GOGA SHA FAMA CIGABAN SARKIN SADAUKI BY MANSUR SUFI.txt

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Arewa Pen

Chapter   6 / 8

15K to 18K   out of 23.1K words

Hibairu ya samu nasara ne akan jaruma Amirat,
Sai dai inda kizo ke saƙar shi ne don HUBAIRU ya samu nasara akan Amirat to lalle bane yakai ga nasara akan sauran jaruman,
Wani ɓangare a zuciyar kuma a zuciyar sa kuma yace dashi kada ka manta cewa nasara da Sa'a a jinin Hibairu take haƙiƙa sai ya samu nasara a wannan gasa,
Domin a halin yanzu babu gwarzon mayaƙi kamar shi a faɗin duniya,
Koda sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin sa sai ya bushe da dariyar farin ciki,
Al'amarin da ya sanya sarki shuraih dake zaune daf dashi ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA,
ya dubi Baddadul-ulƙas da wani irin kallo mai ɗauke da alamar tamabaya,
A bangaren mai girma shaibat kuwa ya zuba idanu ya kallon yadda gasar ke gudana,
Zuciyar sa na dukan uku-uku,
Domin yana ganin cewa haƙiƙa koda yar sa gimbiya haya'ul-nur ta samu nasara gimbiya Rumaisat bai zama tilas ta samu nasara akan Hibairu ɗan Barde Shabbaru ba,
Abangaren teburin alƙalan gasa, al'marin sarkin yaƙi abu-Damraz kuwa ana fara wannan fafatawa tsananin jaruman sai hankalin sa ya dugunzuma ainun ya kasa samun nutsuwa, domin a halin yanzu yana cikin tsaka mai wuya,
Idan sarkin sadaukai Hibairu ya cinye wannan gasa,
Gimbiya haya'ul-nur ta faɗi, dai dai yake da ya rasa rayuwar sa,
A Ɓangaren dabbobin dajin da suka yi Hibairu rakiya izuwa Filin gasa,
Sa'adda suka ga yadda shugaban su Hibairu ya kacame da azababban yaƙi da jaruma Amirat sai suka dunga yin gurnani suna hargagi,
Dake nuna fatan nasara ga sarkin sadaukai Hibairu,
Nan fa mamaki Yakamata jama'ar dake filin gasar bisa ganin yadda dabbobin ke nuna alamun fatan alkairi ga Hibairu,
Abin tambaya anan shine mene ne alaƙar HUBAIRU da waɗannan miyagun dabbobi,
Me ne ne alaƙar dake tsakanin HUBAIRU da Barde Shabbaru tabbas a yadda alamu suka nuna lokacin da aka ambaci sunayen jaruman ya tabbatar dace wa Hibairu ɗan Barde Shabbaru.
Tabbas kyan ɗa ya gaji uban sa,. Nanfa jama'a suka dunga yiwa gwanayen su jinjina,
Amma sai ya zamana fiye da rabin jama'a hubairu suke ɗagawa hannu suna yi masa kirari, masu wake nayi masu shewa nayi.
Nan fa zuciyar sarki shaibat ta kama tafarfasa tamkar zasu ƙone,
Bisa ganin yadda jama'a ke nuna goyon baya ga Hibairu,
A tsakiyar filin gasar kuwa jaruman sun wanzu suna kaiwa junan su sara da suka cikin ɓakin zafin nama juriya da jarumtaka irin ta JARUMAN DUNIYA,
Duk wanda ya gaɓzawa ɗan uwan sa nashi sai kaga shi ma ya mayar da martani Cikin zafin nama tamkar suna casar hatsi.
Kai kace wata na'ura ce ke sarrafa su ba da jini da tsoka ke gudana a jikkunan su ba.
