Turbar Gaskiya 2 By Abdulaziz Madakin Gini

Author :  Abdulaziz Madakin Gini Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 5

3K to 6K   out of 12.1K words

at tini an ei karfin
sama da motum duba a cikin dakarunsu

Yana duban Dakarun nasa suna sulatewa kasa suna faduwa, amma ya kasa ganin wanda yake
musu wannan barnur saboda tsananin zafin namar mai aikata kisan, bai ankara ba ya ga gaba
daya dakarun duk an karkashesu, ya zama dan kauye sai waige yake yana son ganin wani
mala'ikan daukar rai ne ya zo yake girbar masa Dakaru.
Ba shi ba hatta Gimbiya Lushmaira kallon mamaki take, cikin tsananin faduwar gaba Yarima
Zaiyan ya bayyana a daf da shi, wanda saboda tsananin firgici Sadauki Askam sai da ya saki
fitsari a wandonsa.

Gimbiya Lushmaira tsananin mamaki ya hana bakinta rufawa saboda irin jarumtakar da Yarima
zaiyan ya yi amfani da ita wacce bata taba ganin ya yi irinta ba.

Sadauki Askam ya dubi Yarıma yana Rirma ya zuba giwowinsa a kas, yana neman yafewa
Koda Yarima ya dube shi sai ya tsar ta masa yawo a fuskarsa.

"Ahir dinka da a ke kiranka da gwarzon Sadauki kuma har yake jagoranta wadansu Dakaru dan
aiwatar da wani shiri na karkashin Rasa, ina son ka sani duk kan shirin ku mun fara saninsa
daga fara shigowa cikin wannan dajin haka zalika ko da aka fita daga cikin dajin nan ni ban fita
ba ina nan ina son na ga sabon shirin da zaku kulla.
Dajin wannan batu sai jikin Sadauki Askam ya kara rawa, yana makyakkyata, shi kuwa sai
Yarima Zaiyan ya dube shi cikin fushi ya ce, ka dauki daya bayan daya ka dora dukkan dakarun
da na salwantar akan dokinsa ina nan ina jiranka.

Aikuwa nan da nan Sadauki Askam ya fara aikin cikin sauri-sauri gudu-gudu, kafin wani lokaci
har ya kwashe su duka, ya na gama dora su a bisa dawakan kowannensu sai Yarima Zaiyan ya
dube shi ya co.

Ya kai wannan sakaran jarumi kasan abinda ya sa na sa ka aikata haka,?"
Cikin rawar jiki Sadauki Askam ya ce, "ya shugabana ban da masaniya akan bakan.?" Da jin
haka sai Yarima Zaiyad ya yi

murmushi ya cc, "Abinda hakan ke nufi shi no za ka jagoranci gawarwakin izuwa sansaninku ka
labartawa sakaran Samkanku yanda aka yi aka salwantar da rayuwakan wadannan dakaru, ka
basu labari ni ne Yarima Zaiyan daya daga cikin dakarun cikin birnin Baitul Haural ina so ka
sanar dasu cewa guguwar bala'i tana daf da isarsu kuma duk irin shirin da suke tunanin za su yi
a kanmu mun riga mun gama da ku, fatanmu mu hadu a fili daga mu gidaddabaku in har ba
zaku bi TURBAR GASKIYA BA.

Koda Yarima Zaiyan ya gaba sanar da Sadauki Askam wannan sako sai ya juya da niyar ya yi
gaba ya barsu a nan da Gimbiya Lushmaira.

Nan take gimbiya Lushmaira ita ma ta yi gaba batare da damuwa da shi ba. Yana tafiya kawai
ya ga ta zo ta wuce shi ranta kuma в басс

bata ko kallonsa, ga jaririn Zakinta a hannu Koda Yarima Zaiyan ya dubeta sai ya yi sauri ya ya
sha kanta, ita ma ta tsaya su ka yi
cirko cirko suna kallon juna na tsawan lokaci a farko kallon kurillar da sukewa junansu, basu
san a irin matsayin da suke ba, domin kuwa kowannensu wani tunanin ya tafi na daban.

