Zafin Rana Book Compelet Aisha Alto

Author :  Aisha Alto Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 28

18K to 21K   out of 81.6K words

 kun dawo?

Binta tace eh tana kallan bangaren Junaid.

Barira tace  kije ki huta shima ya tafi bangarensa saboda ya gaji wai yana san hutawa.

Binta tai shiru cikin rashin jin dadin ya tafi ya barta ta shiga ciki.

*******

Azeema ta dade acan kafin ta fito ita da kuyanginta.

Junaid ya kalli Hari yace  Hari haryanzu Binta bata karaso ba?

Tace  Yarima!

Itakam Hari girma duk ya fara zuwa mata ta kuma san zamansa da Binta bazai yiwu yanda yake

"tunani na, sai dai batasan me xatace mai ba."

"Junaid ya kalleta yace  Hari ki tura a dubo, dan tazo taga nan. "

Hari tace to Yarima ta fito.

"Shiru tai tare da kallan Azi wanda shima kallanta yake, su sun san yanzu Junaid zai san me ake nufi"

"da sarauta, ilolinta, matsaloli da kums kalubalen dazai fuskanta....."

*********

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Hudu

"Har bayan sallar isha i Junaid baiga Binta tazo ba, ga abincin dare an jera mai amma baibi"

"takansu ba, hankalinsa ne ya tashi, fitowa yai ya kalli Kuyangun dake tsaye bakin kofa ya kalli ta"

farkon yace  Ina Hari?

"Tace tana daki, yace  kinsan bangaren Umma? "

Tace  Gimbiya Azeema?

"Yace  eh, kije kice ma Binta tazo. "

Tace  to Yarima sannan ta juya.

********

"Binta zaune a gaban Azeema, Azeema cikin sakin fuska tace  Binta nasan kin damu da Junaid"

"sannan kin shaku dashi ta yanda bama zato a lokacin da bashida kowa sai ke, sai dai ina neman"

alfarma daya daga gurin ki.

"Binta ta kalleta kadan sannan ta maida kanta kasa, Azeema tace  dan Allah ki dan janye daga"

Junaid.

"Gaban Binta ne ya fadi, hankali a tashe ta kalleta, Azeema ganin yanda abin ya shigeta yasa ta"

murmusa tace  ba cewa nai ki janye daga gareshi gaba daya ba alfarma nake nema ki dan bari wannan uwar data rabu da danta shekara da shekaru ta dan samu damar shakuwa dashi na wasu

yan lokuta.

"Idanun Binta ne suka ciciko. Azeema tace  nasan zaki fahimceni, kimin wannan alfarma kinji"

Binta?

"Binta ta daga kai alamar to hawaye suka gangaro mata, Azeema ta rike hannunta tace  nagode"

"kwarai da yanda kika taimaki dan nan nawa, ma tabbatar samunki kusa dashi ne yasa ya iye jure"

rashin mu.

"Wasu hawayen ne suka cigaba da zubo mata, Azeema ta kalli Barira tace  kuje da ita gobe a"

hado mata abubuwan bukata.

Barira tace  to Gimbiya.

"Nan Binta ya mike tai bangaren su Barira, tana shiga ta tsugunna tana hawaye, duk da ta fahimci"

"Gimbiya sai dai tana ganin ba a mata adalci ba ana neman rabata da Junaid wanda bataji ko yini zata iyayi bashi, a yanzu haka ma ji take kamar ta ruga inda yake."

Binta na shiga daki Barira ta kalli Gimbiya cikin jin dadi tace  Gimbiya kinyi maganinta.

"Azeema ta girgiza kai alamar a a tace  matsalar ba ita bace Junaid ne, me kike tunanin zai faru"

in mutane sukasan ya dawo da mace sannan ba matarsa ba? Macen ma mara asali?

Barira tace  ya zamuyi gobe?

Da safe ki kiramin jakadiya.

"Jakadiya? Barira ta tambaya, Azeema ta mike ba tare da ta amsa mata ba, taje shiga daki baiwar"

da Junaid ya aiko ta shigo ta sanar da Barira sakon Junaid.

"Barira tace  wayyo tayi bacci, tun dazu dama take cewa bacci takeji kanta na ciwo. "

"Kuyangar nan da jin haka ta juya, Azeema ta shiga ciki."

