Bafullatanan Ruga Book 1 Aisha Maman Teddy

Author :  Maman Teddy Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 10

1 to 3K   out of 28.7K words

[4/12, 5:38 PM] Hausad paid: Typing✍



*BAFULLATANAN RUGA*


BY MMN TEDDY

*56/57*

*BONUS*


*ALHERI WRITERS ASSO.*


*A.W.A*


_________________________________


Bangaren Mairo ko bayan fitan Layla ne Ammie ta shigo dauke da tray manya guda biyu,tana
dauke daya,dayan kuma wata yar aikin ta tana dauke da dayan. A daga falo ta ajiye mata akan
center table din sannan tayo cikin Bedroom din nata ta taso ta don taci abinci. Haka Mairo tabi
bayan Ammie suka nufi falon wanda da zaman ta Ammie ta soma sarving din ta. Wanda tun
mairo najin dan nauyin ta har ta sake,musamman ganin yanda take jan ta ajiki da fira. Sai da
Ammie ta tabbatar ma ta koshi sannan tabarta suka cigaba da firan su tana bata labarin yaran
gidan da halayyan ko wannan su tana dary. Suna a haka sai ga Layla ta shigo Nan itama aka
duka da ita suna firan su da dry don yawancin firan akan khalifah ne iyayen an rigima. Anan ne
Ammie kece ma Mairo zataje dubai nan da kwana biyu kuma da ita xata tafi,don Ammie so take
ta gogar da Mairo n a yan watanni. Cike da son tafiya n Mairo ta daga ma Ammie kai hadi da
cewa ehhh Ammie xanje. Don gidan gaba daya yafara fice mata arai,tun da taga Muhammad
Adnan. Itako Layla da jin haka tayi saurin cewa" Ammie nima xanje don nasan daga dubai dole
xaki wuce labanun. Kallon ta Ammie tayi sannan tace a'a Layla idan muka tafi dake ya maganar
school?. Murmushi Layla tayi sannan tace Ammie ai yanxu hutu mukeyi.idan hutun ya kare sai
na dawo gida ai. Haka dai Ammie ta amince mata ganin ta matsa da ita za'ayi. Shikuwa Daddy
da baya a gari sai da yakira yace a bai ma Mairo wayan don yaji lafiyan diyar ta tashi. Sosai
yake tambayan ta ya gajiya da kuma bakunta wanda sai da sukafi mintoci a haka don Daddy
irin mutananne masu barkwanci da iya jan yaro da fira,don duk miskilancin Mairo sai da tasaki
ta dinga taya firan tana dry.
A haka Mairo ta kwana biyu a gidan wanda tuni a kwanaki biyu kaman sun shaikara biyu ne,don

