KANWAR MAZA BOOK 2 COMPLETE BY AYSHACOOL .docx

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   62 / 69

183K to 186K   out of 206.9K words

daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!

*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

"Ya ina ta magana kin yi shiru, me ki ke tunani ne?"

Da sauri ta dawo hayyacinta ta ce "Ba koma" ba dan ya gamsu da babu komai ɗin ba ya ƙyale ta.

Sai dai fa abubuwa suka din ga kai komo a zuciyar rumaisa, har ta rasa wane tunanin ma za ta yi.

Kallon Adam take tana nazari, da jin cewa yakamata komai ya zo ƙarshe haka, ta gaya masa iya abubuwan da ta sani, a wuce wurin kawai.

Mai sunan baba sam bai yi ɗokin aikin nan ba, mussman da ya san dolensa ya tafi ya bar Iman, sai dai ya din ga zuwa yana komawa har ta kammala karatun sa.

Daga mama har sauran ƴan uwansa murna suke yi, da samun aikin da yayi, haka iman ma tana ta yi masa murna, amma ta ga shi sam ko a jikinsa.

"Sweetheart, wai ya naga kamar ba ka murna da samun aikin nan ne? Meke faruwa ne?".

Cikin damuwa ya ce "Kewar matata na fara, zan tafi na barki, yaushe muka yi aure? Muna buƙatar samun isasshen lokaci tare"

Cikin nutsuwa ta ce "Haba my faruk, kar mu yi wa Allah butulci mana, na ɗan lokaci ne fa. Dan Allah ka kwantar da hankalinka sai na koma gida, idan ka dawo sai in dawo gida. Shikenan sai Usman ya cigaba da kula da shagonka".

Mai sunan baba ya ce "Ki koma gida, idan na dawo ki dawo saboda bamu da kunya?"

"Tayi dariya ta ce, to ai kamawa ta yi ne, dan Allah ka yi haƙuri, nima zan yi missing ɗin ka sosai da sosai " ta din ga rarrashin sa tare da haɗa masa da kalaman bayar da ƙwarin gwiwa.

Duk yadda ake jiyewa Iman auren mai sunan baba, ya bawa mutane mamaki sosai da sosai, domin ranar da Ruma ta je gidan, ta ɗau wayar Iman tana kallon hotunan biki, ta sha mamakin yadda ya zage yake kwasar soyayya, videos kala². Ita kanta ammi tana hamdala da yi wa Allah godiya, domin kowa ya ga Iman ya san tana cikin kwanciyar hankali.

Mama ta yi wa mai sunan baba nasiha sosai da sosai, a kan riƙe Addu'a, da kuma nasihar ya ji tsoron Allah a kan aikinsa.

Saura kwanaki uku dukkanin su kowa ya tafi garin da aka yi posting ɗin sa, takawa ya dawo gida, ya tarar da gidan cike da yayyen ruma har da Mahmud, suka gaisa ya tafi ɗakinsa.

Ruma ta bishi, ta bashi abincinsa, tare da yi masa ƙorafin rashin kula Mahmud, sai dai bai tanka mata ba, ya nemi wuri ma ya kwanta.

Bikin Nusaiba ma ya fara ƙaratowa, ammi tana ta shiri, wanda ranar yayi dai-dai da saura kwana ɗaya Mahmud ya tafi shi ma.

Sashin Ammi ya shiga, kasancewar ya ɗan kwana biyu bai shiga ba, saboda zuwa lagos da suka yi, Ammi ta ji daɗin ganinsa.

Kansa ya risunar ya ce "Barka da wannan lokaci"

Ammi ta amsa masa da "Barkanka dai, kana lafiya?"

"Alhamdilillah, na ce gobe in Allah ya kaimu ne tafiyarmu zan fara zuwa aiki"

Ammi ta ce "Haka Iman take gaya mini, Ubangiji Allah ya sa a fara a sa'a"

Ya ce "Amin" ya kalli Nusaiba ya ce "Kira mini baba uwani" Nusaiba ta tashi, ta je ta kira baba uwani.

Tana ganinsa ta washe baki za ta hau kirari ya ce "Bana buƙata, kayanki zaki kwaso ki bar gidan nan a yanzu"

Gaba ɗaya suka kalleshi da mamaki, ya ce "Ke kin san me nake nufi, ni na roƙi rumaisa ta rufa miki asiri, tare da tunanin ko zaki shiryu, tun da ba zaki daina ba, sai kin bar gidan nan yanzu"

Ammi ta ce "Mahmud ban gane me kake nufi ba? Me ta yi ne? Tsawon shekaru ina tare da ita rana tsaka ka ce ta tafi?"

