SIGN MARRIED BOOK 2 BY OUM HAIRAN

Author :  Fauziyya Tasiu Umar Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 12

21K to 24K   out of 33.5K words

aka siya daganan mu koma Abuja idan so mu ɗaga ko me kikace?" Jinjina kai tayi tace “shikenan hakan za'ayi" wanka sukayi sukayiwa ƴaƴansu sukayi sallah suka kwanta bacci.
Kiran Deen ne ya shigo tana ɗagawa tace masa “Ka koma ne? Murmushi yayi yace “Jiya naji damar jikina yau na sauka a Austaralia course Yayana bashida lfy shima but ya fara jin sauƙi, ya shirye shiryen biki?"





Murmushi tayi tace “Nima ina hanya cikin satin nan" zaro ido yayi yace “Ya batun bikin naki?" Murmushi ta sakeyi tace masa “Bazan cuci kaina bane Noor tunda sun hanamu aure to Nima wlh bazan auri wanda sukeso ba su barni na rayu da ƙaddarata" ajiyar zuciya yayi yace “Idan kikazo sai musan abinda ya dace kawai muje Embassy a ɗaura mana aure tunda parents ɗinki sunƙi ɗaura mana" dariya sosai abin ya bata yace “Haba Deen abin na kaɗo ai ba hauka bane nayi Sign married sannan yanzu nazo nayi Embassy married ai kayimin faɗan nabi komai a hankali, tunda dai komai lokaci ne"
Kwantar da kai yayi yana kallon Ma'eesh dake gefensa yace “Nace da Bro Wife ɗina a ɗaya cikin Restaurants nasa take aiki idan kin dawo zamuje mu gaisheshi yasa mana albarka, ko na haɗaku ku gaisa?" Saurin girgiza kai tayi tace “Aa ka bari dai nazo sai muje mu gaisheshi ai yayanmu ne bai kamata ayi masa gaisuwar miƙe ba" Murmushi yayi yace “Hakane kinyi gsky yanzu yaushe zaku taho?" Haka sukayita hirarsu tare dayi musu alƙawarin zai sama musu visa urgent, haka kuwa akayi kwana biyun da sukayi a Kano sunga gidan da Batul ta siyawa inna gidane me kyau ya ƙawatu duk da ba wani babba bane Saida ta zubanta komai na amfani hatta kayan abinci sannan ta bawa Janah kuɗi masu yawa tace taje ta ɗaukota ta dawo da ita nan" washegari kuwa Zakara ya basu Sa'a sai Cairns shigar dare sukayi shigar dare sukayi sosai domin Saida suka yada zango a Canada sannan suka ɗauki hanyar Austaralia.







Dake Turai ba Africa bace a daren suka dangana da gida domin kuwa a airport ɗin suka ishe Deen yana jiransu kallo daya tayi masa ta tabbatar da ramarsa sosai ya bata tausayi ta kwantar da kanta a jikinsa tace “My Noor ka rame da yawa don Allah kar ka sanya damuwa a ranka komai yanada lokaci" shafa kuncinta yayi yace “Bazasu gane bane Fateemah inashan wahala fah ina buƙatar abokiyar rayuwa wlh" murmushi tayi a ranta tace “Gara ma kai baka ɗanɗana ba but a zahiri ce masa tayi lokaci zai zo soon Insha Allahu.
Saukesu yayi bayan sun biya ta Restaurant nasu sun karɓi abinci a ƙaramin office ya tadda Ma'eesh yana zaune ya zuba uban tagumi ya taɓashi yace “Har yanzu bazaka rage damuwar nan ba Bro no condition is permanent please ka rage damuwa ko dan lfyrka" kifa wayar yayi a ƙirjinsa tare da danna sweetch ɗinta ya zubawa ƙaninsa nasa idanu yayi yace “Ka ɗaukosu ne?" Jinjina kai yayi yace “Abinci ma muka biyo su karɓa sai su wucce gida Bro na mutu akan Babyn nan Teemah ta haɗu sosai rayuwa ta ce?" Murmushi yayi yace “Allah yasa rabonka ce Deen Kaje ka kaisu gida dare yayi Ba zamu haɗu a wannan karon ba Ni gobe zan koma Sudan banason mutuwa a garin nan gara naje na mutu a gaban Mom ta dafa kaina tayimin addu'a Inason bata duk wani abu dana mallaka idan na mutu ta nemi Batul ta batashi ita da babynmu su rayu rayuwa me inganci"





