Author : Amina Maaji Category : Read Hausa Novels
ya k'oune tundaga cikinshi har k'afofinshi ihu yayi ko jibatayi ba tanata hira daya k'ara na biyu kafun taji da gudu ta fice lokacin har fatan yatashi sai kuka yaketayi tarasa ,wani taimako zatayi mishi
Kiran Baban shi tayi yazo " garin yaya "karkayi mun magana Mara amfani muwuce asibiti karb'an yaro akayi likitoti suka shiga dashi ciki,duk jikinshi ya sabule ko,ina har fuskan shi ruwan yatab'a wani likitane yafito
" zamu rik'eshi na tsawon sati biyu muyi mishi aiki amma gabanshi kam sai a hankali dan koya girma in badai yasamu magunguna ba akwai matsala salati Baban Sadeeq yayi"
Zuwaira garin yayi hakan yafaru? Kintsaya danna wayako? Gaskiya kincuceni wannan wani,irin abune"karufemun baki harkai ka,isa kayi magana,mamaki yatayi Wanda yanzu ko tsoron shi batayi dakuwa jikinta har karkarwa yakeyi,jinya sukatayi har,aka sallamesu yaro yakoma wani halitta daban ga duk tausayin shi ,sukeji ..
Ko,a jikinta cigaba tayi da charting kodainawa batayiba,amma yanzu a d'aki suke da Baban Sadeeq yanason Sadeeq banda yanzu son yakoma, gun fahad,kullum sai Sadeeq yafita wasa baya dawowa da wuri sai an kira mangariba zaidawo jikinshi duk datti yana tawasa da kare sunata gudu kare yakama k'afanshi yaciza ya,kara kama gannunshi wani ihu dayayi take yagagara tafiya............β
Maman Khairat ceπΈπΈπΈπΈπΈπΈ
ZAMAN TAKEWA
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
(Gajeren labari)
Daga marubuciya
Amina maaji(maman Khairat)ππβπΏ
*Β©οΈHAD'AKAR MARUBUTAN JAHAR YOBE
2023
π
ΏοΈ5οΈβ£
Wani yaro ne ya ruga a guje maman sadeeq kare yaciji sadeeq wani sadeeq d'in aciki ?"na gidan nan ko hijabi bata d'auka ba tawuce waje ihu sadeeq yaketayi d'ayan motar tad'auka aguje tafice daga anguwan sai asibiti ihutakeyi kutai makamun kar yarona ya mutu gacen d'aya ya kwone k'arban yaron sukayi ,awa hudu, sukayi kafun suka fitoh da sauri tazo gunshi "malam nine Wanda nakawo yaro kare yacijeshi
" ina mahaifin shi bayanan kikirashi yanzu yazo"taya kuka bar yaro yana wasa da kare har yacijeshi "ban saniba bansan kare yacijeshi ba ,wucewa yayi yabarta agun tana tsaye, sai hawaye duk tacika wajen da kuka.
Kiran Abbakar tayi ringing d'aya ya d'auka ", mekuma yafaru da jarabarki "karene yaciji sadeeq " garin yaya kare yacijeshi? "banida amsar maganan ka sai kazo kashe wayar tayi .
Minti arba,in sai gashinan " Zuwaira ,ina likitan gashinan mik'a mishi hannu yayi, suka gaisa sunana DR faisal ",taya kare yaciji yaron nan? ban saniba yanzu nazo banida labari " shikenan ga allurai guda shida duk sunada tsada ,a siyo ayi mishi dubu ,bakwai kowani d'aya ",ba matsala a siyo. gaskiya karya wuce Yau dan akwai matsala ,in yawuce yau" bari ,a rubuta maka ,Cikin asibitin ma,babu maganin duk wani babban shago yaje shiru babu ,dawowa yayi bai samuba, kira,akayi a taho da shi ,daga kano .
*****K'wana akayi ba,a samuba anyi mishi wani,allura Wanda zai rage rad'adin amma shiru,kwana biyu kafun aka ,samu alluran ,akayi mishi , watan su d'aya babu wani Sauk'i sai yadinga abubuwa kaman nakare.
DR faisal "yakamata a duba wannan Karen kardai mahaukaci ne dule, aka kira mafarauta suka kamashi ,aka kai Karen asibitin su gwaje gwaje ,akayi angano Karen yasamu tab'en hankali kowa yayi takaicin cizon addu,a ,akeyi Sosai amma abun sai a hankali, dole suka hak'ura sadeeq gurnani yakeyi Sosai.
" Zuwaira kincuceni kin kasheni kinyi sanadiyar rasa yarana maza guda biyu kinnaka, samun su Allah ya,isa bazan yafe mikiba "nikake gayawa haka " angaya miki mezakiyi nasan charting kikeyi ,kikabar yaran nan yafice nace karkibar yaran nan sufita ,shiru wannan wace irin zaman takewa mukeyi.
