Makashin Maza Book 1 Abdulaziz Madakin Gini

Author :  Abdulaziz Madakin Gini Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 2

3K to 4.7K   out of 4.7K words

daya, ba wani ba ne face aljani Daskin.
Ka sani duk duniya babu wanda ya isa ya saka Daskin aiki face boka Arjalu, don haka ka koma
gare shi ka gaya masa bukatarka zai amince, amma zai shimfida maka wadansu sharuddai
guda uku, sai ka duba ka gani idan ka ga zaka iya sai ka yi. Ni kam ina tabbatar maka in dai ya
amince va ba mu aron Daskin, to babu shakka a cikin kwana bakwai za mu samu wadannan
abubuwa guda uku. Da zarar abubuwan sun zo hannuna shekinan mun gama da Marganu,
zaka ci gaba da mulkinka duniya ba tare da wani ya zo ya rabaka da addininka ko karagarka
ba"

Ko da boka Zafaratu ya gama wannan jawabi, sai gumi ya karyowa sarki Larmisu, ya sake
shiga sabon tunani. Take ya ji duniyar gaba daya tai masa zafi, sai da ya sami kusan rabin sa'a
sannan ya dago kai ya dubi boka Zafaratu yace "Ya sarkin bokaye, hakika na ji duk bayaninka
kuma na yi tunani na tabbatar da cewa bani. da wata mafita face na bi shawararka, saboda hak
na amince zan koma gida na sake neman taimakon Doña Arjalu, kuma zan amince da dukkanin
sharuddan da ya shimfida mini."

Da jin haka murna ta kama boka Zafaratu yace "Hakika ka yi tunani mai kyau, kuma idan har ka
yi

hakan ka tsare mutuncinka da namu daga sharrin abokan gabarmu mabiya addinin Musulunci"

A cikin wannan dare sarki Larmisu da matarsa Lamsiya tare da 'yan rakiyarsu suka kimtsa suka
koma garin Ban nur. Da zuwa kai tsaye suka wuce izuwa gidan boka Arjalu, sarkı Larmisu ya
gabatar da bukatarsa.

Yayın da Arjalu ya ji bukatar sarki, sai yai shiru ya sunkuyar da kansa kasa, jim kadan ya dago
yace "Ya sarkin sarakai, ka sani cewa kamar shekaru hudu da suka gabata na taba zuwa
gareka na nemi wata alfarma amma ka ki amincewa, wannan alfarma ba komai ba ce face ka

bani auren kuyangarka Samali, idan har kana so na baka aljani Daskin sai ka bani abu uku, abu
na farko shi ne ina so ka daura aurena da kuyanga Samali, abu na biyu ina so ka raba
dukiyarka gaba daya kasu biyu ka bani kaso guda, abu na uku ka raba kasarka biyu ka bani
rabi na mulka, in dai kai haka zan baka aron aljani Daskin ya je yai maka wannan aiki." -
Sa'adda sarki Larmisu ya ji wadannan sharadai sai bakin ciki ya mamaye zuciyarsa, bai san
sa'adda kwalla ta zo masa ba, duk tashin hankalin da ya shiga a baya _sai ya ji kamar ruwan
sanyi ne akan wanda zai shiga nan gaba idan ya rabu da wadannan abubuwa guda uku,
wadanda boka Arjalu ya bukata daga gareshi. Abu na farko dai ita kuyanga Samali tun tana
shekara shida

