Author : Autar Alheri Category : Read Hausa Novels
agefen da yake zaune. Shigowa yayi yana kuka yana yiwa wannan Alhaji me mutunci godiya da addu'ar gamawa lpy, bakinshi bayi shiruba har sukazo ƙofar gidansu hamisha sha fitoda asiya ta galabaita iya gala baita aka sakata amota hamisha da ummanta ma suka shiga mutane nata kallon wannan dalla dallan motocin har sukabar ƙofar gidan, kai tsaye wata babbar asibitin kuɗi dake cikin garin barno yanufa domin mammalakin asibitin abokin ɗanshi ne....!
Follow me on arewa pen👇
https://arewapen.com/u/autaralheri
KWARATAN
ZAMANI paid book ne akan 1k kacal 👌zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 9112799371 moneypiont sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber👉 07037092176 on WhatsApp.
Autar alheri✍️
[21/04, 8:20 am] Autar Alheri✍️: 💋💋💋💋💋💋💋💋 *KWARATAN*
*ZAMANI*🫣🥳
💋💋💋💋💋💋💋💋
Humm fantastic special sexy and.... 🤭🤭 Love story ❤️
Writer by 🧐
Autar alheri✍️😘
💋💋💋💋💋💋💋💋
🍆🍉🍆💃💃
💋💋💋💋💋💋💋💋
Book 1
Page 19&20
"Suna zuwa aka karɓeta sedai duban farko Dr dake cikin asibitin yafara faɗa domin tagalabaita iya galabaita gaya bata iya haihuwar da kanta dole se anmata CS fitowa yayi gun Baba ila yace "baba wannan yarinyar bazata iya haihuwaba doline se anyi mata cs. "Innalillahi wani'inna ilaihi rajiun, baba yafaɗa cikin tashin hankali. Ganin yadda yake abirkice ne yasa wannan alhajin fitowa yazo gun Dr yana cewa "Dr munir miyafarune? "Wlh dady bazata iya haihuwa da kantaba ne dole se anyi mata cs ne. Subahanallah to Allah yarabasu lpy, kuje ayi duk abinda yadace kaji ku kawo takardar da za'asaka hannu aciki. "Okay dady. Daga hakan yajuya ya koma ciki.
Dady kuwa gun Baba ila yace "bawan Allah karka damu wannan ba komai bane in sha Allah fatanmu dai Allah yarabasu lpy cikin aminci. "Hakane Alhaji ngd sosai Allah yatemakeka kamar yadda ka temakemu Allah yarufama asiri kamar yadda ka rufa mana Alhaji ngd sosai wlh. "Bakomai ba wan Allah yanzu ina mijinta domin ana buƙatar sanya hannunku kafin amata aikin. Kwallah baba ila yashare kana yace "batada miji Alhaji kome za'ayi nizanyi in sha Allah domin ni mahaifinta ne. "Allah sarki to Allah yarabasu lpy? "Ameen aneen. Suna hakan Dr munir ya dawo da takardar da za'asaka hannu, dady ya kerɓa yanunawa baba ila inda za'asaka hannu tukunna yasaka. Shi kuwa Dr munir yana juyawa ya ɗauki wayarshi yana ƙara Kiran Saif. Akaro na huɗu kafin yayi bicking cikin ko in kula yana jan tsaki. "Wai saif miyasa kake ɗan renin hankali inata kiranka kaƙi ɗagawa, dan Allah ka fito theater ce ta gaggawa wlh yarinyar tana gab da rasa ranta domin tabugu da yawa kuma bazata iya haihuwaba, kana wlh dadyn Faris ne dakanshi yakawota garama kasani. Duk maganar da Dr munir keyi banza yayi mishi seda yaji ance dadyn faris ne yakawota tukunna yamiƙe domin yana ba'in ganin girman bawan allan a idonshi. "Okay I'm coming, yafaɗa cikin sweet voice ɗinshi tare da yanke wayar. Miƙewa yayi kawai ya ɗauki cer key ɗinshi ya fice daga gidan, kai tsaye yanufi asibitin
Koda yashiga sun gama shirya komai na theater Shi kawai ake jira, aiki cikin gaggawa aka shiga da asiya, cikin minti biyar segaya anfito musu da ƙaton baby boy Masha Allah fari tass dashi kyakkyawan gaske me matuƙar kama da faris tamkar an tsaga kara, shi kanshi Dr saif yaga wannan makar dashi da duk wasu abokanan aikinshi sedai basu kawo komai aransu ba kasan cewar dadyn Faris ɗin ne yakawota sukayi tunanin ƴar uwarsa ce shiyasa yaron yayi natuƙar kama dashi. Sosai sukayi farin cikin ganin baby musamman hamisha data karɓe tahana kowa gani domin wani irin mugun son baby aka sanya mata, su dady se dariya suke mata wai yanzu kuka yaƙare tunda tasamu baby. Hakan dai alhaji Bashir yakarɓi yaron yagani kafin yayi masa addu'a yabawa hamisha shi yace yanzu kam zeje gida ya kimtsa seya dawo domin dawowarshi daga tafiya kenan ya haɗu dasu, idan ya huta zedawo yaga asiya. Sosai baba ila yaƙara yimasa godiya kana yatafi