Miƙewa yayi ya fice in da sabo ya saba da Waɗannan kalaman na yayan nasa kullum abinda yake cewa kenan matarsa da ɗiyarsa shi ya fara sarewa yanda ya baza ma'aikata ake neman yarinyar nan inda tana raye da tuni an ganota" jan motar yayi ya kaisu gida sukayi masa godiya suka shiga ɗakinsu kawai suka gyara sukayi sallolinsu suka kwanta baccin gajiya sun fara mantawa da sanyin Austaralia gashi sun dawo lokacin saukar Snow abin ba sauƙi haka suka sa shirga shirgan kayan sanyi suka kwanta bacci kuwa ya sacesu cikin dare ta farka a firgice tana furta “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un!" Abinda ya tashi Samha tace “Ya akayi?" Ajiyar zuciya tayi tace “Na godewa Allah daya zama mafarki Samha kwanan nan Ma'eesh ne ya dawo a mafarki na, na fara cire shi a raina har ina jin a raina fah ko bayyana yayi gareni bazan iya sake rayuwa dashi ba saboda hankalina bazai kwanta ba zama da matsafi" tsaki Samha tayi tace “Wlh da kayan haushi kike yanzu yaushe zaki koma aiki yanzu nake gani gobe Shugaba yana neman dukkan ma'aikata zai yi taro dasu zai koma ƙasarsa shan magani" taɓe baki tayi tace “Gsky gobe ba zanje ba zan huta shi kuma Allah ya bashi lfy"
Komawa sukayi suka kwanta da safe Samha ta tafi aiki ita kam zamanta tayi a gida da yamma Deen yazo yake ce mata Bro yakai airport nan suka shantake da hirarsu ta masoya.






Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta kowanne ɓangare babu daɗi Inna ta fuskanci ƙalubale daga ƙarshe ne Alh Khamilu yazo ta zayyane masa komai Aikuwa ya rufe yan uwan nasa da faɗa yace sunci amanar maraici Meyesa yarinya zata kawo wanda takeso suƙi bashi su haɗata da wanda bataso, yanzu in a baya sunce laifin uwarta ne yanzu kuma na waye? Waye yake da alhakin sake fantsamarta duniya?" Dake yanada citta a hannunsa take sukayi nadama suka bashi haƙuri duk kuwa da cewa shi ce masa sukayi batada manemi ne shiyasa sukeson haɗata da ɗan uwanta, da kansa yaje ya bawa Inna Laure haƙuri yayi mata jagora har Kano inda suka samu lambar Batul gurin Janah bai bar sabon gidan Inna ba Saida ya kira Batul lokacin tana gurin aiki ta ɗaga suka gaisa yace “Batula baki ganeni ba ko? To ubanki ne Khamilu" cike da kunya tace “Lahhh Baffa ina yini ya gida da mutan gidan?" Dariya yayi yace “Kinci uwaki ƴar ƙaniya to ki turomin number surukin nawa sai jiya nake sanin abinda ya faru wlh banga laifinki ba Batula Ni daɗi ma naji da kika nuna musu kin san kanki ke kam yanzu idan ba'a rarrasheki ba ai ba'ayi Miki dole ba"
Cikin kunya tace “To Baffa na gode" tana aje wayar ta tura masa number Deen tayi wani tsalle ta rungume Samha tace “Ke burinmu ya kusa cika yanzu baban Anwar ya kirani yace na tura masa number Deen nasan maganar aurenmu za'ayi wlh na gaji da haɗiyar ƙwayar kashe sha'awa nima Gara naje na warwasa na baje masa ya lasa ya tsotsa yaci ya ƙoshi" dariya sukayi tare da tafawa suka kama rawarsu ta yan Iskan gari, ranar basu bari sun tashi ba gida suka koma harda haɗa ƙwaryan party Suda ƙawayensu tun basusan me ke faruwa ba.
Da dare kuwa kiran Inna ya isheta ta ɗaga suka gaisa tace “Yanzu sai yaushe zaki dawo a yau ɗinnan Ƙanin Mamar saurayinki yazo sun kawo dukiyar aure da sadaki Miliyan biyar an tsayar da ranar aure wata guda me zuwa".......




