KUNDIN AL'AJABI BOOK 1 BY MANSUR USMAN SUFI .pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Hausa Read

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 20.6K words

kuma an samu nutsuwa sai sarki Jauwad ya miƙe tsaye daga
kan kujerarshi ya fuskanci al'umma ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku jama'ar wannan faɗa mai
albarka ku yi sani cewa a yau ne 'ya'yan mai martaba sarkinmu za su tafi izuwa fadar sarkin
bokayen duniya domin su tone sihirin tsafin da aka yiwa sarki wanda abokin gabar shi kuma
maƙiyin wannan ƙasa tamu ya yi mashi wato sarki Bazzagul-Nadiyar.
Bisa Wasiyyar da sarki ya bayar cewa dukkanin wanda ya tone wannan sihirin tsafi ya zo da shi
nan shi ne zai gaji karagar shi ya mulki.
Sa'adda boka Jauwad yazo nan azancen shi sai fadar ta kaure da cece kuce kowa na faɗin
albarkacin bakinshi, tsawon daƙiƙa ashirin ana cikin wannan hali sai daga bisani Jauwad ya

ɗaga hannunshi sama fadar ta yi tsit a karo na biyu sannan ya cigaba da cewa "Yanzu dukkan
wani abu na guzuri da abin hawa an tanadar masu abin da ya rage yanzu shi ne za a ɗora
Magajin gari a bisa KARAGAR MULKI, sannan bayan 'ya'yan mai martaba sun yi bankwana da
mahaifinsu mata za'a yi masu rakiya izuwa bakin ƙofar gari. Lokacin da boka Jauwad yazo nan azancen shi sai wani badakare ya matso daf da shi ɗauke
da wata akwatun baƙin ƙarfe ya ajiye a gaban shi ya buɗe ta ya ɗauko wani kambun Sarauta ya
miƙa mashi shi kuma ya ɗora kambun a bisa kan magajin gari da ke zaune a daf dashi a kan
kujerarshi, badakaren ya sake zira hannunshi a cikin akwatun ya ɗauko wata sharbebiyar takobi
a cikin kubenta ya risina cikin ladabi ya miƙa wa Boka Jauwad shi kuma sai ya damƙa a hannun
magajin gari,
Sannan shuraih ya miƙe tsaye ya je ya zauna a bisa KARAGAR MULKI take jama'ar dake fadar
suka risina da kawunansu a gare shi dake nuna mubaya'a a gare shi.
Koda kammala bada riƙon sarauta sai ni da 'yan uwana muka shiga zuwa gidan sarauta
domin yin bankwana da mahaifanmu kamar yadda boka Jauwad ya tsara,
Lokacin da na Kaɗaita da mahaifiyata a cikin turakarta sai na dube ta cikin alamun matuƙar
damuwa na ce "Ya ummina na ji a jikina cewa wannan gasa da aka sanya mana ita babu
tabbacin zan yi nasara domin duk abin da zai kai ga a samu nasarar 'yan uwa sun ɗara ni wato
jarumtaka da ƙarfin sihiri". Koda jin wannan batu daga bakina sai murmushi mai taushi ya suɓucewa mahaifiyata
al'amarin da ya yi matuƙar bani mamaki kenan na dube ta nace "Ya ummina shin ina dalilin
wannan murmushi na ki?.
Dajin wannan tambaya sai mahaifiyata ta yi buɗe baki ta ƙura mani idanu ko kiftawa bata yi ta
fara magana a karo na farko "Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa haƙiƙa bani da wani buri
da huce naga cewa kai ne ka gaji sarki ba 'yan uwanka ba, kuma dukkan maganar da ka faɗa
tana kan gaskiya, Abin da ya sanya ni murmushi kuwa shi ne kana tare da abin da yafi na 'yan uwanka kuma
matsawar ka yi riƙo da shi zai zaka samu nasarar cinye wannan gasa",
Cikin matuƙar mamaki na dubi ummina na ce "Ya ummina shin ina dalilin wannan furuci na ki
kuma wane abubuwa ne nake d su wanda idan na riƙe su zan samu nasara?,
Ummina ta ce "Ya ɗana ka yi sani cewa tun da na mahaife ka na tabbatar da cewa na haifi yaro
nagari kuma mai nasara a rayuwa, tun kana yaro ƙarami na fahimci halayen ka masu kyaune
saɓanin 'yan uwanka,
Ka yi sani cewa a halin yanzu a duniya komai kake taƙama da shi akwai wanda ya huce ka
domin masu iya magana na cewa "Kamai sammakon ka wani a hanya ya kwana"
Wato idan jarumta, sihirin tsafi ko ƙarfin mulki kake taƙama da su cewa sune zasu bada nasara
a cikin 'yan uwanka akwai waɗanda suka shafe ka,
Abin da kake da shi wanda 'yan uwanka basu da shi da idan ka rike su zaka samu nasara su ne
kamar haka,
Gaskiya, Tausayi, Amana da hakuri waɗannan sune halaye mafi daraja da dukkan wanda ya
riƙe su zai cimma nasara a rayuwar shi kuma babu wani abu da zai sanya a gaban shi face ya
samu nasara,
Gaskiya dai zata ƙara maka daraja da ɗaukaka a cikin dukkanin harkokin rayuwa kuma ita ce ke
bayyanawa jama'a darajar da mutumtakar ɗan Adam,
Tausayi kuwa na sanya soyayyarka a cikin zukatan al'umma har da maƙiyan ka,

