Author : Hadiza D Auta Category : Arewa Pen
kowa ya yi musu fad'a tare da jaddada musu hak'uri ne kan gaba a cikin aure.
Dangin Rukayya sun zo da yawansu aka dinga ina ka skaa da su tare don kuwa komai da su ake yi ba'a barsu sun koka rashin wani abu ba. Sai dai duk inda Bilki ta gilma idonsu na kanta. Basu gaji da nunata ga waɗanda basu gama ganeta a bikin Laura ba.
Lallen Bilki da Abida da na Amare ba k'aramin kyau ya yi ba. Kowa sai ya tambayi wacce ta yi. Yaya Hamida ta karɓi lambar ta ce tana komawa Kano zata je itama a ta yarfa mata.
For kanawa contact her for your special lalle......09076460821 farawa layin Alkairi suya.
A lokacin bikin ne da manyan y'ansanda suka je d'aurin auren suka tisa da D.p.o da fad'an ace gida irin na su Oga Asad a garin Funtua babu d'ansanda ko daya da yake tsaron lafiyar iyayensa da danginsa?
Ya dinga bada hak'uri tare da girke y'ansanda har shida a gidan.
Wasu a bakin gate wasu a farfajiyar gidan.
Wasu kuwa a bayan gidan.
Sai da oga Asad ya ce sun yi yawa a bar guda biyu sun isa.
Anyi taro lafiya ana gama lafiya an kai amare gadajensu a Abuja Aysha da Hafcy.
Khadija kuma satin sama zasu wuce da mijinta London a can zata zauna.
Dangin Rukayya sun koma da shatara na kayan arziki iri iri. Tunda kan kayan gara har zuwa kayan sabeniyos kala kala masu d'auke da sunan amare. Mussaman irin plates din ralzaplace08109544470. Da aka ci abinci da su a bikin sannan kuma har da su aka raba. Wato anyi harkar arziki, bikin girma aka yi.
Da kansu sun gamsu Rukayya ta yi aure a cikin ahalin da suka san alheri suke kuma kamanta shi. Don kuwa oga Asad da dukkan iyawarsa yake girmamasu fiye da sadda take raye. Hidimar da ya yi a auran Laura da yadda aka karrama su a wnanan bikin ya rage jin zafinsa da Hajiyarsu Rukayya take yi.
A hankali kowa aka fara tafiya. Munira ta fara wucewa.
Sannan Usman da Salaha da Ansari. Kowa cikin farinciki yake.
Oga Asad kuwa sai da ya yi kukan murna na yadda kafatalin kannensa suka hana shi jigata a bikin. Ya dinga godewa Allah da aka yi hidimar bikin bayan an yi sulhu dan ya tabbatar su Hamida ba zasu zo ba da ba'a yi sulhun ba.
A ranar da zai tafi ya durkusa gaban Baba ya ce "Baba Allah ya saka maka da alheri, Ubangiji ya karbi hidimar da kake yiwa zumunci. Na gode da auren Bilkisu na gode da komai Allah yasa ka gama lafiya".
Baba ya ce "Allah ya tsare ya dafa maka ya taimakeka akan girman da ya hau kanka. Ka zama mai hak'uri ka ninka juriya akan komai. Tawa ta k'are ko yau ma mutu na bar dukkan yaran nan a hannun Allah da hannunka. Ka yi hak'uri da kowa dan Allah".
Dukkansu hawaye suke yi cikin alhini.
Haka ya tisa iyalinsa suka tafi cikin kewa.
Bai kuma bar garin ba sai da aka dasa harsashin fara gina masa tamftsetsan gida da zai dinga sauka shi da iyalinsa a Funtua.
Shi kam ba zai dawo Funtua gabad'aya ba. Amma idan ya yi retire zai yawaita zaman garin. Idan ya gaji ya koma Abuja a haka har rayuwar ta kare.
Watanniin su Aysha shida da aure Bilki ta haifo lafiyayen danta a birnin Newyork din Amurka.
Tare da oga Asad da kuma Alti.
Alti dai ana ta keta hazo. Don bata jima da dawowa daga aikin Hajj ba. Bilki ta roka mata oga ya biya Mata. Shi Kuma ganin yadda take masa hidima da yara gabad'aya babu banbancin ya sanya ya biya babu gardama.
