Makashin Maza Book 1 Abdulaziz Madakin Gini

Author :  Abdulaziz Madakin Gini Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 2

1 to 3K   out of 4.7K words

MAKASHIN MAZA
Rubuta Labari
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
08137237071


Bayan shekaru dari takwas, zamani mai tsawo ya shude, an yi wani mashahurin sarki mai suna
Lamisu a cikin birnin Ban nur. Wannan sarki ya kasance mai tarin dukiya, kuma ma'abocin son
jin dadın duniya ne. A bisa wannan dalili yasa aka tara masa dukkanin magina na kasar, yace
dasa yana so a gina masa kasaitacciyar fada wadda babu kamarta a duniya.
Ko da jin wannan batu sai sarkin magina ya mike yace "Ya sarkin duniya hakika ka zo mana da
babban al'amari, don haka muna bukatar ka ba mu kwana bakwai mu je mu yi tunani"

Sarki Larmisu yayi murmushi yace "Na amince, kuma ina tabbatar muku da cewa komai yawan
dukiyar da za'a kashe a kan wannan gini zan bayar"

Daga nan ya sallame su suka tafi.

Bayan kwana bakwai sarkin magina ya dawo yace da sarki sun gama shiri, nan take sarki ya
bayar da duk abubuwan da ake bukata aka fara aiki.

Ana cikin yin haka sai aka tono wani irin ruwa a cikin karkashin kasa, wanda yai matukar tsorata
wadannan magina. Shi dai ruwan mai kauri ne, kuma wani abu na motsi a cikinsa. Maginan
suka yi iya kokarinsu akan su kwashe wannan ruwa amma sai abu
ya gagara, saboda tsananin santsinsa. Cikin tsananin razana maginan suka ruga izuwa fada
suka sanar da sarki halin da ake ciki. Ko da jin haka, sai sarki Larmisu tare da bokansa Arjalu
suka rugo izuwa wannan wuri. Da zuwa suka iske wannan ruwa, Boka Arjalu ya fiddo wata
battar tsafi yayi wani tsafi, take wannan battar ta zude wannan ruwan gaba dayansa.
Arjalu ya dubi sarki Larmisu yace "Ya sarkin duniya, hakika akwai bayani mai hadari dangane
da wannan ruwan, akwai bukatar bincike, zai fi kyau ka bini zuwa dakin tsafina"

Ba tare da wata gardama ba sarki Larmisu ya amince da shawarar boka Arjalu, suka tafi izuwa
dakin tsafin su biyu kawai.

Daki ne wanda aka gina shi da duwatsun wuta, babu komai a ciki face tarkacen kayan
tsafe-tsafe kamar kahunhuna, gashin dabbobi iri-iri, da kwalabe masu dauke da ruwa mai
launuka da yawa. Da shigarsu cikin dakin sai boka Arjalu yai nuni ga wata kujerar karfe ga sarki
Larmisu yace ya zauna.

Larmisu ya zauna, shi kuma sai ya fiddo battar nan wadda ya zuke ruwannan a ciki, wato ruwan
da aka hako a wajen gini. Take boka Arjalu ya dora battar bisa wani farin gilashi ya fara surutai
na tsafi tare da rufe ido. Jim kadan da faruwar haka, zufa ta lullube Arjalu, jikinsa ya kama
karkarwa, al'amarin ya da ya firgita
sarki Larmisu, daga can kuma sai ya ga wani farin hayaki ya bulbulo ta cikin kunnuwan boka
Arjalu.

Boka Arjalu ya kwalla ihu mai karfi tare da mikewa tsaye zumbur, sai da yayi dogon ajiyar
numfashi gami da atishawa, sannan ya dubi sarki Larmisu yace "Ya sarkin duniya, hakika
wannan ruwan ba ruwa ba ne mutum ne"

Cikin tsananin mamaki sarki Larmisu ya mike tsaye yace "Ban gane ba, me kake nufi?"

