Jamiin Sirri CID Book Compelet By Matar Malam

Author :  Matar Malam Mujaeeda Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 3

3K to 6K   out of 8K words


Delu Mai Aikinsu tazuba Mata takai mata mota Sannan tashiga tawuce,


Parking motar tayi sannan ta d'auke basket d'in tashiga ciki, direct office d'inta tashiga saida
tagama settling komai nata sannan tafito office d'in doctor San taje but Yana Rufe hakan yasa
tanufe D'akin da Aka kwantar da mutumin

Tura k'ofar Tayi da sallama tashiga


Dukansu Ido suka zuba mata bama kamar guy d'in domin ta burgeshi Sosai Komai nata slow
cikin natsuwa da Hankali


Doctor San Yace"Kin manta Damu ba Kuma inatason naje gida Amma ba dama,"




"Dan Allah kayi hak'uri wllh na makara ne Amma Yanzu gani Yaya Ake Ciki kayi Magana da
doctor najib d'in,"?

"Eh yazo tin jiyan ma Kuma yaduba komai normal Saidai eh Yasami loosing memory d'insa
Saidai idan yaga wani Abu daya shafe Rayuwarsa tabaya to zai iya tinawa ya dawo daidai,"



"To Amma doctor San Maganar tasa kuma fa,"



Hahahaha"kinzata Wai Bai magana Yanzu ma Saida mukayi magana dashi yace ruwa Saidai na
lura miskiline na K'arshe shiyasa duk Magana inbatazama dole ba tofa bazai yi taba,"



Maida kallonta tayi kansa saitaga ya d'auke Kansa yawani had'e Rai


Matsawa Kusa Dashi Tayi ta zauna Had'id'a zuba masa Abincin da tazo dashi pepper soup ne
da shinkafa mik'amasa Tayi Tace,"Kaci Abinci kadaina B'ata Rai bafa da gangan na bigeka ba,
Ni banma San na bigeka ba Kawai saiganin ka nayi kwance idan za'ayi tuhuma Kai Zan tuhuma
d'an Samari," tak'arasa maganar tana wani farr da idanuwanta


Murmushi ya sub'uce Masa Dan shi harga Allah dariya tabashi,



"Yawwa idan kanayin magana da murmushi to Zan fasa tuhumarka, Yanzu kaci Abinci ka Huta
Kafin nagama da Sauran patient d'ina sainazo Muyi Magana dakai," Bata jira Ansarshi ba
tawuce dama doctor yajima da fita,


Saida tafita sannan ya d'auke Abincin yaci,

Tajima Kafin tagama tadawo Zaune ta tarar Dashi ya jingina da gadon,


Sallama Tayi Ai kuwa ya Amsa Ahankali Saida taji wani iri dajin saukar Muryarsa,

Zama tayi daga cikin kujerun d'akin Tace"Sannu bawan Allah yajikin naka,"



"Da sauk'i" Yafad'a Atak'aice idanuwansa na rufe




"Masha Allah A yanzu dai kasami sauk'i kaga Yakamata Asallameka so Ina zankaika Ma'ana
Ina Ahlinka suke,"



Shuru harta cire ran Zaiyi magana Sannan ya Ware manyan idanuwansa kanta cikin sanyi da
Alamar tausayi Yace"bansani ba nima bansan kowa ba saike, Ni ba d'an Nan garin bane Amma
namanta Ina nake bansan Komai game Dani ba Yanzu," Wasu Hawaye Suka Soma silalo Masa



Cikin Jin tausayinsa Ta matso inda yake tace"kada kadamu Akai nice silar faruwar Komai Dan
Allah ka yafemin zanje dakai gidanmu ka zauna Kafin Allah yasa Katina Komai naka, Amma ya
sunanka,"?