shakuwa da sabo sun saba sosai wanda hakan ya kuma kwantar ma Umma da hankali. A
ranan da ko xasu wuce dubai Khalifah har kuka yy don Ammie tace baxata je da shi ba. Daga
ita sai Mairo da Layla zasu tafi. Haka mujaddad wanda shima kanin ne a wurin Muhammad
Adnan yadinga yi masa dry,yana cewa" hohohooo wai mai yasa khalifah kai na mamajo ne?.duk
inda mata suka kana nan,Amma ban taba jin kace zakabi Ya Muhammad Partcout ba. Dry duka
a sanya ciki ko har da Umma,sannan ganin ana cin ma Khalifah nata mutunci yasa ta kamashi
ha'di da yimasu Ammie addu'a r Allah ya sauke su lfy,sannan tayo gida cike da kyewansu. Karfe
11am jirgin su ta daga xuwa dubai.wanda a wannan kasa Mairo taga badala taga yan boko taga
kuma yayan hutu gayu da kudi duka. Tun tana kauyanci har ta daina. Wanda a taron bikin Dan
kawan Ammie kuwa taga yanda ake barin arxiki,kuma tun a nan Ammie tafara sawa ana
gyarata dangane da gyaran jiki da kuma gyran nono don Ammie sawa tayi a kira mata mai
wannan sana'ar ta dabam don ta gyara mata Mairo n ta. Don sunan ana biki ne ita Ammie da
biyu da iso kasan don a canja mata kamannun Mairo da da kayan sabulai da mayuuka dana
gyaran jiki. Satin su biyu a dubai don Ammie saboda yawan xuwa n ta kasanne yasata har
gidaje matake dasu acan,da sukayi sati biyu ne suka daga hadi da nufan kasar labanun. Tun
kan sufara zaman kasan Mairo ta goge fatan jikin ta ya canja yana shirning and Glowing abun
kaiiii sai kun gani. Don sometimes Layla ita da kanta sai ta ringa taba fatan jikin ta tana shafa
wa tana cewa" wow Ammie jikin Maryam taushi ga wani sheki da yakeyi,Ammie wai maiye
sirrin?. Harara Ammie ke wurga mata kan tace" wani sirrin kuma bayan kullum kuna tare inda
wani sirri ai sai kin fini sani.....haka dai zatayi dary tayi ta shafa hannun Mairo kaman wata
mayya,don watarana mana sai Mairo ta kwace hannun ta tace" Layla karki isheni,sannan xata
sa dry ta rabuda ita. A wata biyu da suka yi a kasar abunka ga farar mace kuma tashige cikin
larabawan kasan labanun tuni Mairo tasaje ta hade da su kace itama balarabiyan ce saboda
kyau,tayi kiba ta murje gashi Ammie ta dorata akan magungunan gyaran nono don tuni ruwan
nonon ya kafe,ta hada mata magungunan gyaran nonon wanda saboda tsaban gyara da sukayi
har wani irin tuwo² suke gasu a tsaye bb wanda zai ce wai Mairo ta taba aure bare kuma
rayuwar ruga. Don larabawan kasan su kansu deting din ta sukeyi saboda tsaban kyau. Duk da
haka Ammie bai mata anan ma haka ta cigaba da dorata a akan gayu,don shigar arabiyan
gown yaxama mata jiki gashi masifar kyau suke mata.
Kai a takakkaice Ammie sai da sukayi 5 mount a wannan kasar,sannan suka fara shirin dawowa
gida nijeria don kirar ma Daddy ne ya isheta yasata don dole fara shirin dawowa. Kafin ko
wannan lokacin tuni Mairo taxama wata classical baby,don inba'ace maka batayi karatun
zamani ba,toh sam baxakace ba. Musamman yanxu atlist intana mgn xaka ji tana dan saka
english and arabic don komai na Ammie ta kwashe shi gayun ta kyalekyalen ta da iyayin duka.
Don haka Ammie take ko mgn xatayi sai tasa maka daya daga cikin wannan yarukan biyu.
Shiyasa a yanxu takoma dabi'unta hakk na Ammie.

A ranan da suka sauka a nijeria kuwa Mujaddad da su Ameerah sam basu gane taba,don sun
axa irin wa'innan larabawan ne dasu ke xuwa nijeria musamman shigar ta datake sanye cikin
bakar Abaya mai stones da xanan flowers red. Kafannan nata kuwa suna cikin wasu irin
fitinannun hill. Ta yafa mayafin rigar ha'di da yin rolling dashi. Fuskan ta kuwa simple make up
tayi,wanda ya kuma bayyana kyawunta. Yyn da fuskan ta har fitar da wasu kwantattun gashi
yake daga saman goshinta saboda hutu da kwanciyan hankali. Tsayawa duka sukayi sun kasa

