AKWAI IRINSU COMPLETE BOOK BY OUM HAIRAN

Author :  Fauziyya Tasiu Umar Category :  Read Hausa Novels

Chapter   23 / 25

66K to 69K   out of 73.8K words

gabada rayuwarsu a haka sau dayawa takan fara aiki taji bacci ya kamata ta yanda bazata iya ƙarasawa ba hakanan zata kwanta lokuta da dama saidai idan ya shigo yayi murmushi ya gyara mata kwanciya ya sanya a ƙarasa mata ko ya ƙarasa.

Da wannan yace ya ɗauke mata girki ta daina saboda tsaron lafiyarta.

Bashi ba ita kanta bata kawo komai ba haka saida suka ɗauki tsayin watanni biyar wata rana Yayarsa Safiyyah tazo gidan dake bata ƙasar suka dawo tunda tazo Rafi'ah ta fito suka gaisa ta kishingide suna hira sai bacci ya tashi yana cewa Gimbiya sai haƙuri ƙanwar taki ciwon bacci ya sameta ba'a doguwar hira da ita" murmushi tayi tace.

“Ai dama ana samun irin haka wani laulayin kashe jiki da bacci yake sawa saidai fatan Allah ya inganta ya raba lafiya" fasa tafiya yayi ya zauna yace “Wai da gaske Gimbiya Sofsy cikine da Ƙurrah?" Kallonsa tayi da mamaki tace “Au kai nan baka fahimta ba kakeso kacemin Deeny matsayinka na likitan ƙasa da ƙasa kuma naji ance itama Pharmacy Dactor ce" zubawa Rafi'ah idanu yayi so yake ya fahimci abinda zuciyarsa take raya masa gaskiya ne ko ƙarya amma ya kasa hakanan ya miƙe yace “Na fahimci sauye² da yawa a jikinta da yanayin halittarta Gimbiya abinda yasa ban kawo cikina ke jikinta ba saboda tace tanashan wahala sosai amma bari yanzu nasa a bincika ta.

Duk abinda akeyi bata sani ba domin baccin nata da nauyi yake ɗaukarta.

Tashi tayi zaune yace “Unguwa zamu je yanzu zamu dawo" ƙara narkewa tayi tace “Unguwa Zaujh jannah Allah jikina duk a mace yake banjin ƙarfi" “Daure yanzu zamu dawo ba daɗewa zamuyi ba" tashi tayi dake dama da hijjab a jikinta Gimbiya Safiyyah tace “Ato nikam tafiya zanyi Allah ya inganta" sauketa sukayi a gidanta sannan suka wucce asibitin hoto yasa akayi mata abin mamakin da baitaɓa kawowa a yanzu ba Ƙurratul Ayn ɗinsa ciki gareta ya zarce watanni biyar ya shiga na shida tsabar farin ciki baisan sanda yayiwa Ubangiji sujjada ba yana zuba masa kirari tare da tasbihi gareshi buwayi gagara misali gwani Sarkin hikima ashe zai kuma jin irin wannan farin cikin da yaji a shekaru bakwai baya? Miƙewa yayi ya matsa inda take zaune ta kifa kanta a cinyarta yace.

“Na gode Ƙurrah kinga hikima ta Ubangiji ko zaki haifamin baby nima ina mutum zaiyi da rabon wani a hannunsa wannan rabon shi kadai ya isa hana kwanciyar hankali...."

Maganarsa ce ta katse lokacin daya ɗago fuskarta yaga yanda take hawaye kuka da gaske ya shiga mugun mamaki da tashin hankali tare da tunanin dalilin kukan nata yace “Innanillahi Ƙurrah me nayi miki" zamewa tayi ta kwanta a jikinsa ta rungumeshi tana shassheƙar kuka tace “Zaujh Jann ciki fah yanzu kaima saika fara wulaƙantani da juyamin baya akan hakan...."