Lokacin da zaratan Jaruman gasar GOGA SHA FAMA suka wanzu suna kaiwa Juna naushi da bugu cikin matukar zafin nama juriya da jarumtaka ta gaban kwatance,
Sai aka shafe tsawon daƙiƙa arba'in ana wannan fafatawa babu sassauci,
Nan fa wani abun mamaki ya fara wakana,
Domin bangarorin jaruman ana samu ragas ma'ana karfi yazo ɗaya,
Duk sa'adda ɗayan su ya gaɓzawa abokin faɗa sa naushi sai kaga ya shanye dukan,
Shi ma ya taƙarkare ya mayar da martani Cikin gwanin ta da zafin nama.
Nan fa jama'a suka shiga yin shewa da tafi bisa ganin cewa har yanzu babu alamun nasara ga dukkan bangarorin jaruman,
Wannan fa shine abinda masu iya magana ke cewa kyan faɗa akwana ana yi.
A ɓangaren Jarumi Hibairu da jaruma Amirat kuwa sun wanzu suna bawa hammata iska,
Suna kai wa juna hari ta ƙasa da sama,
Wasu lokutan har daka tsalle sama suna kaiwa juna harin.
Lokacin da Hibairu sarkin sadaukai yaga cewa an shafe tsawon Sa'a sittin batare da ya samu nasarar kai Amirat ƙasa ba,
Sai ya cika da matukar al'ajabi da mamaki, kuma hankalinshi ya dugunzuma ainun,
Abin da ya bashi mamaki shine yadda akayi ya kasa samun nasara akan Amirat bayan cewa a zahiri ya nunka a karfin damtse da ƙirar jarumtaka,
Abin da Ya  dugunzuma hankalin sa kuwa shine matsawar ya faɗi wannan gasa shi kenan bazai taɓa samun nasarar fansar rayuwar mahaifinshi daga hannun sarki Baddadul-ulƙas ba,
Sa'adda sarkin sadaukai yazo dai-dai nan  sai kawai ya sake zage damtse yana cigaba da kaiwa Amirat naushi da bugu da wani irin salo na musamman.
A ɓangaren gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih kuwa
Labari yasha bambam domin sun fara haɗawa junan su jini da majina suna  rangaji jiri na ɗibar su amma saboda juriya da bajinta irin ta JARUMAN DUNIYA sai suka ƙi yarda su faɗi ƙasa,
Su ka cigaba da faɗan a haka kawai,
Abangaren sadauki lazwas ibn shaslam da Jarumi nazwar kuwa,
Sun tara zufa sun jiƙe sharkaf saboda yadda suke naushi da bugun juna cikin gwaninta da salon yaƙi mai matukar kwarjini,
Domin idan lazwas ya gabzawa nazwar naushi a fuska ya kife ƙasa,
Sai ya ɗan huta na yan daƙiƙa sannan ya taso sama ya mayar da martani,
Lokacin da Sa'a ɗaya ta cika  da fara wannan artabu sai salon yaƙin ya canza salo,
Kasancewar rana tayi tsananin zafi ainun sai sadaukan suka fara galabaitar da juna,
Ana cikin wannan artabu ne sadauki lazwas ya kaiwa jarumi nazwar naushi a wuya a lokacin da shi ma yakai mishi  harin a kirji,
Cikin nasara kowanne su ya samu nasarar samun ɗan uwan sa nan take suka kurma wawan ihu suka sulale ƙasa 
Babu alamun rai a tare dasu, 
Al'amarin da ya sanya fadar ta kaure  da shewa da tafi kenan kuma ya dugunzuma hankalin attajiran da su ke ɗauke da alhakin sanya jaruman a cikin gasar  
Shin yanzu jaruman nasu sun rasa rayukansu ne ko kuwa doguwar suma su kayi
Cikin hanzari waɗansu zaratan dakaru suka shigo filin Ɗauke da keken doki suka ɗauki jaruman biyu suka ɗora su akai,
Suka fice daga filin gasar domin basu taimakon gaggawa a ceto rayuwar su,
Ana cikin wannan fafatawa sarkin sadaukai Hibairu tare da jaruma Amirat suka kaiwa juna naushi a fuska,
A lokacin da suka Daka tsalle izuwa sama,
Cikin Sa'a kowanne ya gabzawa ɗan uwan sa naushi a fuska,
Take suka hantsilo suka rikoto ƙasa, amma saboda gwanin ta kafin su kai ƙasan sai kowanne su ya ware kafafunsa biyu ya turje a cikin ƙasa,
Sannan suka kaiwa juna karo da kawunan su jika ke gau,
Amma a wannan karon sai suka kife a ƙasa suna haki tamkar waɗansu zakaru,
Koda ganin irin gwanintar da sadaukan ke yi sai filin fadar ya kaure da shewa da jinjina haɗe da ihu,
Al'amarin gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat kuwa,
An cigaba da yin kare jini biri jini babu alamu dake nuna cewa ga gwanar dake da nasara a cikin su,
Lokacin da alƙalan gasa suka cewa an shafe tsawon Sa'a uku ana wannan artabu babu alamun nasara ga dukkan bangarorin sai wannan badakare daya busa ƙahon yaƙi ya sake ɗauko wannan ƙaho ya busa da karfi,
Take kowanne jarumi yaja ya tsaya cak yana haki da hararar abokin gwamin sa.
