Turbar Gaskiya 2 By Abdulaziz Madakin Gini

Author :  Abdulaziz Madakin Gini Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 5

1 to 3K   out of 12.1K words

TURABAR GASKIYA
Book 2
MADAKIN GINI


Da jin wannan ba tu sai Yarima Zaiyan ya yi murmushi domin dama abinda yake son ke nan ya
dubeta ya ce,

"Da alama za mu iya kasancewa anan gurin har safiya abin da nake so ku sani shi ne a baya da
mu kada, na yi tozali da wata Zakanya da take halin laulayi, Wani bajimin zaki da ya zamo shi
ne mijinta yana kewayeta tar da shinshinar jikinta, wannan shi ya tabbatar min shi ne mijinta.

Abin da nake so da ku aikata har ya sa na ji cewar kin isa jaruma ki tafi daga idar da sallar
Asuba zuwa ga wannan zakanyar ki dauko jaririyar da ta haifa."

Koda Lushmaira ta ji wannan umarni daga Yarima Zaiyad sai hankalinta ya dugunzuma ya tashi
ainun ta yi shiru, na dan lokaci daga bisani sai ta dago kai ta yi murmushi hade da cewa.

Ka dauki batunka kamar ka yi rubutu akan dutse in har da rai da lafiya gobe kafin kafin gari ya
gama wayewa zan zo maka da jariryar kada, amma ban damu da ka yardar da jarumtakata, ina
son ka sani ranar wanka ba'a boyon cibi, ranar da zaka gario ma'anar jarumtakata ita ce ranar
da jarumtakarka zata dakushe, a idon duk wani jarumi dake cikin kasar Lautul Barus ya zamana
ni ake gani a matsayin jarumar da ta kaini, kamar yanda aka rasa jarumin da ya kai mahaifina a
duk wannan kasar.

Koda fadin hakan sai ta fice daga cikin Tanti ita kuwa Shadilat sai ta cika da tsananin mamaki,
ta yaya ake Lushmaira take daukar kanta amatsayin wata uwa a harkar jarumtaka, alhalin ni din
nan da muka kara banga wani kumarinta ba.

Shi kuwa Yarima Zaiyan sai mamaki ya cika shi, ba komai bane ya sa shi mamaki face irin
karfin gwiwar da Lushmaira take da shi, bai san sa'ar da ya
fice daga cikin Tanti saboda tsanania mamaki.

sai ta nufi can wani guri da babu kowa ya Ita kuwa ku da ta fita daga cikin tanti samu guri ta
zauna, ta fara tunanin.

Lallai na tsokanowa kaina abinda yafi karfina, zaki ku da makami abin lura ne a lokacin da za ka
yi yaki da shi, ta yaya zata iya yin yaki da Zaki har ta samu ta daukar masa da, sabuwar
haihuwa, sam wannan al'amari ba zai yiwu ba shi kansa Yarima Zaiyan ya yi hakane kawai dan
na rasa rayuwata.
Kai ba zai so mutuwata ba duk da kiyayyar da take tsakaninmu, ya yi hakanne dai kawai dan ya
kore ni, in kuwa hakane ko da zan salwantar da rayuwata sai na yi shiri da asuba na tunkari
gurin wannan zakanyar.

Aikuwa washe gari tun da asuba ana idar da Sallah ko tsayawa yin addu'a
hata yi ba kamar yanda Sarki yake a lokutan da aka gabatar da sallah, sai ta mike ta sulele ta
cikin cryavi ta bi ta wata ennvar hanya. Ta nufi gurin da Yarima Zaivan ya sanar da ita, cikin
rashin sant kuwa tana barin gurin sai aka shafa addu'a, daga nan sai Sarki ya vi umarni akan a
ci gaba da tafiya.
Ko yarima bai yi tsammanin hakan ba amma da ya ji wannan sanarwa sai farin ciki va cika
masa zuciva domin ya na ganin lokacin da Lushmaira ta nausa da gudu cikin dawa, ya tabbata
koda ta dawo bazata taba samunsu a hanya ha dole ne ta koma

Shadilat kuwa sai hankalinta ya dugunzuma ta shiga damuwa ainu cikin rashin karfin haka take
tafiyar duk ta damuu

Sai da Gim Gimbiya Lushmaira ta yi tafiya mai nisa a sannan ta isa inda Yarima zaiyan ya
kwatanta mata sai ta yi tsaye
tana duban wajen, sai an fada da gani biri zai ci mutum. Dajin ya zamo ma'abocin kwarjini
sannan shiru ya mamaye gurin bake daya, dan haka sai ta fara waige waige cikin sanda.