Amana kuwa na ƙara wa maka ƙima da daraja a cikin kowacce irin al'umma ka shiga,Hakuri
kuwa zai sanya ka cimma nasara a dukkan abin da ka sanya a gaba, domin duk kyawun abu
idan baka yi hakuri ka cimma karshen shi ba to abu biyu zai faru,
Da farko shi ne zaka rasa wannan abun, sannan ka yi asarar lokaci da lafiyar da ka ɓata a kan
shi,
Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa waɗannan halaye sune sinadaran shaharar duk wani
tauraro a duniya, Na so a celokaci bai kure ba da baka tsakure daga hikayar jarumi Masnur ibn
Abdullah da wani fasihin marubucin hikayoyin wannan ƙarni wato Sufi ya tattara kuma ya sanya
littafin suna KUNDIN HIKAYA, Tabbas da zaka ƙara tabbatar da batu na kuma ka ƙara ƙanƙame halayen da kyau".
Lokacin da na ji wannan dogon jawabi daga bakin ummina sai na cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa ban sa'adda na rungume ta ba ina mai cewa haƙiƙa na aminta da ke ummina
ɗari-bisa-ɗari, da yardar abin bauta ba zan ketare wannan wasiyya ta ki ba, kuma zan samu
nasara bisa abin da na fita nema fatana na dawo na same ki cikin ƙoshin Lafiya". Sa'adda da na zo nan azance na sai mu duka biyun muka fashe da kukan farin ciki, dakyar da
siɗin goshi muka rabu da juna suna masu zubar da hawayen baƙin ciki na shaƙuwa da juna.
Lokacin da na isa fada sai na tarar dukkan 'yan uwana sun hallara ni kaɗai ake jira domin
haka ina isowa sai aka ɗunguma izuwa wajen fada muka kama dawakai muka haye dake dauke
da abin guzuri, kai tsaye boka Jauwad tare da magajin gari Shuraih haɗe da sauran mutanen
gari suka yi mana rakiya har zuwa bakin iyakar gari suna masu yi mana fatan samun nasara, Lokacin da muka nausa zuwa cikin daji sai muka cigaba da tsala gudu a bisa dawakai sai da
muka shafe tsawon sa'a ɗaya muna tafiya babu sassauci lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta cika a
dai-dai wannan lokaci ne mu ka iso wata mararraba a dajin da ta kasu gida huɗu,
Sai yarima Zafiyar ya durfafi hanyar yamma, Laswil kudu, Rumailat arewa sai ni kuma na yi
gabas, dukkan 'yan suna kallon juna cikin matuƙar ƙiyayya amma ni sai na dunga sakar masu
tattausan murmushi a haka har mu ka ɓacewa juna da gani.
Lokacin da cigaba da tafiya a cikin dajin sai na wanzu ina tsala azababban gudu a bisa dokina
ta hanyar ratsa duwatsu, ƙoramu, bishiyu da sarƙakiya,
Sai da na shafe tsawon sa'a biyar ina wannan tafiya a dai-dai lokacin ne na fahimci cewa dokina
ƙarfin gudun shi ya ƙaru ainun domin haka sai na ja linzamin shi na tsaya cak! na sauka ƙasa
na zauna a ƙarƙashin wata itaciya na fito da abin guzuri na domin na yi kalaci shi kuma dokina
ya shiga yin kiwo yana cin ciyayin da ke dajin, Ina cikin yin kalacin ne kwatsam bazato babu tsammani sai na ji kwantsama wata tsawa gami
walƙiya cikin ƙankanin lokaci sararin samaniya ta canza launi izuwa baƙi,
Cikin wani irin baƙin zafin nama na miƙe tsaye zumbur gami da mayar da abin kalacin izuwa
cikin jakar guzuri na gami da zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayana,
Kwatsam sai na ga dokina ya faɗi ƙasa ƙasa yana shure-shuren mutuwa, Cikin kaɗuwa na ruga
zuwa inda ya ke kafin na isa har rai ya yi halin shi, cikin matuƙar takaici na tsugunna a gaban
shi cikin alhini a lokacin ne na lura cewa wani irin baƙin ruwa mai yauƙi na fitowa daga bakin
shi, koda na shin-shina ruwan sai na ji alamun akwai guba a cikin shi hakan ya sanya na
fahimci cewa tabbas ciyawar da ke dajin ita ce ke ɗauke da wannan guba,
Cikin matuƙar fushi na miƙe tsaye zumbur gami da kwarara wawan ihu, faruwar hakan ke da
wuya sai duhun da ke sararin samaniya ya washe tamkar bai taɓa wanzuwa ba,