Rufe mata baki yayi ya sakar mata murmushin ƙarfafa gwiwa yayi kissing nata yace “Allah ya kasheni kafin zuwan wannan rana da zanyi butulci ga kyautar da banida ikon yiwa kaina Ƙurrah mafi alkhairin duniya samun mata ta ƙwarai ta haifa maka ƴaƴa nagartattu ku basu tarbiyyar addini ta yanda ko bayan ranka zasu kasance masu yi maka addu'a yana cikin ayyukan ɗan adam masu gudana ko bayan baya numfashi, don Allah Ƙurrah ki daina munanamin zato ko iya zaman nan namu na wata takwas ya kamata ki fahimci suna ne kawai mukayi tarayya da tsohon mijinki wato maza amma kowa halinsa daban Ni inason yara sosai Ƙurrah don Allah kiyita haifamin masu kama dake kinji"

_*Oum Hairan*_

[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU....*_

_*Oum Hairan*_

_Paid book via acct 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank proof of pay 09013718241_

Shafa bayanta yaci gaba dayi har saida tayi shiru sannan ya fita ya ɗauko musu magunguna suka tafi gida suna zuwa gida ta zube a kujera tace “wlh bacci nakeji" murmushi yayi yace “Ki kwanta kiyita bacci daganan har ranar da babyna zai buƙaci zuwa duniya bakida matsala kinji" lumshe idonta tayi ya shiga kitchen ya haɗo mata tea me kauri domin ya daɗe da fahimtar shi takeso dakansa ya rinƙa bata Saida tasha isasshe sannan ya fita ita kuma ta kama baccinta.

Daƙyar take tashi tayi sallah ta koma dake ta samu daurin gindi tun kafin yasan matsalarta ya hanata komi saida ya shigo bayan Isha ya ɗagata cak tun shigowarsa tajisa bata buɗe idanunta ba sai bayan ta sanya hannu ta saƙalo wuyansa ta sauke masa wani mayen kiss ta fara lasar wuyansa tana shafa ƙirjinsa cikin Muryar raɗa tace “Yau kayi dare Zaujh Jann ina ka shiga" sauketa yayi a gadon yabita ya danne yana lalubar bakinta ta riƙeshi tare da kanne masa ido tace “Aa Zaujh muje kayi wanka ka huta mana" noƙe kafaɗa yayi yana kama fatun kunnenta ya fara lasa.

Lumshe idonta tayi tana karɓar saƙon nasa saida ya gama abinda zaiyi tana tayashi sannan sukayi wanka tare duk jikinta yayi laushi daƙyar ta ciyar dashi yanacin abincin yana zubanta santi tare da bata labarin yanda suka kwashe da Ammy lokacin dayaje don sanar da ita alkhairin daya sameshi sosai bataji daɗin irin abinda yace tayi masa ba duk da cewa abubuwa da yawa baya sanar da ita abu ɗaya daya sani kawai ya kangeta daga zuwa wajen Ammy ko gidan sukaje baya barta ta daɗe zaice ta tashi su tafi amma a ɓangaren Gimbiyar Dutse yakan barta ta jima sosai.

Yaso fahimtar ta damu da abinda ya sanar da ita saidai tafisa dabara ganin yana shirin ganota ta hanyar tambayoyinsa yasata riƙe ciki tana cewa “Ahhh Zaujh marata" yowa kanta yayi da sauri yana tambayarta meye damuwar me i sameta da wannan ta mantar dashi wancan sanadin ganin ya damu ta ware sukaci gaba da harkokinsu.

Kwanci tashi saiga cikinta ya shiga wata na tara tun watanni bakwai ya gano abinda ke cikinta ba ɗaya bane ya shiga tsananin farin ciki yayiwa Allah cikakkiyar godiya da tasbihi sukaci gaba da rainonsa har kawo yanzu da lokacin haihuwa ya matso basu taɓa samun matsala dashi ba kullum yana ƙoƙarin ganin yayi abinda zai sanyata a farin ciki ne sosai ta saki jiki dashi suke rayuwarsu me armashi da kulawa.

Yau juma'a misalin biyu da rabi na dare bayan sunyi al'amuransu sun gama bacci ya gagaresu ciwo kamar bazata kai labari ba tun farkon ciwon yaso su tafi asibiti amma fir taƙi yarda ce masa takeyi zaiyi sauki yaƙi ganin sauƙin a ƙarshe babu shawara ya rakiceta suka tafi asibitin ita ke ciwon shine da azabar don yafita shiga tashin hankali gani yake itama tafiya zatayi ta barshi kamar yanda Rahana ta tafi ta barshi da wannan ya shiga office ɗinsa yayi wasu cike² ya fito daidai lokacin da Gimbiyar Dutse tazo asibitin yake faɗa mata Gimbiya ina ganin aiki kawai zaayiwa Ƙurrah" kallonsa tayi da sauri tace “Akanmi Deeny dama bata haihuwa da kanta ne?" Sharce gumi yayi yace “Haihuwarta ta farko ta bani labarin da tazo da irin wannan jinkirin Cs akayi mata Gimbiya ina tsoron kar itama ta tafi ta barni...."