"Zama tai a bakin gadon ta kalaman Junaid ne ke mata yawo, tabbas akwai wani dalilin dayasa"

"Sarki ya daukeshi, to menene dalili? Baiso danta yai mulki? Kai ta girgiza da sauri dan tasan ba shi bane, tabbas gobe zata bigi cikin Jakadiya taji ko ta san wani abin, dan da dukkan alamu Abdulsalam ma baisan komai ba."

Ta dade tana juye akan gado kafin ta samu bacci ya dauketa.

***********

"Jin Binta tayi bacci yasa ran Junaid yadan sosu, sai dai baiyi zargin komai ba, yana nan a zaune"

yana tunanin cin abinci Azi ya kwankwasa mai.

Bayan ya shigo ne ya sanarwa Junaid akan Sarki AbdulSalam na san ganinsa.

Tare suka fito da Azi dan dama bai sanshi ba bai taba ganinsa ba.

"Sun isa fadar mai martaba, yana zaune an jera mai abinci a gabansa, Ji Zagi na sanarda isowar"

"Junaid ne yasa ya kalli bakin kofa, har Junaid ya shigo ya zauna daga can gefe idanunsa na kansa, wani sansanyan murmushi ya saka ya nuna masa kusa dashi yace  dawo nan. "

"Junaid ya karasa sannan ya gaisheshi, Abdulsalam ya amsa cikin tsananin kulawa sannan yace"

 Junaid!

Kallansa yai sai gani yai yayi murmushi wanda yasa Junaid din dan murmusawa kadan shima.

Wai kaine ka zama saurayi haka? Wasa wasa in yaro ba agabam mutum ya taso ba saurin girman

sa zaka gani.

Junaid baice komai ba sai dai yanda yake maganar yasa ya dan saki jikinsa.

Abdulsalam yace  bismillah.

"Ya fada yana mikamai spoon, Junaid ya amsa sannan suka fara cin abinci tare, sai turomai gabansa"

"yakeyi wanda yasa Junaid din aake murmusawa, Sarki ya kalleshi bayan sun gama yace  Junaid! "

"Junaid ya kalleshi tare da maida hankalinsa kansa, ka yafemin nasan duk da umarni ne na"

"mahaifinka ban kyauta ba na barinka danai, da alama san kai nane yamin yawa?"

Junaid cikin mamaki tace  san kai?

"Abdulsalam ya jinjina kai alamar eh, yace  kamar yanda kasani mahaifinka ne sarki, ban taba"

"tunanin amsar mulki daga gunsa ba aka sari maban taba kawowa zan mulki kasarnan tamu ba, sai"

"dai daga sanda Yaya ya furta min naji sha awar hakan, sai dai nasan in har kana nan dole wasu sai sunyi tunanin yin amfani dakai gun karya ni. "

Yadanyi shiru kafin ya kalleshi yace  san kai ko?

Junaid ya daga kai alamaf eh yace  san kai ne.

"Sarki ya kalleshi, Junaid ya murmusa yace  amma san kan mai amfani, akalla bakai kayi tunanin"

"fotar dani ba, sannan baka taba tunanin sauke mahaifina ka hau ba, sannan sai daya furta sannan"

kaji kanaso.

"Ido Sarki ya kuramai cikin tsananin jin dadin kalamansa, kafin yace  nayi mamaki. "

"Junaid yace  kayi hakuri in na bata maka, sau da dama nakanyi magana ne akan abinda raina ya"

bani.

"Sarki yace  hakan akeso ai, ya zama ko za aji haushi ka aji amma a kalla ka fadi abinda ka sani. "

"Junaid ya kalleshi suka murmusa a tare, Sarki yace  gobe za ai taron dawowar ka zakaga"

"mutane da dama da baka sani ba, yan uwanka da duk baka san dasu ba. "

Yace  haka Um 

"Sai yai shiru, sunan nama wahalar fada?"

"Ya kalleshi tare da dan shafar wuyansa, Abdulsalam yace  gashi nima so nake ka dinga kirana da"

Abba ba yanda kakecemin Kawu ba sanda kana karami.

"Junaid ya kalleshi da sauri, dariya sosai AbdulSalam yai wanda har fadawa sukai mamakin"

"wannan lamari, yace  wasa nake ma, wato har ka fara hangowa ko? "

Junaid yace  ya nuna?