"Wannan ruwa, ruwa ne na masifa, ruwa ne na bala'i, hakika maginanka sun tono babbar jaraba
ga dukkanin mutanen duniya. Wannan wani tsohon azzulumin matsafin sarki ne wanda ya
gallabi mutanen duniya a zamaninsa, sunansa Marganu dan Jandanu jikan Gundukurki, ina
tabbatar maka da cewa idan ya tashi kowa ya shiga uku. Ba zan iya ci gaba da tsare shi ba a
cikin battar nan fiye da kwana arba'in, ka sani idan ya tashi karagarka tafi karfinka, ba kai ba ma
gaba daya sarakan duniya da matsafan duniya mun shiga cikin mummunan bala'i"

Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki Larmisu ya kara dugunzuma, ya fara kai komo a cikin
dakin tsafin, ya kasa tsaye ko zaune, sai ya kai gwauro ya kai mari. Daga can ya tsaya ya dubi
boka Arjalu suka fuskanci juna sosai yace "Kai boka Arjalu! Ka tuna kai matsafi ne dan matsafa
kuma jikan matsafa, maza ka


shiga aikinka! Ka bincika ko akwai hanyar da za mu bi mu samawa kanmu sauki, mu ceto
rayuwarmu da ta sauran jama'ar duniya"

Yayın da boka Arjalu ya ji haka sai ya tuntsure da mahaukaciyar dariya har sau uku, sannan ya
shafi gemunsa yace "Ya sarkin duniya, hakika ka zuga ni kuma na ji dadi, saboda haka zan yi
aikina, na rantse da darajar tsafi sai na samo mana mafita, amma ina so ka ba ni tsawon kwana
biyu"
Yayin da sarki Larmisu ya ji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya, sannan yace "To shikenan na
amince zan kasance mai sauraronka"

Daga nan suka yi sallama sarki ya tafi.

Sarki Larmisu shi ne sarki na dari hudu da ashirin a jerin sarakan da suka mulki kasar Ban nur,
tun daga zamanin sarki Hafis mahaifin Badiya, macen da ta daukaka a duniya akan baiwar
fassara mafarki, kuma ita ce wadda ta bar babban abin tarihi a masarautar Ban nur wanda har

yau yana nan a rubuce cikin kundin tarihin sarautar garin, a cikin wani daki na musamman a
gidan sarautar.

A halin yanzu sarki Larmisu na da mata goma sha bakwai, kuma yana da 'ya'ya kimanin arba'in
a da doriya. Shi dai wannan sarki ya mallaki dukiya mar tsananin yawan da shi kansa bai san
iya adadinta be. Larmisu mutum ne shagalalle, babu abin da yake tsore

face mutuwa ko rabuwa da mulki, wannan dalili yasa hankalınsa yayi matukar tashi da ya ji
cewa Marganu dan Jandanu zai dawo ya raba shi da karagarsa. Lokacin da Sarki Larmisu ya
baro wajen boka Arjalu, sai ya dawo gida cikin matukar damuwa. Ko da yai arba da amaryarsa
gimbiya Lamsiya, sai ta fuskanci hakika yana cikin damuwa.
Lamsiya ta tarye shi da sauri inda ta rungume shi, sannan ta zaunar da shi bisa wata kujera ta
alfarma suka fuskanci juna sosai tace "Ya sarkin sarakai, me ne ne ya tayar maka da hankali na
ganka a cikin damuwa?"

Larmisu yai gyaran murya yace "Ya ke sarauniyar taurari, kin sani cewa duk irin bacin ran da na
shiga da zarar na yi ido biyu da kyakkyawar fuskar nan ta ki sai na ji zuciyata tai sanyi, amma
kin ga yau an sami sabanin haka, tabbas ina cikin mummunan tashin hankali"

Nan take va kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da boka Arjału ya zayyana mata. Ko da
jin wannan batu sai Lamsiya ta tuntsure da dariya, cikin matukar mamaki sarki Larmisu ya janye
jikinsa daga nata yace "Me ne ne ya baki dariya?"

Lamsiya ta mike tsaye ta yi 'yar tafiya taku uku, sannan ta waigo ta dube shi tana mai murmushi
tace "Yanzu kai akan wannan ne ka tayar da hankalinka? To tsaya ka ji, ni bana tsoron abin da
zai zo muddin na san

da zuwansa, wanda ban san da zuwansa ba shi ke ba ni tsoro. Ka je ka saurari bokanka nan da
kwana biyun idan har baka sami nutsuwa da mafita ba ka zo gare ni. ni zan baka mafita."

