TAWA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN SHAKUR.txt

Author :  Maman Shakur Category :  Arewa Pen

Chapter   2 / 12

3K to 6K   out of 35.6K words

yace thariq banaso na mutu saboda yar baba, ban gama bata tarbiyaba, batasan komi kan rayuwaba, yarinya ce karama wanda take bukatar uwa mace ta koyamata abubuwa da dama, amma hakan baisamuba saboda wasu yan dalilai, baba kuka yake sosai thariq ya rike hanunshi, yace baba babu abunda zai sameka in sha Allah zaka warke, zakabama yarka tarbiya mai kyau be strong baba.

Baba ya girgiza kai, yadau dayan hanunshi yasake daurawa kanna thariq yace thariq wlh naji ajikina kwanakina kadan suka rage, inason nabaka amanar Shukra koda banda rai dan Allah karikemin shukra amana, thariq dukda bansankaba bansan kowa nakaba amma zuciyata ta aminta dakai sama dakowa plz thariq tace care of yar baba. Kabata tarbiya,
Thariq duk karfin zuciyanshi jiyayi hawaye ya gangaro yace baba nama alkwari zan kula da ita kadena magana yanzu hutawa yakamata kayi.
Baba ya girgiza kai yace banni nai magana nasan ta karshe ce thariq YAR BABA! YAR BABA!! YAR BABA!!! nabaka amanarta, inhar kaji kana sonta ka aureta nabaka ita dan nafi yarda dakai, idan kuma baka sonta inlokacin aurenta yayi kazaba mata miji nagari ka aura mata, sauke ajiyan zuciya yayi,
Yace thariq inaso kasani yar baba TAKA CE!! Ka kulan min da ita dan Allah..
Yace baba ina maman shukra?? Ta mutu ne?? Maisa kai kade ke rainonta?? Mesa kukadai ke rayuwarku??

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 8:38 PM] Aishat muhโ€™d: [02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
8โƒฃ
Nan baba yaba thariq labarin komi thariq yaji tausayin baba da shukra sosai, da kyar ya lallaba baba yay shiru. **Gani yake kaman zafin ciwo ne kesa baba yake cewa bazai rayuba yaushe zai shirya da sarkin kwadayin chan shukra inaa** baba yace kawomin shukra yace to baba yajuya yafita, yana zuwa yatarar da ita zaune kuka take tama kasa cin abinci gyaran murya yayi yasa ta dago dara daran idanunta ta kalleshi da sauri yajanye nashi daga nata yace muje baba nason magana dake, da sauri ta share hawayen ta kwalalo idonta waje tace da gaske?? wani irin kallon mai kama da rainin wayo yamata batare daya cemata komiba yay gaba tabishi abaya, suna shiga dakin taje da gudu ta rungume baban tama manta baida lafiya sai murna take baba shima yanata murmushi fira suka dungayi hakan yasa thariq fita zuwa duba wasu patient,. bayan ya fita baba yace shukra duk randa bani a duniya kidau thariq a matsayin wanki, yanada kirki kinji, zumburo baki tayi tace baba baruwana dashi baya dariya kaman kai. Baba yace haba yar baban ta kamota kamota nan tadinga dariya harya samu ta yarda.

Karfe goma yadawo asibitin, direct dakin su baba yawuce yana shiga yaga daga baba har shukra suna bacci dukda karantan gadon baba ya matsa mata tare suka kwanta ta rungume babanta dankwalin kanta ya zamiye gashin kanta gabaki daya yarufe mata fuska.

Baitaba ganin yar Nigeria da tsawon gashi kaman na yan India ba saiyau, shagala yayi yana karemata kallo komeya tuna oho yay maza yajuya yabar dakin.
Wuraren karfe biyun dare taji jikinta kaman ta kwanta kan kankara, tashi tayi taga baba yana bacci ta taba jikinshi taji sanyi sosai tsoro taji wanan sanyi kaman kankara. Mikewa tayi tayi hanyar office din thariq tana shiga ga mamakinta taga yana rubuce rubuce laptop a gabanshi, tsayawa yayi yana Kallonta kanta ko dan kwali babu.