"Sunana Abbas Shine Kawai Zan iya tinawa saboda Naga wannan tare dani, karancin passport
d'auke da sunan Abbas Akai, Amma hakan zaiyu kuwa? Iyayenki zasu Bari na zauna daku
bayan basusan Ni kowaye ba, ko Ni bansan waye Ni ba balantana nayi musu bayani idan Suka
buk'ace hakan,"



"Kada kadamu Kan wannnan idan nayi musu bayani zasu fahimta Kuma ma Daddy na bayanan
A Yanzu Amma nasan very soon zai dawo, Yanzu ka d'auki duk Abunda kake buk'ata Kazo
muje kawai," tana gama maganar tafice


Binta Yayi da kallo Yana Aiyana Abubuwa dayawa Aransa Had'id'a sakin murmushi,

_NI DAI MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR QUEEN OF WRITER
KALLON IKON ALLAH KAWAI NAKE NAKASA FAHIMTAR KOMAI GAME DA WANNNAN
MUTUMIN,"


Saida tagama Komai sannan Sukayi Magana da doctor San ya rakosu har mota suka wuce
shikuma ya koma,



Kallon hanya Kawai yake har Suka Isa bawanda Yayi magana

Bayan Tayi parking ta fito tareda Kiran Mai gadi da Sauran masu kula da Gidan Tace,"kunga
wannnan bak'ona ne, so Yanada ikon Shiga ko fita duk Sanda yatashi idan Kuma wani yanemi
Wani Abu kanshi kawai kuce yasameni, banason sa'ido ko Shiga hurumin da baishafe mutum
ba, Ina fatan kun fahimce Ni,"


"Eh madam munfita Kuma in Sha Allah zamu kiyaye,"



"Yawwa Masha sunanshi Abbas, so Shine kawai zaku iya komawa Kan Aikinku nagode,"


"Muje ciki ko Abbas"

Binta Yayi Suka Shiga parlorn

Kallo Yafara k'arewa palourn


"Zauna Bari Nakira Ammanaaa ku gaisa"


Gyad'a kansa Kawai Yayi tareda zama, itakuma tahaye sama

D'aga kansa Yayi Yana kalle kalle can idanuwansa suka fad'a kan wani photo k'ato Dake manne
A bango, Itace cikin shigarki Likitoci da Sauran mutane gefe sai sai wani mutum data rik'e shima
Yana rik'e da ita suna dariya ga A Ward's tsakansu,


"Ba shakka wannnan Shine," Ya fad'a cikin zuciyarsa tareda cije lip's d'insa na sama,

Jin Alamar Ana saukowa k'asa yasa da sauri yakoma ya zauna,



Fitowa sukayi tareda wata mata,

Sauka yayi k'asa Yana gaida Matar

Cikin fara'a ta Ansa Tace"A'a tashi ka zauna Abbas ai tafad'a mun komai kada kadamu bamuda
matsala kasake ranka kaji ka d'auka kamar gidanku, Kuma itama ka Zama yayanta idan kaga
tayi kuskure kamata fad'a ta Gyara, Ai Nainaaa mutuniyar kirkice tanada tausayi fatanmu Allah
yabaka lafiya Kawai,"


"Ameen Ameen Ammaaa Ngd in Sha Allah zanzamo Nagari gareku," kansa A k'asa yake
Maganar




K'uramasa Ido tayi tana murmushi itadai Yana burgeta Wllh,


"To kin fad'ama Daddyn ki Saboda gudun matsala"



"Ammanaaa kinsan samun wayar Daddy it's not easy Always he is busy but I will trying to charts
on WhatsApp,"




"Hakane Amma kiyi gaggawar fad'a Masa kinsan Yanayin gidan naku dai," Tak'arasa Maganar
tana mik'ewa

"Ammanaaa Ya Hassan ya kirani yace gobe zasu dawo fa,"



"Eh Nima sun fad'amun Allah ya dawo Mana dasu lafiya kawai,"


"Ameen Ameen, Zan Nuna Masa inda zai zauna"



"Eh Hakan ya kamata kam,"



"
Maida kallonta tayi gareshi kanshi Ak'asa, ga Alama Dai yana kunyar Ammaaa



"Ya Abbas kaidana Jin Kunya ko wani d'ari d'ari everything will be normal bamuda matsala ko
gun Daddy bazan Samu matsala ba Domin yana sona kuma Yasan bazanyi Abu Mara Kyau ba,
so tashi na nuna maka inda zaka zauna,"

Tashi sukayi suka nufe waje wani parts dake kusa Dasu Yana Rufe ta kaishi d'akin 2 ciki da
palour sai kitchen store dama Toilet,


D'akin ya had'u ba datty Komai Pink ne ciki shima,


"Fatan d'akin ya maka,"




"Sosai ma kuwa yayi Kyau musamman tsarinsa da kalarsa Komai Pink Amma na Mata ne ai,"

Dariya Tayi Kafin tace"itace best colors d'ina Pink shiyasa duk Abunda Yake Under control d'ina
nakan Masa zab'i irin nawa,"




"Ai Kam dai Yayi Kyau Sosai, Nainaaa"



"Au kasan sunana Ashe,"?