Ko da sarki Larmisu ya ji wannan batu sai yai shiru ya kura mata ido ya kasa cewa komai, ba
dan komai ba sai don ya san cewa tana da babban abin dogaro. Mahaifin Lamsiya wani
kasurgumin matsafi ne wanda ya shahara a duniya, domin a wannan zamanin ana kyautata
zaton babu matsafi kamarsa a duk duniya. Shi ne matsafin da ya mayar da mutanen wani
babban gari birai gaba dayansu, yau shekara ashirin kenan da faruwar al'amarin, har yau
mutanen na nan a matsayin birurruka an rasa wanda zai warkar da su, har ma sun hakura sun
rungumi kaddarar karasa rayuwarsu ta duniya haka, sunan wannan gari na birai Maduwal, shi
kuma matsafin da ya mai da su biran wato mahaifin Lamsiya sunansa boka Zafaratu, a yanzu
haka idan mutum ya je birnin Maduwal zai iske su a cikin rayuwa irinta bil'adama babu abin da
ya sauya na daga al'adu da harkokin yau da kullum, matsala daya kawai basa magana kamar
yadda sauran bil'adama ke yi, idan fatake suka shiga garin sai dai su yi harkar kasuwanci cikin
bebanci.

***

aderbege

*shirya

Bayan kwana biyu sun cika sai sarki Larmisu ya koma gidan boka Arjalu yace da shi "Ya kai
boka Arjalu, ka sani cewa yau ne ranar cikar alkawarinmu, dan haka na zo na ji daga gareka,
me ne ne mafita a bisa wannan masifa da ta tunkaro mu?"

"Wannan zance haka yake, ya sarkin sarakai kamar yadda na gaya maka cewa zan yi bincike,
to na yi kuma an dace, sai dai al'amarin ya zo da wani babban al'amari mai wuyar gaske. Inda
zaka yi bincike a cikin littafin tarihin sarautar kasarka zaka ga yadda wadansu jarumai su biyu
Sham'unal gazi da dan'uwansa Uzaifa suka narkar da Marganu dan Jandanu, ya zagwanye ya
zama wannan ruwa da maginanka suka tono. Ka sani cewa su wadannan 'yan'uwa ma'abota
addinin Musulunci ne, to kasa ni a duk fadin duniyarnan babu wanda ya isa ya kawar da
Marganu idan har ya tashi, face tsantsan ziri'ar su Sham'unal gazi. Yau shekara dari takwas
kenan da zamaninsu, babu sauran ziri'arsu a duniya face wani saurayi guda daya kacal da
mahaifinsa, wadanda suke zaune a can birnin Kashmir da ke kasar Hindu, ana kiran yaron Bilal.
Shekarun Bilal ba za su wuce ashirin da biyu ba, kuma shi jika ne na dari da arba'in ga
Sham'unal gazi dan Safwan. Daga nan zuwa birnin Kashmir tafiyar kwana sittin ce ga matashin
aljaai mai matukar jarumta, amma akwai wani aljani mai suna

Daskin wanda zai iva zuwa čikin kwana goma sha bıyar Idan ka amince zan ıya hadaka da
Daskin va kai ka ka je ka zo da Bilal kafin kwana arba'in, wato kafin Marganu dan Jandanu ya
tashi"

Yayın da sarki Larmisu ya ji wannan batu, sai bankalinsa ya dada dugunzuma fiye da kowanne
lokaci, maimakon ya sami nutsuwa da abin da boka Arjalu ya sanar da shi.

Boka Arjalu ya dubi sarki cikin mamaki yace "Yaya kuma na ga hankalinka ya kara tashi
Larmisu yai ajiyar numfashi yace "Shin ka taba ganin ruwa da wuta sun hadu an zauna lafiya?b
Boka Arjalu yace "A'a"

"Karka manta mu ba mu da wani addini a kasarnan face tsafi, shi kuma Bilal dinnan da kake
magana musulmi ne, baka tsoron idan na zo da shi yai mana maganin Marganu, jama'a za su yi
imani da addininsa?"