"Sarki yace  sosai, sai kayi kokarin gun nuna abinda ke ranka, dan nan masarautace za ai amfani"

da abinda kake so a cutar dakai.

"Junaid ya jinjina kai alamar gamsuwa, me yasa yaji ya sake da mutumin nan daga haduwa daya?"

Lalai y cancanci a kirashi sarki yasan yanda zaiyi yaja mutum jikinsa.

"Sunyi sallama Junaid ya fito fuskarsa a sake, Azi yace da alama Yarima kaji dadin zuwan nan. "

Junaid ya kalleshi yace  ya nuna?

Azi yace  gashinan a fuskarka.

"Da sauri Junaid ya hade fuska yace  Azi, a duk lokacin dakaga ina kokarin bayyana abu a fuskata"

"kamin alama yanda zan gane, kafin na saba. "

Azi yi dariya yace  koyarwar da akai yau kenan?

Junaid ya ce  eh.

Haka suka wuce bangarensa ya zubawa abincin nan ido kafin yasa a kwashe sannan ya shiga ya

"kwanta, kan binta sosai yake mata ciwo? Yaso biyawa daga gun Sarki saidai yana tsoron karya tashesu daga bacci."

***********

"Hajjo ranta yayi mugun baci mikewa zaune tai a kan gadonta cikin tsananin takaici, yanzu"

"bangaren da take so ya barma Zubair har fadamai tayi shine ya ba wa wani Junaid? Fuskar tabta hade ranta yayi mugun baci, dan dama dazu da Ramlatu tazo haushi ya kamata da taga itama"

"Ramlatun yanzu tsoron Azeemar take, yanzu kuma sai taji wannan zance?"

Tayi tsaki yafi cikin kwano kafin bacci ya dauketa.

Da safe tana tashi aka kawo mata labarin cin abinci da hirar da Junaid sukai da Sarki jiya wanda har ana jin dariyarsa har waje.

"Cikin takaici ta cilar da kofin dake hannunta, wanda ya kusa bige Zeena datake kokarin shigowa"

"yanzu, tana ganin haka ta fara kokarin juyawa."

Cikin tsawa tace  ina zaki?

"Zeena ta juyo ta dawo ta zauna, Hajjo ta kalleta tace  kinba Sulaiman din hakuri? Kindai san"

gobe zai koma ko? Da yau dai tafi ma Takawa yace ya bari ayi taro dashi.

"Kallan Hajjo tai tace  ni wlh ba hakurin dazan bashi, koma naje kara batamai rai zanyi dan wlh"

ba sanshi na. 

Hajjo ta buga mata kallo tace  kema nema kike ki batamin rai? Dama tun shigowar yaran nan

masarautar nan raina yake baci kema so kike ki karamin da wani?

Zeena tace  Hajjo kinga Junaid din ne? Baki ganshi ba da ya sa kaya har 

 Kin rufemin baki ko sai na sa an kulleki a daki?

"Zeena ta kalleta a tsorace, Hajjo tace  me kike tunani zamuyi a cikin wannan yanayi, dan in"

muka bari abu yai gaba daga ni har ku ba wanda zai tsira...

"Zeena tai shiru dan tasan gaskiya Hajjo ta fada, dole su san mafita kafin abu yai tsamari......."

*************

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Biyar.

"Bangren Azeema tun safe ake ta baki, sai hidima aketayi, Safiya kam itace shugabar taro, sai"

"karban baki takeyi, suk ala ala take itama ta samu ganin kanin nata."

"Jakadiya ce ta shigo ta baya, inda ta shiga dakinsu Barira, Binta na gyara dakin ta shigo, kallan"

"Binta tai tace wacce ke gaisheta tace ""daga ina? Dan ban sanki anan ba?"""

"Binta tai kasa dakai dan batasan me zatace ba, Jakadiya tai dariya tace kin dade anan ne?"

"Binta tace ""a'a jiya nazo."""

"Jiya? A ranta ta maimaita sannan cikin dabara tace ""oh ko kece kikazo tare da Yarima Junaid?"""

"Binta ta daga kai alamar eh, Jakadiya tace da mace ya dawo kenan? Boyeta ake anan?"

"Jakadiya tace ""amma kamar ke ba baiwa bace bako?"""

"Binta tace eh, Jakadiya tai wani murmushin gamsuwa da abinda take tunani, fuskarta a sake tace"

"""ina Barira kice na shigo."""