Da yake cikin hutu ne sai aka kai yaran Funtua tare da y'an aiki don su kula da tagwaye da suke tafiyarsu ko ina. Sun tafi da Alti me dan ta kula da jariri da Kuma Bilki. Ba yadda za'a yi ka kalli Alti ka ce yar aiki ce. Don suturar mai kyau take snayawa, haka nan Bilki bata mata iyaka da cin abin da take so a gidanta ba. Sai aka yi sa'a ita kuma tasan ya kamata tana yin komai cikin nutusawa bata tsallake iyakarta. Idan Bilki ta ce mata jira take yi danta Faruku ya girma ta danka masa ita Sai ta ji hawaye tana godewa Allah. Don da kansa ya kawo mata d'auki da ya hada ta da Bilki ta zame mata komai ta hana ta zubar da hawayen rashin y'aya' da dangi. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:39]
Abida ta dinga mamakin haihuwar Bilki don boye mata cikin ta yi tunda ba gari daya suke ba. A bikin su Aysha kuma bai wani fito ba.
Kunya take ji domin ta tuna sadda suke gulmar Rukayya ita da Abidan na ta saki jiki tana ta haihuwa rututu babu hutu har suna fadin namiji take so ta haifa ko su ce so take ta tara magada. Ashe ashe ra'ayin mijinta take bi.
Gata itama ta shiga ciki tsundum.
Sati biyar da haihuwar suka sauka a Kano daga nan suka isa Funtua dan kaiwa su momi yaron da ya ci sunan oga Asad ya kuma biyo kammaninsa tamkar dai tagwaye.
Daga nan kuma su kwashe yaransu su wuce Abuja.
Kafin ta bar Funtua ta yi order din maijego package a wajen Bojuwa herbs Kano don matuƙa da gaske ta yarda da kyaun kayan da ingancimsu ga sauk'in farashi.
Tunda Abida mai kyankyanmi ta yaba kyaunsu. Ta gamsu da packaging dinsu da sabbin containers ne ai ba wanda zai kushe kayan ko ya ce ba masu kyau ba ne.
Contact Bojuwa herbs
08032773332
For your order
Nation wide delivery.
Shekaru uku a gaba.
Zuwa Yanzu Amal Noor da Farha me a gaban Bilki. An an aurar da Bilkisu shekarar da ta gabata tana zaune a kasar Italy da mijinta.
Amal ta kammala sakandire tana ajiy daya a jami'a a Riyad tare da Amrah suana hannun Abida da Sulaiman da suka Koma k'asar Saudiya shekaru biyu da suka wuce. Yayin da Noor take ajin biyar a sakandire Farha na aji uku.
Bilki ta ta sake haihuwa bayan Mai sunan Asad da suke kiransa da Sadik. Yanzu mace take shayrwa Har ta yi wayo Mai sunan Momi.
Tuni Faruku ya kammala sakandire yana karatunsa a jami'ar alkalam d take Katsina. Ba yadda oga bai yi ba ha zo Abuja ya yi ko ya tafi waje ya bada hak'urin said zai yi masters zai zo.
Ammar ya kammala masters d'insa a Birmingham Na k'asar biryani ya dawo ya rungumi kasuwanci babansa Na canji a Abuja. Maganarsa da Amrah ta nuna da zarar ta kammala karatunta za'a yi biki.
Shirye shiryen cikar Baba Babba shekaru tamanin da biyar a duniya suke yi. Wata irin liyafa aka shirya mass. Dukkansu yayan gidan sai da suka baro k'asashe da garutuwansu suka dira a Funtua.
Kowa d'auke da kyautukan girma daban daban.
Abida da y'arta ta zo mai sunan MAMI tana yawonta ko ina.
Taro ya kai taro. Ya'ya sun girma sun zama manyan k'asa. Farincikin Baba baya misaltuwa. Ba abinda ya saka shi hawaye irin yadda shi kad'ai yake ganin yadda y'ay'ansu suka zama zarata masu rik'e da mukamai daban daban. Baba K'arami bai ga hakan ba.
Aysha da Hafcy sun zo kowacce da goyonta.
Bayan an gama ciye ciye tare da yanka kawataccen cake din deenasnakck and more Kano. Da Hamida ta zo da shi tare da snacks dinsu masu dadin gaske.