*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*


*Contact me*
*09013718241*



*OUM HAIRAN*
[7/10, 11:18 AM] Oum Hairan: SIGNED MARRIAGE
*_(Kalma ɗaya)_*



*Oum Hairan*



*____________________________________*
*Book 2 page 21-22*
*____________________________________*




Wata alkafura tayi ta tashi a gadon tace “Inna 5Ml saidani zaki kumayi?" Dariya abin yaba Inna Laure tace “Ba saidaki zanyi ba Batool abinda suka kawo kenan sunce saboda yanayin faɗuwar Naira abubuwa sunyi tsada kuma irin wannan auren ba shiryawa akayi ba dole sai jin ƙai ya shiga, yanzu dai yaushe zaki dawo Kano?" Ajiyar zuciya tayi Samha ta karɓe wayar tace “Inna mu bari sai bikin ya rage saura sati biyu inaga Zaifi" a haka suka bar abin sukaci gaba da shirye-shiryensu sabon babi na soyayya ya buɗe tsakanin Batul da Deen ko yaushe suna manne a waya ko suna chat kasancewar tun kwana biyu da sa ranar bikin ya tafi Nigeria da yake anan yake ra'ayin zama a Abuja yanata gyare-gyaren gidan da zasu zauna ranar da zasu tafi ne wani abu me kama da almara ya faru suna zaune a reception suna jiran cikar lokaci wani ƙamshin turare da bazai taɓa ɓacewa a ƙwaƙwalwarta ba ya ziyarceta abinda ya katse mata numfashi na tsayin daƙiƙu ta miƙe zumbur tare da fara dube² ajiyar zuciya tayi ta koma ta zauna tare da dafe kanta.
Samha dake kallonta ta dafa kafaɗarta tace “Me kike nema?" Ajiyar zuciya tayi tace “Babu komai" janye hannunta tayi tunda tace babu komi tasan bazata mata bane, da wannan aka fara kiran matafiya suka tashi suka shiga jirgi bayan kowa ya gama zama jirgi ya tashi bakin Batool ɗauke da addu'ar neman kariyar Ubangiji, har yanzu kuma hancinta bai daina jiyo mata ƙamshin daddaɗan turaren da ta gaza jinsa a gurin kowa sai a gurinsa shi kaɗai wato Ma'eesh inda taketa satar kallon gefe da gefenta amma bataga wata alama da take nuna akwaishi a gurin ba.
Ba su so tafiyar tazo musu a karkatse ba but dole haka suka haƙura ashe jirgin yawo suka biyo Saida suka tsaya a Japan suka kwana biyu abinda yake ƙara bata mamaki kuma ya koma tsoratata yanda wannan ƙamshin turaren yake bibiyarta idan ta duba kuma taga babu kowa.





Daganan suka tashi sai Canada daga Canada suka dira a birnin tarayya suka kwana ɗaya abinda ya bata mamaki duk kiran da takewa Deen wayarsa bata shiga daga ƙarshe aka turo mata saƙo.
“Kiyi haƙuri na turo Muhsin zai ɗaukeku zuwa Kano Nima zan biyo bayanku Fateemah ina ɗakin taro ne" Jinjina kai tayi babu ɓata lokaci batare da tambayar address ba saiga wani saƙon ya kuma cewa “Zai kiraki ƙaninmu ne zama kiga kama" tana gama karanta daƙon kira ya shigo wayarta ta ɗaga “Sosai gabanta ya faɗi jin Muryar tasa, yace “Auntyna ina jiran ku" saurin sauke wayar tayi a kunnenta tace “Nikam na shiga uku Samha komai nashi yake zamemin, meye haɗin ƙanin Deen da Muryar Daddyn Jany?" Murmushi Samha tayi tace “Wannan mayen mutumin zai kashe Miki aure idan bakiyi da gaske ba, yoni na taɓa ganin wannan masifa kin damu da mutumin da neman sanin yanda kike da lafiyar ɗiyarsa dake hannunki ma ya gagareshi"
Iska ta furzar tace “Inashan wahala da Zuciyata akansa Samha kema kin kasa fahimta ta wlh na faɗa Miki a yanzu ko bayyanarmin yayi bazan ɗaukeshi nabar Deen ba but kinsan meye yanzu yake zuwa raina? Shin daga shekara biyun yarjejeniyar ta ƙare kenan?" Tsaki Samha taja tace “Wai yarjejeniya toke ubanwa yace Miki aure kukayi kawai kunyi iskancinku ne amma ko a kafirci aure a curch ake ɗaurashi bare a musulunci da sai anyi siga waliyyay sun haɗu an bada sadaki shaidu sun shaida sannan aure ya ɗauru"