"Binta ta leko, ganin yanda mutane sukai yawa yasa ta koma ciki, Jakadiya ta leka sannan tace"

"""daure ki fita."""

"Binta ta kalleta tace ""ban hango Bariran ba. "

"Jakadiya ta leko da kanta, daga can gefe ta hango Safiya na hidima tace  jeki gun waccen kice"

tazo Jakadiya na nan.

"Binta ta fito tana bin gefe gefe, ba wanda yabi ta kanta saboda sunata hirarsu, kusa da Safiya taje,"

"ta kasa mata magana saboda tanata magana da wasu, Jakadiya dake leke tana kallanta ta girgiza kai tace  tab harna tausayawa rayuwarki. "

Safiya ganin taki tafiya yasa ta kalleta tace  lafiya?

Binta tace  Jakadiya ce wai tana dakin can.

Safiya ta mike da sauri tai ciki gun Azeema.

"Azeema na zaune, Barira tana gyara mata kai, ga kujerar da take kai daga kasa turaren sura ne"

"aka sakashi yake turarata, kayan da zata sa na gefe."

"Safiya ta shigo ta sanar da ita zuwan Jakadiyar, Azeema wacce idanta ke lumshe ta bude su ta"

kalli Safiya tace  ki shigo da ita nan a boye.

"Nan Safiya ta juya ta nufi dakinsu Barira, Binta na tsugunr a gefe ta shigo nan tace  muje. "

Babban mayafi ta rufa mata suka wuce cikin dakin da sauri.

Suna shiga Azeema ta kalli Barira da Safiya tace  ku bamu guri.

Nan suka juya suka fita.

"Jakadiya na zube a kasa, Azeema ta kalleta sannan tace  Jakadiya! Ya zaman gun Hajiya inna? "

"Jakadiya ta dago tace  lafiya kalau sai abinda ba a rasa ba, ya sabuwar Jakadiyar? "

Azeema ta kafeta da ido wanda yasa Jakadiya sauke idanunta kasa tare da shan jinin jikinta.

Wani kasaitacen murmushi ta saki sannan tace  Me kike boyemin?

Kallanta Jakadiya tak tace  ni?

"Idanta na kanta batace komai ba, Jakadiya tace  me zan boye miki ni kuwa Gimbiya? Girma ya"

kamani me zai sa nai abinda zai sani cikin tashin hankali?

Azeema ta murmusa sannan tace  ya akai ni kuma nakeji a jikina kina boyen wani abin?

Jakadiya ta kalleta tace  Wallahi Gimbiya ba abinda nake boye miki

Azeema tace  na yarda wasa nake miki.

"Jakadiya tai ajiyar zuciya, Azeema ta sake kallanta tace  lokacin Marigayi akwai wani abu daya"

faru wanda har ya canza yanayinsa?

Jakadiya tai murmushi tace  Gimbiya dama ai dole akwai ranar da zakaji baka jin dadi ko a

"batama rai, balleshi Sarki? "

" Ba irin wannam nake nufi ba, yanayin da harku kuka san akwai matsala? "

"Jakadiya tai shiru tana nazari kafin ta kalleta tace  na kasa tuno komai Gimbiya, a gafarceni. "

"Azeema tace  shikenan, sai dai duk sanda kika tuno ki sanar dani. "

"Jakadiya ta mike, harzata fita ta juyo da sauri tace  Gimbiya! "

"Azeema ta kalleta, Jakadiya ta sake zubewa tace  akwai wani lokaci guda daya, wanda ko abinci"

"dakyar yakecin kadan, fita inba fadaba baya zuwa ko ina? In baki manta ba ko ku matansa inkum"

nemi ganinsa cewa yake ku koma.

"Azeema ta kalleta da sauri tace  na tuna, amma lokacin ya yanayinsa yake? "

"Tace  ba wanda ya sani, saboda shi kadai yake zama. "

"Azeema tai shiru kafin tace  nagode, zan aiko da sako. "

"Jakadiya tai godiya sannan ta rufa babban mayafin nan, tana fita Barira dama na kofa tai dakinsu"

da ita.

Jakadiya ta bude kanta sannan ta kalli Binta wacce haryanzu ita kadaice a dakin.

Tace  ina Yariman?

