Author : Fauziyya Tasiu Umar Category : Read Hausa Novels
bashi damar ya zama jagoran rayuwarta.
Alwala tayi tasa kayan bacci ta kwanta Zuciyarta cike da tunani barkatai so take ta kawar da tunanin Ma'eesh kamar yanda kowa ke bata shawara saidai ta kasa duk kuwa da cewa itama batajin zata iya yafe masa wofintar dasu da yayi indai yana raye kuma lafiyarsa ƙalau cikin duniya, ta haƙura koda son sa zai zama ajalinta ta amince saboda abinda ta fahimta da rayuwa kawai ka rayu inda ake buƙatar rayuwarka" Washegari kuma da wuri yazo ya kawo mata uwar siyayyar da yayo musu ita da Jany da Jalal idan yayi wani abin har tausayi yake bata gashi da kara bai taɓa siyawa Jany abu bai haɗa da Jalal ba wannan ya ƙara masa ƙima a idanun Samha taketa kafa masa gwamnatinsa, ranar Litinin kuwa zakara ya basu Sa'a a Nigeria suka sauka garin Kano suka kwana biyu tare da bawa Janah manya kyautuka da kaita asibiti aka ɗorata akan magani ashe ma ba HIV ɗin bace sanyi ne yaci jikinta fiye da tunani, washegari sannan suka ɗauki hanyar Niger cike da zullumin abinda zasu tarar.........
_Am so sorry yau naje asibiti na gaji kuyimin haƙurin gobe_
*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay Evidence of payment 09031307566.*
*Oum Hairan*
[7/8, 7:43 AM] Oum Hairan: SIGNED MARRIAGE
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*____________________________________*
*Book 2 page 11-12*
*____________________________________*
Sun isa Niger da dare a babban birnin ƙasar suka sauka suka kwana wani katafaren hotel da safe suka shirya suka fito domin nufar Damagaran tun fitowarsu wata hamshaƙiyar mota take musu horn basu kula ba domin basu ma kawo dasu ɗin ake ba har Saida matashin buzun ya fito a motar cikin shigarsa ta buzaye ya iso garesu yayi musu sallama Samha ce ta amsa tare da kallonsa ya zame ƙallen daya rufe fuskarsa dashi saboda yanayin hunturun da akeyi ya kama hannun Jany yana mata wasa yace “Da alama ku ɗin baƙine ko zan iya sanin masaukinku?" Da farasanci yayi maganar Samha tace.
“Eh zamu karasa Damagaran ne can ammasaukin mu" ba tare da tunanin komi ba yace “Sara kan gaɓa Nima can nayi muna iya tafiya tare?" Da sauri Samha tace “Ah haba ai Bama ɗora maka nauyi ba kaje kawai muma muna tahowa" waya ya zaro yace da drivensa yaja motar ya tafi zai taho da baƙinsa" da sauri Samha tace “Aa kar ayi haka muje" Batul da batasan me suke tattaunawa ba Samha ta kalla tace “Muje Hajiya mun samu lipt zuwa Damagaran ɗin" bata ja ba duk da bata bada fuska ba saboda ta lura hankalinsa a kanta yake.
Address ɗin gidan ta rinƙa basu suna bi cike da mamaki Ansar zai yi magana Anwarr ya hanashi sunyi tafiya me ɗan tsayi sannan suka isa ƙauyen Ƴar kuka inda sukayi parking gaban gidan me unguwa suka fiffito suna kallon garin cikin shekara bakwai da tayi batazo garin ba matuƙa ƙauyen ya canza ga raƙumansu nan turke gaban gidajensu.
