GOGA SHA FAMA CIGABAN SARKIN SADAUKI BY MANSUR SUFI.txt

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Arewa Pen

Chapter   2 / 8

3K to 6K   out of 23.1K words

kala'.  
    Sai daga bisani aljani Marhutul-Azab yayi''''' gyaran murya yace "yaku abokan tafiya kuyi sani cewa wannan waje da muka iso shine waje mafi haɗari fiye da ko ina ,  
    Domin kuwa duka burikan sarakunan duniya, bokaye,da jarumai ya dogara da dajin Baitul-shamshan,  
    Ku sani cewa a subahin gobe ne nan da Sa'a uku Hibairu SARKIN SADAUKAI zai fito daga wannan daji na Baitul-shamshan,  
    Shawarar da zan ba mu ita ce mu dole mu kasance a cikin shirin ko ta kwana domin kowa ne lokaci sauran abokan gaba na iya iso nan,  
    Idan bamu mai da hankali ba zai zamo abin nan da masu iya magana ke cewa  
    Kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,  
    Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai kowa yayi na'am da shawarar.
    Nan take kowa ya zare takobin domin shirin ko ta kwana,
    Aljani Marhutul-Azab ya zare wani zabgegen Gatari a gadon bayan sa,Hizmal goye da yaro Humair makaho,sunaila da budurwar Nihla suka zare waɗansu takubba a damtsen su,  
    Kuma aljani Marhutul-Azab ya dunga rangadi yana kai komo a harabar wajen domin tabbatar da cikekken tsaro,  
    Ana cikin wannan hali ne sunaila ta dubi budurwa Nihla tayi gyaran murya tace da ita"yake wannan jaruma shin mene ne labarin rayuwar ki kuma mene ne dalilin daya sanya wannan azzalumar sarauniya ke farautar rayuwar ki? .  
    Ko da  jin wannan tambaya daga bakin sunaila sai idanun Nihla suka suka ciko da kwalla,  
    Har ta buɗe baki da nufin ta ba wa sunaila amsar tambayar sai kawai a ka ji wani gurnani daga sararin samaniya,  
    Cikin hanzari kowa ya ɗaga kan sa izuwa sama domin ganin abin da zai wakana,  
    Nan take akayi arba da waɗansu halitta na sauka daga sararin samaniya,  
    Sannu a hankali halittun suka dunga sauko ƙasa,  
    Lokacin da suka sauka a turba sai aka fara kallon- kallo tsakanin su da su  saurayi Hizmal,  
    Ba wasu ba ne halittun ba face aljani Haulatul-infal  dauke da  gimbiya Hushriba,sarki shazwan,sarkin bokaye Dargas,da tawagar matsafa biyar,
 Halitta ta biyu kuwa ba wata ba ce aljani Darmanu ibn kauƙas dauke da sa sarki uslaim da boka ƙarzum da tawagar su
 Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma sunaila da yar uwar ta Hushriba,
 Sarki sarki shazwan kuwa da saurayi Hizmal,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sa aljani Marhutul-Azab,
Gimbiya Hushriba ta taka da kafafun ta ta durfafi inda Sunaila ke tsaye yazmana tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma sannan taja ta tsaya,
 Kana ta buɗi baki cikin matukar ƙiyayya tace"yake yar uwa ta kuma babbar abokiyar gaba ta har abada kiyi sani cewa nayi matuƙar baƙin ciki da na gano cewa mahaifin mu ya sanar da ke maganin da zai warkar dashi daga shirin da muka yi masa domin ki samu nasarar hawa Bisa karagar mulkin kasar mu,
 Gashi Ni da dan uwana yarima zufair har kin riga mu  mallakar yaro Humair makaho wanda shine kaɗai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
  Kuma kina tare da aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye inda anan ne za'a ɗauko tsumin tsafi da mahaifan mu zai sha ya warke,
 Duk da waɗannan nasarorin da kika samu Ina mai tabbatar miki dacewa sun tashi a banza domin a yanzu batare da ɓata lokaci ba zan hallaka ki kuma na mallaki yaro Humair makaho da taswirar fadar Sarkin bokaye,
 Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai jaruma sunaila tayi guntun murmushi mai tattare da takaici yace"kaicon ki yake yar uwa ta haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kike tunanin cewa zaki samu nasara akai na kwatar yaro Humair tare mallakar taswirar fadar Sarkin bokaye,