Yarima Zaiyan ya dawo haiyacinsa ya yi saurin dubanta kamar bai shiga wani hali na tsawon
lokacin da ya yi yana dubanta ba, ya ce cikin kakkarfar murya kamar yana doka mata Isawa.

Take ita ma ta dawo haiyacinta ta dube shi da shakka, tana saurarensa.

"Yake wannan karamar yarinyar mai shirin zama jaruma, hakika a yanzu na tabbatar da cewar
kin yi kokarin da idanuwanki za su iya jure ganin irin gagarumin gumurzun da zamu kwafsa
tsakaninmu da makiyanmu, tabbas, bana da haufi ba zaki tsorota ba a yayin da idanuwanki
suke kallon wannan gumurzu, sakamakon wannan bajintar da kike na dauko jariririyar dabba."
Yana zuwa nan a cikin zancensa sai ya juya da niyar ya wuce gaba, da ganin haka sai Gimbiya
Lushmaira ta dakatar da shi da cewa.

"Kai kuma a yau ne na fara tunanin dinbin
shekaru da ka dauka kana kowan yaki, duka ka yi su ne a banza, domin kuwa ka bani mamaki
da har kake fada na shammata, duk wani jarumi mai ji da tumbatsarsa jarumtarsa, baya yaki da
wanda bai shirya ba, dan haka akwai saura rina a gabanka."

Tana zuwa nan a jawabinta sai ta cilla masa jaririn Zakin ta yi gaba cikin gudu kafin ya dawo
daga mamaki kalamanta tuni ta yi nisa.

Cikin sanyi jiki ya baro cikin dajin Shi kuwa Askam tuni ya dauke hanya yabi wata siririyar hanya
wacce ta zagaya ce ya tura dawakan da matattun dakarun da suke kal

Koda Gimbiya Lushmaira ta isa cikin tawagarsu ta yi sauri karasa inda sahunsu yake ta tarar da
Shadilat a cikin sahu tana tafiya, koda Shadilat ta ganta sai mamaki ya rufeta har ta kasa yin
hakuri ta kamo hannun gimbiya Lushmaira ta cc.

"Ya ke 'yar uwata shin yaya a ka yi kika kamo a cikin wannan tafiya, da tuni na cire rai dake.?"

Da jin haka sai Gimbiya Lushmaira ta yi murmushi tun daga lokacin da tafi kawo irin

waggwarmayar da ta yi da Zakunan zuwa lokacım da Yarima Zaiyan ya ise ya yi yaki de Dakaru
sama da duhu goma da irin bajintar da ya yi, ta kuma dora irin yanda Yariman ya gwasalets a
cikin tafiyarta da kwazonta sannan ta Kare da ita ma irin gwasale shin da ta yi, duk ta sanar da
ita
Da jin wannan bayani sai Shadilat ta ce, "A gaskiya kin yi kokari kuma na yaba da irin kwazonki
domin kuwa ban yi tsammanin samun nasararki ba, ni kuwa yanzu a hali da nake ciki na fara
tsanar jarumtakata, kai in takai ce miki na duda da duk wani Rudiri nawa.

Gimbiya Cikin tsanenin mamaki Lushmaira ta dubi Shadilat ta ce.

"Ke kuwa akan me yasa?"

Shadilat ta yi wani kayataccen murmushi ta dubi Gimbiya Lushmaira ta ce.

"Ke kuwa mai kike tunanin zai saka ni a cikin irin wannan hali in ba soyayya ba, ya ke ananiyata
ina so ki sani a cikin 'yar gajeriyar tafiyar da muke, sakamakon rashinki a tare da ni, sai Yarima
ya ke zuwan min lokaci lokaci yana aya ni hira, a wannan lokaci han yi sune ba

tsananin soyayyarsa ta shuga cikin raina"

Kafin Shadilat ta gama zuwa Kurshen maganaria gaban Gimbiya Lashmaira ya yanke ya fadi
want iris kashi ya turnukata, da kyar ta iya kawar da damuwarta ta dubi Shadilat cikin mma
rashin damewa ta ce

"Amma dai ke kuwa kin yi asara a kan soyayya ki zubar da irin burukanki tabbas na yi dana
sanin Kulla Kawance dake, domin kuwa a tafiyata bana son sakarci ni kuwa ban dauki soyayyar
komu face sakarci in har zaki yi soyayya to babu shakka ke sakaryace."

