Hira Da Matattu Complete Hausa Novel By Jamila Umar Tanko.txt

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Hausa Read

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 35.3K words

ji hawaye yana ta sirnano ma ta na tausayin Sharifah.
Aliyu ya shigo ya iske ta na kuka, ya razana a tunaninsa ko mutuwa ma aka yi. Dakyar dai ta iya bashi labarin abinda ya faru tsakaninta da Mama, da labarin da su Nana suka ba ta cewa sun ga Sharifah a wajen lauya. Tabbas Sharifa tana buqatar kulawa, tana bukatar wani da zai tsaya a gefenta ya na karfafa ma ta guiwa ko da baa taimake ta da kudi ba.
Tambayar da Aliyu ya yi ita ce "ina mijinta yake yanzu ko basa tare?"
Samha ta ce "tare da kai fa ta ba mu labari, ba mu ji karshen labarin ba amma kamar da alama basa tare dan tana ta ambaton rashin kirkinsa. Ba ta taba jin dadin zama da shi ba."
Aliyu ya tambaye ta "menene abin yi yanzu?"
Ta ce su Nana sun ce zasu sami dama su zo ta jagorance su zuwa gida Sharifah dan su ba ta hakuri. Ba su saka rana ba dai amma zasu zo.
Ya ce duk ranar da suka zo ya bata izini ta je koda ba ya gari. Samha ta ji dadi ta yi godiya sosai.
Ta shiga tunano irin abincin da Sharifah ta fi so idan zasu je sai ta dafa ma ta ta kai ma ta. Dan ta san ita da yaran za su ji dadi a kalla zasu ga an kula su.

*** *** ***
Bayan wasu kwanaki ne qawayen Samha su ka hadu su dukka suka zo gidan Samha.
Anan aka tayar da magana aka dinga hayani, maryam da Nana dai an basu laifi an ce ba su kyauta ba akan tsoronta da suke ji bayan sun tabbatar ba fatalwa ba ce yanzu.
Samha ta na daga kicin ta na tsomo baki. Ta yi musu girke-girke kala-kala daman ita cikakkiyar chef ce har ma tana da makarantar da take koyar da girki. Ta na son girki kuma ta iya girki, tabbas ta sha karbar kambun yabo idan aka yi gasa ita ke cinyewa. Sunanta ya yadu ya bazu a fadin birnin Kano da ma arewa baki daya.
Ashe da walakin goro a miya shiyasa dangin Aliyu su ka kasa yin nasara wajen tursasa shi akan ya rabu da ita ya auro wata. Ya qi fur ya ce shi sai Samha ita kadai. Allah sarki ya ce haihuwa ta Allah ce, tunda likita ya tabbatar mu su shi da ita dukka lafiyarsu kalau lokaci kawai suke jira. Ga shi kuwa lokaci ya zo, bai yi garaje ba, ya yarda da cewa baa yiwa Allah shishshigi, baa yi maSa tilas. Allahu akbar! Mai yadda Ya so a lokacin da Ya so.
Su Nanah su ka ci su ka yi haniqan har da ma su daukarwa miji da yara a 'yar roba, saboda dadin abincin ba zasu taba iya dafa irinsu ba.
Samha ta saba ganin hakan dan haka baya bata mamaki, dan duk wanda ya ci abincinta sai ya yi santi kuma sai ya so ya kaiwa masoyansa su ma su dandana.
Amma fa ba dukka abincin ta kawo musu ba, ta ware na Sharifah daban ta adana a kicin. Abincin me yawa kuwa kasancewar ta ga su na da yawa, ga yara, ga Bello.
Samha ba ta karbi lambar wayar Sharifah ba duk da ma alamu sun nuna ba ta riqe waya, sai wata karamar waya ce a hannu Hamidah. Amma dai za su yi shahada su je sun san ko ba ta gida yara na gida tunda akwai makaranta islamiyya da boko, ba za ta fita da su ba.
A mota daya su ka dunguma suka tafi wato motar Nana ita ce babba. Su ka isa gidan Sharifah suka iske Bello ya fito zai shiga motar nan da su Nana su ka ga Sharifah a ciki a wajen barista, ashe motar Bello ce.