Sarkin yaƙi abu-Damraz ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu yayi gyaran murya ya fuskanci jama'a yace"yaku mahalarta wannan gasa mai albarka kuyi sani cewa duba da yadda har sa'o'i uku suka shuɗe babu alamun nasara ga dukkan bangarorin,
Bisa tsarin wannan gasa za'a tafi hutu na rabin Sa'a domin jarumai su sake kimtsa wa suyi sabon shiri domin yin karon batta ta biyu wacce a cikin ta ne muke sa ran za'a ƙarƙare wannan gasa domin fitar da gwarzon mayaƙi,
Koda jin wannan jawabi daga bakin Sarkin yaƙi abu-Damraz sai fadar ta sake ruɗewa da shewa cikin Hanzari  dukkan jaruman huɗu suka fice daga filin gasar,
Kai tsaye sarki Baddadul-ulƙas ya sanya hadiamn sa suka shiga duba lafiyar jarumi Hibairu domin ya samu wartsakewa kafin a koma zagayen gasa ta biyu,
Shi kuwa sarki shuraih cikin tashin hankali ya tari yarsa gimbiya Rumaisat tare da duba halin da take ciki koda yaga cewa ta galabaita ainun  sai hankalinsa ya dugunzuma ya umarci wadansu kwararrun likitoci suka shiga duba lafiyar ta,
Abangaren mai girma shaibat kuwa da kansa ya a shiga gasawa yarsa gimbiya haya'ul-nur fuskan ta ta ruwan ɗumi domin kumburin dake fuskantar ya sabe,
Sakamakon jinin da ya taru a fuskar saboda naushin da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih tayi mata,
Kuma duk bayan daƙiƙa uku ya tambaye ta shin ya a bar alfaharina a wane hali kike jin jikin ki yana sauƙi kuwa,
Al'amarin jaruma nihla, sunaila, Hizmal,yaro Humair makaho, sarauniya Abidatul-auliya, Nuwairat da matsafi shubairu kuwa,
Lokacin da suka ga yadda sarkin sadaukai Hibairu ya jigata ainun,
Sai hankulan suka dugunzuma ainun, suka  dunga kai komo a  bakin ɗakin da ake duba lafiyar Hibairu.
Kamar yadda sarkin yaƙi abu-Damraz ya faɗa haka al'amarin yakasance,
Wato rabin Sa'a na kammala cika sai dukkan jaruman gasa gami da sauran jama'a suka sake hallara a karo na biyu,
A lokaci guda jaruman gasa suka shiga izuwa Filin fama suna masu zagaye juna,
Amma a wannan karon babu jarumai biyu, wato sadauki lazwas da jarumi shazwas,
Har a wannan lokaci fuskar jaruma Amirat na sanye cikin rawani idanuwan ta kaɗai ake gani,
Koda ganin cewa Jaruman suna shirin fafatawa,
Sai wannan badakare ya sake ɗauko wannan gabgegen ƙaho ya kafa a bakinshi ya busa da karfi
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan babu ƙasa nanne ake gardamar kokawa.