Wannan magana ba Karami bakantawa Shadilat rai ya yi amma sai ta yi murmushi ta ce, Ko da
zaki rabu dam, ha zan ji takaici ba tun da dai ina tare da gwarzon namijn duniya kuma shugaba
ga wannan tafiya ina so kuma ki yi sani, Yarima Zaiyan ne kadai zai iya yin nasara akan
dukkanin Kudirinki domin kuwa a yanzu a kaf cikin wannan nahiyar babu sadauki mai karfinsa

da kwarjinsa dan haka kada kı taba tunanin ke ce zaki iya soke daya idaniyar Maciyar Burukul
Kursum, kuma shi ne zai zama gwarzon kami a cikin wannan gagarumin yaki da za a kwafsa,
tabbas idan ya zamo abin gabarki a yanzu zai zamo abin son ki a nan da wani dan lokaci mai
zowa, ina mai shawartarki da ki yi biyayya a gare shi domin ki samu saukin bakin cikin rugaza
miki kudiri da zai yi

Koda gimbiya Lushmaira ta ji wannan ba tu sai ta fusata ta cire hannu daga rikon da Shadila ta
yi mata ta bar gun cikin tsananin fushi, tana barın gun kuwa ta shiga wani sahu a na ci gaba da
tafiya.

A dai-dai wannan lokacin kuwa aka tsaya yin sallar Azahar, wannan damar ce ta sa Gimbiya
Lushamaira ta samu guri ta zauna dukkanin abubuwan da Shadilat take sanar da ita nan take
ya dinga dawo mata, wani tsananin kishinta ta ji, tabbas a yanayin jarumtakar da Yarima yake
nunawa zai iya zamowa gwarzon Karninmu dan haka abinda ya kamata ta yi shi ne ta ta yi
kokarin da zata zamo itama za a yabeta tana da masaniya ko da bata kai Kokarinsa in har ta
zamo masa na biyu to bai isa ya yi mata wani kuri ba, da wannan tunanin Gimbiya Lushmaira ta
ta shi ta tafi ta yi alwala, sai dai lokacin da ta dawo daga yin tsarki sai ta hango Shadilat da
yarima Zaiyan suna hira har da kyalkyalewa da dariya, wannan abu ba Karamin yi mata ciwo ya
yi nan take wani tukokin kishi ya rufcta

Koda aka idar da sallah za'a ci abinci bata bari ta je inda Shadilat take ba saboda yanzu
haushinta ma take ji, a haka aka ei gaba da tafiya

A can kuma san sanin su Sarki Madhan lokacin da suka iso bakin filin da za yi wannan yaki sai
suka isaya da tafiya nan take kuma aka kama kafa tantun domin a samu hucewa kafin.su samu
sako daga jama'ar Sarkı Abu Zaiyan.

Koda aka kammala da kafatuntunan su Sarki sai Sarki Madham Sarki Tarma da kuma Sarki
Husaka suka kadaice a cikin nasu tantin da dubu da irin abubuwan da yake gabansu

Koda yin shiru na dan wani lokaci kowannensu yana tunanin abin da zai faru, sai Sarki madhan
ya yi ajiyar zuciya ya dubi Sarakan gudu biyu ya ce.

"Ya ku Sarakai 'yan uwana yanzu ya kuke tunanin jama'armu da muka turo don yin
kwantan bauna don su hallakar da wasu daga cikin jaruman Sarki Abu Zaiyan ta hanya musu
ruwan kibiyo.

