YAN ABUJA BOOK COMPLETE BY HAERMEEBRAERH.pdf

Author :  HAERMEEBRAERH Category :  Hausa Read

Chapter   12 / 24

33K to 36K   out of 70.7K words

ta hau kuka, zama tai gefen tamfatsetsen gadon ta da ta sake
mai matuqar kyau da girma, kukan ta tasha ta miqe ta kwanta, yau ita Bilki ke bigewa baki da
luddai??? Oh duniya, da kudin ka da komai ba za a ji tsoron ka ba yanda taga ana yi wa masu
kudi, to kwarjini ne bata da shi ko me, miqewa tai taje gaban madubi, ta kalli kanta daga sama
har qasa, ga atampa nan mai tsada sarqar gwal.da zobuna, komai ya ji, dubawa tai taga ashe
fa har yanzu ko umara bata taba zuwa ba balle Hajji? Murmushi tai tace " Gaskiya mana, to ai
ko kashin ku ya bude dan kuwa dole ne wannan shekarar a sake farali da ni naga ta raini"
komawa tai ta kwanta, bacci ya dauke ta, cike da mafarkai kala2 na ban tsoro, ta dade tana irin
mafarkan nan, 'Ya'yan ta na cikin matsala, amma sai ta dangan ta shinda sharrin maqiya, in
suka dawo za su je neman taimako.








Yau ce ranar da Juwairah ta wate domin gyaran jikin ta, Yah Jabeer din ta na gida, in da ba zata
iya kaiwa ba shi yake taimaka bata ya mata, misali yanzu ba dika take iya wanke bayan ta ba,
to ga wannan abin gyaran jikin da zatai yana buqatar taimako, da farko na ga ta hada lemon
zaqi a wani kwano qarami, ta zuba sugar cokali daya, da zuma cokali daya, sai ta saka lemon
tsami daya, ta juya su sai da sugar n ya narke sannan ta dakko soson ta, ta miqa mai daga shi
sai gajeren wando( yammaza zasui aiki�) gani nai zai tsoma soson a wannan hadin kan ya
tsoma da sauri ta riqe hannun shi" Yah pls i want some ya ban sha'awa" tana turo baki, gaba
cike da shagwaba" ke fa kk ce kin ware kwanon nan na gyaran jiki ne ko abu za a debo kin
dinga kyankyami kenan shine yai zaki sha abun ciki?" Cike da mamaki," ni dai zan sha ,