cewa umm bare um'ummm. Sai Ameerah ce ta kalli Ammie tana cewa Ammie wai ina Maryam?.
Dry Ammie tasa yyn da Layla ma ta hau mata dry tana cewa yanxu bakiga Maryam anan ba.
Amma lallai ke yar kauyen Nijeria ce. Tsaki tayi tana cewa nidai Layla ba dake nayi ba,kimga
daga dawowanki xamu fara ko. Cike da zakuwa da son ganin Mairo Khalifah yafara bubbuga
kafa yana kallon Daddy dake tsaye yana murmushi ganin draman da Ameerah da Layla keyi.
Ganin xai sa daru yasa Ammie nuna Mairo da hannu tana cewa tohm duk ya isa ga Maryam dai
period.
Xaro ido duka sukayi don har mujaddad yayi mmkin ganin yanda Mairo ta chanja takoma
kaman ba ita ce BAFULLATANAN RUGAR da suka sani ba. Cike da murna Ameera da khalifah
suka rungume mairo yyn da Mairo itama ta rungume su don sosai tayi missing din su..... A haka
suka nufi motocin da suka taho daukan su wanda da shigarsu securities suka mara masu baya.
A bun da yafaru a airport shi ya maimaita kanshi ,don da suka nufa part din Umma ita kanta
bata gane Mairo ba. Nan ko Duka aka sa dry,wanda Mujaddad ne ya hau cewa" tabdijam
Umma gsky dole aniima inxan tafi hospital dina kixo mije a duba lfyn idon ki. Duk da haka
Umma bata fahimce shi ba balle ta gane diyar tata. Ganin haka yasa Mairo nufo ta ta kamo
hannun ta tana cewa" Umma nice fah. Sai a sannan ta xaro ido waje tana cewa " wai Maryam
kece haka?... Dariya duka suka kuma harda Mairon sannan suka zauna akan royal cushines din
falon ana mai cigaba da firan kasar labanun. Da yanda Mairo ta chanja kaman balarabiyya ta
koma.
Dry Mujaddad yy sannan yace wai har da wannan yar kauyen Ameeran bata gane ta ba.koda
yake bai dace nayi mmki ba,tunda nasan daga kauyen da ta fito. Dry suka kuma nan Umma
tace kai Mujaddad wannan abu haka kanafa damun Amira na. Murmushi yy ha'di da cigaba da
cewa " wai umma kinga yanda ta saki baki tana tambayan wai ina maryam?. To wannan inki
kaga matana ai suma xakiyi saboda kyaunta ba irin ki baka ba. Ae bai kai ga rufe baki ba ta
amshe da cema sa a haka kuma akemun rushing. Zaro ido yy waje yana cewa" a haka duk
wannan bakin naki,inah aeni matana fara ce xan aura iri na ba baka irin ki ba.
Ganin abun nashi na yawa yasa Umma cema sa kai Mujaddad kodai kana neman iri ne?. Kafito
fili ka fada mana sai muyi yar gida. Dry aka sa nan cike dajin nauyin Umma yace wahhh Umma
ni,na auri baka Allah ya kiyaye. Yana fadin haka yana kokarin barin falon.aiko nan Mairo tace
masa ya Mujaddad ai irin wannan hadin tafi ma kyau. Cocacola and fanta kenan. Dry aka kuma
sawa nan Layla tace gsky fah ya Mujaddad haka ne. Ficewa daga falon yy yana dry yyn da
Ameerah ke cewa Allah y kikyaye ta auri fitinannane irin Mujaddad. Haka a wannan yinin ranar
suka kasance cikin farin ciki da walwala. A washe garin dawo wansu ne suka shirya don fita
outing wanda tuni su Ameerah da layla suke jiran ta daga kasa. Tun daga fitowanta wani
sanyayyar kamshin ta ya manaye falon,yyn da a hankali ta hau sakkowa daga stairs din.
Muryan Ammie taji tana cewa" Muhammad Adnan ga Maryam sai yau Allah yy xaku ga juna.
Gaban ta ne yafadi. Amma duk da hakan cike da salon ta ta cigaba da sakkowa daga stairs din
har ta isa tsakiyar falon inda nan idon ta ya sauka ga na Muhammad Adnan dakuma Anisa da
take rike da baby sajida.... Ammie ne ba tare da ta fahimci wani abu game dasu ba tace Anisa
ga fa Maryam. So Anisa take tayi mgn amma kuma bakin ta yagaxa,shikuwa Adnan ganin
komai yake kamar ba gsky ba,wai Mairo n shi ne wannan ko dai mafarkin ta da yabayi ne.
Muryan ta suka tsinkaya tana cewa" Layla wannan itace baby sajida ko?.bude baki Anisa tayi
cike da mmkin yanda Mairo n ta nuna kaman bata taba ganin su a duniya ba,irin wannan shine

d firt time da ta taba ganin su.