Da jin wannan ba lu sau Sarki Huzuka di Sarki Tarmas su ka ajiye zuclya a tare sammas suka
tsai da kallon su ga Sarki Madham Sark tarmas ya ce

"Laliai kam akwai abin duba a cikin tafiyar tasu dole muna bukatar mu san abın da ya faru ko
sun samu nasara ko kuma basu samu ha domin mu yi yunkuri yin wani tunanin tun kalin su
Sarki su iso wannan fili a fara ym yaki dasu

Shi kuma Sarki Husuka sai ya cc, "Wannan haka yake, amma kuma ta yaya kuke ganin zamu
san saman nasararsu, tun da dai kun sani ba mu tura su dan su je su yi nasara su dawo ba,
mun tabhatar da nowar Ronar hakin wake su kai, domin kuwa babu wanda zai sha a cikinsu,
fatanmu dai su yi bama ko yaya take."
Sarki Madhan cilin karfin gwiwa ya ce, "Babd ko kokwanto za su samu nasara abin da ya
kamata yanzu mu yi shi ne mu kara nemo wata hanyar da zamu yi amfani da ita dan samun
biyan bukatarmu."
Kafin want daga cikinsu ya yi wata magana sai Shugaban dakaru na bimin Sarki Husuka ya
shigo cikin tanti cikin rissanawa ya ce. "Ya shugabana Sadauki Askam ya iso cikin mawuyacin
hali tare da gawarwakin duka dakarun da ya tafi da su

Koda suka ji waman ha tu sai dukkaninsu suka cika da firgiei ainu, har vai da aka samu dan
lokacin sannan suka dawo hayyacinsu, Sarki Husuka ya yi saurin duban Sadaukin Rauwal ya
ce, "Ka koma ku duka ku sauran fitowarmu. Sannan ina so kafin nan ka tura Dan leken asiri dan
gano mana a halin yanzu a ma abokan gabar mu suke.
Koda jin wannan ba tu sai Sadauki Rauwal ya yi sujjada ga Sarakan sannan ya fice.

Fitarsa ke da wuya sai Sarki Tarmas ya ce, "Tirkashi lallai sai mun yi da paske domin kuwa
jama'ar nan sun gano mu, kuma ba za su taba yarda da duk wani shurin da za mu zo mu su da
shi ba domin kuwa za su ce yaudara ce, kuma sanin kanku ne gaba da gaba da su ba karamin
ta'adi za su yi mana domin Kasar Baitul Haural sun kware wajen iya yaki mamaya a duk duniya
duk wanda zai yi gaba da gaba da su a fafata a filin daga babu shakka sai sun sha jininsa sai
sun samu nasara akan ku, don haka yanzu sauya shiri ya zama dole, mai kuke tunani wata
shawara za ku zo mana da ita?"

Koda Sarki Husaka da Sarki Madhan suka ji wannan jawabai na Sarki Tarmas sai dukkaninsu
suka yi shiru na rabin lokaci. Daga bisani Sarki Madham ya ce "Ai kuwa in haka ne tusa
ta-karewa budari domin kuwa ni ban ga ta yanda za a yi mu samu nasara akan Sarki Abu
Zaiyan ba in har ya zama dole yin gaba da gaba da su babu nasara.
Da jin haka sai Sarki Husuka ya yi sauri dagowa ya cc, "Bai kamata mu dinga sagewa kanmu
gwiwa ba, kamata ya yi mu samu hanya mafi dacewa damu domin yin gaba da gaba da su koda
za'a samu nakasu. A yanzu a cikin tafiyarmu muna da manyan Dakaru da ko a duniya za a sasu
a cikin sahun manyan dakarun duniya, abinda ya kamata da a yi shi ne, a yanzu take mu
jarraba tura dan sako da mun tabbatar da i sowar su mu shailanta musu cewa za'a yi yaki
amma ba na mamaya ba, za a yi yaki irin
yakin na gasa, ma'ana jarumi da jarumi, ni na tabbata idan suka aminta da haka to babu shakka
za mu iya yi musu a sarar manyan dakarunsu."

Da Sarki Husaka ya zo nan a cikin batunsa sai dukkaninsu suka yi shiru na tsawon lokaci kana
suka dubi juna. Sarki Madham

"Ai kuwa in har za su amince da wannan ni kaina ina kallon samun nasara amma kumal
amincewarsu shi ne badakalar."

Da jin haka sai Sarki Husaka ya ce, "Ai sai mun jarraba, kuma shi mai nema ai yana tare da
samu."