Yace waike bakisan dare bane kin fito ba dan kwali ba hijabi, kin shigo babu sallama, magana yake mata fada fada, rudewa tayi jikinta yafara rawa, ta lankwasa kai kaman yarinya tace yakuri, yanda tayi saiyaji wani iri, dauke kanshi yayi yace menene?? Tace dama baba ne natashi naji jikinshi sanyi sosai, kasan tare muka kwana a gadon, toshine naji sanyi saina farka kuma shine naโ€ฆ. dafe kanshi yayi baitaba ganin yarinya irin shukra ba, abu daya zata fada amma tana koro bayani sama da ashirin, Kallonta yayi naji kawai tafi ina zuwa. Tajuya tafita. girgiza kai yayi tasowa batare da uwa akusada yara mataba akwai matsala gaskiya,inhar namiji ya raini yaro dole kaga banbanci. Tashi yayi yatafi dakinโ€ฆ

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
9โƒฃ
Tare da nurse suka shigo. yana shiga dakin yaganta zaune kusa da baba tai shiru tana kallonshi,
Kallonshi da ido kawai yayi yasan rai yay halinsa INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJIโ€™UN shine kalmar dayake fada a zuciyanshi, yanzu dama baba da gaske yake mutuwa zaiyi?? Yanzu ya zaiyi ya sanar da shukra?? Dabara ne yafado mishi yay ma nurse din magana a kunne yace tarufe baban, bari yakai shukra waje.

Ya kalli shukra yace mata come, tasowa tayi tazo office dinshi suka shiga yace ta zauna kan kujera tako zauna, yazo kusa da ita shima ya zauna, ahankali yace shukra wake rayawa?? Tace Allah, wake kashewa?? Tace Allah, idan kaddara tasamu mumini mai akeso yayi?? Tace anaso yayi imani da ita, yace good. Ita bata kawo komi arantaba, yace shukra babanki ya rasu, zumbur ta mike tsaye, tace baba fa bacci yake ba yanzunan mukaje ka ganshifa,

For d first tym yaji tabashi tausayi, yakara tausasa murya yace shukra bakinji jikinshi yay sanyiba?? Ai rasuwa yayi tun alokacin, zaro ido tayi tana kallonshi sai kuma tafara ganin baki baki luuuuuuu tayi bayi zata fadi ya tarota tafada jikinshi a sume, daukanta yayi chak yasata akan gado yacire mata hijabin yafara bata taimakon gaggawa, ta farka amma tai shiru ita batai kuka ba, ita gatanan dai kukan ma yaki zuwa, riko hanunta yayi yace shukra kiyi kuka plz shizaisa kiji bakin cikin ranki ya ragu. Kiyima baban ki adduโ€™a, Shiru batacemai uppan ba. Haka ya zauna kusa da ita yana tofa mata adduโ€™a da asuba yasa wata nurse ta zauna da ita karta bari taje ko ina.

Shikuma yatafi masallaci akai sallan asuba dashi da limamin masallacin sukaima baba wanka akamai sutura aka kaishi gidan gaskiya Allah yasa mucika da imani.

Suna dawowa daga makabarta tunanin shukra yake kawai, shi yanzu yazaiyi program yazoyi na 1 month a asibitin nan ko sati daya baima yiba ga abunda yafaru, shikuma gaskiya bazai iya zama da mace a gidaba dan yasan yanda yake, daukan waya yayi yakira dad dinshi yafadi musu komi, dad yace Thariq ka kawota yau inkazo mayi maganan yace to dad tareda kashe wayan.

Saida yabiya gida yay wanka sanan yatafi asibitin ya tarar shukra na nan yanda ya barta salla kadai ya dagata, ta mugun bashi tausayi ya zauna kusada ita yana mata waโ€™azi da adduโ€™a abinci ma takasa ci.