Kuma ranar  bikin sarakai  babu e fitowa ya taka rawa face wacce da wane,
Kafin sautin ƙahon ya kammala mamaye fadar 
Sarkin sadaukai Hibairu yayi ɗauki izuwa kan jaruma Amirat,
Gimbiya haya'ul-nur kuwa ya ruga izuwa kan gimbiya Rumaisat,
Su dukan ukun suna ihu da kururuwa mai firgitar wa,
Jaruma Amirat na ambaton sunayen Ubangiji a cikin ran ta,
Lokacin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban sha'awa,
Jaruman huɗu suka wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa,
Cikin matukar zafin nama juriya da jarumtaka irin ta zaratan Jarumai
Nan fa ƙura ta turnuƙe, sautin naushi da ihun mazaje ya cika filin baki ɗaya
Ana fara wannan artabu ne wani abin mamaki ya fara gudana domin kuwa a wannan karon jarumi Hibairu da jaruma Amirat na tashi izuwa sararin samaniya suna yaƙar junan su,
Tamkar sun kasance masu fuka-fukai,
Nan fa filin gasar ya ruɗe da shewa masoyan Hibairu da jaruma Amirat nayi musu tafi,ihu da jinjina,
Al'amarin da ya harzuƙa zuciyar mai girma shaibat kenan,
Zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata faso kirjinshi ta fito waje,
Ya dubi Sarkin matsafan masarauta yace dashi a cikin raɗa a fusace "shin mene ne amfanin alƙalancin da aka baku,
Shin bakwa ganin anyi amfani da karfin sihirin tsafi ga wadancan jarumai biyu,
Koda jin wannan tuhuma sai sarkin matsafa ya risina ya dubi sarki cikin ladabi da girmamawa yace"ya shugabana ai tuni dukkan tawagar alƙalanci sun gudanar da bincike bisa abinda ke wakana tsakanin jarumi Hibairu da jaruma Amirat,
Kuka kuma abin da  Binciken ya tabbatar mana cewa sam wannan tashin saman da suke yi babu aikin sihiri a cikin shi.
Ni kaina al'marin ya firgita ni kuma ya ɗimauta domin ko da a tarihi ban taɓa ganin wanda yayi wannnan aikin almara ba batare da yayi amfani da sihiri ba,
Sai dai irin mutanen nan da ake wa lakabi da ma'abota addinin Musulunci,
Ka da jin wannan bayani daga bakin Sarkin matsafa,
Sai takaici ya sake turnuƙe sarki shaibat yaji tamkar ya zare takobin sa ya afkawa hubairu sarkin sadaukai ya hallaka shi,
Kuma ya tambayi kanshi a cikin ranshi yana mai cewa 
Shin tsakanin HUBAIRU da Amirat wane ne yakasance ma'abocin addinin musulunci?
Amma kuma yadda sunan ya nuna Amirat suna ne Musulmi,
Amma shi hubairu ya ƙarbi addinin ne ko kuwa,
Taya ya yake yin wannan abin bajinta batare da yayi amfani da sihiri ba,
Haƙiƙa idan har ɗaya daga cikin su yakasance
Musulmi abune mai matukar wahala bazasu samu nasarar lashe wannan gasa ba,
Koda ya sake zuwa Nan a  tunaninshi sai yaji tamkar ya kwala ihu 
Abangaren sarki Baddadul-ulƙas kuwa sa'adda yaga yadda jaruma Amirat take yaƙar hubairu cikin gwanin ta da kwarewar yaƙi,
Kuma babu alamun dake nuna cewa HUBAIRU zai samu nasara akan ta.
Sai hankalin sa ya dugunzuma ainun kuma ya fusata 
Abinda ya dugunzuma hankalin shi shi ne yadda  alamu ke nuna cewa abu ne mai matukar wahala hubairu ya lashe wannan gasar jarumtaka,
Shin ko kuwa hubairu baya tare da zoben sihirin sa ne,
Abin da ya fusata shi shine shin wace wannan boyayyen jaruma Amirat dake ƙoƙarin ganin ta tozarta shi,
A wannan gasa ta sanya yayi muguwar asarar dukiya mai tarin yawa wacce  ban taɓa yin kamar ta ba.