 Ki sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA basa taɓa haɗuwa a waje guda,  Domin kuwa keda ɗan uwan ki kuna kwaɗayin mulki ne domin ku zalunci talakawa,
   Wanda akan dalilin hakan ku kayi yunkurin hallaka mahaifin mu,   Ni kuwa ina so na warkar da mahaifin mu ne daga sihirin da kuka yi masa domin na samu nasarar hawa Bisa karagar mulki domin na gaji mulkin adalci irin na mahaifin mu,
Sannan da kike iƙirarin cewa za ki samu nasara akai na shin kin manta ne cewa a halin yanzu ina ɗauke da dukkan sirrikan tsafin mahaifin mu,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hushriba ta cika da matukar baƙin ciki zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata kone,
Abangaren sarki shazwan kuwa bayan ya kammala karewa saurayi Hizmal dake goye da yaro Humair makaho kallo sai ya dube sa cikin matukar fushi yace "yakai Hizmal kayi sani cewa haƙiƙa ka aikata mini laifi mafi munin gaske sanadiyyar tseratar da rayuwar yaro Humair makaho da kayi wanda sanadin hakan ya jefa al'umma ta cikin gagarumar tashin hankali sakamakon GOBARAR DAJI,
Ina mai tabbatar maka da cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne,
 Cikin ruwan sanyi ka damƙa mini yaro Humair domin na yanke maka hukunci cikin lumana ta hanyar daddatsa sassan jikin ka,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai saurayi Hizmal ya bushe da dariyar ƙarfin hali sannan daga bisani ya murtuke fuska yace"kaicon ka yakai wannan azzalumin sarki da bai damu da darajar ran ɗan adam ba face buƙatar kansa,
 Ai a halin yanzu yaro Humair yayi maka nisa, domin bazaka taɓa samun nasarar hallaka sa ba matsawar ruhina yana tare da gangar jiki,
Da jin wannan batu sai takaici ya turnuƙe sarki Shazwan jikin sa ya kama tsuma,
Har ya sake buɗar baki da nufin ya furta wani abu sai aka ga wani haske na ratsowa daga sararin samaniya
  Koda kowa ya mayar da duban sa zuwa ga wajen take aka yi ido biyu da wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance tare da wani dattijo mai karin shekaru zaune abisa kan wata dardumar sihiri,
  Ba wasu  ba ne face sarauniya Nuwairat tare da boka Jadwar dake farautar Budurwa Nihla domin su hallaka ta,
Domin Nuwairat ɗin ta samu nasarar kasance mace ta farko da Hibairu zai fara gani a rayuwar sa kuma ta  samu soyayyar sa.
  Nan fa  sabon kallon kallo ya fara guda na tsakanin sarauniya Nuwairat da budurwar Nihla dake tsaye hannun ta riƙe da takobi,
Bisa mamaki a wannan karon sai sarauniya Nuwairat taga Nihla ta ƙura mata idanu babu tsaro ko fargaba a tare da ita duk kuwa da irin kwarjinin ta,
Abangaren jaruma Husnaila kuwa koda ta gama faɗin hakan sai yar uwar ta gimbiya Hushriba ta zare waɗansu tagwayen takubba guda biyu a gadon bayan ta ta falfala da azababban gudu izuwa kan ta, tana mai ihu da kururuwa mai firgitar wa, Koda ganin hakan sai sunaila ta falfala da gudun izuwa kan ta riƙe da takobi domin tarar juna,
 Tamakar haɗin baki a lokaci guda jaruman kowane bangare sukayi kukan kura domin yin karon battar karfe,
Sarki shazwan da boka Dargas suka ruga izuwa kan saurayi Hizmal, Sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka ruga izuwa kan Budurwa Nihla,
Aljani Marhutul-Azab da aljani Darmanu  suka  tari juna,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sai suka tari tawagar sarki uslaim domin ganin sun tseratar da yaro Humair domin shine abin buƙatar su.
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin jaruma sunaila da Hushriba,  
Sarauniya Nuwairat,boka Jadwar da budurwa Nihla,  
Saurayi Hizmal, boka Dargas, da sarki shazwan,  
Aljani Marhutul-Azab da aljani Darmanu, sarki   
Sarki uslaim, boka ƙarzum da tawagar sarki shazwan,  
A gabar shiga dajin Baitul-shamshan,  
Sai yakin yazamo abin tsoro kuma tashin hankali ga kowa ne bangare.  