"Ke kin ɗauketa mutum, kin kula da ita da iyalinta, ita kuma tsawon shekaru tana cin dunduniyarki, duk abubuwan da suke faruwa a sashin ki, Mummy na da masaniya a kai"

Gaban Ammi ya faɗi ta kalli baba uwani ta ce "Uwani, da gaske yake yi?"

"Wuce ki kwaso kayanki ki bar gidan nan, ki je dan kanki, ko ba a ɗauki wani mataki a kanki ba, hakkin mutanen da ki ka ɗauka ba zai barki ba"

Mahmud ya ƙi yi wa ammi cikakken bayani, ya kori baba uwani a gaban sauran hadimai, wanda ya san tilas maganar za ta watsu, ace ya yi mata korar kare ba tare da cikakken dalili ba".

Baba uwani na kuka, ta kwashi tsummokaranta, ta fita.

Gaba ɗaya ammi ta zama confused, Barira ta ce "Ai ni na san baba uwani ba zata sauya hali ba, nayi mamakin rashin tona mata asiri, da maman sabir ba ta yi ba".

Jin abun da ta faɗa, ya sanya ammi ritsa Barira, barira kuwa ta kwashe komai ta gaya mata.

Ammi sai da ƙafafuwanta suka nemi gaza ɗaukarta, saboda tashin hankali da zullumi, hadimar da ta amincewa tsayin shekaru, ita ce ta ci amanar ta.

Kasa jurewa tayi, a daren ta je gidan takawa, hankali a tashe, dan kuka take suka je gidan. Wanda hakan ba ƙaramin ɗagawa ruma da takawa hankali yayi ba.

Rumaisa ta tabbatar mata da ta san baba uwani muguwa ce, tun a lokacin da ta din ga gaya mata takawa mahaukaci ne, da lokacin da ta ce Mummy tana yi wa takawa asiri maganar ta koma kunnen Mummy.

Rumaisa ta tabbatar mata da cewa, Mahmud ya gaya mata ya sha ganinta cikin dare a sashin Mummy, amma ya ce kar su tona mata asiri a lokacin, saboda basu da cikakkiyar hujja, yanzun ma tun da ya ce ta tafi, yana da dalilin yin hakan, kuma ko daga baya an tayar da magana, suna da cikakkiyar hujja a kan ta yanzu.

Sai a lokacin ammi ta din ga tuna wasu daga cikin abubuwan da suka gabata, tabbas idan da babu munafuki a sashin ta, babu yadda za ayi wasu maganganun su din ga fita.

Sai dai a hakan ma, ruma ta ɓoyewa ammi binne-binnen da baba uwanin ke yi mata a cikin gidan.

Takawa ya din ga rarrashin ammi yana bata haƙuri, tare da yin faɗa dalilin da ya sanya Mahmud ya kori baba uwani kai tsaye, ba tare da girbar abun da ta shuka ba.

Ammi ta daɗe abun nan yana ci mata zuciya, ta daɗe tana jinjina tsawon lokacin da baba Uwani ta yi, tana zaluntar ta, ta hanyar kwasar sirrinta tana kaiwa wajen Mummy.

Baba uwani bayan ta fita cikin kuka, ta kira Mummy ta sanar da ita halin da ake ciki, wanda hakan ya faru a dalilin ritsa Mummy da yayi suna waya da baba uwani, dan sai da suka samu saɓani ma.

Babu kunya Mummy ta ce "Ba abun da za ta iya yi mata, sakacinta ne ya janyo mata"

Baba uwani ta sha mamaki, ba ta taɓa tunanin abun da Mummy zata gaya mata kenan ba.

Sannu a hankali rumaisa ciki ke tasawa, tayi ta ɓoye-ɓoye, gashi yau da lafiya gobe babu, haka nan take zuwa makaranta.

Ga koke-koken ba gaira ba dalili, wai ita rasa abun da yake yi mata daɗi.

Sai dai takawa yayi ta rarrashin ta, ya san ƙuruciya ce da rashin sabo.

Iman kuwa kusan awanni kaɗan sai sun yi waya da mai sunan baba, idan ta maƙale a kan waya, har mantawa Ammi take yi da ita.

Ammi ta ce "Iman dan Allah ki ƙyale yaron nan yayi aikinsa mana, maƙal-maƙal a kan waya ko gajiya ba kwa yi ne?"

Rufe fuska tayi tana murmushi, dan kuwa ba ta yi zaton ammi ta ɗagota da yawan wayar nan ba.

Ɓangaren mai sunan baba, yanayin aikinsa yayi masa daɗi, sai dai kewar gida da yake yi sosai, sannan ya fuskanci akwai tarin kitimurmura da rashawa a aikin.

Sai dai yadda yake umar ɗin sa bai canza ba, ba ruwansa da kowa aikinsa ne kawai ya dame shi.

Sallama aka yi a office ɗin sa, ya amsa tare da kallon ƙofar.