Nan take su ka yi na'am da wannan ba tu suka nemo Sadauki Rauwal ya shigo ya sanar dasu
gabatowar rundunonin kasar Baitul Haural har sun kafa tantuna sun fara fito da kayan
makamansu.

Koda suka gama jin wannan batu sai suka sanar da shi sakon a sanar da dan aiki ya je zuwa ga
sansaninsu domin isar da sakon da suka tanadar musu.

Nan take ya karbi sakon ya bayar aka kai ba dauki tsawan rabin sa'a ba dan aikin ya dawo
Cikin girmamawa ya mikawa Sarki Husaka Sarki Husaka ya mikawa Madham nan take sai Sarki
Madhan ya warwareta ya fara karantawa suka kasa kunne cikin doki sun jin abinda yake kushe
a ciki

Zuwa ga azzaluman Sarakai marasa son gaskiya ba su bawa Turbawa gaskiya baya, hakika,
tabbas ko yanzu mun gano cewa tsoro ne yake bibiyarku har yasa kuke neman sassauci daga
irin azabobin da za ku riska, ina son ku sani babu tudun da a ba hawansa ake ba, abinda zai
hana kasar Baitul Haural su sassaraku su mai da jininku abin shan kasa, shi ne karbar addinin
mu na gaskiya, wato addininmu, ina son ku yi sani mun yarda da dukkan irin zabin yaki da zaku
zo mana da shi, sai dai ina so ku sani duk wanda kuka zaba ba za a daina yinsa har sai an ga
wanda ya ci nasara.

Daga Sarki Abu Zaiyan dodon kafurai.

koda ya zo nan a cikin karatunsa sai su duka suka dubi juna daga bisani kuma sai suka kece da
wata shu'umar dariya mai firgita mai saurarc, koda kammala wannan dariya sai suka fito suka
sa a ka kira manyan jarumin na kowace
kasa daga kowane Sarki kowane Sarki gawurtaccen Sadauki ashirin a cikin a kuma aka zabi
goma wanda suka fi kwarc zamana sun kai su talatin kowannensu ba s fada ba da gani kasan
maye zai ci mutum.

Lokacin da aka fito da da Wada samudawan Dakarun kowa dake gurin sa gabansa ya yanke ya
fadi da ganinsu do kuwa mamaki ne ya kama su suka rasa ta ina fito da wadannan samudawan
abinda jam basu sani ba shi ne kebantattu ne da aka boye ake kuma kula da lafiyarsu ake
saboda ka ciwo ya kama su su mutu, irin mutuwar cuta ba filin daga ba. Domin a ganinsu
wannan t karamar asara bacc.

Acan kuma sansanin Sarki Abu zaiyaı lokacin da dan aiki ya baro sansanin sai Sarki ya tara
manyan kasar da dukkanin jama'ar da ake tafe dasu.

Koda kowa ya nutsu sai Sarki ya numfasa ya ce, "Ya ku jama'ata ku yi sani cewa wannan shiri
ne abokan gabarmu suka zo mana da shi, domin sun san cewar idan har muka yi yakin
mamaya da su


Koda Sarki Abu Zaiyan ya zo nan cikin natunsa sai jama'arsa suka kaure da kabbara. Lokacin
da sarakan uku da kuma manya dakaru da aka ware sai farin ciki ya mamayesu domin suna
gani sun samu nasara sun gama da haka suma sai suka barke da ihu.

Koda aka natsa da ihu da kabbara na kowane sansani sai Sadauki fangaren su Tarmas da
akewa lakabi da Mukanu, ya ei gaba da girgiza yana wani motsa sassan jikinsa yana daga
makami.

Nan da nan sai kowa ya ja da baya Sarki Tarmas da Sarki Husaka, Sarki madhman suka koma
kan kujerunsų suka zauna suna kallon wannan al'amari, cike da farin ciki domin sun san nasara
ta samu.

Shi kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya dubi gabas ya yi sujjada ga Allah sannan ya mike ya daga
hannu yı yi addu'a kana ya shafa ya dubi Sadauki Mukanu.
Hakikanin gaskiya banda Sarki Abu Zaiya bashi da tsoro kuma bai san tsoro ba

2 / 5