Jaruman  suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance,  
Ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihun mazaje ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya,  
A bangaren jaruma sunaila da yar Uwar ta Hushriba kuwa,   
Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi ta hanyar kaiwa juna sara da takubban su,  
Cikin ɓakin zafin mama juriya da nacin tsiya,  
Duk sa'adda takubban su suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da kara marar daɗin sauraro,  
Babu abinda zai burge ka ga zaratan matan biyu sama da yadda suke kaiwa juna sara da suka tamkar jikkunnan su ba su kasance na jini da tsoka ba,  
Abangaren sarki shazwan,boka Dargas da saurayi Hizmal labari yasha bamban,  
Domin duk karfin damtsen zaratan sarakunan biyu sai yazamo ya tashi a banza.  
Domin kuwa sun kasa koda lakutar jikin saurayi Hizmal da makaman yakin su.  
Sai dai ga wanda yake kallon yadda artabun ke wakana zai iya fahimtar cewa ƙarfin damtsen Sarki shazwan da boka Dargas ya nun ka na Hizmal sau goma,  
Saboda wasu lokutan idan su ka kai masa hari da takobin sa,  
Idan ya sanya takobin sa ya kare sai kaga har durkushewa ƙasa yake yi,  
Amma saboda da juriya da bajinta irin ta JARUMAN DUNIYA sai kaga ya taso sama ya mayar da martani.  
Duk wannan fafatawa da akeyi tsakanin su Hizmal, yaro Humair makaho dake goye a gadon bayan sa yana jin duk irin fafatawar da akeyi,  
A bangaren manyan aljanu biyu kuwa aljani Darmanu da Marhutul-Azab,  
Sun wanzu suna ba wa hammata iska yazamana cewa,  
Suna yin ragas idan Darmanu ya samu nasarar kaftawa Marhutul-Azab sara a hannu sai kaga shi ma ya mayar da martani ,  
Ko iya hargagin su ma ya isa ya firgita lahittun  
Dake wajen ,  
Amma a bangaren sarki uslaim da boka ƙarzum da tawagar sarki shazwan kuwa,  
Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi,  
Duk inda sarki uslaim ya sanya gaba sai kaga dakaru na zubewa ƙasa magashiyan ,  
Ita kuwa budurwa Nihla ta zamo tamkar wata shaiɗaniya a tsakanin sarauniya Nuwairat da boka Jadwar,  
Domin sun kasa samun nasarar murƙusheta    
Al'amarin daya fusata sarauniya Nuwairat da boka Jadwar kenan, zukatan su suka kama tafarfasa tamkar zasu ƙone  
Abu na farko da ya dugunzuma hankalin su shine yaushe Nihla ta samu wannan gagarumin karfin damtse,  
Har su gaza samun nasara akan ta a matsayin su na zaratan Jarumai masu juriya da bajinta,  
Sannan idan har aka cigaba da wannan artabu a haka zasu iya yin biyu babu,  
Domin abinda zai faru shi ne dazarar ɗaya daga cikin abokan gaba ya samu nasarar kashe a bikin faɗan sa zai iya rigasu saduwa da SARKIN SADAUKAI,  
Kai ga kenan sunyi aikin banza, kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,  
Sa'adda suka zo nan a tunanin su sai suka  canza salon faɗan su.  
Wohoho haƙiƙa   masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta canza.  
Faruwar hakan keda wuya sai yazmana cewa a wannan karon su boka Jadwar suna haɗawa da bugu da kafa da kai sara da takobi,  
Nan fa suka fara haɗawa Nihla jini da majina,  
A cikin wannan fafatawa ne Nihla ta kai musu wani sara da takobin ta a kirjin su,  
Adai dai lokacin ne sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka kai mata duka da ƙafafuwan su ɗia ɗin,  
Bisa Sa'a sai suka dake ta a kirji da dukkan karfin su,  
Saboda karfin dukan sai da Nihla tayi katantanwa a sama sau uku sannan ya kife ƙasa da ruf da ciki,  
Kawai sai sarauniya Nuwairat ta zare takobin ta ta durfafi inda take tana mai yi mata murmushi mugun ta,  
Tana isa ta ɗaya takobin ta domin ta sare mata wuya.  
Dai dai lokacin da jini ke kwaranya daga bakin. Budurwa Nihla kuma numfashin ta na sarkewa.