Hijab yabata tasa yace zan kaiki wurin mamana zaki zauna da itako?? Sai alokacin ta make kafada tace babana ka kaini gidanmu dan Allah yako kaita tana shiga taga kayan babanta yasa ta zauna a wurin ta dinga kuka kaman ranta zai fita, thariq saida yay hawaye fito da ita yayi tace dan Allah ka kaini gareji zan kwaso kayan aikin babana zan adana mishi ne, saida yadanyi tunanin sanan yace tooo.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
๐Ÿ”Ÿ
Suna shiga garejin, tabude shagon ta shiga gani take kaman gata ga baba kuka tafara tana dukan kasa why?? Why baba?? Maisa zaka tafi ka barni?? Mesa zakamin haka?? Yanzu gashi bani da kowa, maisa bazaka gayamin zaka mutuba saboda nima nabika why baba?? Baba plz kadawo wlh ina sonka, jitayi kaman ance โ€œyar babaโ€ da sauri ta mike tana waige waige naam babana, ganinan, nidama nasan baka mutuwa wanchan doc thariq din karya yakemin babana fito kaji, thariq gani yayi tafara fita hayyacinta yasa yakaraso ya zaunar da ita yana bata baki da kyar tai shiru tashi tayi tana kwashe tools dinsu na aiki bai hanataba dan yaji dadima yanda tai shiru, takwashe tools din aikin tass tasa a mota yace mata to mutafi,

Hanyar kano suka dauka sunyi nisa sosai atafiya dan sunma kusa shiga kano sunadai kan hanya suka shiga wani hold up sunfi awa biyu, motoci ko moving basuyi, itadai tana zaune tai shiru ta lumshe idanunta.

Bude kofan motan yayi danyaje yaduba maiya kawo hold up dinan yana fita itama tabude mota tabi bayanshi baicemata komiba suka dinga tafiya, yawancin mutane duksun fito anata masifa ana fada, suna kaiwa wurin ta tsaya tana kallon mota, kallo daya taima motan tagano matsalan mota exhaus din yabaci dan hayakima yakeyi sosai, sanan tayan motan tai less, gashi babu bakanike, driver yace yay waya bakanike na zuwa daga cikin kano dan ya gyara.

Tunawa tayi da maganar baba tadinga taimako yasata Juyawa takoma motarsu tabude boot ta dauko kayan dazata gyra musu motan dashi ta dawo da sauri bataima kowa maganaba ta kutsa kanta cikin jamaโ€™a ta shiga karkashin motan ta kwance exhaus din tafito daga karkashin mota ashe kasane ya cika exhaus din. Tacire kasan takoma ta daure abun, mutane an taru kallon yar yarinya ake dambazata wuce 16 ba tana gyara mota, da yawa daga cikin mutane sun fito da wayarsu suna mata video, thariq jingina yayi dawata mota ya daura hannu kan kirjinshu yana Kallonta,

Tana gamawa da exhaust din takoma kan tayan, dago kanta tayi taga wani saurayi kakkyawa black beauty yana Kallonta tace mishi plz help me, murmushi yayi yace mata sure, ya tsugunna yatayata kwance notin nan tayan dayake batada karfin kwance su, tacire tayan ta kalli driver daya sake baki yana Kallonta tace kanada sapayan taya?? yace mata eh, yabude booth yadauko ta karba taje tasa saurayin yatayata daure notin. Tacema driver din ya gwada motan yako gwada mota tafara aiki da dako kunnuwa batayi saboda exhaus, raf raf raf tafi kakeji ana ihu a wurin, yawancin yan wurin basu taba ganin mace bakanikiya ba, thariq hardashi dan tai balaโ€™in burgeshi.

Driver yaciro kudi mai yawa yabata taki karba, tajuya zata tafi wanan saurayi yace yan mata sunana NAZIR, wlh kin burgeni ke kakkyawace, ina sonki, juyawa tayi da sauri kamo hanunta yayi jikinta yahau rawa bakice komiba, thariq yace malam sake mata hannu, yasaki. thariq yace wuce mutafi suka tafi, saurayin har motansu yabisu ya kalli shukra yace yan mata kisa azuciyanki cewa ke TAWA CE!!! Wlh sai kin zama TAWA ni kadai, ke TAWA CE!! yajuya yatafi..

Maman shakur ๐Ÿ˜˜


[03/11 2:13 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
1โƒฃ1โƒฃ
Shukra kuka tafara sosai, shikuma thariq ya girgiza kai ya cije lebe, sanan ya kunna motan dayake motoci sun fara moving.