Bata kuma cewa komai ba suka isa jikin motar ta Zubawa Muhsin ido da yayi caraf ya cafe Jany yana cillata yana dariya dimple ɗinsa na lotsawa hatta dariyarsa irin ta Ma'eesh ce hasken tsananin kamar har ta zarce misali hasken fatar sa ne kawai ba irin na Ma'eesh ba shi nasa da sirkin duhu a ciki saɓanin Ma'eesh da yake tar irin hasken Turawa har wani ɗaukar idanu yakeyi. Juyowa yayi yana kama hannun Jalal ya rusuna yace “Gaisuwar ban girma matar Babban Yaya Uwar sha lelen Mom!" Zuba masa idanu tayi ya buɗe musu motar suka shiga ya lura da kallon ƙurullar da take yi masa but yasan dalilinta domin kaf gidansu babu wanda suke kama ta Kwabo da Kwabo irin shi da Mijinta duk kuwa da cewa Uwa suka haɗa koda yake dukka da Mommy suke kama dama Deen da Aunty Nuwairah ne suke basuyi kama dasu sak ba su sunfi kama da Abbuh Hakeem amma a hakan akwai wasu yanayiyyika da suma ake cewa suna kama da Mom, jan motar yayi a guje kiɗansu na Sudanies na tashi a motar ita kanta motar ƙamshin turaren da yake rikita mata lissafi takeyi, Samha sai magana takeyi mata ita kuwa kanta ya kulle sai juya mata yake yi musamman da take jiyo hirarsu da Jany, yarinyar tana masa surutu shima ya dage sai tayata yakeyi yana ce mata “Babyna yau taga Dad ɗinta, kina cikin alkhairi yarinya"
Nisa na tsakanin Kano da Abuja ita dai Batool sai ji tayi yana cewa da ita “Matar Big bro ko baki gaji bane mu juya?" Firgigit tayi ta dawo hayyaci ta dauki jakarta ta fito ta nufi gidan ya ɗaga murya yace “Am Matar Big bro sai nazo ɗaukar amaryata" cije lips ɗinta tayi ta nufi cikin gidan tana ayyana ya fahimci halin da ta shiga da ganinsa ma shine yasa yake neman zautata.





Duk yawan mutanen dake tsakar gidan na Inna bata iya kula kowa ba ta shige ɗaki ta fincike mayafin kanta ta wullar tare da zubewa kan gadon tana furta “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'akalifni khairin Minha!" Jin yanda lazumin "hasbunallahu wa ni'imal wakil" ne yasa Samha zubanta ido tace “Na lura da rikicewarki tun fitowarmu da kikayi arba da wannan kyakkyawan guy ɗin, ya hayyu ya ƙayyumu Teemah An ƙure kyau a wajen nan nifa Saida nace to wai samarin aljanna sun fara kawo mana ziyara duniya ne?"
Miƙewa tayi tace “Kinsan me ya bani mamaki? Samha bayan Muryarsa da yanayin dariyarsa da kuma kama ta zahiri dana gani hatta tsayinsa da faɗinsa irin nasa ne, Jany bata kama dani but daya ɗauke kasa bambamce bambancin tsakaninsu nayi, kince Jany tana ɗiban kama da Deen shi kuma wannan me Jany takeyi dashi?" Kama hannunta Samha tayi tace “Ba kama bace gaurayar jini ce, wallahi azza wa jallah badon nasan komai game da Jany ba babu yanda zaayi naga mutumin nan ɗauke da Jany naki bada shaidar shine ubanta, saidai karki manta duniya tanada faɗi kuma dukkanmu Allah ɗaya ne ya haliccemu sannan inaso ki rinƙa tuna abu guda ɗaya nasabar gari ɗaya ma tana bin jini, Batool kince Kakar Jany ammana mahaifiyar Daddynta itama Sudanese ce kuma kince Ma'eesh da mahaifiyarsa yake kama Kinga kenan maybe ko sun haɗa wata alaƙa ta jini ta nesa ma bata kusa ba, wannan dai ƙanin angonki me jiran gado ne nan da 10 days Kinga kenan bashida alaƙa da Ex-husb ɗinki a cewarki"