Wasu matasan buzaye sukaga sun nufosu ita dai bata iya gane wani cikinsu ba suna ƙarasowa suka fara gaisawa dasu Anwar ya tambaye su me garin yananan, nan suka sanar dasu yaje gona amma bashi jimawa yaka zakkuwa itadai Batul kallonsu tayi tayi musu Godiya ta nufi cikin gidan gabanta na faɗuwa Zuciyarta fal da tunanin irin kallon da zasuyiwa juna ita da Inna Laure, sallama tayi daidai lokacin da Inna ta fito daga makewayi, tana ganin tilon ɗiyar Tata ta saki butar ta nufi Batul da gudu tana cewa "ga Batula ga Batula" nandanan dukkan matan dake ɗakunansu suka firfito domin ganin ɗiyar data sallamu duniya yau a gidansu kowa kallonta yakeyi da mamaki suna kallon Jany da tsoron mutane yasata kanƙame mamanta tana kuka tana cewa a ɗauketa, Samha dake shigowa itane ta ɗauki Jany tana cewa da ita “Ke kin cika rigima Jany meye kuma na kukan?" Jansu Inna Laure tayi har ɗakinta itadai Batul kallonta takeyi cike da tsoro badan Inna haihuwarta tayi ba da bazata gane ta ba saboda muguwar ramar da tayi tunda take bata taɓa ganin Inna tayi baƙi ba sai wannan karon, haka suka shiga dakin da aka shimfiɗawa ledar buhu a ƙasansa da ɗan karamin gadon ƙarfe Inna ta kuma shimfiɗa musu darduma sunata kallon kallo da Batul bayan dukkan matan gidan sunzo sun gaggaisa yaran ma sunata zuwa ganinsu suna cewa wai baƙin Turawa ne sukazo, to jiki yaci kuɗi sun saje da masu jajayen kunnen.
Kallon Nutsuwa Inna tayiwa Batul tace “Yanzu Batul akwai daɗin da zaisa ki manta Dani a duniya inanan abin duniya yayimin zafi nadama ta baibayeni inata tunanin ta inda zanjiki ko na ganki ke kuwa kina can kin samu guri kin manta dani" girgiza kai tayi wato har yanzu Inna tananan da ɓirɓushin halinta wai ta samu duniya ma take cewa ba tambayarta zatayi halin da rayuwarta ta shiga ba, murmushi kawai tayi ta share hawaye tace “Inna wannan ƙawata ce Kuma uwar ɗakina Samha a lokacin da aka saceni daga Nigeria aka kaini Austaralia bayan kin siyar dani a hannun matsafa sun ɗaukeni sun kaini can da zummar idan na haifi wannan yarinyar dake jikinki wadda kuka siyarwa da ubanta Ni na shekara biyu, su kasheni su kashe yaron da na haifa don cika burinsu na tsafi.
Nan ta kwashe labarin komai ta labartawa Inna Laure Aikuwa ta shiga tashin hankali da ɗimuwa tayi kuka kamar ranta zai fita ta rinƙa yiwa Samha godiya data gatanta mata ɗiyar tana.
Suna tsaka da wannan tattaunawa ne Mal Garbu da yake matsayin uba a gurin Inna Laure ya shigo, kasancewar shi ƙanine ga baban Inna Laure ya kalli Batul yace “Ke ar baƙauyiyar kawai kizo da baƙi ki barsu a waje badan ƴan gari bane Wagga ɗiya da tabawa mutane kunya Laure ɗiyan Alh Khamilu ƙanin me unguwa dake zaune a Niamey ne ya kawosu yaron nan mazaunin France Anwarr yake kamar ko?"
Dafe kai tayi tace “Kai tsohon nan har yanzu kananan da azarɓaɓinka to naga bani suka biyo ba wannan sarkin kwashe²n ce ta ɗebosu" tashi yayi ya fita ya shigo dasu aka shimfiɗa musu wata dardumar suka gaisa da mutanen gidan har suna zolayar Anwarr yaushe zai yi aure ko sai ya gama cin bokon?" Murmushi yayi yana kallon Jumaire matar Mal Garbu yace.
“Inna Jumre Ni ai na samu mata a gidanki gani sai ki ƙwaɗani ki cinye dama rabonta ne ya hanani ganin kowa sai gashi yau nayi gamon Katar gashi cikin ikon Allah tuwonku manku ko ƙanwata?" Wata harara ta watsa mashi da ta sanya hantar cikinsa kaɗawa yayi ƙasa da kai Jumre tace “Kai kuwa Anwaru ina zaka kai Ta Manzo Wagga ɗiya da shaiɗan yayima fitsari a ƙafa ta zama karuwar ƙasa da ƙasa ita zakace zaka ɗiba to kuwa kasan kaima uwayenka basu barinka saboda haka ka ruha mamu asiri ka barmu mu ƙarasa da ƙwarinmu"
Koda bashi aka faɗawa maganar ba Saida ta girgiza shi kuma ta ɓata masa rai ya kuwa haɗe rai yayi shiru itama ganin kallon da Mal Garbu yake yi mata yasata lallaɓa tsufanta tayi gaba abinta.
