Hira Da Matattu Complete Hausa Novel By Jamila Umar Tanko.txt

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Hausa Read

Chapter   2 / 12

3K to 6K   out of 35.3K words

yi su tsoma bakinsu?
Wataran ledar pure water da za ta siya su sha ta gagare ta, bata da shi komai bai wadace taba.
Idan ma asiri ya yi ya rufe mana baki toh asirinsa ya ci dan babu wanda ya iya yi masa magana.
Ta yi hakurin jiran kudin hayar gidanta na gado dan ta gyara kujerunta amma da kudin suka zo sai ya karbe. Ya ce shi zai samo mai gyaran. Ta san halinsa ba zai taba bari maza su shigo su kwashi kujerun ba, har gara ta lallabashi shi din ya gyara sai ta bashi kudin.
Mutumin nan ya karbe dukka kuma ya qi kawo masu gyaran. Mafarin da ta kamu da ciwon zuciya kenan."
[2/28, 5:50 PM] Jamila Umar Tanko: 2
Ban san ma ta je asibiti an ce tana da ciwon zuciya ba, sai daga baya take fada min a waya. Dan a lokacin ba na zama a Kano, ina zama a Rivers ni da mijina.
A lokacin Hamidah ta dawo wajena tunda babu inda za ta zauna kasancewar Mamarmu ta rasu.
Na ji hankalina ya tashi matuqa na shiga damuwa ba 'yar kadan ba gami da tunanin me ya jawo ma ta kamuwa da ciwon zuciya da kananan shekarunta? Amma ban yi mamaki ba domin kowa ya dube ta ya san bata jin dadin gidan mijin..Sai a lokacin ne Hamidah ta ke fada min wasu daga cikin matsalolin da Shariqah take ciki. Da irin cin kashin da mijin da kishiya da 'yayan miji ke yi ma ta. Su yi ma ta rashin kunya kuma su daki 'ya'yanta."
Sharifah ta juya ta dubi Hamidah wacce ke sharbar kuka ta ce " ki tashi ki shiga daki tunda ke zuciyarki ba ta iya jurewa idan ana labarin Shariqah."
Hamidah ta ja kannenta suka shiga daki, masu wayon dai jikinsu ya yi sanyi sun ji an ambaci mahaifiyarsu, yayin da kananan suke wasansu basu kawo a ka ba ma. Allah sarki, Allah ba Ya barin wani dan wani ya ji dadi.