Kuka tayi sosai daganan kuma bacci yay gaba da ita, dama ance anacin bashin komi amma banda na bacci, hamdala yayi yanda tai baccin dan kukanta balaโ€™in sosamai rai yake, parking yayi gefen hanya yafito yazagayo ta inda take ya bubbuga kujeran yana kiranta da โ€œyar baba, yar babaโ€ shi kwata kwata yama manta sunan kawai yazo bakinshi ne alokacin.

Bude ido tayi ahankali ta kalleshi kadan sai kuma tamaida idon tarufe yasake cewa shukra tashi mana ki koma baya zakifijin dadin baccin ki, kin cika nauyin bacci, da kyar ta iya bude baki tace ni babana ka kyaleni, wlh nagaji anjima zan tashi, zanma kuka fa karka kara tashina. saikuma tacigaba da gwalan gwalan din bacci ahankali har takoma bacci duka.

Girgiza kai yayi yarufe kofan yakoma yashiga motan yafara driving har ya shiga cikin kano acikin gaida gidansu yake, horn yayi gaban wani tamfatsetsen gida wanda idan kaga kyawun shi saika zata government house ne.

Mai gadi yazo yabude mai gate, yashiga ciki. NAZIR na ganin gidan da motansu yar kakkyawan yarinyan shi tashiga yay murmushi yace wlh koke wacece sai kin zama TAWA!! Nazir bai taba neman abu ya rasaba KE TAWA CE baby, yaja motanshi yay gaba, NAZIR matashi ne kakkyawa shikadai iyayenshi suka haifa saisa suka sangartashi dayawa, komai yakeso sai sun bashi, yagama karatunshi inda ya karanci ELECTRICAL ENGINEERING wanan kenan.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[03/11 2:35 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
1โƒฃ2โƒฃ
Yana gama parking yafito daga motar, mai gadi yazo yana kwasan gaisuwa suka gaisa yaciro kudi mai yawa yabashi yadinga godiya, wanan shine halin thariq dayasa kowa na sonshi akwai yawan kyauta ga tausayi.

Bude kofan yayi yana dukan kujeran ahankali, shukra takara zumburo baki babana wlh asuba batayiba, da dai yaga bata da niyan tashi ya daka mata wani irin tsawa a firgice ta tashi jikinta narawa, ya kalleta yace biyoni mun iso gidanmu.

Yay gaba tsayawa tayi tana kallon gidan ita bata taba ganin gida mai kyau hakaba, haryakai bakin kofan shiga ya juyo yaga ita ko tahoha batayiba, ya tsaya ya kuramata ido fuskanshi a daure da sauri tataho da sallama suka shiga dakin dad da mum dinshi suna zaune suna kallon news.

Amsawa sukayi da murmushi a fuskansu, itadai shukra tana ganin mutane a dakin ta labe a bayanshi tana matsar hawaye, yagaida mum dinshi da dad shukra tai shiru yajuyo ya kalleta yanda talabe a bayanshi bazaki gaisuwaba, ahankali murya na rawa tace ina wuni, mum ce tana murmushi ta tashi tace haba bakuwarmu tsoranmu kikeji ne tazo zata kama hanunta,

Ihu shukra tayi ta kankame bayan thariq tare da chusa fuskanta abayanshi, mum ta tsaya turus, tace thariq bakuwar tamu tsoran mutane take ne?? Thariq ya cirota daga jikinshi ya dago kanta yanda take kuka yasa ya kwantar da murya shukra kidena kuka, iyayena ne babu abunda zasu miki kinji,

Share hawayen idonta tayi, tace babana yace kai kadai zan dinga yarda dakai, kumama ai ranan muna kwance a gadon nan na asibiti,kuma yace kanada kirki bazaka cutar daniba, yace kai kadai zan dinga yarda dakai ko bayan ranshi, ai baice dasuba, kumani babana yahanani magana da maza tana nuna dad dinshi, kumaโ€ฆ. Dayaga maganan nata bamai karewa bane yace to naji, ba baba yace kidingajin magana naba?? Tace eh, yace to ni yanzu kidinga yarda da iyayena babu abunda zasu miki kinji ko?