Me ne ne dalilin daya sanya halarar tsafi na bata bayyana mini jaruma Amirat ba,
Haƙiƙa matsawar jaruma Amirat ta lashe wannan gasa sai na  shafe Birnin su daga doran ƙasa koda kuwa kiyashin birnin su bazan bari a raye ba.
Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunaninshi sai ya sake murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA.
A binda sarki shaibat da sauran jama'a basu sani ba shine 
Bakomai yasanya Amirat take samun nasarar tashi sama batare da fuska fukai ba.
Sai domin ta na yin hakan ne bisa iko da karfin buwayar Ubangiji
Shi kuwa  jarumi Hibairu yana samun nasarar tashi saman ne bisa sirrin tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN sa,
Abinda yasanya alƙalan gasar basu gane sihirin tsafin ba,
Sai domin bisa tsarin sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN sune makarin dukkan sirrikan tsafin duniya,
Duk wani sirrin tsafi da ya haɗu da na jikin ZOBEN SHIRIN 
Sai ya lalata sirrikan tsafin gaba ɗaya koda kuwa sun kai guda miliyan guda,
A tsakiyar filin fama kuwa an cigaba da yin ɗauki ba daɗi,
Jaruman sun wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu cikin matukar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance,
Ana cikin wannan fafatawa ne Hibairu da jaruma Amirat suka kaiwa juna wawan naushi a ciki,
A lokaci guda bisa Sa'a sai kowannen su ya samu ɗan uwan sa nan take su duka biyun suka sulale ƙasa,
Babu alamun rai a tare dasu har idanuwan su sun fara ƙafewa.
Lokacin da jama'a suka ga halin da manyan gwanayen biyun ke ciki,
Sai hankulan su suka dugunzuma ainun.
Har wasu daga cikinsu suka fara zubar da hawayen baƙin ciki.
Domin fargabar kada ace gwanayen su sun rasa rayukansu a wannan gumurzu.
A wannan karon ne gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat suka baje a ƙasa suna haki, gami da hararar juna tamkar waɗansu zakaru,
Abangaren tawagar sarki Baddadul-ulƙas kuwa,
Wato dukkan sarakuna da jaruman da sukayi masa rakiya su ka ga halin da gwanin su SARKIN SADAUKAI Hibairu ke ciki sai kwallar takaici ta  
A dai dai wannan lokaci shugaban alƙalan gasa wato sarkin yaƙi abu-Damraz ya lura cewa lokacin da aka ɗibarwa gasar ya kusa ƙarewa gashi babu alamun nasara ga dukkan bangarorin,
Sai kawai ya miƙe tsaye tsam daga kan karagar sa da nufin yace wani abu sai kawai ya jiyo gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat daga filin gasar,
Ai kuwa yana dubawa sai ya ga ashe dukkan su san sake zubewa ƙasa ne babu alamun nasara,
Daga can sai kawai akaga HUBAIRU da Amirat sun miƙe tsaye zumbur tamkar haɗin baki gami da kaiwa juna bugu da naushi,
Tamkar babu wani abu da ya sameshi,
Koda ganin hakan sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka ruɗe da shewar murna.
Jaruma nihla masoyiyar hubairu bata san sa'adda ta miƙe tsaye ba ta kama yiwa masoyin ta jinjina,
Sarki Baddadul-ulƙas da dukkan tawagar murna ce ta kama su ainun,
Ana fara wannan sabon artabu ne sai Hibairu ya shiga ambaton waɗannan kalmomi da yaji ameerat na ambata a duk lokacin da suka fara gumurzu wato Allahu Akbar!