Kwatsam ! Bazato  babu tsammani  sai sarauniya Nuwairat taji an dankara mata wawan naushi a dagon bayan ta saboda karfin naushin sai Nuwairat ta tayi gundumbala sau uku sannan ta kife a ƙasa,  
Amma sai ta miƙe tsaye zumbur cikin matuƙar fushi da zafin nama,  
Ta wai ga bayan ta domin taga wane ne ya dake ta ɗin,  
Ai kuwa koda juyawar ta sai tayi Turus, bawa Ni ta gani ba face,  
Wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa zaune a bisa kan wani tsuntsun tsafi tare da wani zabgegen kyakkyawan saurayi,  
Ba wata ba ce wannan budurwa ba face sarauniya Abidatul-auliya ta birnin Tehran tare da matsafi shubairu,  
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin sarauniya Nuwairat da sarauniya Abidatul-auliya,  
Tsawon wani lokaci sai daga bisani Abidatul-auliya ta a dubi Nuwairat ta daka mata tsawa sannan ta buɗi baki cikin kakkausar murya tace"yake tsohuwar azzaluma kuma abokiyar gaba tun iyaye da kakanni ina fatan a halin yanzu kin shaida Ni ko?  
Dajin wannan tambaya sai Nuwairat ta bushe da dariyar ƙarfin hali sannan tace "Ai kuwa ni na gane domin na sanki fiye da yunwar ciki na,  
Abidatul-auliya bintu shafwaz ta birnin Tehran,  
Ban taɓa tsammani cewa akwai sauran zuri'ar  mahaifin ki a doran ƙasa ba,  
Abidatul-auliya ta ce"Idan barci kike sai ki farka a yanzu ne zuri'ar mahaifi na take gab da yaɗuwa a duniya,  
Hakika ke da zuri'ar gidan ku kun dade kuna aiwatar da mulkin zalunci,  
Amma ina so ki sani cewa a waje zan hallaka ki na tsira kokon kan ki,na tsire sa da mashi na ajiye sa a fada ta domin ya zamo inza ga sarakunan azzalumai,  
Kuma ina mai tabbatar miki dacewa bazaki taɓa burin ki na saduwa da SARKIN SADAUKAI,  
Ballantana ki cika burin ki, na sarrafa sa yadda kike so har ki sanya duniya a cikin musiba,  
Koda jin wannan batu daga bakin Abidatul-auliya sai Nuwairat ta bushe da dariyar mugun ta sannan tace"Fiye da shekaru ashirin baya mahaifin ki yayi wannan furuci amma sai da Abba na yaga bayan sa don haka,  
Wannan bayani naki tamkar a zuba ruwa a faifai,  
Ina mai tabbatar miki dacewa a yanzu zan hallaka na zare ruhin ki daga gangar jiki,  
Kuma na hallaka budurwa Nihla da kika ceci rayuwar ta a halin yanzu,  
A bangaren matsafi shubairu da boka Jadwar kuwa koda suka yi kallon kallo  
Sai boka Jadwar ya dubi matsafi shubairu yace"yakai shubairu kayi sani cewa zuwa wannan waje domin saduwa da SARKIN SADAUKAI Hibairu domin ya tafi izuwa fadar Sarkin bokaye ya ɗebo maka Tsumin tsafi   
Kayi maganin lalurar tsagin jikin da ta addabe ka,  
Ka sani ya tashi a banza domin kuwa matsawar ina numfashi a doran ƙasa bazaka taɓa cika  wannan buri maka ba Ballantana ka zama dodon bokaye na wannan nahiya,  
Koda jin wannan batu sai matsafi shubairu yayi murmushi ya dubi boka Jadwar cikin kaskanci yace "Ai kuwa ina da tabbacin cewa zan cika wannan buri na wa domin dai masu iya magana na cewa   
In da rai da rabo! Kuma tabbatar mai nema yana tare da samu,  
Kuma ita karya fure take bata yaya tabbas rana dubu ta barawo ce rana ɗaya ta kai kaya  
Na tabbata cewa da ace sarauniya Nuwairat tasan cewa ka shafe tsawon shekaru kana cin amanar ta da ta daɗe da sheƙaka barzahu,  
Na sani cewa a duniya baka da burin da ya huce kaga ka mallake ta a matsayin abokiyar rayuwar ka domin a halin yanzu a duniya samun wata ya mace mai kyawun sura kamar ta abu ne mai  wahala,  