Binta tace  yana bangarensa.

"Jakadiya ta kalleta tace  inhar kinasan kasancewa dashi sai kin cire tsoron dake ranki, nan"

masarautace in kika cigaba da haka rayuwarki ma bazaki tsira da ita ba.

"Tana kaiwa nan ta fita, Binta tai shiru tana maimaita kalaman nata, itakam Junaid take san gani"

duk abin duniya ya dameta.

Tunani tai ko ta fita ta kofar itama ta nemeshi? Ko kallansa tai ta dawo?

Wannan shawarar tasata ta fita.

*************

"Yana zaune yayi shiru, wata hadadiyar alkyabba dakakiya mai matukar tsada da kyau Azeema ta"

"aiko mai da ita, kallo daya kayima Alkyabar nan sai ka sake kallanta saboda tsananin daukan idon da take dashi, ga wani hadaden takalmi na sarauta a gefe."

Fuskarsa kawai inka kalla zaka san duk wannan abin baya gabansa. Azi ne ya shigo ya kalleshi

yace  Yarima ya baka shirya ba?

Junaid ya kalleshi yace  an dubo Bintan?

Azi yace  anje itama wanka takeyi.

Junaid ya kalli kayan yace  jiranta nake tazo ga gani kafin nasa.

"Azi ya kalleshi yace  inka saka zaku hadu acan gun taron, kaga sai taci gani dakyau. "

Junaid ya kalleshi sannan yace  rikemin wannan nata ne.

"Azi ya kalli ledar ya bude ciki, dariya yasa yace  yanzu Yarima duk abinda kaci sai ka tafi mata"

dashi?

"Yace  kaima kasan Binta, ba lalai ta iya cin abinci acan ba, shiyasa zanyi magana mu dawo nan"

da ita.

"Hari dake shirin shigowa ta tsaya jikinta a sanyaye, sai dai tasan bazai taba yiwuwa ba."

"Azi ma kallansa kawai yake, dan yasan rayuwar dayai acan shida Binta basu isa ko rabi suyi anan"

ba.

"Junaid ya dau kayan ya shiga daki ya shirya, murmushi yai yace  harna hango idanki. "

"Aikowa akai akan ya fito, hakan yasa ya karasa shiryawa ya sa turare sannan ya fito."

Hari na hangoshi ta hau guda tana cewa  Yarima Allah ya kara lafiya ya kawo zuri a ta gari.

************

Cikin fada Hajjo ta kalli Fure tace  bata gama ba?

"Fure ta kara lekawa dakin sannan tace  yanzu take karasawa, Hajjo ta kalli Zubair ta mai alama"

daya mata magana sannan ta hade fuska tana cewa  ko uban me takewa kwalliya?

Fitowa tai tare da hade fuska tana cewa  dan Allah Hajjo ki bari na kara gyara fuska ba.

"Kallan mamaki Hajjo ta mata tundaga sama har kasa, bugagiyar hamshakiyar alkyabbar da akai"

rabin shekara ana yinta saboda taron sallah shi ta sa?

Zeenatu ta kalleta tace  nayi kyau?

"A hankali Hajjo ta kalli fuskarta, sannan ta maida idanunta kan kafarta, takalmin da Mai Martaba"

ya kawo mata wanda ko sashi batai ba shi ta sa?

Zeenatu tace  Hajjo!

"Bakin ciki tsabar ya cikawa Hajjo rai kasa magana tai, gaba kawai tai Zubair yabi bayanta, sannan"

itama ta bisu.

"Duk inda suka wuce kallan Zeenatu ake saboda tsabar haduwar datai, wanda koni sai dana sake"

waigawa.

*******

"Katan filin da aka gyara shi dan yin wannan taran suka nufa, masu hawan doki suna gefe suna jiran a fara dan suyi wasa."

"Masu wasan takobi ma na gefe, masu kidan kalangu ma suna ciki, busar sarewa kawai ke tashi."

Yarima wanda ya taho akan doki ne ya nufi bangaren Azeema dan su tafi tare kamar yanda ta

aika a sanar mai.

"Yana shiga yaga bangarenta makil da mutane, mamaki ne ya kamashi ganin jiya fa aka aika, ya"

akai mutane dayawa suka samu halarta haka?

"Nan ya fara gaisawa da mutane, kowa sai fara a yake ana

7 / 28