Wani babban mutum ne ya shigo, fari sol da shi, cikin manyan kayansa.

Mai sunan baba ya yi masa ƙuri da ido, ya ƙaraso ya zauna suka yi musabuha da mai sunan baba.

Ya ce "Namu ne ka na jin hausa ko da turanci zan yi" yayi maganar cikin guɓatacciyar hausarsa ta cikakken bafulatani"

Mai sunan baba yayi murmushi ya ce "Ina kama da bayerabe ne?"

"To ai abun naku ne, wasu lokutan ba a banbance ku hausawa".

"Eh amma irin naku da kun ga junanku ku ke ganewa"

Mutumin yayi dariya, duk da yau ya fara ganin mai sunan baba, kamalarsa ta burge shi.

Ya ce "Masha Allah ya aiki?"

"Aiki Alhamdilillah"

"To da dai ba kai nake tararwa a office ɗin nan ba".

"Eh, sabon ma'aikaci ne ni"

Ya ce "Yauwwa ni fa in ce. Kayana ne nake ta sintiri ayi mini clearance, amma bayan gama biyan duk wani haraji sai wani hanya-hanya ake yi mini, ana dai nuna mini sai na bayar da cin hanci, sai dai ba dan babu kuɗin ba, bayarwa ne ba zan yi ba. Tun da na san kayana ba na laifi bane"

Ikon Allah mai sunan baba yake gani, hatta yadda mutumin yake kallonsa, tamkar iman ce a zaune a gabansa.

Ya ce "Wasu irin kaya ne? Fanta ne, buredi da ƙosai ne ko kuma shanu"

Mutumin ya sake yin dariya ya ce "Ka fa dame ni fa, ko dai babarbare ne?"

Cikin murmushin sa na ƙasaita ya ce "Ba ɗaya, mai ɗakina ce bafulatana, ai ni akwai amana a tsakaninmu"

"Ahhh ashe ma sirikinmu ne, ina fatan ka bayar da nagge 100, kafin a baka" yayi maganar yana ciro wayarsa daga aljihu da take ringing.

Ya cewa mai sunan baba "Afuwan dan Allah"

Ya kara wayar a kunnensa, yana magana da fulatanci, mai sunan baba yana fahimtar wani abun, sai dai ya ji yana cewa Ade a cikin maganarsa.

Ya gama wayar ya girgiza kai ya ce "Ade na da damuwa. Wai mahaifiyata na ɗaukko daga garinmu, na dawo da ita nan Lagos gabana, na din ga ganinta. Ni da matata fa ƴan uwa ne, kuma akwai wasu ƴan uwana da na ɗaukko duk muke zaune tare. Amma ta saka an kirani a waya, wai na rabota da danginta na zo na ajiyeta a nan, ita tunanin shanunta da awakinta ma take yi. Ace Allah ya yi mini rufin asiri, amma uwata na ƙauye ai lamari ya ɓaci"

Mai sunan baba ba wai dan halayyarsa ce sakin jiki hira da mutane ba, sai dan son cigaba da kallon ƘUDURAR ALLAH (Kar ku manta da sabon littafin NAZEEFA SABO NASHE, da tuni ya fara zuwar muku, kar ku yi ƙasa a gwiwa wurin bin wannan ƙayattacen littafin)

Mutum mai matukar kama da matarsa, ya fara tambayar kansa anya mutumin ba shi da alaƙa da Iman ɗin sa.

Hira suka ɗan yi da mutumin, yana bashi labarin rigimar Ade, kuma ya ke gaya masa akwai mataimakin shugaban ƙungiyar fulani ta ƙasa a familynsu, Ade Allah ya yi wa iyalanta rufin asiri, amma ita ta dage sai zaman ƙauye.

Mai sunan baba ya bashi labarin, shi nasu gidan, da ƴan uwansa, tare da tattaunawa a kan jajircewar iyaye mata idan aka mutu aka bar su da yara.

Haka suka din ga hira, daga baya suka yi exchange ɗin numbern waya, mai sunan baba ya ce zai sake duba maganar kayan na sa.

***

Ƴan kwanakin nan, Mummy tana ta fama da ciwon kai, ta je asibiti an yi mata teses amma bai daina ba, ko san haske ba ta yi sosai.

A hankali kuma Allah ya taimaketa ya fara sauka, shiryawa tayi zata fita, tana son yin waya, amma tata ba network, dan haka ta karɓi wayar ruƙayya ta saka lambar wayar da zata kira, ta yi wayarta.

Sai dai bayan kammala wayar, ta ga saƙo ya shigo wayar ruƙayya daga Jabir.