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[03/11 3:01 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
1โƒฃ3โƒฃ
Ta girgiza kai alamun to, yace oya je wajan mum dina, mum ta miko mata hannu ahankali taje tana tafiya tana waigen thariq ya gyada mata kai mum ta rungumeta, sannu kinji bakuwarmu babu abunda zamu miki dagayau ke yatace, ya sunanki?? murya na rawa tace shukra, mum tace wow sunanki mai dadi. Jeki gaida alh sai kije kiyi wanka kici abinci ko ai gobe zaki samu abokin fira harsaikin gaji.

Ta tashi adan tsorace ta kalli thariq yamata alamun ta gaida dad, taje gaban dad ta tsugunna ina wuni dad, dago kanshi yayi ya kalleta baisan mesaba jiyayi gabanshi yace rasssss, Kallonta ya tsaya yanayi wanda hakan saida yabama mum da thariq mamaki, mum tace alh ana gaisheka yace lpy lau ya kk shukra, tace lpy lau yace sannu da zuwa karkiji tsoranmu zamu kula dake mu iyayenkine kinji ko?? Tace to.

Mum tace thariq zoka kaita dakinta yamike yace muje, mum ta dauko sabuwan doguwan riga tace gashi kisa inkinyi wankan, saida takara kallon thariq yadaga matakai alamun ta karba sanan ta karba tace Nagode,

Yana gaba tana binshi abaya harsukakai dakin yabude suka shiga, zama yayi abakin gadon ita kuma ta ajiye doguwan rigan kan gado tacire hijabin tafara kokarin cire rigan jikinta, thariq ne yace ke mehaka?? Juyowa tayi ta kalleshi tace kaya zan cire inyi wanka, yace to shine agabana zaki cire kayan.

Tace agaban babana nake cire kaya, kuma babana yace nadinga yarda dakai, kaga yanzu tunda ya rasu kaine babana nabiyu ta fashe da kuka ta zauna akasa ta matukar bashi tausaya,โ€ฆ.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[03/11 3:27 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
1โƒฃ4โƒฃ
Zuwa yayi ya durkusa gabanta yace shukra kidena kuka adduโ€™a zakima baba, nariga naima baba alkawari zan kula dake kinga baikamata nabarki kina kukaba, share hawayenki to, ahankali tashare.

Ta mike zata cire rigan, kanshi yarike yace subhanallah yay maza yajuya zai fita daga dakin tazo da gudu tarike hanunshi ina zaka?? Babana narakani bayi ya jirani fa, yace sa hijab dinki saida tasa sanan yajuyo ya kalleta yace zauna ta zauna kan gado.

Yace shukra nifa ba baba bane, abunda kikeyi gaban baba kidenayi agabana ko agaban wani kinjiko?? Tace amma babana yace na yarda dakai. Dafe kanshi yayi yace shekaranki nawa ahankali tace 16 da rabi, yace kinga baba muharramin kine, shiya haifeki, saboda baba yace ki yarda danu baisa nazama muharraminkiba, yace mai akacemuku a islamiyya game na nuna jinku??

Tace ance muharaminka ne zai iya ganin jikinka, yace toni muharamin kine? tace aโ€™a, yace yauwa kinga to duk randa zakizo inda nake kisa hijab ko kuma zaki fita tsakar gida saboda akwai masu gadi kinjiko?? Tace to.

Yace jekiyi wanka tace wlh tsoro nakeji karakani dan Allah, tausayi tabashi gaskiya rashin uwa babban abu ne, yace kiyi adduโ€™a shiga bayi babu abunda zai kamaki keje inanan bazan fitaba, tace to hartakai kofan shiga bayin tana waigenshi, koda tashiga bata kulle kofan dukaba, saida ya tabbatar tafara wanka sanan yabar dakin, wajen su dad yatafi suna tattauna matsalan shukra sunji tausayinta sosai, mum tai alkawarin tazama mamanta daga yanzu, zata koya mata komi, zata jiyar da shukra dadin uwa.

Shukra nafitowa daga wanka taga baya dakin kuka, tafara tai maza ta zira doguwan rigan ko kanta bata tsaya ta tsanar ba tafito tana nemanshi,

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[03/11 8:45 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA

2 / 12