Tashi Anwar da Ansar sukayi sukai masu sallama da cewar zasu dawo zuwa dare dai lokacin ne suka samu hutawa sukayi wanka sukayi sallolinsu duk da cewa duk basu nutsu da gidan ba da alama Inna ba zaman lafiya sukeyi da mutanen gidan ba sai zubar musu da maganganu sukeyi suna yan waƙensu na mutanen ƙauye na habaici, itadai Inna tsumu a ɗaki bata cewa ƙala ganin abin nasu bana daraja bane ya sanya Samha samun Batul tace mata “Nifa ba komi raina yake ɗauka ba Teemah duk da cewa Innanki tayi kuskure amma bai kamata zuwanki yasa waɗannan ƙauyawan matan suyita yi mata ɗan bikin nan ba magana ta Allah zan kira Anwar yazo su nema mana hotel mu kama idan kuma da wani abu da za'ayi to ayi amma idan naci gaba da zama a wannan gidan tsaf zanmusu duka" share hawayen daya zubo mata tayi tace “Nima bazan iya zama a nan ba kinji fah yanda suketa ƙyararmin Jany duk taƙi sakewa sai kuka take yi" kiran Inna sukayi Samha ta sanar da ita sufa zasu shiga gari su nemi masauki “Nan Inna take faɗa masu suyi haƙuri Haladu ƙaninta yazo ta karɓi mukullin gidan Mahaifin Batul ɗin da tasa aka kwaskware zata koma ciki da zama itama zaman gidan ya isheta kullum sai sun sata kuka akan rashin Batul ɗin yanzu kuma ta dawo da yarinya tasan abin ƙaruwa zai yi" haka akayi Halliru yana zuwa ya rakasu ba laifi gidan yafi wanda suka baro kyau domin ginin zamani ne ya gama ginawa kenan zasu dawo Yar kuka da zama Allah yayi masa rasuwa dake sunyi canjin kuɗi sosai a Kano haka suka cire kuɗi aka siyo musu katifu guda biyu manya six by six sai ƙarama guda ɗaya ta yara suka sanya ɗaya a ɗakinsu ɗaya a ɗakin Inna gefe suka saka ƙarama ta yara suka saka glub aka simunte bayin cikin kwana ɗaya suka mai da gidan yanda sukeson ya kasance kafin su tafi domin kuwa tuni Batul tasa a nema mata gida a Kano kuɗaɗen da suke account ɗinta da Ma'eesh ya zuba mata sunada nauyi sosai sannan ga na wajen Lateef suma batayi komai dasu ba Gara ta nema musu gida inda babu wanda ya sansu su zauna su nutsu su nemi mafitar rayuwarsu.
Da safe sukaje gidan me unguwa inda nan ne aka haifi Mal Daheer mahaifin Batul sosai sukayi murnar ganinta Musamman kakarta mahaifiyar babanta da mugun halin Inna Laure yasa basa ga maciji dake tun jiya sun san da zuwanta gurin Anwar da yake matsayin abokin wasa gareta domin da Mal Ɗaheer da Alh Halliru yan turaka suke ma'ana ubansu ɗaya zumunci ne dake bayinsa sukeyi ba domin shi Mal Ɗaheer da baƙin halin Inna Laure ya ishi danginsa sukace sai ya sake ta ne shi kuma yace yanason matarsa bazai rabu da ita ba ta wannan sukaji haushi suka sallamawa Inna shi shine dalilin da yasa ko sun shigo ƙauyen Ƴar kuka Inna bata bari Batul taje ta gaida dangin mahaifinta kwatsam kuma sai gashi lokaci guda Inna ta sauko.
Tunda sukazo kullum suna maƙale da Deen a waya nan yake gaya mata shima nan da kwana huɗu zai taho, a ɓangare ɗaya kuwa Anwarr daya taho Damagaran da niyyar kwana ɗaya sai gashi ya nemi gurin zama duk da cewa Batul taƙi bashi fuskar yace mata komai amma matsayinsa na ɗan uwanta yasa bata wulaƙantashi.
Kwanansu biyar da zuwa Deen ya kiratd yake cewa da ita yana Damagaran ta bashi address, sosai suka cika da mamaki matuƙa nan take bashi kwantancen inda za'a kawo shi ta tashi ya shiga wanka ta fito ta sheƙa kwalliyarta cikin shigarsu ta buzaye.