Fitowar wata nurse ce ta katse masa zancen da cewa “Yallaɓai ta sauka yaranta biyu duk maza" bata gama rufe baki ba tuni shi ya shiga ɗakin ya isa inda take kwance tana mayar da numfashin wahala ya shafa kanta tare da sunkuya yayi kissing goshinta yace “Say alhmdllh Ƙurrah" lumshe idonta tayi wahalar da tasha bata sata jin ɗigo na haushin mijinta ba saima wata sabuwar ƙaunarsa da taji tana mamaye duk wata kusurwa ta jikinta cikin kasalar harshe tace.

“Alhamdulillahi bi ni'imatihi tatimussaliha Zaujh Jann na gode" kama hannunta yayi ya matsa ga yaran suna kwance sai tsotsar hannunsu sukeyi babu wanda yayi kama da ita duka dashi suke kama ƴaƴan buzaye kamar ɗiyan larabawa murmushi yayi yace “Duka nawa ne Ƙurrah?" Gimbiyar Dutse ce data shigo yanzu tace “Aa nawa ne Deeny" Murmushi yayi yana shafa sumarsa yace “Gani nakeyi kamar mafalki Gimbiya" lakace masa hanci tayi tace “Kyautar Allah kenan Deeny ka rasa ɗaya kayi da matarka yanzu ga biyu da matarka an baka" ajiyar zuciya ya sauke tare suka gyara yaran suka shiryasu cikin kayan sanyi suka kwantar dasu Gimbiyar Dutse ta haɗa mata ruwa ta taimaka mata ta gyara jikinta tana fitowa kiran Daddy ya shigo wayarta daƙyar ta ɗaga saboda jirin da takeyi kasantuwar ta zubar da jini sosai ta kara a kunnenta tace “Daddyna" dariya yayi sosai yace “Ina sabbin ƴan Niger?" Murmushi tayi tace “Aa ƴan Nigeria dai ko Daddy"

“Haba yarinya Nigeria da larabawa ne ai saidai Niger ɗin wadannan kyawawan yara haka masha Allah Ubangiji ya ɗorar da lafiya ya bada lafiyar shayarwa ki kula da shan magani sosai Deeny yace kinsha wahala har jini ma da zasu sanya miki shine ya hana saboda gudun matsala"

Godiya tayi masa sukayi sallama ta juya ta kalli Deeny da yaketa juya shayi ya diba a cokali yakai mata bakinta ta karbi cup ɗin tace “Yunwa nakeji Zaujh" saida ta shanye tea ɗin ya duba drip na hannunta yace “Sunci kinyi tear sunyi miki ɗinki ko?" Jinjina kai tayi yace “Ok"

Kwana sukayi a asibitin sai da safe suka tafi gida ƙarfe tara kuwa saiga Mommy da Munirah wannan haihuwar ta zamo mata daban da sauran haihuwarta uku mijinta na tattalinta da kulawa da ita ga mahaifiyarta tare da ita sannan ga ƴaƴanta ababen so ga kowa, kwana ɗaya Mommy taso tayi a gidan taga jikokin ta amma fir Deeny ya hanasu tafiya saida akayi suna saiga Mommy harda gayyatar danginta daga Gombe sukazo suna ƙanwarta da matar yayanta daga Maiduguri ma dangin Daddy sun zo harda Hajiya Nuratu tayita santin yaran tana yabawa da kulawar da Deeny yakewa Rafi'ah “Yanzu kikayi aure Rafi'ah" ta faɗi haka yafi a ƙirga da dare ne da suka keɓe take tambayarta ina su Ablah da Hisham tayi murmushi tace “Hisham Yana United state of America yana karatu Ablah kuma tana gurina ya haƙura ya sallamata da yaga Allah ba wasa ba, kinsan yayi aure matar tace bazata iya zama da ƴaƴansa ba shine ya saketa ya kawo Ablah garemu yaci gaba da zamansa haka"

Bataji daɗin labarin ba ta rasa ya zatayi ta cire lissafin Abdulƙadir cikin rayuwarta shi mutum ne da baya ciruwa a zuciya duk da cewa tasan mijinta yafi kowanne namiji dacewa da zama abokin rayuwarta kuma zaɓinsa alkhairi ne gareta miji ɗaya tamkar da billions samun irinsa a wannan zamanin da maza suka cika da son kansu sai an tona zata zauna dashi ta rayu dashi da gaske da zuciya guda dan yafi kowa cancanta kuma zataci gaba da koyawa zuciyarta sonsa domin yafi dacewa data soshi.