Baka san cewa hatta mafarkin da sarauniya Nuwairat tayi ba akan dole ne ta fara arba da SARKIN SADAUKAI domin tazamo mace ta Farko da zai gani yaji yana kaunar ta ba,  
Duk kai ne. Ka shirya sa domin kawai  ka yi amfani da ita wajen mallakar ta dashi kansa SARKIN SADAUKAI, domin ka kwashe sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN sa domin ka zama Sarkin bokaye na wannan nahiya,  
Hatta zaluncin da sarauniya Nuwairat ke aiwatar wa kai ne ke sarrafa ta ta hanyar wani bakin aljani,  
Na sani cewa Nuwairat ba zata taɓa gano wannan sirri ba face an karya sirihin dake tsakanin ta da masarautar su,  
Abinda ba ka sani ba shine babban kuskuren da kayi shine,  
Matsawar Nuwairat tayi arba da SARKIN SADAUKAI take dukkanin sirrikan tsafin dake jikin ta zasu lalace su daina aiki,  
Domin bisa tsarin sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN Hibairu duk wanda yafara arba da shi sai ya rasa nasa sirrikan tsafin,  
Wannan shi ne fa abin da masu iya magana ke cewa karyar ƙasa wai malamin duba ya dubo ranar mutuwar sa,  
Kuma idan za ka gina ramin mutunta to gina sa gajere,  
Sa'adda matsafi shubairu yazo nan azancen sa sai idanun boka Jadwar suka kaɗa sukayi jajur har wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita kai da gani kasan aiki ne na sihirin tsafi,  
Kawai ya buɗi baki yace"Na rantse da kushewar mahaifina boka  sahibul -ƙarnas sai na mai sheka gawa domin a halin yanzu kai ne kadai kasan sirri na,  
Koda gama faɗin sai boka Jadwar ya ɗaya daga hannun sa izuwa sama,.sai ga wani narkeken Gatari ta bayyana a hannun sa mai matukar kaifi tamkar takobi,  
Tamkar hadin baki a lokaci guda jaruman huɗu sukayi kukan kura suka afkawa juna ta hanyar ɗaga makaman yaƙin su,  
Wato sarauniya Nuwairat ta afkawa sarauniya Abidatul-auliya,  
Boka Jadwar kuwa ya afkawa matsafi shubairu,  
Aka ruguntsume  da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro,  
A dai dai lokacin ne akaga sararin samaniya tayi duhu dunɗum,  
Kwatsam sai wata runduna ta bayyana mai ɗauke da dakarun bil'adama da aljanu haɗe da miyagun dabbobi.  
Ba wata bace wannan runduna ba face rundunar Sarki Baddadul-ulkas na birnin Rum,  
Daga cikin dajin Baitul-shamshan kuwa sai kaji wani kara ya cika wajen kuma wata irin guguwar iska ta bayyana ta dunga sanyawa bishiyoyi na karairayewa suna zubewa ƙasa,  
Duwatsu suna karo da juna suna yin bindiga,  
Wata irin walkiya na bayyana a sararin samaniya tamkar hadari ne ya hadu ake shirin ɓarkewa da ruwan sama,  
Alamun  dake nuna cewa HUBAIRU SARKIN SADAUKAI na gab da bayyana Daga cikin dakin Baitul-shamshan .
Kwatsam bazato babu tsammani sai akaji wani irin gurnani na fitowa daga dajin haɗe da waɗansu irin sauti ka da kunnawa ba su taɓa jin su ba,
Al'amarin daya sanya budurwa Nihla dake kwance a ƙasa ta ɗimauce kenan,
Bata san sa'adda ta kama rarrafe ba ta shiga izuwa dajin Baitul-shamshan saboda da ɗimauce wa,
Tsaye tayi arba dashi sanye da kayan fata riga da bante iya kaurin sa,
Kyakkyawan saurayi ne nagaban kwatance wanda kallon farko zai ɗimauta zuciyar duk wata ya mace mai hankali,
A gadon bayan sa yana rataye da wata rantsattsiyar kwari da baka hannun sa riƙe da wani dogon mashi mai baki biyu,
A gefen sa na dama wani irin tsuntsun tsafi ne mai ɗauke da siffar mikiya da girman sa bai huce na jakin dawa ba,
A gefen daman sa kuwa wani murgujejen zaki ne mai kwarjini daban tsoro,
Tsaye a bayan sa kuwa

2 / 8