*** *** ***
Maman Samha ce take ta kiransu a waya hankalinta a tashe yake, ta kira lambobi kowannensu bai amsa ba. Ta shiga gagarumar damuwa dsn ta na zaton fatalwar ce ta tafi da su.
Sai yanzu wayar Samha ta shiga girgiza, ta dauko da sauri ta duba taga 7 missed calls din Mama.
Ta dubi Anas da Aliyu a gigice ta ce "Mama ce fa take ta kira ashe. Waye ya ce ma ta mun fita ne?"
Anas ya tabbatar ma ta da cewa shine ya fadawa Samira, ko da ta Allah kan kasance aksnsu asan inda suka tafi . Kowannesu ya zaro wayarsa daga aljihu ya duba ashe ta kikkira su babu adadi.
Anas ne ya zabura ya tashi da sauri ya ce "bari in sauka kasa in kira ta."
Ya na sauka ya kira Mama ya fara yi ma ta bayani.
Sharifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " dole hankalin Mama fa ya tashi, kun zo gidan fatalwoyi ta ji shiru, ku ce ina gaishe ta kuma zan kawo ma ta ziyara."
Sai su dukka suka kwashe da dariya har da Sharifah. Yayin da Samha da Aliyu kowannensu nauyinta ya kama su.
Anas dai ya na ta faman yiwa Mama bayanin cewar ga su ga Sharifah da iyalanta mutane ne ba fatalwa ba, ta fayyace musu komai ashe duk rashin fahimta ne ya sa ake yi ma ta kallon fatalwa.
Mama ta ji bayanansa banbarakwai zuciyarta ba ta yarda ba.
Ta hau shi da fada ta ce "babu irin sigar da shu'umar yarainyar nan bata iya biyowa ba, dan ta yaudare ku, ta halakar da ku. In ga fatalwa da idanuwana har sau biyu. Daya da yamma a gidana daya a asibiti da tsakar dare a sigar gurguwa yanzu ka yi min musu ka ce ta gyaru ta dawo mutum. Ka fadawa Samha da Aliyu ku gaggauta barin gidan nan ko in yi muku baki."
Anas ya zabura ya ce "Ah Mama me ya yi zafi haka? Allah Ya baki hakuri bari in kira su mu taho. Menene abin yi mana baki kuma? Tunda ba ki fahimta ba shi kenan ai."
Anas ya ji nauyin yadda zai shiga ya fada musu wannan sako na Mama a gaban Sharifah, ga labari ya kwaranyo dadi.
Anan ya tsaya ya tuttura musu text massages ta waya ya ce lallai-lallai su taso su tafi, ran Mama ya baci ta ce su taso."
Kowannensu ya karanta sai suka hada ido su ka yi shiru, can da aka jima kadan sai Anas ya shigo ya sami waje ya zauna.
Sharifah ta duba agogo ta ce "ya kamata ku tafi Mama na kira nima.kuma ina da ganawa da zan yi da Matar gwamna akan wasu harkoki. In sha Allah za mu hadu wataran ma karasa labarin."
Daga dukkan alamu ta fahimci abinda Mama ta ce da sakonni da Anas ya turo mu su a waya.
Sharifah ta raka su har kofar gida bakin get inda suka ajiye motarsu suka shiga su ka tafi.
Kowannensu zuciyarsu cika da mamaki su na ganinsu kamar a mafarki, ga su tare da Sharifah da ake gudun famfalaqi idan an ganta, yau gata ga su har ta yi musu rakiya.
Tabbas su na cike da mamaki gami da samun nutsuwa da kwanciyar hankali da Allah Ya sa suka gane ba fatalwa ba ce, sannan kuma dan cikin Samha mutum ne.
Gidan Mama aka wuce kai tsaye aka same ta a farfajiyar get ta na ta kai kawo ta kasa zama a waje daya dan fargaba.
Ta na ganinsu sai ta ji hankalinta ya kwanta bayan sun gaishe ta, aka dunguma zuwa cikin gida. Bayani suka yi mata tsaf akan tabbacin Sharifah mutum ce ga dalilan abubuwan da suka faru har ake zaton ba mutum ba ce.
Wasu dalilan Mama ta aminta wasu ne basu kwanta ma ta ba, ita dai koma menene ayi baya-baya da Sharifah kawai.
Samha da Aliyu suka sauke Anas a gidansa, kamar yadda suka dauko shi sannan suka wuce gidansu suma. Samha na shiga gida ta bugawa kawayenta su Nana Ahmad waya ta basu labarin Sharifah cewa mutum ce ba fatalwa ba ce.
Ta fada musu dalilan da ya jawo suke tunanin ba mutum ba ce. Su ka tambaye ta ko ta bata labarin abubuwan da suka faru da rayuwarta ya jawo har kamanninta suka canja kuma menene maqasudin shariar ta a kotu?
Samha ta tabbatar musu Sharifah ta shirya bata labarin rayuwarta bayan rabuwarsu sai kuma Mama ta kira su ta tubure ta ce su bar gidan. Amma za ta samu ta lallaba Mama ta bar ta su sake haduwa da Sharifah don jin ci gaban labarin. Sai dai ba ta sani ba ko sirri ne tsakaninta da ita, ko ita kadai ta fadawa ko kuma zata so kowa ya ji. Idan sirri ne toh ba za ta fada musu ba amma idan Sharifah ta amince kowa ya ji toh za ta sanar musu.
Su Nana suka nemi da ta samo musu lokaci su hadu su dukka su je gidan Sharifah su ba ta hakuri akan gudun ta da suka yi, a lokacin da ta kawo musu ziyara gidajensu. Samha ta tabbatar musu cewa zata fada mata.
Aliyu ya kula da matarsa ta dawo yadda take ada, ga hira da girken-girken da aka saba yi masa ana yi yanzu, bayan kwalliya da kalaman soyayya wanda dukka ya rasa su a baya.
Sai ya ji dadi sosai kuma sai a lokacin ya sanarwa da 'yan gidansu labarin bayyanar cikin Samha. Dan duk tsawon lokacin nan bai fadawa kowa ba dan ana tunanin fatalwa ce ta yi ajiya. Amma yanzu komai yayi daidai dan haka ya daki kirji ya fada.