Komawa tayi ta zauna tana sake dage kanta tace “Idan ko ya zama haka maganar gaskiya zan sanar da Deen banason wannan ƙanin nasa a sashina saboda zai rinƙa firgitani Samha Ni kaɗai nasan me nake gani a tare da yaron nan kuma na fahimci ya gane yanda na ruɗe da ganinsa har wani zolayata yake yi" dariya Samha tayi tace “Wannan ango yana ganin rayuwa tun yanzu za'a fara kafa masa dokar wanda zaizo da wanda bazai zoba" bayi ta shiga ta sakarwa kanta ruwa tana wankan taji shigowar Janah fitowa tayi suka rungume juna tace “Kaga manyan mata ke batool kiji tsoron Allah wannan uwar ƙiba da kikayi me kikeci ne a Turain"
Murmushi tayi taci gaba da shafa manta tana gamawa ta zura riga Janah tace “Ba kwanciya zakiyi ba kitse Sarkin bacci tashi zakiyi muje ga motarki can ta rigaki zuwa ki jamu ki kaimu inda angon namu ya ce zamuje gyaran jiki na kwana takwas" kallonta tayi tace “Wai ina kikasan Deen ne Janah?" Dariya tayi sosai tace “Taya bazan san Deen ba bayan kusan koyaushe yana gidannan"
Taɓe baki tayi ta ɗauki wata kanannaɗaɗiyar hula ta ɗora saman sumarta data baje saman bayanta ta yafa mayafin a kafaɗa ta zura takalmi suka fito sai yanzu ta gaisa da danginta da suka cika gidan yan uwan Inna da ƙannen mahaifinta Inna tace “motoci ne guda biyu aka kawosu jiya yace saboda zirga zirgar da zakuyi yanzu key ɗin wacce za'a baki?" Murmushi tayi tace “ki bani na tawa Inna girgiza kai tayi tace “Aa bazaayi haka dani ba Ta Manzo yaba kyauta ai tukuici ki hau tasa don Allah"



Cikin zaƙuwa tace “Shikenan bani key ɗin" remote ɗin Inna ta miƙo mata duka ukun ta fita compound na gidan ta latsa na farko wata hamshaƙiyar mota ta amsa mata ta nufeta gabanta yana faɗuwa ta shiga ta zauna Janah da Samha suka fara baza mata hoto suna mata kirari Janah tace “Wannan amaryar tafi kowacce amarya a shekarar nan Capacity" dariya tayi data sanya kyawawan haƙoranta suka bayyana yar siririyar wushiryarta ta bayyana Janah tayi maza ta baza mata hoto ta shiga motar suka tafi.
Wani katafaren gurin kwalliya da gyaran jikin amare ne me suna MB Bridal Beauty nan Janah tace su tsaya suka tsaya Batul ta tsaya tana ƙarewa wajen kallo iyakar haɗuwa tun daga haraba gurin ya haɗu ta sauke ajiyar zuciya wani sihirtaccen ƙamshi na tashi a gurin, suka taka suka hau saman kamar yanda Janah tace musu, suna shiga taga ma'aikatan suna zubewa suna gaisheta tare da wata irin girmamawa ita dai bata fahimci komai ba ta ɗauka dabi'arsu ce girmama customer.
Wata kyakkyawar mace ce ta fito da ganinta kasan ba tamu bace cikin hausarta da bata fita tace “Barka da zuwa Hajiya mu shiga daga ciki" babu musu sukabi bayanta a parlour tace su Janah su zauna ita kuma suka shiga ciki matar tace “Ranki ya daɗe sunana Nuriyyah Surukarki ita ta bani damar yi Miki gyaran da ba'a taɓa yiwa wata amarya irinsa tace keɗin ta musamman ce" ƙasa tayi da kanta batare da tace komai ba, tun daga wannan lokaci suka fara gyaran jikin wannan amarya taga masifa yanda ake durzar jikinta da haɗin dilka saida tayi kamar tace ta shiga uku ta lalace" iya gyaran na rana ɗaya tayi wani fitinannen kyau da haske, sai yamma Hajiya Nuriyyah take sanar da ita gidanta zasu wucce akwai abubuwan da bazasu yiwu a shagon ba da tayi tunanin zuwa gidansu to kuma aikin baya buƙatar hayaniy.


Saida su Samha suka shiga maganar sannan ta yarda suka tafi can ɗin Jany kam da Jalal a Inna suka barsu a takaice Saida aka ɗauki sati guda ana wannan gyaran jiki ita kanta Batool bata gajiya da kallon kanta tayi wani fitinannen kyau ga wani zaunannen ƙsmshi daya zauna daram a jikinta ko wuccewa tayi sai guri ya haura sama da 1 hour yana ƙamshinta duk

8 / 12