Ranar suna yaran sukaci suna Jamil da Jalal akasha taron suna aka watse kowa ya kama gabansa kwanaki uku dayin suna Deeny ya tafi Canada ya kasance daga ita sai bayin dake hidima a ɓangaren dake duk abinda akace yaji akwai baya zama damuwa idan aka ɗauki yaran aka kai su gurin Gimbiyar Dutse saita manta ma tana da ƙananan yara suke dawowa kullum sukan kasance a chat suna hira soyayyarsa sannu a hankali mamayarta takeyi kafin ta ankara ya jima da huda zuciyarta sannu a hankali har ya cire mata kowa a ranta ita da kanta take ganin wautarta da tayi garajen zaɓi ashe rabon yin ilimi ne gareta tabbas yanzu takejin ta samu abokin rayuwar da bazata iya sakacin ya suɓce mata ba zata riritashi kamar ƙwai zata darajashi fiye da dutse diamond domin duk wani matsayi shiɗin a samansa yake.

Kwanaki sukayita tafiya saida yaranta sukayi watanni biyu sannan ya dawo a Nigeria ya ishesu tunda sukazo yawon arba'in yace tayi zamanta a gidansa na nan kawai basai ta koma ba domin shi kawai yafison zamanta a Abuja, can yaje ya samesu yayi wata guda yace tare zasu koma batayi masa gardama ba domin itama tafison rayuwa kusa dashi suka ɗaga zuwa Canada sukaci gabada rayuwarsu a can cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Ƴan Hausa sukace tafiya sannu sannu kwana nesa shekara kwana sai gashi ta samu shekara goma tare da Deeny lokacin yaransu huɗu Jamal Jalal Hameed da Hameedah suna rayuwarsu cikin soyayya da kulawa wata rashin lafiya da Mai martaba yayi ne yasasu komawa Niger urgent har lokacin Kilishi basa wani ga maciji da Rafi'ah ko guri ɗaya basa zama abin na damunta saidai ta kasa magance matsalar ta rasa meye yasa da surukarta da yan'uwan mijinta da suke daki daya duka basa ƙaunarta Gimbiya Safiyyah ce kawai Zakka a cikinsu itane kawai suke ɗasawa.

Abinda yake bata mamaki ko ganin waɗannan yaran da suke tsakaninta da Deeny sai takega ya kamata koma meye a ransu ya wucce su ɗauketa matsayin tasu domin ko bata tare da Deeny sun riga sun haɗu haihuwa huɗu ba wasa ba.

Watanninsu biyar a Niger wannan karon saida tayi ziyara sosai har Maiduguri sukaje ganin yaranta sunyi murna da ganinta musamman Ablah dake mace kamarta da mahaifiyarta ta fita sosai shikam Hisham sak ubansa ne hutu yazo kwanansa ɗaya da dawowa haka sukayita shige mata Hisham ya ɗebi ƙannensa suka fita sun jima sosai dake ya girma sosai shekara sha tara.

Gidan Daddynsu ya nufa da yaran ya tarar dashi kwance a parlour yana danna waya yana ganinsa ya tashi zaune yace “Son, wow! Masha Allah ina ka samo yaran larabawa?" Zama yayi yace “Ƙannanmu ne Daddy Mommyn mu ce yau ta kawo mana ziyara kamo hannun yaran yayi zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yace “Rafi'ah ce tazo ganinku Hisham itan yanzu tana ina?".....



_*Oum Hairan*_

[11/21, 11:41 AM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU....*_

_*Oum Hairan*_

_Me son complete book One 300 via acct 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank proof of pay 09013718241_

*End book One*

_Don Allah karku zargeni da son kai cikin wannan littafin babu wani abu dana canza yanda labarin yake haka yake tafiya rashin lokaci ne yasa yake tafiyar hawainiya._