Bata ji doriyar wata dabbar ba, dan haka sai ta rasa abinda ya kamata ta yi, domin ta samu ta
gano inda Zakanyar take, tana tsaye cikin dube dube sai kawai ta ji gurnani daga can nesa
kadan, ko da ta tabbatar da wannan gurnani ba na komai bane face gurnani zaki sai ta gyara
tsayuwarta ta kuma Kurawa gurin idanu, tana tsaye sai ga wani narkeke Zaki ya fito daga wani
kogo na bishiyar darbejiya.

Da fitowar wannan Zaki sai ya yi girgiza wanda ya haddasar da korar jikinsa ta tashi sama, ya
saka kafarsa yana sosa kansa.

Da sauri Gimbiya Lushmaira ta koma da baya ta boye domin ganin Zakin ya yi mutukar ranata,
tabbas ko da ita da Shadilat da kuma Yarima Zaiyan za su hadu ba za su iya da wannan Zakin
ba.

Tana nan raße tana son ganin ya kauce domin ta sulele ta koma can in
da ta fito domin ta san wutsiyar Rakuni ta yi nesa da kasa, in ma ha rainin hankalin ba ta yaya
za gwada jarumtakar dan adam da Zaki irin wannan alhalin kuma baka rike da komai.

tabbas sai yau ta kara yarda Yarima Zaiyan makivinta ne kuma bava kaunarta.....

Numfashinta ya dauke lokacin da ta hango Zakin ya nufo inda take boye gadan-gadan ta yi
sauri janye jikinta dan kada ya Jura da ita domin ta fuskanci ba ita ya gano ba a kwai inda ya yi
niyar nufa.

Tana makale a jikin bishiya ya zo ya wuce, yana gurnani. Yana wucewa Gimbiya Lushmaira ta yi
ajiyar zuciya har ta dauki hanya zata koma sai kuma ta tuna da cewa waye mahaifinta ta tuno

irin gwagwarmayar da mahaifinta ya yi a duniya kafin ya rasa rayuwarsa, ta tuna irin bajintar da
take so ta yi anan gaba na soke idanuwan Macijiya Burukul Kursum.

Nan da nan wani irin karfin ya shigeta ta koma da baya ta dubi Zakin da ya yi nesa ya nufi wata
fadama dake nesa.

Cikin sanda ya juya ta nufi inda
Zakin ya fito, koda karasawarta sai ta sunkuya ta leka cikin abin da bata zato ba shi ya faru tana
lekawa sai taga jariran zakuna gudu biyu suna kwance, uwarsa tana nesa da su tana sharar
barci.

Koda gimbiya Lushmaira ta ga wannas al'amari sai farin cikin ya cika mata zuciya ainu nan take
ta yi farin ciki ta tabbatar da cewa zata yi abinda Yarima ya umarceta, muddin kuwa ta samu
nasara, to zata hada shi da gagarumi aikin da ba zai iya ba. Domin ta haka ne zata nuna duniya
cewar ita jaruma ce, kuma ta haka ne karfin da yake takama da shi, zai dusashe a cikin
birninsu.

Koda yin wannan tunanin sai ta zura hannu ta dauki daya daga cikin jariran zakunan, a cikin
sanda. Amma me ta na dago kai ta hango Namjin Zakin nan ya na dawowa da cikin
matsanancin gudu.

Ganin haka yasa Lushmaira yunkurin mikewa da sauri ta falfala da gudu tana rike da wannan
jaririn Zakin.

Zakin ya kurma wani uban ihu mai tsananin firgici ya bi bayanta. Ita kanta
Gimbiya bata san tana da irin wannan gudun da take yi ba, sai dai duk irin gudun da take Zakin
nan ya ninka nata domin sau tari yana kamota sai ta zille ta sauya hanya.