sarki Larmisu ya kwato ta daga hannun wani sarki da Karfin tsiya, ma'ana sai da ya yake shi.
Samali kyakkyawar yarinya ce wadda bokayen duniya na wannan lokaci suka tabbatar da cewa
duk sarkin daya aureta ba shi ba talauci har bada, kuma ba za'a taßа cinsa da yaki ba. Bokayen
sunce ba za'a auri Samali ba sai ta kai shekara ashirin a duniya, a halin yanzu shekararta goma
sha takwas kenan yana kowonta, a yanzu kyawun Samali ya bayyana sosai karara a fili yadda
duk namijin daya dubeta sai ya kamu da sha'awarta. Bakin cikin sarki Larmisu shi ne yanzu
saura shekara biyu lokacin daurin aurensu da Samali yayi gashi boka Arjalu zai raba shi da ita.
Abu na biyu wanda ya sosa ran sarki Larmisu shi ne ya tabbatar da cewa idan ya raba
dukiyarsa da kasarsa biyu ya baiwa Arjalu rabi, ai tamkar sun zama daya ne. Idan suka zama
daidai kuwa babu mamaki wata ran Arjalu ya neme korarsa daga Bar nur ya mamaye garin
gaba daya. wannan shi ne abin da yai ta kai komo a cikin zuciyar sarki Larmisu.

"Ya sarkin sarakai lafiya na ji ka yi shiru?" Boka Arjalu ya tambaye shi

Larmisu ya dago kai ya dube shi sannan ya dubi Lamsiya yai shiru, jam kadan kuma ya sake
dago kai yace "Ya kai wannan boka kasan ance aikin mai shawara baya baci sai dai ba sirri, na
ji duk sharaddan

da ka shimfida mini, kuma zan je na yi shawara, zaka ji daga gare ni gobe da yamma."

Take su ka yi sallama, sarki Larmisu da Lamsiya suka tafi gida, dakarun rakiya na biye da su.

Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Larmisu da boka Arjalu, bayan ya dawo daga ziyarar
boka Zafaratu na birnin Hazaras.

***

A can birnin Kashmir kuwa rayuwar Bilal ta kasance cikin yawan bautar Allah dare da rana,
yana zaune ne tare da iyayensa wadanda suka kasance ma abota ilimin addinin Musulunci, da
yawan jama'a sukan zo garesu daukar karatu fanni-fanni, sunan mahaifin Bilal Ababakari, kuma
sunan mahaifiyarsa Hasiya.

Ababakari ya kasance mai farauta, yayi tafiye- tafiye zuwa kasashe da dama a duniya, saboda
haka ba shi da tsayayyen wurin zama guda. Wannan sana'a tasa ita ce ta kawo shi birnin
Kashmir, amma usulinsa ya fito ne daga yankin kasashen larabawa, kuma yana da cikakken
tarihin kakannin kakanninsa a rubuce cikin wani kundi. Wannan kudi na tarihinsa ya na ajiye ne
a cikin wata farar akwatu wadda aka yi ta da tagulla.

Tun Bilal yana yaro karami ya taso ya ke gının wannan akwatu a tare da mahaifiniša, kuma bai
tafa ganiu ranar da ya bude ta ba. A duk abubuwan da Ababakarı ya mallaka a duniya babu
abinda ya fi taka tsantsan da shi sama da wannan farar akwari, haria matarsa Hasiya bata taba
bude wannan akwati ba, bare taga abin da ke ciki, duk sa'adda Ababakari ya so bude akwatin,
ya kan bari dare ya raba sannan ya budeta. wannan al'amari ba karamin barwa iyalansa
mamaki ya ke ba. shi dai Bilal ya kudurce a ransa komai daren dadewa in dai wannan akwatun
na nan sai ya ga abin da ke cikinta, duk da ya san mahaifin nasa ba zai amince da hakan ba. Ita
dai akwatun an rufe ta da wata katuwar kuba ta musamman, wadda Bilal bai taba ganin katuwar
kuba irin ta ba. bare ya nemo mukulli da zai iya budeta.