Ko da Arjalu ya ji wannan batu sai yayi shiru yana mai tunani, daga can yace "Hakika ka zo da
magana mai karfi, hakika sam ban yi tunanin wannan al'amari ba, to amma ka da wannan ta
tayar maka da hankali, kafin ya zo sai mu sihiree zuciyoyin jama'arka"

Sarki Larmisu yace "Kai al'amarinnan yana da wuya, abinda za a yi nima ka bani kwana biyu na
je na yi nawa tunanin, in ya so sai na zo mu yanke shawara"

Boka Arjalu yayi murmushi yace "Ya sarkin duniya, kada ka wahalar da kanka, na rantse da
girman tsafi babu abin da za'a yi a sami nasara fiye da wanda nace ayi"

Nan dai sarki Larmisu yai sallama da boka Arjalu ya dawo gida cikin damuwa, da zuwa ya sanar
da Lamsiya duk abin da ya faru tsakaninsa da boka Arjalu.

Da jin haka Lamsiya ta bushe da dariya tace "Ai na gaya maka cewa kada ka damu zan kaika
wajen babana boka Zafaratu, shi kadai ne a doron kasa zai iya yi mana maganin masifar nan."

Larmisu yace "Hakika na amince, abin da za'a yi yanzu ki tashi mu yi shiri yanzun nan sai nasa
a shirya mana 'yan rakiya"

Lamsiya tace "Haba ranka ya dade saurin me ka ke yi?"

"Dole na yi sauri don ba ni da isasshen lokaci, yau fa saura kwana takatin da takwas Marganu
ya tashi, kuma kin sani cewa daga nan zuwa garinku tafiyar kwana guda da yini ce."

Lamsiya tace "Hakika ka yi gaskiya, don a bari ya huce shi ke kawo rabon wani"

"Kwarai kuwa, kuma Zama a waje daya tsautsayi ne ba"

Nan take sarki yasa aka shirya dawakai da guzurin tafiya tare da barade hamsin, suka dau
hanya izuwa

burnin Hazaras inda mashahurin matsafın yake wato boka Zafaratu mahaifin gimbiya Lamsiya
amaryar sarki Larmisu na garin Ban nur.

***

Sannu-sannu sarki Larmisu da amaryarsa Lamsiya uka iso birnin Hazaras. Birnin Hazaras
karamin gari ne mai dauke da jama'a kadan da daidaikun gidaje. Gaba daya mutanen garin sun
yi imani da sarkinsu wanda shi ke sanar da su komai na dangane da rayuwarsu, a karshen
kowacce shekara sukan taru a kofar gidansa ya sanar da su abubuwan da za su faru a sabuwar
shekara Ya kan sanar da su mutuwa, fari, yabanya da sauran al'amuran rayuwa.

Tun kafin su sarki Larmisu su karaso kofar gar suka yi kicibus da 'yan tarya, wasu kartin saman
mutum hudu sanye cikin jajayen fatu, wadannan su kasance barorin gidan su Lamsiya ne. Ko
da ganinsu bisa dawakai sai Lamsiya ta kira sunayensu, suka amsa take suka sauko daga kan
dawakansu suka zube kasa su kai gaisuwa a gareta da kuma sarki Larmisu.
Lamsiya ta dube su tace "Ina zaku je ne?"

Daya daga cikinsu wanda ya fi sauran kwarjin yace "Ranki ya dade ai dama ku muka zo tarya,
ai tur jiya sarki ya sanar da mu zuwanku"

Duk da sarki Larmisu ya san al'amarin boka Zafararu, sai da yayi alajabin yadda akai ya san da
Puwansu. Nan dai yan tarya suka juya suka wuce gaba su sarki Larmisu suka bisu a baya,
tafiya kadan suka iso gidan boka Zafaratu, aka shigar da su har cikin fadarsa.

Boka Zafaratu yai musu marhaban aka gaisa. sannan ya dubi sarki Larmisu yace "Na san kana
cikin zumudin ganawa da ni, amma ina so ka yi hakuri ku huta tukunna ku ci abinci, in ya so sai
mu gana da daddare."

