace sai dai kace amma wallahi ba school din da zance ba tare da Kai ba, idan Kuma ka dage na rantse da Allah sai dai a warware..... Dal!.. ya buge bakin da yatsa... Mutu ka raba yarinya duk yanda kike so haka zanyi what next?
Ta zumbure baki shikenan....
Yayi murmushi yace *nawaoooo*
Har na siya Miki mota wallahi gata can awaje don bana son wani driver kawai da akwai masu binki a baya da tsaronki Koda yaushe..... Sai ka koma da abinka su Kuma ka canza masu aiki.... Ya tuntsure da dariya.... Anya Baki fini kishi ba????
Ta Dan harareshi cikin kunya.
Ya Kama dariya, Watau bazaki yarda gani ga mufeeda bakya Nan ba ko?
Ta rufe fuska nidai ya Isa,
Ya Kara dariya anya wannan semester din Babu damuwa????
Ba wata damuwa,
Ba Kya Jin tsoron anything can happen bayan nasan ke matata ce Bilkisu?
Ta harareshi ashe baza ka iya ba daddyn mamaki ba...... Yayi murmushi Zan iya Mana.
To Kuma.
Ya bi ta da kallo, ya zuki iska ya fesar tare da sakin ajiyar zuciya.
Gaskiya rigimar ki tafi tawa... Ta dan harareshi, but I'll try my best ya karasa maganar Yana murmushi.
Ta Dan sunkuyar da Kai, ya Mike Amma bazaki koma gobe ba sai next week ki fadawa daddy Zan Aiko a daukeki Zaki hau private jet na from Abuja direct to katsina zamu tare ki a can kinji ko?
Ta daga Kai kawai.
Yana Isa gida ya tarar da sadeeq a basket ball ground, ya chabe ball din .... Malam ya akayi ? Ya rike kugu,
Wai kasan nayi wa yarinyar nan transfer taki yarda?
Ka mayar da ita Ina?
Wallahi nan Abuja , ya danyi dariya, could you imagine kishi ke damunta??.... Sadeeq ya kyalkyace da dariya na fada ma miskilanci ke hana Bilkisu nuna maka so amma wallahi zaka Sha wahalar ta idan ta goge ...Amma fa ta birgeni.
Kai ta birge ko Ni sadeeq kasan dai akwai rigima ko?
Babba ma kuwa suka kyalkyace da dariya tare da tafawa.
Ya wurga mishi ball din suka Fara bugawa cikin nishadi.
Yanzu ya zakayi kenan?
Zan siyi gidan nan Wanda naga angama sabo na darawa ko nawane yayi Masa kudin bala'i Zan biya Mata,sai ta zauna ita da Aisha da Maryam Amma banda khausar don bana son yarinyar... Daddy zai yarda?
Dolen sa ma, Zan Sanya Mata masu gadi sosai Nima na siya Mana gida bayan gidan redio zamu bar hostel...... Sadeeq ya buga tsalle amma ka gama birgeni nawan suka tafa suna dariya...
Na Kira VC na fada mishi ayi meeting wallahi duk lecturer din da ya Kara Kira mun Mata Zan daure Shi..... Sadeeq ya zaro ido ai FUDMA sun gama shiga uku Yanzu...... Suleiman Kuma na mishi text na fada mishi na auri Bilkisu kallonta idan yayi ya gama Jin dadi har abada don zai Kare rayuwar sa a prison..... Anwar kada ka firgita makarantar can.... Yayi dariya kawai.
Da mota zamu koma yanzu?
Ya kyalkyace da dariya Kai mota ce dakuwar ka Wai?
To motoci ba mota ba, Zan fito musu a mutum sak!
Nawaoooo... Sadeeq ya fada.
Bilkisu kuwa, Miskilancin ta da zurfin ciki ya hana ta fada wa mommy abinda ya faru ba.
Haka suka taru sukayi Mata nasiha cikin hikima na duk darasin maganar bai wuce ta kiyaye tarayya da shi Kuma ta kula.
*******************
*Federal University dutsinma*
Aisha da Maryam abun ya daure musu Kai, gidan tsoro ma yake Basu, har basa son fita saboda kattin da gewaye da gidan, komai an saka gida abinda ke gida ga masu aikin abinci da gyaran gida.....
Da yake sun rigata komawa da kwana biyu shine yakai su ya masu bayanin anan zasu zauna tare da Bilkisu ranar duk da suka gayyato wata kawa ko namiji wallahi sai yayi maganin su....
Su Kam sunyi tsuru tsuru gashi har yau basuyi waya da Bilkisu ba.
Misalain karfe shidda na marece jirgin ya ajiyeta motoci hudu an musu layi Yana tsaye ya goya hannu a kirji ta Fara saukowa da zumbuleliyar hijab har kasa ya kura Mata ido tun kafin ta karaso ya bude Mata kofa....
Tana shiga ya shiga suka rufe kofa aka fizgesu sai dutsinma.....
Ya kalleta ba gaisuwa hajia?
Ta danyi murmushi,
Kin gaji ko?
Ta ce hmm kawai,
Ya makarantar?
Ta tambayeshi tana kallon fuskar Wayarta,
Lafiya Lau, Amma fa ban shiga ba har yau sai gobe nima Zan Fara zuwa lecture... Ta Dan kalleshi saboda me?
Ya Dan yamutsa fuska haka kawai.... Sai tayi dariya.
Dariyar me kikeyi?
Naga kana mun karairaya kamar mace... Ya kyalkyace da dariya Wai Ina son in birgeki.... Ta dalla mishi harara.... Ya Kara dariya.
Su Aisha sun kagara ki dawo...
Kai meye hadin ka da Aisha???.... Ya zaro ido ya watsa hannuwa ba komai fa....
Sai tayi murmushi,
Anya Bilkisu???, Ya leka fuskar ta.
Ta rufe tana Yar dariya.
Kin iya mota?
Um.
Good, to na ajiye Miki tana nan, zaku zauna keda su Maryam, nima nabar hostel muna bayan gidan redio nida sadeeq, idan daddy ya Miki magana kice ninayi Haka, akwai masu gadi da ma'aikata Amma fa ki sani idan zakiyi mun abinci kada kisa kowa naki nake so kin gane ko?
Ta mishi banza.
Ko bakiji ba?
Karatu nazo ko girki?
Komai ma kinzo yi, kin sani cewa akwai Aure na akanki ko?
Gabanta ya bada ras!
A bakin gate ya fita yabar su suka shiga gidan driver ya fito yabar Mata motar tare da Mika Mata key, ta zaro ido Wai wannan motar ce tawa?
Ya sunya eh Hajia, ta amsa kawai tayi ciki..... Su Aisha suka kwaso da gudu tana ganin su ta fasa ihu itama sukayi ciki suna Murna.........Suka tsareta da tambaya