"Habadai sau nawa Aka Kira sunanki gabana? Ai dole na rik'e,"



"Um hakane Bari na Barka kahuta ko, sai Anjima Amma idan kana buk'atar wani Abu kamin
Magana Kuma ba shamaki ka iya zuwa part d'inmu Koda bana Nan Ammaaa tana Nan zata
yimaka koma meye,"



"Ina godiya sosai da wannan karamcin Nainaaa Allah yasaka da Alkhairi Yabani damar yimiki
Abunda Kika min koma fiye da Hakan My Nainaaahh," Yaja sunan Cikin Cool voice d'insa,


Sosai taji dad'in hakan murmushi Kawai tamasa Had'id'a juyawa tafice................................




_BASEERATA ITACE ARZIKINA_





WhatsApp number 07064904617
*JAMI'IN SIRRI*
*C~I~D‍*

_PAID BOOK #300 ONLY_


_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR ..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar
namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book,
(6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9)
Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12)
Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN
ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE
BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P
ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22)
FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR
SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID
BOOK 300 ONLY.
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar QUEEN OF WRITER ```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda
yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake
kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~D‍*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka
bayar....._


_SATURDAY 16/9/2023 SEPTEMBER_



*Free ️ 16 to 20*

_SECON TO THE LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH_

*IDAN KINA SO KANA SO KABIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA MASU SIYE KU FITARMUN
DA BOOK KUDA ALLAH BAMASU KARANTAWA BASU BIYABA SUNAGANIN SUNSAMI
BANZA KUMA KUDA ALLAH, BAZAN YIWA KOWA ALLAH YA ISA BA AMMA KUNSAN
BAKUMIN ADALCI BA HAKAN YASA NACE KUDA ALLAH,.. 300 NE KAWAI BA YAWA, ALLAH
YASA MUDACE AMEEN*

...........Kwanaki sunfara tafiya inda Yanzu satin Abbas 3 Cikin gidan shak'uwa soyayya Mai
tsanani tashiga tsakaninsu Musamman Nainaaa sosai take son Abbas ba kad'an ba, Kullum
suna tare indai tadawo Aiki ko in bataje ba, Duka Ahlin gidan sunsan da Soyayyar da ke
tsakaninsu,,



Yanzuma tana Zaune A garding d'in gidan tana Shan iska laptop ce gabanta tana Magana
da Daddy,



"Allah daddy mutumin kirki ne na k'agu kadawo ku had'u Daddy harda Aiki nakeson kabashi,
Daddy yaushe zaka dawo,"?




"Oh Daughter Lalle wannnan Yaron kina Sonshi ba kad'an ba, Amma kina ganin Bawata
matsala kinsan fa d'an Adam sanin sirrin zuciyar mak'iyi sai Allah, sautari Mutum zai rab'ekane
don biyan buk'atar sa dazaran Yasamu saiya gujeka,"




"Daddy shikam ba Haka yake ba, Kuma in Sha Allah had'uwar mu Alkhairi ce nidai da Zuciya
d'aya nake tare dashi shima hakan ne in sha Allah,"



"Shikenan daughter nalura dai wannnan Abbas d'in yagama siyemin zuciyar Y'a, in Sha Allah
cikin satin Nan zandawo Kinga saina zauna dashi daganan muyi Abunda yadace Ai duk Abunda
kikeso shi Zanmiki daughter,"



"Yawwa Sweet Daddy Inasonka Sosai, bay bay," ta k'atse Kiran



Duk Abunda take Yana hangosu ta window d'in d'akinsa domin tanan garding d'in yake,
murmushi Kawai yake zubawa Had'id'a cizar lip's d'insa,

Komawa yayi ya zauna Yajanyo wata jaka Naga ya fidda wata laptop Yasoma dannawa Yajima
Yana Aikin sannan ya Rufe, Jin motsinta zata shigo yasa Yayi sauri b'oye laptop d'in da jakar
duka Yadawo Cikin sauri ya kwanta Had'id'a rufe idanuwansa Kamar Mai bacci,


Da sallama tashigo Ganin Yana bacci yasa tayi murmushi Had'id'a juyawa tafice,



A parlourn ta tarar dasu Duka suna fira gwanin Sha'awa itama ta zauna Suka soma tanajin
inama Ace su Daddy da Ummeen tane haka?