_Sannan dayawa suna cemin to meye yayi saura Rafi'ah ta auri Deeny har sun haifi yara biyar kuma nace akwai part 2 na labarin to ku sani wannan labarin yanada faɗi zan iya gajarce shi kuma zan iya tafiyar dashi yanda yake duk wanda kuka zaɓa shi zanyi muku, in kunce na gajarceshi shikenan in kuma in tafi dashi yanda yake ne to zaku ƙara payment 300, sannan wannan karon bazanci gaba da VIP ba zan tafi dashi single ne course zanyi wani uzuri shima me cin lokaci kuma shima aikin ƙwaƙwalwa ne,_



_*35*_

Zama yaron yayi yace “Tana gida naji tana anan zata kwana gobe zata wuce Dubai ne" jinjina kai yayi can yace “Ok" daga haka ya koma ya kwanta yana mawa Hameed da Hameedah wasa sune ƙananu don haka dasu ta taho a ransa yana raya wai Rafi'ansa ce ta auri wani bashi ba har ta haifa masa waɗannan kyawawan yaran kuma bayan wadannan ma da wasu?

Zuciyarsa yaji tana neman karyewa ya tashi ya shiga ɗakinsa ya zura kayansa ya fito yana cewa da Hisham “Son kaje gida zan kawosu in mun dawo daga shopping" tsalle Hameedah ta fara tace “Daddy harda sweet zaka suyi mana" murmushi yayi yanajin a ransa dama shine ya saka ƙwan ta ƙyanƙyashe masa yaransa sun girma yana buƙatar ƙari gashi ita tanada shida shi kuwa ya maƙale a biyu.

Fita sukayi ya yawata da yaran ya kuma haɗo musu shop sannan ya wucce dasu gidan lokacin da yaje akace batanan mijinta yazo sun tafi amma akwai driver da zaizo ya ɗauki yaran, zama yayi suna ɗan taɓa hira da Ya Hajja nan ta shiga yi masa nasiha akan aure yaja fasali yace “Hankalina ya koma kansa Zanyi Ya Hajja na rasa irin macen da nakeso ne wlh" murmushi tayi tace bazaka samu wacce zatayi maka daidai da wacce kake hange ba Audu ba'a ɓari a kwashe duka" miƙewa yayi kullum haka take faɗa masa kalamin kashe gwiwa shikam ya haƙura da lissafa waiwayowar Rafi'ah rayuwarsa zai rayu yanda Allah ya tsara masa.

Wani gurin cin abinci ya nufa ya zauna ba don cin abincin ba saidon samun nutsuwar zuciyarsa kawai

Hawayen daya zubo a idanunsa ya ɗauke zahiri Rafi'ah rayuwarsa ce ya kasa samun madadinta tun yana lissafa yini ya koma kwana ya koma wata yanzu shekaru yake lissafawa suma kuma sun fara nauyi alama ta bayyana masa haƙuri da cire matar wani a ransa shine yafi masa alkhairi.

Wayarsa ya ɗauka ya daga kiran Abdallah yace “Mutumin ashe Gimbiya Rafi'ah ta shigo ganin ƴaƴanta wlh yanzu sukazo gidana da mijinta kaga yanda ta zama babbar mace..." Katse shi yayi da cewa “Kana ina kenan Abdallah inason a nemomin mata wlh zan zauce in ban samu me kula dani ba" dariya yayi yace “ya za'ayi na nemo maka mata Abdulƙadir ka aura da kanka ma ka kun kasa fahimtar juna..." Just please Abdallah na shiryu rashin Rayuwata ya bani darasi ta kasa barin raina ita kuma tana rayuwarta da mijinta da yaranta cikin kwanciyar hankali.

Jinjina kai Abdallah yayi yace “Ok kayi addu'a Allah zai baka mafita" godiya yayi sukayi sallama ya tashi da niyyar barin gurin daidai inda zai shiga mota yaga wata arniyar Jeep ta parker ya wani Balarabe ya fito riƙe da jakar mata a hannunsa ya xaga ya bude ɗaya ƙofar wata matashiyar Hajiya ce ta fito da cikinta tsoho idanun Abdulƙadir ya sauka a kanta itama shiɗin take kallo zuciyarsu ta buga da ƙarfi daidai lokacin da Deeny ya kamota yana zuba mata sannu yana cewa “Kinsan dake keɗin ta musamman ce yanzu ma twins zaki yimin Kinga haihuwa uku yara shida ko?" Inda take kallo ya kalla ganin wanda ke tsaye a wajen yasashi sakinta ya taka daidai lokacin da Abdulƙadir ya sauke wata ajiyar zuciya baitaɓa ganin dacewa irin ta Gwanar tasa da mijin nata ba lallai

23 / 25