Labarin ta kudice gamai son jin cigaba n shi zai turo #200 VIP normal#100 VTU #200 MTN
duka ta wannan Number n 08081202932/09137392680.





Maman teddy
[4/12, 5:38 PM] Hausad paid: Typing✍




*BAFULLATANAN RUGA*



*54/55*



Don haka iyayen Umma ba wasu karfi ne dasu ba,shiyasa ma koda Abba lamido yafito akan
neman Aure n Umma,da'akayi binciken shi akaga usulun shi aka amince mai...ko a lokacin da
umma ta auri Abba lamido yana da Auren Umma Hausi kuma bata taba haihuwa ba,shiyasa ko
da Umma ta haifi Mairo tayi matukar bakin ciki, shiyasa ta shiga ta fita ganin ta dasa ma Abba
lamido kiyayyan Umma dakuma Mairo,wanda da haka Allah yabata iko tasamu wani
gahurtaccen boka wanda kafin aikin nata yaci sao da ta kauce hanya. Don sai da wannan
bokan yasata ta siyo zakara ta murde wuyan ta a haka har ta mutu sannan.
Tun daga wannan lokacin kiyayya mai zafi ta shiga tsakanin Umma da Abba.wanda ana a haka
ya auro umma yadikko don tuni ya jingine Umma da ita da bb duk daya suke a wurin shi. A
haka kullum Umma tana hakuri don ta kwana a wajen rugar su bb adadi.don dik inya tashi
tijaran shi sai ya kado ta wajen bukka yace yagaji da ita tabar masa gida.Amma a haka tana
ana ce saboda tana duba rayuwar diyar ta ta. Duk da haka bai mawa Abba lamido ba don a
wata rana ne yaxo cike da tijara yace Umma ta tattara ta koma garin su ya saketa kar ta kuma
dawo wa inda yake. A ranan ba umma ce kadai tayi ta kuka ba har da Umma yadikko don sosai

suke zaman lfy. Da xata tafi da Mairo ne Abba ya fixgeta yana cewa" ta kara gaba ita kadai
tabar masa gida,Amma banda Mairo. Haka Umma tabar masa rugar wanda rabuwanta da Mairo
sai da yasata ciwo amma a haka tayi hakuri ta dangana. Umma bata kuma shekara 1 a gidan
ba Daddy ya wanda a haka suke zaune lfy da Ammie da kuma yayan ta...don dama tun kan tayi
Auren ta nafari suke tare da Ammie kuma dama shi Muhammad Adnan dan gidan ta ne
dama,shiyasa sa ta dawo gidan su da Aure yazama dan dakin Umman cikakke.
Wannan kenan yan team Mairo.........
[4/12, 5:38 PM] Hausad paid: Typing✍