Wannan al'amari ya yi mutukar tayar da hankalin Lushmaira domin Zakin nan ya kuntata ga shi
gajiya ta fara sarkarta, ta saduda tana ganin ba zata iya samun nasara

Koda ta fara layi juwa na dibarta sai ta dake ta ci gaba da gudun tana rike da jaririn Zakin, a
hannunta.

ba

A haka har ta iso inda suka yada sansanin a lokaci, hankalinta ba karamin ta shi ya yi da ganin
yanda gurin ya yi shiru ba kowa da alamar sun ji ma da yin gaba. tana tsaye cikin tsoro da
fargaba Zakin ya kara so filin gurin yana gurmanin shi kansa ya gaji likes su ka yi gaba da gaba
da ita babu halin gudu.
Gimbiya Lushmaira ta cire dankwalin kanta ta yi sauri daure karar jaririn Zakin sannan ta yi zafin
naman daure shi da jikin wata siririyar bashiya.

Aikuwa kafin ta kara wani Yunkuri Zakin nan ya yi sufa kanta da niyar ya tarmusheta, amma sai
ta azama ta bar gun ta sauka akan kasa, gurin ya cika da kura.

Da ganin haka sai ta ja daga kamar yanda shima ya dago yana fuskantarta da kara damara. A
wannan lokaci sai ita ta nufeshi cikin fushi zuciya suka kauri da hargitsatsten yaki.

Gimbiya Lushmaira ta yi danasan kaiwa wannan Zakin bara a karon farko kai tsaye domin
lokaci guda ya yagar mata fatar bayanta gurin ya kwalane ya yi fari ya kuma saka hakuransa
akan kafarta yana neman ya cisgeta, da kyar Lushmaira ta iya kwace kanta

Ba tare da ya jira ta samu sukuni ba zakin nan ya kara nufarta da niyar ya turmesheta amma sai
ta yi ta 'yan maza ta murgina ta kuma mike tsaye duk da jini na zuba daga jikinsa sai ta dunkule
hannuwanta cikin karfin halin ta tsaya kan kafafuwanta tana jiran isowar Zakin.

Shi kuwa sai ya saka kafarsa a kasa
cami da tona Rasa ya yi kuka mai cike da athon ya yi kanta koda ya iso gare sai ta Jeddané ta
ku masa naushi a fuska.

Ta yi kuwa sa'ar samunsa a idonsa nan okesu ya kauri da wani hargitsantsan thu mara dadin ji

Lokacin da ya kife kasa kafin ya kara samon want Rarfin halin ta sauri juya da niyar Caukar
jaririn zakin nan da ta daure shi.

Abinda ta gani shi ya yi mutukar masala ta ji gabanta ya yanke ya fadi ba Lomal ta gani face,
uwar Zakin tana shimhinar ilin dan.

Wani hargıtsantsan kuka ta ji, a bayan tama waijawa taga daya Zakin ya mike ya yo Kanta



Lokacin da Gimbiya Lushmaira take duban wadannan Zakuna miji da mata sun yi mata
kawanya sai nan take ta shiga cikin tsananin ta shi hankali
Cikin 'yar sarsaría suka dinga matsuwa inda take, tana masu wani hargitsantsan gurnani mai
zaranar da zukatan ma'abota saurare.
Nan ta tsaya ita ba abin ta zura da gudu ba, ba kuma abin ta yi yaki dasu ba domin ko ba
gwadaba linzami ya fi karfin bakin kaza, amma lokacin da ta ga sun yo kanta cikin fushi sai ita
ma hankalinta ya dugunzuma domin ta aiyana a ranta cewa, idan ta tsaya tabbas za su sami
nasara akanta idan kuma ta ta shi tsaye ta kare kanta, watakila ta samu ta yi nasara akanta.
Nan take tunanin irin jarumtakar da mahaifinta ya yi a lokacin da macijiyar Burukul Kursum ta
shi go birninsu ya fado mata a lokacin da mahaifiyarta take bata labarin irin namijin kokarin da
ya yi har ya soke idon macijiya a yanda aka siffanta mata macijiyar loma guda
zata yi wa wadannan Zakuna ta gama da su, tabbas idan ta kasa karo da wadannan Zakuna
babu shakka ko inda ake yaki da Macijiya ba za ta iya zuwa ba, in kuwa hakane Kudirinta ba zai
taba cika ba.