Ya kalle su ya kawar da kansa gefe, kafin ma su sami waje su gyara tsayuwar motar, ya shige motarsa ya tafi, da alama har yanzu haushinsu yake ji musamman ma Samha.
Su ka fito suka iske get din a rufe, sai su ka cika da fargabar ko babu kowa a gidan. Wadanda har yanzu zuciyoyinsu basu gama yarda da cewa ba gidan fatalwa ba ne, suka ji fargabar kwankwasawa yayin da wasunsu irin su Samha gaba gadi suka hau bugawa.
Sai can da jimawa suka jiyo motsin tafiya, aka zo aka bude. Hamidah ce ta bayyana wannan karon idanuwanta sun yi jajawur, alamar ta sha kuka.
Su Nanah su ka daka tsalle suka yi gefe, Samha ta harare su alamar su daina yin abinda suke yi haka.
Samha ta rungume Hamidah ta na lallashi ta tambaye ta ko lafiya take kuka?
Amsar ita ce "babu komai."
Samha ta ci gaba da lallashinta akan ta fada ma ta abinda yake faruwa. Amma Hamidah ta dage ta ce ita babu komai.
Samha ba ta yi mamakin kukan da Hamidah ke yi ba, saboda ta ji labarin shakuwarta da Shariqa dole har yanzu ta yi kukan rabuwarsu.
Samha ta tambaya "Mamarku na cikin gida?"
Hamidah ta gyada kai ta ce "Eh ta na sama."
Samha ta kama hannun Hamidah su ka yi gaba tana ci gaba da ba ta hakuri da yi ma ta nasiha akan ta yi hakuri, kowanne mai rai mamaci ne. Mu dukka anan wataran za mu mutu mu tarar da su acan."
Su Nana su na ta jan kafa su na tafe su na sanda yayin da zuciyoyinsu ke karkarwa. Har yanzu gidan tsoro yake basu duk da dai an gyara, ba irin yadda su ka gan shi rannan ba, ada dai ga duhun bishiya, ga na datti da kura amma yanzu fes da shi.
Su ka hau sama cikin wani katafaren falo mai girman gaske kuma ya tsaru kamar a turai. Sai mamaki ya rufe su, ai basu taba zaton har da gyararren waje a gidan nan ba, sun zaci kwango ne kawai.
Kowacce ta sami kujera ta zauna yayin da suka bawa Hamidah fulasan abincin da suka kawo mu su, ta karba gami da godiya sannan ta dora akan dining table, ta koma gefe ta tsaya.
Sun tambaye ta ya fi a kirga shin ina Mamarta take dan ba su ganta a falo ba, sai Hamidah ta yi shiru ba ta ba su amsa ba.
Ba su ankara ba muryar Sharifah su ka jiyo a daya daga cikin dakunan.
Ta na magana cikin fushi da daga murya ta na cewa "ke 'yar uwata Shariqah ki koma ki kwanta. Na rantse da Ubangijin da Ya busa min numfashi kuma Ya raya ni nake yawo a doron kasa, kuma Shine Ubangijin da Ya dauke miki numfashi kina kwance a karkashin kasa, ba zan bari 'ya'yanki su wulaqanta ba. Ki koma ki kwanta, ki koma ki kwanta na ce , ki je ki huta abinki. Wannan yaqin na rayayyu ne ba na Matattu ba ne."
Daga Samha har kawayenta su ka daka tsalle suka miqe tsaye, yayin da su ka bazama neman kofar da za ta sada su zuwa waje. Aka hau damben bude qofar da ta qi buduwa sai da kyar.
Su ka falfala da gudu kai ka ce gudun famfalaqi suke yi, ba su tsaya a ko ina ba sai da suka gansu a farfajiyar kofar gida a bakin motarsu.
Huci su ke musamman Nanah 'yar lukata. Ta na ta huci ta zaro mukullin motar daga cikin jakarta ta ce sai dai wata ta karba ta tuqa.
Ta ci gaba da cewa "Samha ai na fada miki Sharifah ba cikakkiyar mutum ba ce, kika nece kika ce kin tabbatar mutum ce, ai gashi nan zaa kashe mu."