*BAFULLATANAN RUGA*



*52/53*



Dariya Ameerah tayi ha'di da cewa habawa my Layla sau 1 fa. Tsaki Layla tayi ha'di da jawo
kafan nata tana matsa mata.itako Ameerah sai lumshe ido take tana cewa wow Layla kin iya.
Tsaki Layla tayi ha'di da ture kafanta tana cewa tom ya isheki hajya ta haka nima inada abunyi
ai. Tana fadin haka ta mike ta nufi toilet ta dauro alwala don ta gabatar da sallah, wanda da
fitowa n ta ta kalli Mairo tana cewa Maryam ki tashi ki dauro alwala muyi sallah. Mikewa tayi jiki
bb kwari ta nufi privacy don har a yanxu kallon Abun take kamar Almara ko a mafarki . wai
Muhammad Adnan din da tasani ne yau ta ganshi cikin gidan da Umman ta ke Aure. Itakuwa
Amira mikewa tayi ha'di da nufan bangaren Ammie don ba anan suka saba maruri ba,yyn da ita
kuma Layla ta dauki sallaya ta shimfida ha'di da tayar da sallah. Sai da ta gama kukan ta a toilet
sannan ta dauro Alwala ta fito inda ta riski Layla ta idar da sallan tana a zaune a gyefen gado
tana dan goge fuska wanda da alama fita xatayi. Kallon ta Mairo tayi ha'di da cewa Layla kin
idar da sallahn kenan?. Sai a lokacin da taji muryan ta ne ta lura da fitowan ta, nan tayi mata
murmushi tana cewa" hmm wlh kuwa Kedai bari kawai Maryam,wai so nake na dan fita da Baby
na yau xai xo. Tunda ya Muhammad ya dawo nace masa kar ya kuma xuwa sai yau. Saka hijab
Mairo tayi tana kallon ta sannan sai da taji tayi shiru ne tace saboda mene yasa kkce yabar
xuwa to?. Nisawa Layla tayi ha'di da taba baki tace wai yace ba mu isah tsayawa da samari ba.
Shaikaru na fa 20 to yaushe ne za'a bar ni don Allah. Hmm kedai maganan tsaurin halin yayan
nan namu wlh yawa ne dashi,ai har ke yanxu kin shiga uku kuma,ga saka aikin fitina shiyasa
duk na ganshi ban bari ya ganni nake guduwa. Duk da bacin ran da Mairo ke ciki ganin yanda
Layla ke mata mgnan Adnan rada² kaman mai tsoron kar yajita ko yana kusa yasata kwashewa
da dry. Wanda ganin hakan yasa Layla cema ta hmm lailai ne ma dry kk ko? Wlh xaki fahimci ci
abun da nake fada maki inya dawo yafara ta kanki,don shi fitinan shi har matan shi bai bari ba.
Gyara mata sallayan tayi tana cewa " kiyi sallah n kafin na dawo na cigaba da baki labarin ya
Muhammad don wlh sai kin tsorata da mugun tan shi. Dry Mairo tayi na ciki na ciki wanda a

ranta take cewa " Layla kenan ni xan baki lbarn yayan ki ciki da waje........ Bangaren Mutanen
ruga kuwa tun da Abba lamido yasa aka duba masa inda sa Inda Umma da Mairo take ba'a
samo masa labarin ba yafara ciwo a tsaitsaye wanda tun yana a haka yanxu har ciwon ya
kwantar da shi don sai a yanxu yafara nadamar abun da yy mawa Mairo a rayuwa, itako Umma
yadikko bi ta kansu batayi sai dai tabar shi da Umma Hausi da yakejin balain tssnarta a zuciyan
shi............ *HMM WAI WACCE UMMA NE?* Umma ta kasance a salin yar garin kano wanda ta
taso a cikin sharada....da ita da Daddyn Adnan sun kasance yan uwa ne,don da mahaifiyar
Umma da Hajiya Babba iyayen su guda ne. Don haka auren zuminci ne suka kullah. Duk da
kunsan ba ita ce matanshi Aure n saurayi da budurwa ba,Ammie ce matar shi ta farko..........





Anjima xanyo maku new update yau sau uku zanyo maku bonanza...yan VIP a sha karatu lfy
anjima naji ruwar Comment don wannan pagen na kune.






Maman teddy
[4/12, 5:39 PM] Hausad paid: *BAFULLATAN RUGA* *60/61*
Zaro ido waje duka sukayi yyn da gaban Mairo yafara fadi,don a yanzu taga ma karantan halin
Adnan, tasan rama duk wani wulakanci da tayi masa zai yi. Tana a haka nan take wata zuciyan
tace Mata to sai mene ai salo salon na tajara yanxu ma yasoma gani. Cike da dakewa ta dauki
spoon din tafara kai shinkafan bakin ta, sarai ta fahimci inda Matsalar yake,amma a haka ta
cigaba da ci batare da tanuna wani sauyi akan fuskan ta ba. Su kuwa su Layla tun da suka kai 1
spoon suka kai d second spoon, kawai sai suka fara hawayen sharrrr...sharrr don a tunanin su
wannan shini karshen azaban da Muhammad Adnan yayi masu... Ci gaba da

1 / 10