Kwatsam! sai wani ƙaton kai mai ɗauke da kawo biyu da fala-falan kunnuwa irin na Zomo haɗi
baki irin na jemage ya faɗo tim, sannan hannaye, kafafuwa, gangar jiki suka biyo baya, ko da
ganin hakan sai na ƙara riƙon takobina ina zuba idanun,

Sannu a hankali sai sassan jikin suka dunga haɗuwa da 'yan uwan su har sai da halittar surar ta
kammala, kafin na ƙarewa surar kallo wani sulken yaƙi da makamai sun bayyana a gare ta,
A lokacin ne na fahimci cewa tabbas surar aljani ne ba bil'adama ba saboda waɗansu fuka-fukai
da suka bayyana a gwiɓin hammatarsa guda biyu,
Tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin halitta mai kwarjini da ban tsoro tamkar halittar ba domin
haka sai yanayin tsoro ya kama ni har gumi ya fara tsattsafo mani a fuska amma saboda ƙi faɗi
Irin ta 'ya'yan sarakai sai na basar.
Ko da aljanin ya lura da hakan sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da
haniniyar doki, Sai da ya yi dariyar ta ishe shi sannan ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi
da Saƙon mutuwa,
Kawai sai ya zare wani makami a jikinshi mai kama da lauje ya yi ɗauki izuwa Kai na yana ihu
da kururuwa mai firgitarwa,
Ko da ganin hakan sai nima na ruga gare shi domin tarar juna muna haɗuwa muka ruguntsume
da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
Muka wanzu muna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta
MAZAN JIYA masu juriya a filin fama, Idan ka ɗauke sautin kaɗawar iskar dake sanya rassan
bishiyu rangaji babu abin da kunne ke ji face ƙarar karafniyar makaman yaƙin mu da ke
haddasa tartsatsin wuta gami da ƙara mara daɗin saurare,
Sai da muka shafe tsawon rabin sa'a muna wannan baƙin artabu babu sassauci a lokacin ne na
fahimci cewa tabbas na gamu da gamo na, Domin ƙarfin saran aljanin ya nunka nawa sau uku,