*** *** ***
Sharifah ce ke tukawa, ta tsaya sannan ta fito daga cikin wata tsaleliyar motar. Daidai lokacin Nana Ahmad da Maryam Alqali su ma sun fito daga cikin motar Nana. Sai kawai aka yi kicibus da su da Sharifah. Ko ba su fada ba ta gane sun razana.
Maryam Alqali da yake 'yar karama ce sai ta labe a bayan Nana Ahmad ita ce barkekiya, Nana ta hau muzurai ita ba abin ta taka da gudu ba dan lokaci ya kure, su na daf da juna. Duk da an fada musu yanzu an tabbatar Sharifah mutum ce amma basu gama yarda ba.
Sharifah ta dube su sai ta yi murmushi ta ce " Su Nana manyan mata."
Ta wuce ta bar su anan a jikin mota su na makerketa. Nana ta fusata ta figo Maryam daga bayanta inda ta labe.
Ta ce " munafukar Allah sai ki labe a bayana saboda ke 'yar karama ce, ni kadai ake kullata gashi nan ta ga baqina har da wani habaici take yi min. Muddin ka ga Fatalwa tana habaici akwai magana kenan nan gaba. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Shikenan na ga ta kaina."
Maryam ta yi dariya ta ce "ance ba fatalwa ba ce ba fa mutum ce an tabbatar da hakan."
Haushi ya sake rufe Nana ta ce " ai kin tabbatar da mutum din ce amma kika gudu kika buya a bayana. Ni da yake barkekiya ce babu in da zan labe ni ake gani ga shi nan ta kullace ni."
Su ka hau kan bene ofishin lauyoyi, Nana ta zo wajen babban yayanta Bar. Inuwa Ahmad ta rako Maryam zasu tattauna akan wani case da Maryam Alqali take so ta shigar.
Anan aka sake yin arangama da Sharifah tana zaune a reception itama tana jiran layi ya zo kanta za ta ga lauyanta Bar.Inuwa Ahmad yayan Nana Ahmad ba tare da kowannensu ya sani ba. Ashe waje daya su ka zo an sake cakuduwa.
Nan ma suka yi turus suka ji kamar su koma amma ba hali saboda Sharifah ta tsare su da idanuwan nan na ta masha Allah manya-manya. Ga kujerun da za su iya zama dole sai a kusa da Sharifah ne. Da alama yana ganawa da wasu mutane a cikin ofishin, dan haka dole su jira.
Kallon da Sharifah take yi mu su ya wuce na mutane dan ba ta ko qiftawa. Sun kasa gane dalilin wannan tsare su da idanuwan da ta ke yi.
Maryam ta sake daka tsalle ta koma ta maqale a bayan Nana, dan tafi ta tsawo da qiba da fadi, Idan ta labe a bayanta baa hango ta ko kadan, takaici ya kara kama Nana. Ta shiga zulumin shin ta je su gaisa da Sharifah ko itama ta share ta su kalli juma kawai.
Su na tsaye basu zauna ba duk da tayin da sakataren yake ta yi musu akan su zo su zauna amma suka ki zama. Su sun san dalilin da ya hana su zama, tsoron Sharifah ne.
Ana cikin wannan hali ne sai mutanen cikin ofishin suka fito, Sharifah ta tashi ta shiga sannan su Nana suka samu damar zama. Nana da Maryam sai fada ake yi saboda labewar da take yi a bayanta, Nana ta ce ta daina yi ma ta haka. Maryam ta sha aradu muddin ta ga abin buya wallahi sai ta buya a bayanta kuwa.
Sharifah ta dade a cikin ofishin Barista, su na ta tattaunawa da shi da alama case dinta babba ne. Ta fi awa guda sannan ta fito, har Nana ta shiga fargabar ko dai Sharifah ta bace tare da yayanta, ta ji kamar ta je ta leqa ta gani.
[3/1, 12:30 PM] Jamila Umar Tanko: 3
Sharifah ta fito daga ofis bayan ta gama, ta same su a zaune, ta kalle su suka kalle ta sannan ta fita. Su Nana ba su ji dadin wannan abinda ya faru ba, ya kamata ace sun yi ma ta magana duk da itama ba ta yi mu su magana ba ai amma tana da dalili tunda sun dauke ta fatalwa zata ji tsoron ta yi mu su magana don kada su baje da gudu. Sai dai sun rasa abinda za su zaba shin ita ce ko fatalwa ce?
Su ka shiga ofishin Barista da sauri bayan sun yi ma sa sallama, ko gaisawa basu yi ba Nana ta shiga jero masa tambayoyi.
" Yaya ka san wannan matar ashe, wacce ta fita yanzu?"
Ya ce "kwarai kuwa mun dade tare nine lauyanta duk da sai daga baya ta dawo wajena bayan ta gama shan wahala da wasu lauyoyin."
Nana da Maryam su ka hada ido sannan suka sami waje suka zauna. Nanah ta sake cewa "Yaya ka ce kun dade tare ko?"
Ya harare ta ya ce " ina ruwanki da mutanen da su ke aiki tare da ni ne? Menene matsalarki? Kin santa ne?"
Nanah ta gyara zama ta ce "akan me ake yin shari'a da ita? Ita ta kai kara ko ita aka kai kara?"
Wannan karon sai ya qi ba ta amsa, ransa ya baci har sai da fuskarsa ta nuna.
Ya ce "ku fadi abinda yake tafe da ku kawai,babu ruwanki da case din wasu."
Maryam ta gaishe shi sannan ta fara bayani. Shi kuma ya na sauraronta.
Su na fitowa Samha suka kira a waya, su ka shaida ma ta sun hadu da Sharifah a ofishin lauya amma sun kasa yi ma ta magana kuma har ta gane su na jin tsorona har yanzu.
Samha ta nuna bata ji dadi ba, basu kyauta ba. Sharifah a halin yanzu soyayya take bukata da kulawa, saboda ta rasa kusan kowa na ta, ta rasa komai.
Duk da ba ta kammala ba ta labarinta ba amma alamu sun nuna haka, kowa ya guje ta saboda an ganta da wahalar yara. Game da shari'ar ce ma baa san ko da wa suke yi ba. Shin Shariqah take nemowa hakkinta ne bayan ta rasu ko wani zalumci aka yi ma ta daban?
Nanah ta na dorawa Maryam laifi, Maryam na dorawa Nanah laifin cewa ita ce ta fara razana. Su ka yiwa Samha alqawari zasu sami lokaci su zo gidanta sai ta jagorance su zuwa gidan Sharifah su ba ta hakuri.