A halin yanzu Bilal ya cika shekara ashirin da biyu cif-cif a duniya, kuma ya sami ilimin addinin
Musulunci mai yawa, a bangaren sana'a kuwa ya kware akan farauta, domin sau tari tare suke
tafiye-tafiye da mahaifin nasa. Duk sa'adda Ababakari zai vi tafiya yakan tafi tareda farar
akwatunsa, bai taba barinta a gida ba.
Wata rana tafiya ta kama Ababakari wadda ya so yayita tare da Bilal, amma Bilal ya kamu da
zazzabi mai zafi. A bisa dole Ababakari ya hakura da ya tafiya da Bilal, ya bar shi a gida. Bayan
Ababakari ya gama

shirya kayansa bisa rakumi a kofar gida, sar ya koma cikin gida domin ya dauko farar akwatun
nan tasa, shigarsa ke da wuya aka aiko cewa ana sallama da shi. A wannan lokaci tuni ya
dauko akwatun har ya iso zaure. ko da ya ji cewar wani abokin kasuwancinsa ne ya zo za su
gana, sai ya ajiye akwatun a zaure ya fita da niyyar idan sun gama ganawa zai dawo ya dauka.
Daman tuni a wannan lokaci yayi sallama da Hasiya da Bilal har ma yai masa addu'ar Allah ya
ba shi lafiya. Bayan sun dan zanta tsawon dan lokaci sai suka rabu, Ababakar ya hau kan
rakuminsa yai gaba.

Lokacin da Hasiya ta fara kokarin hada abinci a tsakar gida sai ta ji motsin akuya a zaure tana
kusur- kusur. da yake wannan ba sabon al'amari ba ne sai ta ci gaba a aikinta. Jim kadan ta ji
kursur-kusur din yayi yawa, don haka sai ta mike ta nufi zauren don tsoron kada akuyar ta kawo
shara ta bata wurin, ai kuwa da zuwanta ta iske akuyar na ta kokawa da farar akwatun nan ta
mijinta, a iya tunanin akuyar akwai sharar abinci a cikin akwatun domin an saba zubawa a cikin
akwatun shara a daidai inda aka ajiye wannan akwatin.

Ko da Hasiya tai ido biyu da wannan akwati sai ta ji zuciyarta ta buga da karfi, cikin hanzari ta
kori akuyar ta dau akwatin ta koma cikin gida tana mamakin dalilin da yasa Ababakari bai tafi da
ita ba, shin mance akwatin yayi, ko kuwa yana sane ya barta? Kai sam-

in Ababakari ba zat taba barin wannan akwatin ba a azure yana sane, don haka babu shakka
mantata yayi, amsar da Hasiya ta baiwa kanta kenan.

Yana daga kwance bisa shimfida a cikin daki ya ruke casbaha yana istigfari, ta shigo rike da
farar akwatin a hunnunta, ko da idanunsa su kai arba da ita ya ga abın da ke hannunta sai ya
mike zumbur kamar bai tuba ko da ciwon kai ba. cikin tsananin mamaki ya dubets yače "Unami
ya akai Abba ya baki wannan akwatın!"
Hasiya ta yi murmushin jin dadin ganin ya mike zaune, tare da mamaki, sannan ta zauna daf da
shi tace "Kai kuma ya akai ka samu lafiya yanzu-yanzu?"

Lokaci guda suka yi dariya "Wallahi ni kaina ban san yadda akai ba, ni dai ina ganin wannan
akwatun a hannunki sai na ji kamar an yaye mini rashin lafiyar"

Hasiya tace "Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki shi ne mai bayarwa kuma shi ne mai
hanawa"

"Haka ya ke Ummi" Bilal ya fasdl, sannan shi ma ya sake godiya ga Allah.

"Kamar yadda ka ga akwatun nan yanzu a hannuna haka nima na ganta ajiye a zaure, bana
raba daya biyu mahaifinka ne ya manta ta, hakika na san zai yi matukar bakin ciki idan har ya
tuno da cewa ya barta a



Mu haɗu a Makashin Maza littafi Na biyu Domin jin cigaban wannan kayataccen littafi.

Abdul'aziz Sani Madakin Gini
08137237071

2 / 2