Tana tsaka da shiryawa Anwar ya shigo ya tsaya yana kallonta ta ɗago tayi masa murmushi tace “Yada kallo haka Yaya Anwar?" Ajiyar zuciya yayi yace “Aa babu komai wankan ne ga kin karɓeshi Masha Allah"
*Contact me*
*09013718241*
*OUM HAIRAN*
[7/8, 10:29 AM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*____________________________________*
*Book 2 page 13-14*
*____________________________________*
Ajiyar zuciya tayi tace “Allah da gaske nayi kyau da shigar gado na, wow! Hammah Anwarr kace zanja magana...." Numfashinta taji yana barazanar ɗaukewa tayi maza ta dawo hayyacinta ta sauke idanunta kan Anwar daya ƙure mata guri numfashinsu na dukan juna ya sanya hannu yana zagaye lips ɗinta tare da janyota ya shigar da ita jikinsa ya ɗaga kanta sama yace “Kalli waɗancan tsuntsayen Batul basu burgeki gani ba?" Ɗaga kanta tayi ta zubasu kan wasu kyawawan tsuntsaye da ko a Turai bata taɓa katarin ganin ƙananun tsuntsaye masu kyawunsu ba bakinsu yana cikin na juna ɗayan yana rerawa ɗaya kukansa me jan hankali, sosai tsuntsayen suka sanyata a shauƙi sosai ta kamu da sha'awarsu da kewar abinda sukeyiwa juna, ta kuwa lafe a jikin Anwar me fitar da wani sihirtaccen ƙamshi me kashe jiki.
Bata fahimci abinda take aikatawa ba Saida taji saukar Muryarsa a dodon kunnenta yace “Kamar haka ya kasance Ni dake ne ƙanwata cikin wannan shauƙin da begen rayuwar da zanji daɗi zanji kamar nafi kowa Sa'a, saidai baƙin cikina nasan kin fahimci me nake nufi amma kinƙi nunamin ganewarki bari nasa ran zaki juyo ki dubeni, Batul Ni ba yaro bane shekaru na sun fara nauyi fah inada shekaru talatin da biyar na kusa alba'in kinga dole ina buƙatar abokiyar rayuwa, wlh ban fahimci haka ba Saida idanuna ya sauka a kanki, dama zaki bani dama tabbas da na nunawa duniya irin saarki da kika sameni matsayin abokin rayuwa"......
Tureshi tayi ta nufi ƙofa zata fice ya sake cafkar hannunta yace “Laifi ne don na buɗe maki Zuciyata Batul meye ne kikeso na baki shi wlh Ni ke kaɗai nakeso ki bani dama kinsani komai son da wani zai nuna Miki bayakai yani da jininmu yake gudana iri ɗaya don Allah ki bani dama Batul"...... Ficewa tayi daga ɗakin ta nufi ɗakin Inna inda suke hirarsu ita da Samha tanawa Jany kitso tana cewa “Yo ace a barwa yarinya kai ba'a kumbushe matashi Wagga wannan suma mu a nan ai baki lalata zaiyi"....... Faɗowarta cikin ɗakin ne yasa Su Inna miƙewa suna tambayarta “menene?" Tsayawa yayi jikin ƙofar “Bafa wani abu bane Inna kawai don na roƙeta alfarma ne shine take wannan abin Wlh Inna Inason Batul kuma ina raye bazata tafi dangin wasu ba"
Murmushi Inna tayi tace “Anwaru kenan ba laifi bane don kaso ƴar uwarka amma kasan ƙura zaka tayar idan maganar nan ta fita sanin kankane uwayenku basasona bare su so halwata, ta yaya kake tunanin zasu yarje maka auren ta Manzo?" Sosai zuffa take keto masa amma dake Buzun gaske ne sau cewa yayi “Nifa Inna zata soni to kowama ya barni bana neman tallafin kowa wajen kula da iyali na" daƙyar Inna ta lallaɓashi ya tafi sannan itama ta fito suka dubi juna da Samha, Samha tace “Ke kiji wata lukutar masifa Teemah wannan Anwar ɗin da gaske gaɓo ne daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi kuma fah akwai ƙura wlh don jiya da mukaje gaida Inna Yaure Tayi wata magana dana kasa gane me take nufi lokacin da take cewa “Tunda Allah yasa kin dawo cikinsu basu kuma bari kiyi nisa dasu zasu sama Miki Samrayi cikin Samarinsu buzaye su amra miki kin tuna lokacin kuma kinsan lokacin Anwar da Mustapha suna wajen suma har sun kalli juna kallon dana kasa gane wanne iri ne inda Mustapha yayi saurin cewa “Inna Inaso nikam in za'a bani shi kuma Anwar yayi ƙwafa ya fice kin tuna?"