Wannan tunanin shi ya yi tsananin karawa Gimbiya Lushmaira karfin ta ji wani sabon karfi ya
shigeta bata san lokacin da ta kwarara Kabbara ba. Ta tunkari Zakunan kamar yanda suke
tunkarota.

A tare suka yi sufa kanta, ita ma sai ta daka tsalle ta yi kansu a ka wata babagoyar haduwa a
cikin sararin iska, su duka suka gauro, wani taimako da Allah ya yi mata, a lokacin da aka ta shi
sama da niyar ta yi karo da wadannan Zakuna sai suka fita ta shi sama, dan haka su biyu suka
gauro suka zube kasa bisa faduwar rashin tsammanin domin dukkanin su basu fadi akan
kafafunsu ba kamar yanda ita ta fadi a kan nata kafafun.

Kafin su yi yunkuri mikewa sai ta yi azama ta yi kan Namijin Zakin da yake Rokaritt mikewa a
cikin tsananin fushi.

Tun daga inda take ta yi alkafira ta fada
kan Zakin ta mai da shi, ya kara wani yunkuri zai mike ta saka kafa ta taka wuyansa iyaka
Karfinta.

Nan take ya kama kakarin mutuwa itu kuwa sai sa kara dagewa tana cikin haka hata ankara ha
ta ji an sureta an doka ta da kasa.

Cikin rashin bazata ta dubi wannan Zakanyar ce ta kara yunkuruwa cikin ta shin hankali ta kara
hiyota zata kara turmesheta.

A wannan lokacin karfin Gimbiya ya gama karewa amma ta ta kwala wata Kabhara domin ta
riga ta san idan wannan Zakanyar la turme sheta to sai dan Buzunta, ai kuwa yin wannan
kabbara sai ta yi sama tamkar wacce aka saka kugiya aka shillata, koda ta ta shi fadowa sai ta
sauko a kan kafafuwanta
Ai kuwa tana faduwa Zakanyar nan ta Kara yin kukan kura ta yo kanta. Irin mahaukacin gudun
da take yi yusa Gimbiya Lushmaira ta fahinci dan ta samicia za su yi muguwar ragwabza, ar
kuwa sai ta falfala da gudu. Ita ma Zakanyar ta bi bayanta suka kasa tsire cikin Isananin gudu,
wata dabara ta fadowa Gimhiya Lushmami lokacin da ta ga Zakanyar ta Kara tsananta, wajen
ne man ranta, dabarar da ta fado mata ita ce wata dogowar bishiya ta taku gabanta, suna cikin
gudun sai kawai Gimbiya Lushmaira ta kara azama dan ta nuli jikin bishiya tana kuwa isa sai ta
kama tattaka bishiyar tamkar wata 'yar biri, sai da ta yi nisa a saman bishiya a lokacin da
Zakanyar ta dako tsalle da niyar ta cafkota sai kawai Gimbiyar Lushmaira ta wultsila da haya,
Zakanyar ta dake bishiyar.

Saboda karfin da Zakanyar ta yi wajen dokan bishiyar sai da Bishiyar ta karya biyu rabi ya zubi
kasan jijjigen bishiyar ya kuma ya tumboko amma bai gama tumbukewa ba, amma rabin
bishiyar ya cire sun yi tafiyar ruwa da zakanyar, Zakanyar ta fadi kasa ko shuruwa bata yi ba

Aikuwa ganin wannan nasara da Gimbiya Lushmaira ta yi sai ta yi sauri zuwa inda jaririn Zakin
nan yake ta dauke shi ta kara falfalawa da gudu domin kuwa duk Zakunan ta lura basu mutu ba,
domin kuwa sai motsi suke.