plsssss" miqa mata yai a spoon din, aiko ido alumshe ta shanye kusan sai da ta shanye rabi
yace " tsaya za mui abunnan ko na dawo ta gaba na qarasa baki ki shanye?" Kada kai tai
alamar Aa su ci gaba da gyaran jikin, sai sude bakin take, fara wanke mata fuskar ta yai, da
wuyan ta da bayan ta , da wannan hadin da soson, zuwa hammatar ta, sai ya dawo ta gaba ya
wanke mata tsakanin cinyoyin ta zuwa cinyoyin ta, guiwar ta a haka saida ya hade kaf jikin ta,
bayan sun gama ne tai mai godiya, tare da furta mai kalmar da ta zama masu al'ada wato" I
love u" maimaita mata shima yai ya daga ta, " wai wai wai Babyna gaba daya kinyi nauyi yanzu,
da gyar fa na dago ki" turo baki tai kamar zatai kuka, dama yasani tsokana ce, dariya ya fara
yana kame bakin shi, tura hannun shi tai daga kafadat ta zata fara tafiya, " Mai ciki ihmmm
ganinan tafe, me ciki, wallahi bani son sunan nan" juyo watai ta biyo shi suka fara zagaye
bangaren su tana kukan shagwaba, " inna kama ka a yau a gidannan ka fara tsallen kwado,da
kaji ka shiga hannu na" tana ta huci ita a dole an tsokane ta, dariya yake harda riqe ciki dayaga
ta gaji ta nemi waje ta zauna, zuwa yai kamar yana son yai tsallen kwado a gaban ta," Haba
Babyn Yaya, kiyi hakuri, in dai nine i promise i will never do dat again ever, ya fada yana watsa
hannu alamun yayi nadama yana karya wuya" na hakura amma ka jawa kan ka kai zaka kaini
toilet a hannun ka ka dawo da ni, dama na kula tinda cikin nan yai girma sai dai ka tallebe ni ta
gefe baka daukata, bazan lamunta ba ehe" " an gama ranki ya dade da imani" murmushi sukai
a tare suka furta" I love u" wucewa yai ya je ya hada ruwa mai dan sauqin zafi ba wani mai
yawa ba yaje ya dauke ta kan su fita tace ina zuwa zan dau wayata, a hakan ya kaita daki ta
miqa hannu ta dau wayar, " Kashhhh ashe ma Nafee bata da waya, bari inna fito na leqa na
karbo dankalin in ta gama hada min din" kai ta yai ya dauraye mata wannan danqon, sai ga jikin
ta yana wani laushi da haske, kamar wata matat masu kudi, fatar taji hutu, sun fito kenan yana
dauke da ita ya bada baya ya shihe daki Nafee tai sallama, dakata wa tai, sai da aka bata izini
sannan ta shiga,baje ta tadda Juwaira a kujera, " me ciki, 🙊 Ooupsy ! Ga dankalin na mai da
shi yai laushin kamar yanda kk ce na saka lalle dakwai amma ba dikan na juye ba bayan na
kada kamar dai yanda kk ce gishiri da kuma manjan, sai kin ci dariya Innarmu cewa take wani
abun dadin ne, wai Nafee, irin abun rannan zaku mana mai kwai?" ���dariya suka saka
harda jabeer, sai da sukai mai isar su sannan ya bata rai" ya ishe ku Innata ce fa" dariya suka
qara tintsirewa harda shi din," Feena taso ayi wannan dake, kuma kiyi a hankali karki ji ma mata
ta ciwo" " masu mata" ta fusta a hankali" me kk ce?" " niiiii me na isa cewa, ba abinda na ce ko
nake shirin fada" dariya suka ba Juwairah tai ta yi kuwa, daga naya suka samu wannan hadin
sukai ta murza mata a jiki kamar dilka, kafin kace me juwairah ta yi kamar wata amarya, suna
cikin yi Nafee ta miqe ta dakko ayaba daya, da kwai, sai zuma da markadadden dankalin
hausan da markade yai laushi, hade su tai har ayabar sukai laushi sosai ta koka ta saman kan
ta tana tsagawa tana shafawa a can qasan kanta, shi kuma yana mata dilka, bayan ta kusa
gama wan ne Juwairah tace" Amma dai Nafee baki saka albasa a hadin yau ba ko? Dan naji ba
wari" " eh ban saka ba na san ba zaki so ba mayb ya saka ki amai"" kaiiii amma ko na gode yar
uwa"( wannan hadin na dankalin turawa da lalle da kwai d manja kadan da gishiri ko baqar
mace ce take yi tana haske , tana fitar da kalar ta mai kyau, ga laushin jiki, shi kuma hadin dan
kalin hausa ana yin zallah na albasa madadin dankalin ko dan kali madadin albasa, kowanne
yana fidda gashi sosai kuma ya hana shi karyewa, yai laushi da santsi, sai dai na albasa na da
wari, dan haka in uwargida ta gama ana son ta samu abun wanke kai mai qamshi sosai ta
wanke kuma in an saka ana son ai massaging scalf din sosai ya shiga ko ina) ba su suka gama

ba sai wajen azahar, tayi bacci kan su gama, tashi yai yana miqa" wai gayu da dadi da wuya" "
hhhhh Yah to ai kai zaka mora gwanda ka taba yau kaji ya take ji da da take yi ita daya" " waya
fada maki da din ban taya ta wasu qana nan abubuwan? Ban dai taba irin wannan bane, ashe
haka take shan wuya duk dan ta burgeni baiwar Allah" ya fada yana shafa gefen fuskar ta, bude
idon ta tai" what ar u two talking about" nan da nan ta tsargu da qibar da tai suke, aiki hde fuska
tai, Nafee da ta gane dariya ce taso kwace mata, amma tace bari nasan me zan" Ni dai daya
fafa cewa nai ba ruwana in kk ji, dan haka ba ruwana yanzun ma zance na tafi innar mu na
kirana, Yah ka fada mata" kama baki yai yana mamakin sharrin da yarinyar ke sn hada mai, kan
yai yunqurin wani abu yaji ta janyo hannun shi gaba daya ya zube agefen kujerar, hawaye ta
fara ta dora kanta a qafar shi" shikenan dan nai qiba sai a dinga tsokana ta, ai ba muni nai ba",
tana yi tana shan majina, rasa me zai yai dan yasan sharri kam Nafee ta hada mai shi bai da
hanyar fita, kamo ta yai ya hau massaging kafadun ta" kiyi hakuri princess, dama gani nai cikin
yai girma sosai shinr nace ko yan biyu zaki haifa?" " cikin zumudi tace "Allah yasa yayana" "
Ameen to tashi muje mui wanka an kusa kiran sallah" miqewa tai, a ranshi yace " wai that went
well, Nafee Allah na son ki da ta burkicen yau sai kin wahala kema" wanka sukai ya gyara mata
kan ta ya saka mata riga doguwa har qasa mai budadden qugu, ba qaranin kyau tai ba, kallon
ta yake kamar kar ya daina, ita ko murmushi take , bayan sunyi sallah ne Innar mu ta aika masu
da abinci suka ci, tin da ya saka mata ruwa ta sha ta bingire a zaunen ta hau bacci, daga ta yai
ya kwantar shima ya kwanta, suka sha baccin su, Yah Jabeer kam ya dade kan ya samu
wannann bacci, dan komai na shi nemaj kwace mai yai, ga rijiya da ruwa amma guga ta hana,
ga princess din shi a kusa baccin me ciki ya hana shi more gayun da ta sha domin shi.ni ko
nace sai kun tashi asha bacci laaaafiyaaa.......
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼




BY HAERMEEBRAERH



QAWAYEN ARZIQI
Widad Ummu Hafeezah
My Roumie 💖
Sis Ramlat
Baba larens
Aunty Ummu
Buzu nawa�
Aseeya Ahmad Bunzu
Aisha Ali Garkuwar mu
Zahrah muhammad
Maryam( Mero tsokana�) Maryam Alkali( Autan Hajiya)
Fateema( Mum Sultan)

Aisha Bizzy
Zeenour Mustapha
Hussaina Cute one( kwaila�)
And so many more of my good and loving freinds, that i can't write ur names, kuna da yawa, kun
san kan ku na san ku, ina son ku sosai, Allah ya barmu tare da alkairi mai yawa, ya kare mu
daga dikkan sharrin zaman tare. Haermeen Haermma love u XoXo💖.






Page 19:





Da asuba yau Salma ta tashi da matsanancin ciwon kai da mara, in da Talle hankalin shi ya
tashi ba kadan ba, kar 'Yar mutane ta mutu a hannun shi, shi dai Allah ya gani ba wani son ta
yake ba dama, kuma shi ba zai yarda ya kashe 'yan kudaden dayake tarawa ba in sun rabu ya
baro wata sabuwa ya dirza ba, tabbbb yaushe ma zai yarda ya taba bayan neman auren ma ya
kankama, kuma yanzu haka dama wa'adi ya debar mata," kawai bari Alhj ya fita nan dai da
Kano na auna ta gida, nace sai nazo ba shikenan ba" yana maganar zucin nan ne ya ji Alhjn na
kiran shi, da gudu ya fita, " To ga wannan a kula da gida, ni zan tafi , wannan karon xan dan
kwana biyu gaskiya wataqila bam dawo ba, dan amaryata kasan na fada maka ta samu
qaruwar diya mace, so ina ganin zan dan jima kadan fiye da yanda aka saba, a kula da gida,
kar na dawo na ji shigen labaran dana saba ji, ba zamu kwashe da kyau ba Talle" gyada kai
yake kamar qadangare, Allah Allah kawai yake ya tafi ya kai Salma tasha ya dawo, kar ta mutu
a hannun shi, " Allah ya kiyaye Oga ba zaka taba samun wani labari mara dadi ba" daga kafada
Alhj yai alamar" ruwan ka" yana fita bayan ya rufe gate din ne ya koma dakin da gudu, samu yai
ta dan samu dama ba kamar yanda ya barta ba, ta fito daga toilet da alama amai tai," ke hada
kayan ki yau zaki ganin gida" cikin kaduwa da murna a gefe kuma kunya da tashin hankalin da
wanne ido zata kalli su Juwairah da Mama Bilki? Uwa uba Goggon ta, tace mata waye mijin ta,
driver? Ko gate man? Zubewa tai a katifa," Nikam Sweet na fasa ba yanzu ba ka bari na
murmure, sannan mu dan samu kudi, ko a haka zan tafi ai sai a zage ka" "a zage ki dai yo ni
meye nawa in zaki miqe ki miqe ki kwashi dan abinda zaki iya dan kin ga ni daga yanzu ma
barin gidanan zn ko kin dawo ba ganina zaki ba nima na bar aiki anan daga yau, dan na kwashi
rabona wajen Alhj, qauye zan koma, na ji da iyalina, kuma ba yanda zaki ki san qauyen mu nan
ma tinda ko sunan baki sani ba, ba kuma ki san hanyar bama, so in kin tafi ki manta mai suna
Talle, ko Alhj Mansur da kk taba aura, ki manta kin sanni, sai dai in kin tashi tuna ni ki min
godiya a ranki na sama maki hanyar zuwa ABUJA, harda qauyen ta ma, dan haka ga wannan"
takarda da kudi dubu goma cass ya miqa mata, a zaunen ta daskare, bata gaskata me ake fada