"Wallahi ruƙayya idan ba ki zo kin same ni ba, mun cigaba daga in da muka tsaya ba, zan watsa videos ɗinki, duniya kowa ya gani, and i mean it"

Bakin Mummy ne ya fara rawa, ƙafafuwan ta suka nemi gaza ɗaukar gangar jikinta, cikin tsananin tashin hankali da mamki, ta dawo falo in da ruƙayya ke kallo. Fauziyya na chatting.

Tana zuwa ta jefa nata mata wayar, ta ce "Me wannan saƙon yake nufi?"

Gaban ruƙayya ya faɗi, ta ɗauki wayar, ta karanta, a take ta fara kuka tana girgiza wa Mummy kai.

"Ki gaya mini me saƙon nan yake nufi?"

"Mummy zan yi miki bayani dan Allah"

Danneta mummy ta yi tana hargagi ta ce "Ni zaki tonawa asiri ruƙayya, wace irin alaƙa ce a tsakanin ki da Jabir? Wallahi gara na kashe ki, na kashe banza, akuya ce ke? Da ke za a haɗa kai a janyo mini abun faɗa? Ni Lubabatu da Jabir za su haɗa kai su cuta? Ni?" Da ƙyar Fauziyya ta janye Mummy daga kan ruƙayya da tuni numfashinta ya fara sama-sama.

Ruma ce zaune daga ita sai mini skirt da brezia, domin kuwa kayan ma ita yanzu damunta suke yi.

Ta ƙurawa Adam ido, "Ya dai babyna, jikin ne?"

"To jiki ai sai Alhamdilillah, papa baka gano smoke ɗin ba haryanzu?"

"Mimi da na gano, ai da na gaya miki, bashir suna nan suna bincike a kan al'amarin, kuma an gano wurin da ki ka ce ana ɗibar ma'adanai, mun yi magana da hukumar mu ta katsina ana targeting wurin, kama su ake son yi red handed kamar yadda na gaya miki"

"Papa, na san na yi maka laifi, tun haɗuwarmu yakamata ka san komai, amma na din ga yi maka wasa da hankali. Ka san dalili?"

Ya ce "A'a"

"A wannan lokacin da ka san komai, zaka yi aiki da zuciya ne, zaka iya ɓata aikin, saboda kana kan jin raɗaɗin abun da ya faru.

Anty Aisha ta bani labarin komai, wanene kai, abubuwan da suka faru a rayuwarta da taka, rashin jituwaku tsakaninka da Mahmud, sannan a ƙarshe ta roƙi da na auri mijinta, saboda tana ji a jikinta zan iya taimakonka, idan har zan rayu a tsakanin ƴan bindigar daji marasa imani da tausayi, in zauna a cikinsu da baƙin taurin kai, har na din ga abun da nake so wasu lokutan, su ƙyaleni, to lallai zan iya tanƙwara zuciyarka da koya maka haƙuri da sassauta fushinka.

Na tubure na ce ni fa ba zan aureka ba, dan ba ka yi mini ba, mussaman da ba ma jituwa, amma ta cigaba da yi miki magiya, tare da roƙon in taimaki rayuwar mijinta, ita tayi iya nata ƙoƙarin ta kasa".

Rumaisa ta ɗan yi shiru sannan ta ce masa "Lokacin da anty aisha za ta mutu, ta cigaba da nanata mini, ta bar mini jaririn ta, kuma ta bar mini mijinta, dan Allah kar in bari ƴar uwatta ta aureka, kuma in tabattar an samu daidaito tsakanin ka da ɗan uwanka, domin samun farincikin ammi.

Papa, wakili na da saka hannu a yin garkuwa da anty aisha, dan ƴan bindiga sun ambaci sunansa, cikin dare suna zaton duk mun yi bacci".

Ƙirjinsa ya buga da saurin gaske ya kalleta.

"Amanarka na karɓo papa, shiyasa nake iya ƙoƙarina da zuciyata da jikina domin baka kariya, da tabattar da cika alƙawarin da na yi wa anty aisha. Ina neman afuwarka bisa wahalar da kai da na din ga yi, but Alhamdilillah atleast na cika wasu daga cikin alwashin da na yi"

Shiru yayi ya sunkuyar da kai, ya kasa cewa komai.

Rumaisa ta ɗago kansa ta ce "Papa fushi ka yi?"

Cikin tsananin ƙarfin hali, da hawayen idonsa ya kasa ɓoye damuwar, ya ce "Mimi ba ki yi mini komai ba, ni ya cancanci na yi miki godiya mimi, ban san da wasu kalaman zan yi amfani ba ma" yayi maganar yana kwanciya a jikin ta.

Ta kalli hannunta da hawayen sa yake ɗiga a kan hannunta, ta saka hannu tana share masa hawayen, tare da shafa sumar kansa.

"Mimi ba kya so na? Saboda alƙawarin aisha kawai ki ke tare da ni?"

"To ai ban san me zan ji idan ina son ka ba"

62 / 69