Cikin nutsuwa aka dinga yin hotuna.
*Na ce kin karanta littafin Malamin bogi na Maman Afra kuwa?*
*To Ruwa cikin cokali fa?*
*Gaskiya ku bibiyi books din nan zaku nishadantu*.
*Ku tuntubeta kai tsaye*
9030283375.
Sai da ya jasu sallah.
Kowa ya nutsu gaban Ubangiji.
Sannan Baba ya juya garesu gabad'aya yana mamakin yawansu su da y'ay'ansu.
Ya yi gyaran muraya tare da yi musu sallama.
Suka amsa dukkansu a sanyaye don kuwa lallai Baba nasiha zai yi musu mai shiga jiki.
Ya ce "Na yi farincikin ganinku gabadaya. Na samu nutsuwar ba zaku kaskanta ba don kuwa kun hada kai kowa kuma yana neman na kansa.
Ina yi muku nasiha ku ji tsoron Allah, ku yi ibada, ku tsare ya'yanku daga fitowa a social media suna bayyana tsaraicinsu da sunan wayewa. Ku guji barci mai yawa don kuwa mabudin lalaci ne, lalaci kuwa yana haifar da dauwammen talauci. Ku guji shirka don cinye imani take yi tamkar yadda wuta ke cinye karmami. Shirka kala kala ce. To ku kula don da yawa mutanen yau suna cikin halakar sun kafirta basu ankara ba. Da yawa idan tsautsayi ko azal ya samu mutum ko jarabawa sai a jinginawa wani tare da gasgata sa hannuna ko wanene ya yi mini shihiri ko sammu. Duk abin da kuka ga same ku mai kyau, to ku jinginawa Allah. Ku yi masa godiya mai yawa. Idan marar dad'ine ku jinginawa jarraba da k'addara da ta same ku kai tsaye da aka rubuta cikin littafin k'addararku. K'addara kuwa bata sauyawa amma tasirin addu'a yana dakushe kaifinta. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:50]
Kada ku ci kudin ruwa don Annabi ya la'anci mai cinsa.
Ku guji sauya halitta Annabi ya ce tsinannunu masu feke hakori don su yi wishirya da masu aske gira. Manyan malaman addini sun ce masu sauya halitta daga bak'i zuwa launin fari da masu k'ara girman mazaunai ko kirji duk sun shiga cikin tsinuwar. Kunsan kuwa ko LIMAMIN unguwarku ne matuƙar mumini ne ya tsine muku ai kun yi hannun riga da yin albarka bare ma'aikin Allah.
Ku yi iyakacin k'ok'arinku akan tarbiyar yaranku, ku kula da wa suke mu'amala.
Ku guji hassada don kuwa durk'ushe mai yi take yi. Ku guji yanke hukunci cikin tsanani don yana janyo nadama. Ku guji b'arin zance don tuntuben harshe yafi tuntuben k'afa zafi.
Ku kame daga yawan surutu marar amfani, ku yawaita istigifari. Ku dinga nazarin yadda aka yi mana kunnuwa biyu, idanuwa biyu amma baki daya. Ba dan komai ba ne illah jinmu da ganinmu su fi furucinmu yawa.
Ku guji zina, ku nisance ta don kuwa tana kan gaba wajen gadar da talauci bayan haka kuma naso take yi cikin zuri'a tare da cinye imani. Annabi ya ce zina bashi ce. Ku tsare kanku, ku tsare bayanku daga fad'awa tarkonta.
Ku guji yada bacin rai. Ku dinga boye laifin wanda suka saba muku don yada shi yana haifar da gaba.
Ku yawaita yiwa magabatanku addu'ar rahma.