mata ba sai da taji tsawar shi yana maimaita mata da kuma bata umarnin tana bata mai lokaci
zai fita ya gudu shi,( qarya yake mata ba inda zai gudu kawai sanin bata ko san sunan inda
suke ba shi ya sa shi fadin haka, baya son ta yi tinanin dawowa ma) miqewa tai da taimakon
shi, take ciwon kan ta ya dawo sabo, wani jiri ke diban ta, haka ta gama komai, ko nace ya
gama hada mata komai, yana bata a hannu tana riqewa, idon ta a tsaye, hawaye na zuba, haka
ya gama ya sata gaba ya kulle qofar ya dau wata jaka dan tsabar ya raina mata wayo ta zaci
tare zasu bar gidan, mota suka dauka ya saka ta suka bar gidan kifa kanya tai a cinyar ta tai ta
kuka sun isa ta tasha a bakin tashar ya sauke ta yai gaba ko waiwaye bai ba, a haka ta samu ta
isa bata ko magana, in da taji ana kiran Kano nan ta isa ta shiga wata mota sauran mutum biyu,
tana shiga wata arniya ta shiga itama, sunayen su aka basu su rubuta, amma ita tai shiru, kudi
suka buqata ta miqa masu ko da ya qirgi kudin shi ya miqa mata sauran ta nade a hannun ta,
tafiya sukai ta awanni haka ta zauna idon ta ya bushe qayau, har suka iso kano, adaidaita sahu
ta dauka ya kaita har gida ta miqa mai kudi ya bata canji, har tai gaba ya bita ya miqa mata a
hannun ta, yai gaba, yana " Allah ya kyauta" shiga tai ba ko sallama, Goggo Sarai tana zaune
hakimar ana kada qafa akan kujera, tana hango Salma sai da ta kusa tintsirawa, da gudun ta
zani na warwarewa tana gyarawa ta taro ta" Lafiya ? Me nake gani haka? Ina mijin naki? Daga
wace qasar kuka dawo haka? Fashi akai muku? " duk wannan tambayoyin ne jere a bakin ta
tana qoqarin shiga da ita daki, har Mama Bilki zata fita, Abba ya riqe ta, yace bassu, ni na je ,
yanzj da kinje kin ja magana,cewa za tai gulma ta kai ki" " To Abban su Allah ya jiyar da mu
alkairi" " Ameen" fita yai ya isa dakin, zaune Salma take, idon ta na kallon waje daya kawai, ko
qiftawa bata yi, kukan kuma ya tsaya, tambayar duniya taqi magana, Goggo banda kuka ba
abinda take, " Subhanallahi, me ke faruwa ne, kin saka yarinya a gaba kina ta kuka haka? Ke
Salma ki mana bayani, me aka miki, ina mijin naki kuma? Daga ina kk haka?" A sannan ne
Salma ta saki wani kuka mai cin rai, ta dakko takardar ta miqawa Abban nata, dan yanzu
haushin Goggo take sosai, duk ita ce bata basu tarbiyya mai kyau ba, uban su na son basu ta
musu hudubar shedan,ta hana su saurara, wannan wace irin rayuwa ce haka, Salati sukaji ya
sake ya aje takardar ya zauna" Malam me ya faru? Ku sanar dani ko hankalina ya kwanta" "
mijin nata na can garin ABUJAN NE YA SAKE TA SAKI UKU" dora hannu a ka tai ta kurma ihu,
ta hau jibgar Salma tana" Shegiyar yarinya me kk mai ya sakon ke, kk kama asara haka,
mutumin da kuka fita qasar waje? Kuke shaqatawar ku cikin jin dadin rayuwa, ki zalunce ni ki
zalunci kanki, ki sa ya sako ki, da dukkan alamu ma ciki ne da ke, amma ba zaki bar dan ki ya
taso cikin jin dadi ba" kalmar ciki ne ya razana Salma kenan, tasan Talle ya mata illa, dan ko
giyar wake ta sha, a yanda ta san waye Talle ba ma zatai gigin ta haihu ba ta kai dan ta qayen
su, ai kamar yanda yace sun rabu ta manta da shi hakan za tai,ture hannun Goggo tai a jikin ta
ta je gaban Abban ta ta durqusa," Abba na ka yafe min, ka ji tausayi na ba dan halayyata
mummuna da nai a baya ba, ka duba girman Allah da soyayyae da da iyayen shi, ka yafen, ka
tausaya ma abinda ke cikina in ya tabbata ina dauke da cikin kenan, karkai fushi da mu, ka
bamu wajen zama a gidannan karka kori abinda zan samu, zan wahala ta hanyar halal na kula
da abinda Allah zai ban, amma kar ka ce za a sake daga zancen uban dannan na gama shafin
shi, sabon shafi nake son budewa" kuka ne yaci qarfin ta sosai, wanda yasan ya Abban su
hawayen tausayawa diyar tashi, yarinya fara mai kyau duk 'ya'yan shi Juwairah ce kawai ta fisu
komai, amma Salma na bayan ta, dubi yanda ta koma, ga qananan shekaru, har yau bata rufe
ashirin din ba, daga ta yai tsaye ya rungume ta,aiko kamar jira take,dama she needs a shulder

to cry on, ta rasa, for so long, ga strong and loving arms nan sun huging din

12 / 24