A wasu lokutan idan ya kawo mani hari idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa sannan
na taso sama na mayar da martani,

A cikin wannan artabu ne aljanin ya kawo mani wani nagartaccen sara da nufin ya tsinke mani
wuya, cikin zafin nama na sunkuya makaminshi ya sari iska, Kafin ya sake wani yunƙuri ya sake
kawo mani wani harin a kwaɓin cinyata ta hagu duk ƙoƙarin da nayi domin naga na kaure amma
sai da makamin ya yanke ni a cinya jini ya yi tsartuwa na kurma ihu sakamakon raɗaɗi da zugin
da na ji.
Kafin cikar daƙiƙa ashirin ya samu nasarar yi mani raunuka biyar ɗaya a cinya biyu a
kafaɗata ta dama sauran biyun a damtsen hannuna na hagu kowanne rauni na zubar da jini,
Nan fa wani irin zazzaɓi mai matuƙar zafi ya kama ni, jiri ya fara ɗiba ta ina faɗuwa ƙasa, amma
saboda da JURIYA DA JARUMTA irin ta MAZAN JIYA sai na miƙe tsaye a haka na ci gaba da
kare kaina ba tare da mayar da martani ba.
Lokacin da rabin sa'a da daƙiƙa ɗari biyu da hamsin ta shuɗe ana wannan artabu
kwatsam! Bazato babu tsammani sai na wata hikima ta faɗo mani a rai, koda jin hakan sai na yi
wuf na dunƙule hannuna ya kirɓawa aljanin naushi a kwiɓin hammatarshi saboda ƙarfin naushin
sai da ƙashin hannun ya karye ya yi ƙara ruƙus! Aljanin ya kurma ihu sakamakon zafi da
raɗaɗin da ya ji.

Koda na fahimci cewa ashe sam makami ba ya tasiri akan shi nan take na yi jifa da
takobina na shiga kai mashi bugu da naushi hannu da ƙafa.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta
canja, nan fa yazamana cewa cikin ƙanƙanin lokaci na yi mashi jini-jina baya iya mayar da
martani, kawai sai na yi wuf na kama wuyan shi na murɗe da ƙarfin tsiya, nan take na jefar da
gawarshi gefe guda ko shurawa bai yi ba. Koda samun wannan gagarumar nasara sai na cika da matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa
na ɗauki takobina na ci-gaba da tafiya ina takawa daƙyar bisa ƙafafuna na durfafi wata hanya,
tafiyar daƙiƙa ɗari kacal nayi na iso wata ƙorama da ruwan cikinta yakasance garai-garai
gwanin ban sha'awa, cikin matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa ya sanya hannayena biyu ina
kamfatar ruwan ciki ina sha. Sannan na miƙe tsaye na durfafi wata bishiyar tuffa na tsinka na ci
na ƙoshi.
A sannanne na ji ƙarfin jikina ya dawo kuma sanyi da zazzaɓin da nake ji sun rabu da ni.
Nan take na ci gaba da tafiya ina sake kunna kai izuwa cikin dajin ina tafiya cikin hanzari.
Tsawon kwanaki uku na shafe ina tafiya a ranar kwana na ukun ne na iso izuwa gabar wani
ƙaramin tsibiri mai ɗauke da bukka guda ɗaya jal, a gaɓar tsibirin wani makeken kogi ne mai
tsawon gaske da ba a iya hango ƙarshen shi. Nan take na fahimci cewa ba zai yiwu na iya
ƙetare wannan kogi ba face na ha samu kwale-kwale, don haka sai na isa izuwa bakin wannan
bukka na yi gyaran murya har sau uku. Jim kaɗan sai ƙofar bukkar ta buɗe sai ga wani dattijo
dogo mai matsakaicin kaurin jiki ma'abocin kamala da haiba sanye da jajayen tufafi a hannun
shi yana dogare da wani kwagiri. Sannu a hankali ya tako da ƙafafuwanshi har yazamana ya iso
daf da ni ya ƙura min idanu.
Fuska ta cike da annuri na dube shi na yi gyaran murya na ce "ya kai wannan dattijo
ma'abocin kamala ni matafiya ne hanya ta biyo da ni domin nemo wani abu mai matuƙar alfanu
gare ni, ina so ka taimake ni da jirgin ruwan da zan iya ƙetare wannan kogi, kasancewar na rasa
abin hawa na? Koda jin wannan tambaya sai dattijon ya buɗi baki ya yi gyaran murya cikin kakkausar murya
ya ce "ya kai wannan matashi ka yi sani cewa idan har ka amince da wasu sharuɗɗa da zan
gindaya maka to zan ƙetarar da kai daga wannan kogi.
Sharaɗi na farko shine zaka zauna da ni na tsawon mako takwas domin ka taya 'yata noma da
kiwo.
Sharaɗi na biyu kai ne zaka dinga nemo mana abin kalaci na nau'in dabbobi,
Sharaɗi na ƙarshe shine duk kaine zaka bamu tsaro a duk lokacin da muke barci.
Waɗannan su ne sharuɗɗan kuma ka yi aiki bisa amana to ina mai tabbatar maka da cewa zan
haurar da kai akan wannan teku kuma zaka cimma nasara akan abin da ka fito nema.
Sa'adda na ji waɗannan sharuɗɗa daga bakin dattijon sai nayi shiru ina mai zurfafa cikin
kogin tunani.
Abu na farko da ya faɗo min a rai shi ne "shin yanzun kana ganin cewa idan ka ɓata tsawon
mako huɗu 'yan uwanka ba za su cimma nasara ba.
To amma kuwa shin akwai wata hanya da mutum zai iya isa gidan boka Bazzagul-Nadiyar
batare da ya ƙetare wannan kogi ba,
Kenan hakan ya tabbatar cewa dukkanin 'yan uwana sun iso wannan waje ko kuma za su iso
anan gaba.
Kaga kenan a cikin su babu wanda zai iya amincewa da sharuɗɗan dattijon".