Samha ta na ta nishi ta dafe kirji ta ce " Sharifah daman ta fada min, bayan ta yi rantsuwa da Ubangijin da ya halicce ta Ya halicci Shariqah ta ce tana magana da Shariqah fuska da fuska kamar yadda take magana da ni. Ta sake yin rantsuwa cewa Mamaci ya na sanin abinda yake faruwa a duniya kafin mu bil'adama mu sani. Ta ce idan malaman garin nan ko na duniya kaf zasu taru akanta su karyata ta ita fa ta fada ba za ta janye ba, cewa mamaci ya san abinda yake faruwa a duniya saboda ita ganau ce akan Sharqah ba labari aka ba ta ba."
Maryam ta zabura ta dafe kirji ta ce "wato dai yanzu Shariqah na cikin dakin da Sharifah take magana, tare suke hira kenan? Ban taba ji ana HIRA DA MATATTU ba sai a yau. Mun shiga uku, innalilahi wa inna ilaihi rajuun.Wannan wacce irin Sharifah ce mu ka kwasowa kanmu?"
Hamidah ce ta bayyana a bayansu har yanzu idanuwanta na cike da hawaye sun yi jajajur abin tsoro. Sai su ka razana su dukka, har wasu sun ruga da gudu baya mota sun sami mafaka.
Hamidah ta sharce hawaye cikin sanyin murya ta ce "Mamana ta ce ku hawo sama, ta fito falo yanzu, ta na jiranku."
Aka hau kalllon-kallo a junansu.
Nanah ta yi karfin hali daga nesa ta ce "wacce Mamar ta ki daga ciki Sharifah ko Shariqah?"
Maryam ta nisa ta ce "tab! ai ni kam sai dai a kai gawata cikin gidan nan kuma."
Samha ta yi sauri ta katse su dan ba ta so su sake ganewa har yanzu a fatalwa aka dauke su.
Ta ce " 'ya ta Hamidah ki fadawa Mamarki wani emergency kira aka yi mana zuwa asibiti. Ki ce ma ta za mu dawo a cikin satin nan in sha Allah. Ga abinci nan na dafa mu ku. Ku ci ke da kanananki. Su na ina ne ban gansu ba?"
Hamida ta sharce hawaye ta ce " ba sa nan an sace su."
Samha ta zabura ta dafe kirji ta ce "an sace su kamar yaya?"
Muryar Bello su ka ji a bayansu ya dakawa Hamidah tsawa ya ce "ke Hamidah! shiga gida kuma ki saka sakata kada in kara ganin kafarki a waje."
Jikinta na rawa ta shiga gida. Su ka juya su na kallonsa, ya na zaune a cikin motarsa yayin da ya wurgo musu wata uwar harara. Nan da nan kowacce ta hau laluben kofar shiga mota.
Samha ce ke tuqawa dan Nana ta sha aradu ba za ta iya tuqi ba. Aka yi shiru babu wacce ta ke magana sai zulumi da tunani. Abin ya fi bawa Samha mamaki dan ada ta yarda Sharifah mutum ce dari bisa dari amma ta yaya take iya yin HIRA DA MATATTU?
Su daman su Nana basu gama yarda Sharifah mutum ba ce dan haka ba su yi mamaki da yawa da ta fito a wata sabuwar sigar ba.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun kowacce ke kira. Samha tuqi take kamar za su tashi sama saboda zuciyarta tafasa take ta yi kawai, wannan labari ba za ta iya fadawa Mama ko Aliyu ba dan za ta iya saka babban kokonto a ransu bayan sun cire zargi a baya.
Nanah ta yi ajiyar zuciya ta ce "Samha yanzu duk nacinki dai za ki rabu da Sharifah ko kuwa har yanzu za ki sake bata wata damar kuma? Ni dai na gama, na sallama ta, na hakura da kawancen nan, kawaye har sun yi min yawa dan na rasa ta ba komai, ni dai na yafe."
Maryam ta zabura ta ce "ai ko ita kadai ce kawata a duniya na yafe ma ta wallahi, itama ta yafe min mu yi sallama."
Rukayya ta yi ajiyar zuciya ta ce " daman ni da Sharifah ba shiri mu ke yi ba tun a jami'a, dan ta ga tana da kokari a jami'a ina cewa ta koya min karatu sai ta dinga yi min wani gani-gani. Daman can ma jinina da ita bai hadu ba, a dalilinku ne ma mu ke gaisawa."