*** ***. ***
Samha na zaune sai ta ga kiran wayar Mamarta ya shigo wayarta, bayan ta amsa sun gaisa kamar yadda su ka saba.
Kwatsam sai Mama ta ce " Samha! Yanzu na ji wa'azi a radio yadda kika san da mu ake, game da Sharifah. Malam ya ce babu fatalwa a duniya, babu wanda ya mutu ya taba dawowa duniya. Mun yiwa yarinyar nan mummunan zato."
Samha ta ji dadi da jin kalaman da suka fito daga bakin Mama. Alhamdulullah.
Mama ta dora da cewa "idan kin sami lokaci ko ki je gidanta ko ta zo gidanki ki saurare ta ki ji meye matsalarta in sha Allah za mu taimaka ma ta idan bai fi karfinmu ba. Mahaifiyarsu mutuniyar kirki ce bana manta alkhairan da su ka yi mana a lokacin aurenki. Lokacin da komai ya cabe min, ba mu da kudi su ne masu kudi babu abinda ba su dafa sun kawo gidan nan ba kowa ya ci ya sha ya koshi a taron biki. Bayan haka kuma kayan dakinkin ma su suka siya mana abubuwa da yawa."
Samha ta gyada kai ta ce "kwarai kuwa Mama ban taba manta alkhairan bayin Allah nan ba. Mamarsu da su kansu, wallahi Mama ban taba mantawa da yiwa iyayen Sharifa addu'a ba har lokacin da ba ma tare, mun yi zumunci a baya sosai dan ba zan manta lokacin da Babansu yake zuwa mata visiting a sakandire ba, dukka kawayenta sai ya raba mana kudi da littattafai. In sha Allah zan sami lokaci in je gidanta, dan na san a yanzu dai ba zata zo gidana ba, dan tana da zuciya mun yi mata laifi akan abubuwan da mu ka yi zatonta da su. Ba ta ji dadi ba sam."
Su na kashe waya sai Samha ta

2 / 12