Lokacin da nazo dai-dai nan a tununi na sai na dubi dattijon na ce da shi na amince da
dukkan sharuɗɗan ka kuma ina mai tabbatar maka da cewa ba za ka same ni mai cin amana
ba";
Koda jin wannan batu sai dattijon ya yi murmushi mai taushi ya ce "zuwa gobe da safe bayan ka
huce gajiyar dake tattare da kai.
Daga wannan batu ne dattijon ya juya ya kunna kai izuwa cikin bukkar yana mai yafito ni da
hannu yana nuni da na biyo bayan shi.
Lokacin da muka shiga izuwa cikin bukkar sai na tarar ta kasance mai girma da faɗi kuma tana
ɗauke da ababan more rayuwa abin da ya haɗar da gadaje biyu, shimfiɗu da sauransu, bayan
na zauna a bisa shimfiɗar sai dattijon ya yi gyaran murya da ƙarfi jim kaɗan sai ga ƙofar bukkar
ta buɗe sai ga wata budurwa ta shigo ɗauke da Alhaji da salkar ruwa, budurwar takasance mai
matsakaicin kaurin jiki ba doguwa ba ne ba gajere ba, fatar jikinta takasance mai tsantsi
luwai-luwai tamkar ta jariri sabon haihuwa, ƙugunta mai faɗi ne da tudu ta yadda koda kofin
lemo aka ɗora zai zauna daram daga gaba kuma ya tsuke, ƙirjinta a cike yake kuma a tsaye
ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, fuskarta rufe take da baƙin yanki
idanunwanta kaɗai ake gani waɗanda suka kasance dara-dara farare ƙal masu haske tamkar
tacacciyar madarar shanu baƙin cikinsu yakasance ɓaƙi siɗik, gashin kanta baƙi ne mai sheƙi ya
zuba har izuwa kan kwankwasonta. Sanye take cikin tufafi masu yalwa na fatun dabbobi.
Koda na haɗa idanu da budurwar sai na ji zuciyata ta buga da ƙarfi wani abu ya ɗarsu a
zuciyata.
Budurwar tana takawa a hankali cikin ƙasaita irinta JININ SARAKAI ta iso

2 / 7