Sarki Larmisu yace "Godiya na ke, ya sarki bokayen duniya"

Ba tare da bata lokaci ba aka kawo masa ababan ci da sha na alfarma, ya ci ya sha, sannan ya
kwanta ya huta, ita kuwa Lamsiya tuni dama ta wuce cikin gida wajen mahaifiyarta. Sai da aka
sami sa'a biyu da faruwar wadannan abubuwa, sannan boka Zafaratu ya aika aka kirawo sarki
Larmisu da Lamsiya suka gabata gareshi.
Boka Zafaratu wani dattijo ne wanda shekarunsa sun haura dari da arba'in, duk da wannan
tsufa na sa babu alamar gajiyawa a jikinsa ko kadan. Yana da farin dogon gemu mai tsananin
haske da shekl, gashin girar sa ma fari ne, yana da kwala-kwalan idanu masu girma kamar na
mujiya, hancinsa mai tsini ne, kuma yana da
karamin baki, dogo ne matuka kuma kakkaura, kai da ganinsa ka san da can an yi kasurgumin
jarumi.

Lokacin da sarki Larmisu da Lamsiya suka shigo cikin dakin boka Zafaratu, sai suka iske shi
zaune bisa wani buzu mai kyawun gaske. Cikin biyayya Larmisu da Lamsiya suka zauna a gefe
guda aka sake gaisuwa, sannan shiru ya biyo baya, har tsawon dakika goma.

Sarki Larmisu yai gyaran murya sannan ya bude baki zai Magana, sai boka Zafaratu ya tari
numfashinsa yace "Kada ka wahalar da bakinka duk abin da ke tafe da ku na san da shi fiye da
shekaru sittin baya, boka Arjalu ya sanar da kai cewa Marganu dan Jandanu zai tashi nan da
kwana talatin da takwas, kuma idan ya tashin kowa zai shiga tashin hankali a duniya, kwarai
kuwa abin da ya gaya maka gaskiya ne. Kuma ka nemi ya sanar maka da mafita, inda yayi
binciken kwana biyu sannan ya sanar da kai cewa sai ka je birnin Kashmir ka dauko Bilal,
wannar ma haka ne, amma idan kai hakan har abada ka rabu da mulkinka kenan da dukiyarka,
wannan yaro Bilal shi zai maye gurbinka"

Ko da jin wannan batu sai sarki Larmisu yace "Ya sarkin bokayen duniya, kai mini rai, ka ceto
matsayina da kimata, ka dubi darajar 'yarka guda daya cal a duniya ka taimake ni"

Boka Zafaratu ya tuntsire da dariya, sannan ya hade fuska yace "Hakika Marganu dan Jandanu

cikakken hatsabibi ne, ina da labarinsa tun ina da shekara takwas a duniya, duk irin tsafe-tsafen
da yayi ya sami daukaka a duniya na yi bincike akansu na gano yadda yayi su, ina tabbatar
muku da cewa ni ma zan iya yin duk abin da yayi, sai dai kash! ni ba ni da wannan burin a
zuciyata, saboda yanzu tsufa ya riske ni kuma gani na sami nisan kwana a duniya. Ya kai
wannan sarki ina sanar da kai cewa ya zama dole mai laya ya kiyayi mai zamani, Marganu ya ci
zamaninsa tuni. yanzu ni nake cin nawa, bai isa ya dawo ba ya fi karfina. Tun ina da shekara
takwas na san da cewa akwai ranar da Marganu zai dawo duniya, kuma tun a sannan na fara
kokarin neman abin da zan hallaka shi. a cikin bincikena na gano cewa idan ina so na hallaka
Marganu yadda har abada ya tafi kenan, sai na samo wadansu abubuwa guda uku, abu na
farko shi ne gashin jelar Ifiritu na kwalba, wato takadarin aljanin nan wanda aka kulle shi a cikin
kwalba aka jefa cikin teku ya bace a karkashin ruwa, har yau ba'a sake ganinsa ba. Abu na biyu
shi ne ainihin sandar sarki na farko wanda ya fara sarautar aljanu a doron kasa, wadda a halin
yanzu tana nan ajiye, kuma a tsare cikin gidan sarautar sarkin aljanu na birnin Sin. Abu na uku
wanda gaba daya yafi wadannan wahala, shi ne kitsen kifin da yafi kowanne kifi girma a duniya.
Tuntuni na gano cewa ni da aljanuna masu yi mini hidima baza mu iya samo

wadannan abubuwa ba, face da taimakon aljani guda

1 / 2