Halima ta girgiza kai ta ce "kai Rukayya ko a bayan idon mutum ne ka fadi gaskiya mana. Babu wanda zai yiwa Sharifa shaidar baqin hali wallahi, ga kyauta ba ta da mugunta. Kawai dai yanzu ta zama abar a gudu dan ba ta da kammannin mutane sak."
Samha dai ba ta magana har suka isa gida suka fito suka shiga falonta aka zauna, aka yi jugum kamar gidan makoki.
Samha ta zabura ta jawo wayarta ta kira Fanna ta saka ta a hand's free.Fanna na dauka ko gaisawa ba su ba.
A gigice Samha ta ce "Fanna! dan girman Allah me kika sani akan matsalar da ke damun Sharifah. Ba ta fada miki wasu daga cikin matsalolinta ba?"
Fanna ta yi dariya ta ce "ai kun yarda Sharifah fatalwa ce ta mutu ta dawo ko? Toh a je a hakan. Ban sani ba ko dan ni ma mun samu matsala iri daya da ita ne shiyasa ba na jin tsoronta. Dan nima na yi ciwo na mutu fa, mata da maza sun cika gida an fasa kukan mutuwata. Har an yi min wankan gawa, an saka min likkafani, maza sun kinkimi gawa za su fita da ni waje, zaa yi min salla a kai ni kabarina sai na farfado."
Samha da kawayenta su ka daka tsalle har da Rukayya da take sallah suka fafara da gudu, suka yi waje. Anan Samha ta bar wayar a yashe, su na jiyo dariyar Fanna, ta na ta dariya babu kakkautawa, irin ta muguntar nan. Wannan karon yaren KANURI ta juye harshe take yi. Ta na ambaton sunanta da na Sharifah da na Shariqah.
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Me yake shirin faruwa kenan? Fanna ma fatalwa ce ashe shiyasa bata tsoron Sharifah, an ce ta zo ta raka mu gidan ta ki zuwa." Nana ce take magana har da hawaye.
Su na ta kai kawo a farfajiyar gidan an rasa wacce ta iya shiga cikin falon. Su mayafansu ma suke so su dauko su tafi gidajensu. Kowacce na tunanin in da za ta kaura ta kwana ko mutanen da zata biya ta dauko a cikin danginsu su taya su kwana.
Samha ta fi su dimaucewa ba ta so ta dawo gidan jiya na firgici da susucewa, kuma da alama dai sai ta dawo saboda duk yadda ta kai ga yiwa Sharifah kyakykywan zato abin ya ci tura.
Da kyar suka samu suka yi jarumta suka shiga falon, ga waya nan a yashe a kasa. Da Samha ta duba 9 missed calls Fanna da 3missed calls din wata lamba wacce ta yi ma ta kama da ta Sharifah wacce ta taba kiranta da ita, ta gani.
Samha ta sha aradu ba za ta amsa kiransu ba, ta ma kashe wayar gaba daya.
Su Rukayya da aka yi sallah raka biyu baa idar ba aka runtuma da gudu ta ce za ta rama sallar a gida. Wasu ma sun manta take way din da suka yiwa miji anan saboda gigita, kowacce ta suri jaka da mayafi jiki na karkarwa ta fita. Daman dukkansu da motocinsu suka zo dan haka kowacce ta shiga ta ja ta tafi tana addu'a.
Aka bar Samha ita kadai a gida tana muzurai, da sauki ma tunda Aliyu yana gari zai dawo komai dare, amma ta tabbatar zai neme ta a waya kafin ya iso, ga shi kuma ta kashe wayar.
Ta hau kan abin sallah ta na lazumi amma fa dukka motsin da ta ji sai ta zabura ta waiwaya.
Aliyu bai dawo gida da wuri ba sai bayan qarfe goma na dare ta wuce. Lokacin Samha ta gama zabura-zaburenta har ya zame ma ta jiki.
Wani irin tsoro mai tsanani ne ke damunta. Amma ta kasa bawa Aliyu amsa a dukkannin tambayoyin da yake jero ma ta. Musamman akan dalilin da ya sa ta kashe wayarta.
Amsar da ta bashi ba ta gamsar da shi ba na cewa babu caji. Sai ya kalli fitilar lantarki a kunne, ya jiyo ya

3 / 12