Bayan kamar minti goma da fitowa da yaron sega asiya itama anfito da ita amma tana bacci. Hakan aka kaita ɗakin hutu. Dukkansu suna cikin ɗakin daga umman hamisha har ita hamisha da baba ila, hakan har akayi azzahar baba yaje masallaci sukuwa sukayi tasu sallar anan, bayan sun idar da sallar kowanne yajima yana addu'a akan asiya idan tafarka taga baby Allah yakawo musu abin da sauƙi domin fa asiya har kawo yanzu batasan tanada wani cikiba tana zaune ne akan setin hamisha na macijin cikine da ita, abinka da yaran karkara sam batawani takura kanta ba akan setasan matsalarta. Yanzu kusa haya hai Allah yabata baby boy yazata ɗauki abin?
Koda baba ila yadawo bata farkaba suna nan zaune dai har wuraren uku kafin Allah yafarkar da ita. Tana buɗe idonta ta yunƙura zata tashi seta saka ihu jin yadda cikinta yake atanke gaya kamar ana tsagata da Reza. Arazane duk suka taso gareta suna mata sannu cikin tausayawa. Itako idonta na kan baby dake hannun hamisha. Cikin mama tace "hamee ina kika samo yaro? Ni wlh nama ɗauka mutuwa nayi hamee taƙarasa zancen tana riƙo hannun hamisha ɗin. Cikin sauri tashare ƙwallar idonta dan kar asiya taga karaya atare da ita tace "asey kintashi? "Eh. "Sannu kinji Allah yabaki lpy. "Ameen ameen y allah. "Sannu asiya Allah yabaki lafiyer shayarwa, cewar umma cikin suɓutar baki sam tamanta akan setin da ƴarta ta ɗora asiyar.
Ido tawaro ta kalli hamisha ta kuma kalli babyn dake hannunta jin abinda umma tace kafin tashiga nuna baby bakinta har rawa yakeyi wurin faɗar "ya.. yaron waye wannan hamisha? Miyasameni? Kiyimin magana dan Allah yadda zan fahimta, tafaɗa da ɗan ƙarfi, hakan yasa Alhaji Bashir dakatawa yafasa shiga ɗakin dayayi niyya. Cikin sauri umma tariƙeta, tana cewa "kibi ahankali mana asiya dan Allah ki kwantarda hankalinki karki raunata kanki kinji bakiga ga ciyonan ajikinkiba. "To umma Amma ciyon minene? Miyasameni? Kigayawa hamee tagayamin wai miyake faruwa danine dan Allah? Ƙona haukace ne bansaniba? Tafaɗa cikin kuka. Cikin sauri hamisha tace "a'a ƴar uwata baki haukaceba sedai inaga nice na haukace,
Nidanake ɓoye miki abinda ya zama dole kisani, share hawayenta tayi kana tace "asiya ki nutsu kuma a yau ne ranar da zaki ɗauki karatun da malam kemana kiyi aiki dashi amatsayinki na musulma, wato ɗaukar ƙaddara me kyau ko akasinta wanda shine cikar imani duk wani mumini, asiya wannan yaro dakike gani shine cikar ƙaddararki shine ƙaddarar datasaka Inna ɗora miki talla har ta kaiki gonar bayan layi, shine ƙaddarar datasaka wannan azalumin yimiki fyaɗe, shine ƙaddarar daya kwantar dake akan gadon asibiti yanzu. Asiya sanadin fyaɗen da wannan azzalumin yayi miki Allah yabada cikin wannan yaron, tun lokacinda muka kawoki asibiti nida baba aka sanar muna da hakan, asiya nayi kukan baƙin cikin da basan adadinshiba kuma na gayawa baba da umma komai yadda yafaru ba abinda na ɓoye musu, wanda hakan shine sanadin zamanki gidanmu, duk zancen motsi da kikeji nace miki macijin cikine wannan duk shirinane asiya domin banaso kishiga cikin baƙin ciki da ƙuncin danake ciki wanda nasan idan kika sani abinda zakiji seyafi nawa kuma hakan ze iya shafar abinda kecikinki wanda bejiba beganiba, shine dalilina naɓoye Miki wannan danayi datemakon iyayenmu, sabida hakan asey dan girman Allah da zatinsa ayanzu dakika sani karki bari ya zama sanadin wani tashin hankalinki wanda har ze iya shafar yaron nan da baba dan Allah, taƙarasa zancen tana sakin kuka.