Saurin kawar da tinanin tayi domin zai iya sakata damuwa Kuma Babu Abunda ta rasaga
Ammaaa, itadai batasan dad'in Uwa ba hakama Mahaifinta batasan shak'uwa ba Saidai suyi
waya ko video call on WhatsApp tana wata bataga mahaifinta A Zahiri ba, batasan Aikin me
Yake fita ba, Always Yana k'asar waje Abun Yana damunta Amma Batada yarda zatayi,

*SU WAYE SU NAINAAA?*


Alhaji Salman Cikakken d'an kasuwa ne Wanda duniya tasan da zamansa Yana had'akar
kasuwa da mutane daban daban Cikin kasuwancin nasa ya had'u da Alhaji Sale Mai gold suka
Soma kasuwanci tare, sosai suke Samun riba kuma Ahankali Aminci yake k'aruwa tsakaninsu,
hakan Yasa sale Mai gold yabawa sale Mai gold yabawa Salman Auren k'anwarsa Hajara
bayan tanuna tana sonshi shima Haka, Sosai Aka Sha biki saidai Abunda Basu sani ba Alhaji
Salman Yanada mata A b'oye batare da Yafad'a musu ba Wadda ko iyayensa basusan da
Aurenta ba, zaman lafiya suke cikin wasu Y'an Shekaru Tasami Ciki ta haife Y'arta Mai Suna
Nainaaa zo kaga murna tattali kulawa soyayya wadda Daddy yake yiwa Nainaaa Domin sunan
mahaifiyarsa data rasu Aka samata,



Duk wata k'addara tashi dawasu company wad'anda Yasami ta k'ark'ashin Alhaji Sale Mai gold
yayan Hajara duk ya mallaka Komai da Sunan Nainaaa,


Koda d'ayar matarsa Mommy taji hanakalinta Yayi Mugun tashi ganin ta Shekara dashi Kuma
ga d'anta Namiji Amma ba'a yimasa wannnan Kyautar ba sai waccan Mai kamada Aljanu,
hakan Yasa taja k'awarta Suka garzaya Bak'in daji inda bokan Tsauni sukayi Mugun Asiri ga
Alhaji Kuma ranar ta kwaso kaya suka dawo gidansu Nainaaa,

Suna Zaune palourn itada Alhaji suna fira Cikin Soyayya y'arsu naga Hannunsa Yana mata
Wasa A Lokacin Bata Wuce wata 3 ba,

Kwatsam saiga Mommy tafad'o d'akin ko sallama Babu tafara masifa, "Lalle Alhaji wato Saboda
ka Aure Y'ar masu Kud'i Shine zaka walak'anta mu to muma mundawo Nan da Zama ba inda
zamu,"



Mik'ewa tsaye Ummee Tayi Cikin mamaki tace,"Baiwar Allah lafiya Zaki shigowa mutane cikin
gida Haka kina d'aga Muna murya,"



"Ke dakata kada ki fad'amun maganar Banza Ni Nan dakike Gani Ni matarsa ce wannnan Kuma
d'ansa sai d'an k'aramin cikinsa dake jikina yanzu haka, dama Bai fad'a Miki Yanada mata ba ya
Aure ki,"?