Numfashi ta sauke tace “Ina sane Samha duk wannan abinda sukeyi ai babu wanda ya Isa goge zanen ƙaddara Ni har yanzu fa banjin akwai mijina a cikinsu kawai dai suna abinsu ne in banda haka Ni yanzu yama za'ayi ace za'a min aure a zaunar dani a ƴar kuka suma sun san bazai yiwu ba, ke nifa gabaɗaya Niger ma ba taƙamarsu Niamey ba to Ni batamun a zama ba"
Wayarta ne ya shiga ruri tana dubawa taga number Deen ta kalli Samha tace “Deen ne kije gareshi ki shigo dashi" fita tayi iya kuma ta koma ɗakin Inna ta ɗauki awarwaronta ta saka tana fitowa suna shigowa idanunsa a kanta tayi saurin janye nata tana murmushi, ya sauke ajiyar zuciya ya shiga inda aka saukeshi bayan sun gaisa da Inna ya zauna itama ta shigo da sallamarta ya amsa idanunsa na kanta tana shirin zama ya riƙo hannunta tare da zaunar da ita a gabansa ya saki wata ajiyar zuciya me ƙarfi yace “Alhmdllh Fateemah ranar da za'a kaiki gidana irin wannan dressing ɗin zakiyimin wlh kin tashi kaina kin jiƙamin aiki ji nake dama abani dama yau ɗin nan!"
Cike da kunya ta zame hannunta ta zauna tana sunne kai kamar wata muminar gaske tace “Noor kasha hanya, ya gajiya" lumshe idanunsa yayi yace “Bangaji ba sai yanzu dai kike gajiyar Dani" Sosai sukayi masa sauka me kyau shayinsu na buzaye shine yafi komai burgeshi yasha shayi babu ƙarya a ƙarshe yake faɗa mata Sudan zai wucce ya dawo ya tarar Mom da Dad duka suna can daga can kuma zasuyi waya da ita a basu lokacin da zasuzo ayi komai a gama a tsayar musu da lokacin bikin.
Itadai batace masa komai ba haka Inna tace ta rakashi ya gaisa da uwayenta suna tafe cikin garin cike da shauƙin juna zuwa yanzu da gaske zuciyar Batul ta fara buɗewa a hankali ta fara koyawa kanta soyayyar Deen, yanda hadari ya lulluɓe sararin samaniya ya ƙarawa yinin masoyan armashi suna tafe suna hirarsu ta ƙauna har suka isa gidan me gari sukayi Sa'a yana zaune a faɗa shida yan uwansa suna ganinta suka washe baki Baffa Lame yace “Aa ta Manzo yanzu muke tamtamnawa akanki sai gaki dama ɗiyan halak yaƙi ambato kice baƙo kikayi daga birni" zama tayi cike da kunyar iyayen nata suka gaisa da Deen tayi ƙasa da kai sunason tayi masu bayani ita kuma kunya ta hanata.
Sai shine yayi ƙarfin halin gabatar da kansa sukayi shiru na lokaci kafin daga bisani Mal me gari yace “Ta Manzo bamu guri ko?" Cike da girmamawa da kunya ta tashi ta fice tana fita Suka haɗu da Almustapha a ƙofar fada yace “Yawwa amaryata dama yanzu nake shirin zakkuwa gareki ance kinyi baƙo daga Nigeria cikin ɗiyan iskan da sunka ɓata mani rayuwarki ko? To maza ki dakatar dashi zowa gareki ki hwaɗi masa niya ammijinki yanzu haka taɗi yaje gaba ga manya kinjiya"
Wani mugun kallo ta watsa masa tayi gaba abinta Zuciyarta na rawa ita kam bata yarda da wannan zama da akace Deen yayi ba to me zasu hwaɗi mashi da sai batta gurin?" Ji tayi an damƙi hannunta ta juya taga Mustapha ne yake mata wani kallo yana washe mata baki takaicin yanda yake mata kallon ne yasa batasan sanda da zuba masa wani mari ba, ta ja da baya da sauri tana huci idanunta ya kawo ruwa tace “Mustapha tun ranar da na shigo garin nan nasan akwai irinku da yawa marasa tarbiyya marasa ɗa'a kuma marasa manner ta furuci, don Allah kar mu ƙara gauraya dakai a gonata zan