Tunda fara magana gaban asiya ke dukan tara tara har inda tadasa aya, cikin tsoro da fargaba asiya tariƙo hannu ta tace "hamee. Hamee shege nahaifa? Hamee yazanyi da da bala'in inna da tsangwamar mutanen unguwa? Hamisha Waze yadda dani? Tayaya? Ta ina nasamo cikin sheg... Da sauri hamisha ta rufe mata baki cikin fishi tace "karki ƙara shegantamin yaro wlh domin kuwa ba shege bane mutun ne kamar kowa kuma bawan Allah, domin kuwa ba'ashege awaje sedai agidan aure. Yadda kuma kar Allah yasa kowa ya yadda dake mana, ai duk yardar da kike nema kinsamu domin yardar Allah da iyayenki itace kan gaba kuma kinsameta, Allah ya san abinda ze faru dake tunkafin ya faru, hakama yasani bayan yafaru, kinga yafi kowa yadda dake domin shine mafi sanin dede akan komai. Mahaifinki kuwa ya yadda dake domin yasan abinda yafaru dake ƙaddara ce wadda tariga fata. Zancen mutanen unguwa da inna dakikeyi Bama wanda yasan kinada ciki balle yasan kin haifeshi, yanzu haka muna shawarar zuwa zariya dake harse baby na yayi wayo kinsamu miji kinyi aure kafin mudawo barno. "Aa hamisha baza'ayi hakaba ɗawai niyar tayi yawa, amma ni kaina dazan samu wanda ze aureta tabbas ni zan aura mishi ita kafin musan abinyi game da wannan matsalar data tunkaromu, sedai ba yadda muka iya Allah yana sane damu kuyi haƙuri duk ku kwantar da hankalinku kafin Allah yabata alafiya in sha zamu sami mafita.
"Ni zan aureta in sha Allah, suka tsinkayo muryar Alhaji Bashir yana shigowa daƙin idonshi tab da hawaye. Arazane duk suke kallonshi cikin tsoro har baba ila. Shi kuwa jinjina kanshi yayi cikin tabbatar wa kana yace "tabbas zan aurea idai zaka bani ita baba domin kuwa naji duk abinda kuke tattaunawa akai bana bunƙatar wani ƙarin bayani, wlh zan riƙe maka ita amana tamkar tana hannunka ne indai zaka iya aurawa mutum kamana yarka to wlh Zan aureta, tunda nafarajin labarinta nake raya hakan araina inada ɗa namiji saurayi shi naso karɓawa aurenta to amma hali irinna yaran zamani ka haifesune baka haifi halinsuba shine abinda yasareni karna aura mishi yakasa riƙeta yadda nake fata. Baba ka shiga cikin garin barno da kewaye katanbaya waye Alhaji Bashir Kaita, kayi duk binciken daya dace aikaina wanda shari'a tace ayi kafin aure, wlh nabaka dama nidai buƙatata anan shine kawai ka auramin wannan yarinyar dan Allah. Ajiyar zuciya baba ila yau sauke yana kallon yadda babban mutun ke mishi magiya kuma wanda yatemakeshi akan abinda idan ma ya yadda shine aka rufawa asiri. Cikin mutuntawa yace "Alhaji karka damu Indai wannan ne in sha Allah zan baka auren asiya ai idan ma akayi haka temakonmu kadaɗayi Alhaji nukuwa dame zan sakama? Sedai fatan alkhairi da addu'ar gamawa lafiya akoyoshe, Alhaji...murmushi Alhaji Bashir yayi cikin farin ciki yace "ngd sosai baba Allah yaƙara girma. Kafin baba yakomayin magana sukaga hamisha tamiƙe fuska a ɗaure tace mudai bazamu auri tsohoba wlh yawwa, tana gama faɗar hakan tafice abinta. Dukkansu da kallo suka bita, kafin umma tace "babbar magana aiko dai in hamisha bata aminceba akwai aiki ja gabanku mlm ila domin wlh nasan asiya ma ba amincewa zatayiba. "Tofa aiko aiki yasameni doline nashawo kanta kenan, dan Allah baba atayani lallaɓata. Murmushi baba ila yayi kana yace "karka damu Alhaji da hamisha da asiya duka yarana ne kana basufi ƙarfina ba duk abinda nace suka ƙoƙarin yimin biyayya in sha Allah ba abinda ze faru. "Masha Allah. Ngd sosai baba, yafaɗa yana ajiye kayan abincin daya zo musu dasu domin tunda yashigo suna hannun shi seyanzu ya ajiye. Kana yafice daga room ɗin