Ku yiwa kanku tanadin lahira tamkar yanzu zaku tafi. Haka nan ku nemi duniya tamkar ba zaku mutu ba. Kowa ya nemi na kansa kada ku dogara da mutum guda. Duk zuri'ar da ta zubawa mutum d'aya ido take jiran tallafinsa da wuri zasu dirkake don kuwa Allah ne kad'ai zai iya da bukatunku babu gajiyawa. Ku nunawa ya'y'anku muhimmanci dogaro da kai. Kowa ya nemi na kansa sai zumunci ya yi dad'i. Duk zuri'ar da kowa yake neman na kansa suke karatu zasu yi karfi su d'aukaka zasu daina zubawa mutum d'aya da ya yi shura a cikinsu idon ya yi musu hidimar dole da bata dole ba, idan bai yi ba kuma, sai a tisa shi a gaba da kushe da gaba. Mafi yawa irin wadannan sun yi iyakacin kokarinsu yau da gobe ce ta sanya suka gaza ko suka daina yi. Amma idan kowa na da sana'a komin ƙanƙantarta za'a samu sauk'in zarmewar da ake yi na jiran wane ya bayar.
Masu kud'in ma a yanzu da rayuwa ta tsananta nemansa suke yi kasuwanci suke yi iri iri, ya'yanasu ma sana'a suke yi don su samu kudin, to akan me za'a yi ta zuba musu ido a kullum su bayar?"
Daidai nan ya yi shiru yana nazarin yadda jikinsu ya mutu tub'us wasu ma k'walla suke gogewa. Ya nisa ya cigaba da fadin ku rarraba ya'yanku su karanci fanni daban daban ta yadda duk wata kafa kuna da k'afa. Ku yi kasuwanci, ku yi Nima Annabi ya ce arzikin Duniya na kasuwa da gona. Ku yawaita istigifari don mabudin alheri ne. Duk abin da ya yi muku tsanani ku yawaita zubar masa istigifari Allah zai warware muku cikin hikimarsa.
Kada ku tsangwami wanda kowacce ta samu jinkirin aure don wannan ikon Allah ne. Duk saurin mai sauri sai ya jira ikon Allah. Aure, haihuwa da mutuwa lokaci ne ba'a yinsu sai lokacinsu ya yi.
Annabawa uku a jere da Allah ya ambacesu cikin suratul Maryam. Ilyas Yahya da Isa (A.S.). Basu taba aure ba. Amma rashin aurensu bai hana a basu annabta ba kenan idan mutum a kame yake rashin yin aure ba tawaya ba ce, tunda ko a shari'a ma ba farilla ba ce, sunna ce mai karfi.
Nana Aisha bata taɓa haihuwa ba, ita ko bari bata taba yi ba, amma sunanta ba zai shafe ba a doron kasa ba, don kuwa sai aka azurta ta da ilimin da ta yada shi ciki al'umma. Rashin haihuwarta bai hana miji ya sonta fiye da kowa cikin matansa ba. Allah kuma da kansa ya ce yana jin nauyin wanda bai bawa haihuwa ba Ashe kuwa duk wanda ya tsangwamesu Allah yake yiwa isgili, ya jira kuma hukunci ta inda bai yi zato ba.
Ku dinga rabon gado da wuri tare da iyakance dukiyar kowa ya hanyar rubutu.
Wataƙila yaune had'uwarmuta k'arshe da wasu daga cikinku. Ina rokonku ku girmama manyanku, manyan kuma ku tausayawa kannenku, ku mu'amalancesu da kyautatawa.
Allah ya taimakemu gabad'aya. Allah ya yi muku albarka ya rufa muku asiri duniya da lahira ".
suka amsa da fadin ",Ameen Baba Allah ya kara maka lafiya da imani".
Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:54]
*DINGISHIN KWAD'O*
*SURAYYA GWARAM*
08032773332.
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
*Epilogue*
Bayan shekara biyu.
Ana ta Shirin auren Ammar da Amrah ta kammala karatun likitanci tana housemanship a specialist Hospital Abuja.
Farha tana jikin Bilki ta ce "Mahmah kinsan me ya ya Faruku ya ce min?"
Bilki ta jijjiga kai tare da fadin a a ".
"Wai na tambaye shi budurwarsa ta alkalam ya ce abokiyar karatunsa ce. Farha ce matarsa. Na ce a ina take wai a Abuja gidan Mahmah".
Mahma to dama Yaya da kanwa suna yin aure ne?"
Bilki ta ce "Basa yi ".
Daga haka ta shige wanka ta barta zaune a bakin gado.
Ta koma d'akinta.
Ta kira shi a waya. Yaya Faruku ka rikita ni fa. Kuma Mahma ta ce "no".
Ya ce "saboda me to?"
Saboda Yaya da kanwa basa yin aure mana".