Domin ya tabbatar dacewa tunda har nasara da jarumtakarsa bata sanya yayi galaba akan Amirat ba,
To lallai kalmomin da amirat ke amfani dasu zasu iya bashi nasara,
Domin dai ya samu nasara akan Amirat ɗin,
Amma wani abu daya fahimta shine tabbas jaruma Amirat Bata niyyar taga ta cinye shi a wannan gasa,
Domin sau arba'in tana samun damar da zata illatashi kada yayi nasara amma taƙi aiwatar da hakan,
Faruwar hakan keda wuya sai hubairu yaga cewa a halin yanzu yana samun nasarar kai Amirat ƙasa,
Har takai bata iya mayar da martani, ana cikin wannan hali ne hubairu ya shammaci ta ya gabza mata wawan naushi a gadon bayan ta.
Saboda da karfin naushi,
Sai da amirat tayi sama tamakar an janye ta da ƙugiya,
Sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim! Hancinta da bakinta na yoyon jini,
Numfashin ta na fita sama-sama, adai dai lokacin ne gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat suka suka bajewa a ƙasa wanwar sakamakon naushin juna da sukayi a cikin su,
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa hamsin acikin wannan hali batare da an ga ɗaya daga cikin jaruman uku ya miƙa tsaye ba domin cigaba da artabu,
Har sai da badakaren dake busa ƙahon gasa ya ɗauko ƙahon ya busa sau uku amma babu wanda yayi yunkurin miƙewa.
Nan fa magoya bayan jaruma Amirat, gimbiya haya'ul-nur,da gimbiya Rumaisat suka shiga kiran sunayen gwanayen su domin su miƙe kafin wa'adin busa ƙahon ya cika.
Shi kansa sarki shaibat bai sa'adda ya shiga kwallawa yar shi gimbiya haya'ul-nur kira amma shiru kake ji.
Amma sai badakaren a kammala busa ƙahon gasar,
Abin da ya tabbatar dacewa sarkin sadaukai Hibairu shine ya zamo gwarzon daya lashe gasar GOGA SHA FAMA,
Nan fa fadar ta ruɗe da shewa, kide-kide da raye-raye kamar za'ayi shagalin nadin sarautar,
Saboda da murna,
Jaruma sunaila, Hizmal, Abidatul-auliya, Nuwairat,yaro Humair, matsafi shubairu,sarki shazwan da tawagar sa, aljani Marhutul-Azab da sauran dabbobi tawagar sarkin sadaukai basu san sa'adda suka shiga tiƙar rawa ba suna shewa da murna tamkar waɗanda suka zautu.
Sarki Baddadul-ulƙas kuwa kururuwar murna ya shiga yi tamkar wani tsohon mahaukaci,
Bisa ganin jarumin sa ya lashe gasar GOGA SHA FAMA ta sabuwar Shekara,.
Cikin hanzari dakaru na musamman suka shiga izuwa Filin yakin suka ɗauki 
Jaruma Amirat, gimbiya haya'ul-nur da gimbiya Rumaisat abisa keken doki aka fice dasu daga filin gasar, domin duba lafiyar su,
Cikin kaɗuwa da matukar fushi da sarki shaibat bai taɓa yin kamar sa ba,
A wannan lokaci in da ace  mutum yana tsaye a wannan waje sai ya rantse yace "garwashin wuta aka watsa masa akan fuskar tashi saboda yadda ya murtuke ta tamkar bai taɓa dariya ba.
Kawai ya miƙa tsaye zumbur daga kan karagar shi ya yabi bayan keken dokin da gimbiya haya'ul-nur ke ciki da sauri,
Dakarun shi na biye dashi cikin tashin hankali,
Sarkin yaƙi abu-Damraz kuwa saboda tashin hankali dakyar ya samu dama yayi wa mutane bayanin cewa 
A gobe ne za'a gabatar da bikin naɗin Jarumi Hibairu a matsayin GOGA SHA FAMA,
Tare miƙa kyautuka gareshi da bawa wakilin daya sakashi a cikin gasar dukkanin dukiyar sauran sarakunan da jaruman su sukayi rashin nasara a cikin gasar.
Yana kammala jawabin ya miƙe zumbur yaja tawagar dakarun shi suka fiye daga fadar,
Shi kuwa jarumi Hibairu koda yaga an fice da jaruma Amirat cikin halin dake tsakanin Rayuwa da mutuwa sai ya tsinci kanshi cikin alamun tsananin

6 / 8