Hamisha tana fita wani corido tashige ta shiga darzar kukanta babu baƙin cikinta irin tarasa samun faris adnan dakuma Saif Sam tarasa ina zatagansu musamman faris daya lalata mata rayuwar ƙawarta, tacika da burin fansa akanshi amma haryanzu nata samu damaba, seda tayi kukanta me isarta kafin tamiƙe ta fito daga cikin corindon, sedai tana fitowa idonta ya sauka akan faris yana tsaye shida Dr munir suna magana yana dariya, dagani bayada damuwar komai yana cikin farin ciki abinshi, waro duka manyan idanuwanta tayi jikinta har rawa yakeyi sabida fishi tana tunanin ta inama zata ɓullo mai, kamar daga sama sega Alhaji Bashir ya fito daga room ɗinda asiya take yana faɗar "muje son ka karɓo doccuments ɗin ka kai company kafin nazo. "Okey dady, kana ya kalli Dr munir yace "Ina dawowa Dr bara naƙare da saƙon dady. " To shikenan seka dawo. Yafaɗa yanabin bayan Alhaji Bashir. Cikin sauri hamisha tabi bayansu amma koda taje suntada motocinsu kasan cewar tana ɗauke da baby takasa sauri, runtse idonta tayi daƙarfi kafin tajuya gun Dr munir, yana ganinta yataso yana cewa "aa maman baby anfitone ko dady kika biyo gaya kuwa yafita? "Eh wlh Amma abari seya dawo kawai, hala waye wannan dasuka fita tare? Tatambaya kanta tsaye....da sauri Dr munir ya kalleta domin yasan waye faris tunda duk sune amma bayaso yasamu sa'a akan wannan babyn domin ta haɗu iya haɗuwa shikanshi mashiga yake nema, ɗan murmushi yayi kafin yace "faris wai ai ɗan Alhaji ne shine babban ɗanshi. Amugun razane tawaro duka manyan idanuwanta kafin ta juya kawai da gudu zuwa room dinshi. Shikuwa Saif tafowarshi Kenan idonshi ya sauka akan idanuwan dake neman tarwatsa ƙwaƙwalwarshi kuma anyi dede ta zaresu kamar yadda tayi awancan kokacin. Shima waro nashi idon yayi domin ganin abin yayi kamar mafarki kafin yanufi inda yaga ta shiga sedai kafin yakaiga shiga wani doctor yatareshi ana yimishi neman gaggawa sabida wata data haihu kuma tana combination, haka dole ya nufi inda take badan yasoba domin gaba ɗaya rayuwarshi nakan hamisha ne yanaso yasani wacece ita.
Itakuwa tana shiga ɗakin tasamu ummanta na toilet Baba ila kuma yafita sallar la'asar, bata tsaya komaiba tace "asiya zaki auri wannan Alhajin dayace yanason aurenki kinji. Da mamaki asiya data gama cin kukanta ke kallonta ganin ta sauya lokaci ɗaya. Cikin tabbatarwa tace "eh hakane abinda na faɗa asiya inaso ki aureshi tabbas kuma banaso auren ya ɗauki lokaci zan roƙi baba indai da gaske yakeyi ze aureki to a ɗaura auren aranarda babyna zecika sati ɗaya domin itace hanya mafi sauƙi ta ɗaukar fansar abinda baba wannan yaron yayimana, wlh billahi asey Sekin ɗanɗana masa baƙin ciki kamar yadda yasaka miki sekin sakashi kuka fiye da yadda kikayi, kana sekin wulaƙantashi fiyeda yadda ya wukaƙanta miku rayuwa, kuma duk zamu samu wannan damar ne kaɗai ta hanyar auren ubanshi, tafaɗa cikin ƙunarrai....!
Tofa laifi daɗi ƙarewa🥳🥳.
END
OF BOOK
Semun haɗu a book 2 wanda yake paid ne idan kina buƙatarshi zaki iya 👇
KWARATAN
ZAMANI paid book ne akan 1k kacal 👌zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 9112799371 moneypiont sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber👉 07037092176 on WhatsApp.
Autar alheri✍️