Cikin tashin Hankali ta juya ta kalle Daddy da kansa ke k'asa ya kasa magana Saboda Kunya

Tace"kenan Abunda wannnan Matar ta fad'a Gaskiya ne,"


Kasa magana Yayi



Dariya Mommy ta shek'a tace"Taya ko zai fad'a Miki tinda bakece gabansa ba tinfarko saboda
Tara dukiya ya Aureki yanzu Kuma muntara to saiki k'ara gaba, Kai Alhaji Salman ka saketa
Tak'ara Gaba,"



"Kije na sakeki saki d'aya Hajara, Kuma ba Wanda zai rabani da Y'ata Wllh duk duniya," Yana
Gama maganar Yawuce d'auke da Yarsa,


Kuka ya kwacewa Ummee tana danasanin Auren Daddy, Haka Mommy tasa d'anta Sagar yama

Ummee walak'anci ya korata waje bako takalmi,


Tana kuka tabar Gidan, ba kalar wahalar da Bata Sha Saida tasamu wani gida Aka d'auketa Ai
katau Sannan tasami Kud'in komawa gida labari tabawa yayanta tana kuka, Abun yayi matik'ar
k'ona Ransa Shida d'ansa Na'if Kuma ya kullace ganin bayan Daddy,



Koda sukayo bincike ba inda Basu duba ba Amma ba ko Alamar Daddy ya kwashe komai nasa
yabar gari, Bayan yabasu wata takarda Mai d'auke da shaidar mutuwar Nainaaa,


Hakan yak'ara d'aga hanakalin Ummee har Rashin Lafiya tayi Domin tana masifar son Y'arta,
da kyar Asami ceto Rayuwarta Bayan wasu shekaru ta Aure wani mutum Saidai koyaya ne
Zuciyarta nagun Salman Allah baisawa Auran Albarka ba suka Rabu,



A yanzu duk Iyayen Salman sunjima da rasuwa Y'ar Uwarsa Binta ce kawai tarage Ammanaaa
tana Auren talaka yaronta d'aya Hassan Domin Hussain d'in sa ya rasu, mijinta bamai k'arfi
bane hakan Yasa Alhaji Salman ya maidasu Sabon gidansa daya Gina A Abuja suka tare
Dukansu Nan yabata Nainaaa Rik'o domin Mommy Tace Wllh bazata Rik'a taba,

Ammanaaa tayi fad'a Sosai ga d'an Uwanta na wannnan Abun dayayi Amma baice Komai ba
Domin kuwa sihiri Yana yawo Kanshi,



Ammanaaa tarik'e Nainaaa tamkar itace ta haifeta kulawa Sosai take bata, duk iya k'ok'arin
Mommy ganin taga bayan Nainaaa da Ammaaa Abun ya faskara Hakan Yasa ta d'aura musu
muguwar tsana A gidan,



Tayi duk Abunda zatayi Wanda ko Labarin Hajara Daddy baison Yaji Kuma ya damfareta Kud'i
Masu nauyi yakawo gida Mommy ta kwashe, tayi sama da Fad'i Dasu Amma ya kasa magana,


Abunda duk Basu sani ba tindaga Kan Rabuwarsa da Ummeeen Nainaaa zuwa Kud'insu daya
damfara duk Aikin sihiri ne Mommy Tayi Kuma Sagar dayake ma kallon d'ansa yana kashe
Masa duniya ba d'ansa bane d'an bokanta ne can tasamo cikin Amma ta Nana Masa Batareda

ya sani ba, Hairat ce kawai Y'arsa Shiyasa take k'aunar Nainaaa...




*MUNDAWO LABARIN.....*



Tsaf suka shirya ita dashi gwanin burgewa suka fito,

"Wai nikam Ina Zamuje ne my Nainaaa,"?


"Oh my Abbas bafa saidaka Zanyi ba,"




"Hahaha Inama Zaki iya Saida gudan jinin Masoyin ki,"



Dariya tayi tana bud'e Masa motar "yau Kai zakayi driving d'inmu,"



"Laaaa My sister and brother Shine zaku fita badani ba? Aikuwa Allah ya kawoni Dan Dani
Za'a," tana Gama maganar tashige bayan motar



Dariya sukayi duka suka shiga Suma Suna fira,


"Ina muka nufa ne wai,"



"Wannan Mall d'in kasan gobe Daddy zai dawo shine nakeson muyi siyayya,"

Cije lip's d'insa Yayi cike da Samun nasara Yace"Amma kuwa nayi farinciki da Zan had'u da
Daddy zakuyi surprise Ashe,"




"Surprise kuma,"?




Cikin sauya Akalar maganar Yace" Eh surprise d'in ganin surukinsa ba, Munkawo, mushiga,"




Rufe fuskarta tayi suka fito Suna dariya,


Ciki Suka Shiga suka Lodi

2 / 3