Koda ta yi nisa sai ta fara tafiya a hankali domin wata shu'umar gajiya ta sarketa haka nan bata
san lokacin da ta zube kasa ba amma saboda tsananin naci irin na gimbiya Lushmaira bata saki
wannan jaririyar Zakin ba.

Al'amarin su Yarima Zaiyan da sauran tawagar su Sarki kuwa lokacin da suka kara nisa a cikin
tafiyarsu, har ya zamana sun shigo cikin dajin da 'yan sumamen daga bangaren Su Sarki
Madham suka boye cikin ciyayi suke. Koda Suka shi go wannan gurin sai tafiyarsu ta koma
sassarfa kuma da yawa daga cikin mayakan da suke kan gaba sun zare makamansu.
Ba komai ya sa haka face, kawai sun lura cewar akwai alamar wasu halitton a gun, ba dan
komai suka gane haka sai ganin da yawan Tsunsayen dajin sun ta shi sama, sannan kananun
namun dawa sun komo wajen dajin idanuwansu na kallon cikin korayen ganyayyarki

Lokacin da suka isa tsakiyar dajin basu gushe ba suna kara falfalawa da gudu suna kabbara
tare da daga makamansu sama.

Haka nan suka wuce wannan dajin batare da maboyan Dakarun sun yi illar komai a gare su ba

Lokacin da Ayarin Dakarun suka gama wucewa sahu-sahu, su ka yi nisa sai Dakarun suka firfito
suka taaya su ka yi cirko cirko suna numfarfashi. Domin wani irin tauro ne ya cika misu zuciya
har ya haifar musu da kasa aiwatar da koman

Su ka fito daga cikin mañoyar Sadauki Aksar ya tsaki gami da doka kafarsa a kasa, ya co.

"Tir da wannan jarumtakarmu da har kwarjinin wasu zai hanamu mu siwatar da abinda
shugabanmu ya umareemu, yanzu mai kuke zaton za mu je mu sanar da Sarki.

Wani mai bi masa da ake wa lakabi da Kuffuru, ya numfasa ya co, "Ya shugaba ni kaina abinda
yake raina ke nan, kuma na tabbata idan har muka komawa Sarki da labarin wannan ragwanta
da mu kai ba mu da hukunci da ya wuce harshensu ya karce kasa, ma'ana kaifin takohinsu ta
datsa wuyanmu, sai dai ba za mu talia barın haka ta faru kuma aikata hakan ba ya na nufin mun
gama asarar aikinmu hane, yanzu ma skwal dama tunda yanzu muna bayan wadannan Dakaru
abu na farko da za mu yi saurin yi yanzu shi ne mu bi bayansu tun kafin su Isa Sansanin da za
a yi wannan gumurzun mu
bi su da tsananin harbin kibiyoyi yanda za mu rage yawansu idan ya so kafin su ankara damu
sai mu juya da baya mu gudo"

Koda Sadauki Askam ya ji wannan shawara daga yaronsa Kuffura sai ya yi aminci da wannan
shawara nan take ya yi umarni da a ci gaba da bin bayansu, sannan ya yi umami kowa ya fitar
da masunsa.

Nan take dakarun suka bi umaminsa suka nikata abinda ya umarce su da su yi.

Koda suka dunguma zasu fara tafiya sai suka ga mutum a bayansu, su duka suka waiga. Suna
waigawa sai su ka yi ido biyu da gimbiya Shadilat, sune ganinta suka gancta kamar yanda ita
ma ta gane su, ba komai yasa suka shaidata sai ganin kamanin da su ka yi da Sarki Abu
Zaiyan, nan take sai Askam ya kyaikyale da dariyar mugunta, Sakamakon dariyar da yake yasn
daukacin jama'arsa su ma suka kaure da wannan shu'aumar dariya.

Gimbiya Lushmaira tana tsaye da jaririn Zakinta a hannunta tans binsu da kallo cikin tsananin
mamakinsu

Nan suka kuma daina dariya da kansa
Sadauki. Askam ya yi kanta da niyar ya kamata, amma kafin ya isa gareta sai kawai ya ji wani
irin ibu yana ta shi daga bayansa, kukan fitar rai ko da ya waiga sai yaga

1 / 5