Ya ce "Ki ce mata da gaske nake yi dan haka mu za'a fara a kanmu.'
Kwanaki biyu a tsakani ta sake tambayar Bilki. Mahma dan Allah ki fad'a mini wacece babar Yaya Faruku dan Allah? Don har cikin zuciyarta ga ni take yi sai dai idan ba shi Mahmah ta haifa ba amma ba ita ba kam.
Bilki ta ce "Alti ce'.
Farha ta rike kirjinta tare da fadin Ashe "Da gaske yake da ya ce ba ke kika haife shi ba. Allah sarki".
Bilki ta wuce ta tana jin yanzu ya yi wuri da yawa.
Tunda Bana zai kammala digirin dole ya wuce wata k'asar ko baya so don ba zata yarda ya damawa Farha lissafi ba.
Zuwa yanzu Farha ta wasiwasi take yi akan su waye suka haife su ita da Faruku?
Dole akwia wanda ba Mahmah ce ta haifa ba a cikikinsu. Haka kawia take fatan Allah yasa ita ta haife ta. Amma tana jin soyayyar ammi da su junior a ranta fiye da kowa a cikin daginsu. Sannan yadda take ganin soyayyarta a idanuwan Mahmah haka take gani a idanuwan ammi.
Ana yin hutu Noor da Farha suka cewa Dady suna son tafiya Saudi gidansu junior daga nan su yi umrah. Bai k'i ya amince aka fara nema musu visa.
Da zasu tafi sai da Abida ta matsa a tafi mata da ciccibi da kazar sababi tunda freezing dinsu ake yi ba zasu narke ba tunda ba doguwar tafiya ba ce. Sanyi flusher ne aka tafi mata da saiwowin tunda bojuwa herbs suna bayarwa sia ka dafa da kanka tunda ba'a shiga da abu mai ruwa cikin jirgi.
*08032773332 contact Bojuwa herbs Kano for your special kayan mata ingattau amintattu.*.
Haka aka Abida ta matsa sai da aka yiwa maminta d'inkunan native wears don ta gamsu da k'warewar teler da Bilki take bawa dinkin Farha da take k'arama.
08080266674 ku wannan layin masu buk'atar su a dinga yiwa y'ay'ansu mata dinkuna irin na yan gayu y'anuwan masu kud'i.
Sun isa lafiya, junior ya yi murna ganinsu kamar me. Mami kanwarsa dai bata kama da shi da Farha. Gana ganinta ka Ga Abida. Tafi kama da khadijan oga da twins.
Farha ta daure ta tambayi Abida da ta ga Noor na barci, akan wacece ta haife ta ita ko Mahmah?
Abida ta murmusa ta ce itace mamanki mana. Shi kuma Alti ce ta haife shi".
Abida ta shige daki ta fashe da kuka.
Sulaiman ya diririce ya ce "menene?"
Ta ce "Tsufan da bana so ne yake sake shirin yanko mana ni da Bilki. Tunda aka saka auren Amrah nake ta rarrashin zuciyata kada na yi kuka. Sai kawai yanzu Farha take tambayata wacece ta haife ta, wacece ta haifi Faruk don ya ce yana sonta. Har y'ar Farhar nan ma girman ya zo kenan?"
Kuka take yi bilhakki.
Ya jijjiga kai ya yi dariya tare da fadin Abida duniya Farha na shirin kammala sakandire kina fadin yar yarinyace. Kuma wa ya ce tsufa zai yanko muku? Ni fa har yanzu kallon ki nake yi tamkar MAMI. Diyarsu mai shekaru hud'u. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:57]
Dad'i ya kamata ta goge hawayenta tare da fadin "Har na ji sanyi da nutsuwa."
Ya k'yalkyale da dariya tare da mamakinta.
Farha ta sake tambayar Sulaiman akan wacece ta haife ta a tsakanin Mahmah da Ammi dan Allah?
Kaitsaye ya ce mata Ammi ce ta haife ki. Amma Mahma ce mamanki don tun kafin ki zo duniya da shekeru goma ta bata ke".
Farha ta yi shiru. Ta ce "Kenan kaine Dadyna?"
Ya yi mata shiru.
Ta rike hannunsa ta ce "Ashe shiyasa nake jin ku tamkar yadda nake jin Mahmah