"Kayimun shiru ka,auroni dan kagayamun magana ko gadi kabani dazakata,yimun surutu ,d'auketa da mari yayi "Zuwaira kinyi kad'an banzama lusarin namiji dazaki juyaba ", duk abunda kikeyi ina kallon kine nazuba miki ,ido .
Zanyi maganin ki banza kawai munguwa,Wanda bata d'auki aure da daraja ba, ficewa yayi daga gidan kiran Aisha tayi" Qawata akwai matsala yanzu Baban sadeeq yayimun tas "daman inaso in gayamiki wancen malamin yarasu jiya" rasuwa eh"kinsan koda rashin lafiya yakeyi magungunan shi k'aryewa yakeyi yanzu kuma yarasu"komai ya tsaya.
Ikon Allah!
Meye abun yi kenan ?
Hak'uri zakiyi kawai kibari zansama miki wani,"kibari yanzu kare ya ciji sadeeq " zanzo in duba shi bana gari sai kindawo.
Watan sadeeq biyu sai yadinga abu kaman nakare sai an rufeshi ,a d'aki kafun zai samu Sauk'i kowama yahuta .
"Zuwaira daga na kalleki kaman ,in shak'eki nakeji dan haushi " yanzu ke duk abun nan dayafaru bazaki daina charting d'inba ,kiduba Cikin sadeeq yadda ya kumbura da hannun shi ya cenza kama ga yaron nan ya nakasa, hak'uri zakayi ba,a son raina hakan yafaruba
"matsamun bakida amfani ,a gareni ko kad'an .
Wani rana antashi da safe ,Cikin sadeeq ya kumbura yanata nishi, kafun su,isa asibiti rai yayi halinshi ,kuka Baban sadeeq yayi yanason sadeeq Sosai gaisuwa ,akeyi mishi Wanda suka San son dayake yiwa sadeeq, sai yaji yatsani anguwar gaba d'aya ma sadaka, akayi har kowa ya watse ko, kallon shi batayi tak'ara had'uwa da wasu shegun ,qawaye marasa hankali, wata uku tsakanin sadeeq fahad yarasu ,saura Yasmin da fa,iza, kullum takaici yakeyi yagaji da halin Zuwaira.....βπΏ
Maman Khairat ceπΈπΈπΈπΈπΈπΈ
ZAMAN TAKEWA
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
(Gajeren labari)
Daga Marubuciya
Amina maaji(maman Khairat)ππβ
*Β©οΈ HAD'AKAR MARUBUTAN JAHAR YOBE*
2023
ππππππππ
π
ΏοΈ6οΈβ£
*Zuwaira*
Kullum rashin mutunci Zuwaira kemishi "nagaji da halinki banason ,in bude ,idona in kalleki ko kad'an ke munguwace " na yadda kadaina zagewa kana zagina kai meyasa baka yadda da k'addara ne ? Ban saniba bazan tab'a yadda da k'addaran ba tunda ke bakisan ,kibawa mutum hak'uri ba.
"Meye hak'uri na zaibaka yanzu duk rashin mutuncin dakakeyi mun ,bai isheka ba dankaga nafara ramawa shine zaka ta ,tada jijiyan wuya kayi a banza kenan dan banida lokacin ka kokadan kaji da kyau .
Fa,iza Mommy " Baba waiki zo "kice mishi bazan zoba kinji"Mommy Babane fa "shi Baban ubana ne ,inace ubanku ne", zanci miki mutunci Fa,iza kinajina ko wucewa tayi dan fad'an sak'on Mommyn nata" Baba wai bazata zoba injita shikenan barta zanfita sai kadawo .
Yasmin nikuwa Mommy tanaban mamaki ,kiga yadda take walak'anta Baba "nima yana damuna zancewa Baba yayi aure kawai muma muhuta, babu ruwanmu ,da ita tunda hakane halinta gashi takashe mana sadeeq da fahad" karki k'ara fad'a k'wanan sune yak'are Allah ya jik'ansu .
A k'wana, a tashi Abbakar yad'auki shawaran yaransa yafara neman, aure anyikuwa, sa,a andace yargidan babban malami ya aura ,suna zaman lafiya ko takan Zuwaira bayabi, wannan abu yana kwona ran Zuwaira yara duk sunkoma gun amarya Habiba kullum ,acen suke.
Yana bacci yaji sauk'an ruwa ,a kanshi "Abbakar baka,isaba kayi kad'an kacimun mutunci kai ,asuwa "yanzu Zuwaira nikika jik'a kibiyoni har d'akina gun matana kinemi cimun mutunci " lalle yau ko, da zuciyana kike zaune ,in kuma akwai Wanda yake zugaki zanyi maganin ki,"Anty Zuwaira yazakiyi kishigomun d'aki ki jik'amun "anjik'a sai me, dan ubanki matsiyaciya banza mai kwaicen miji anyi asara.
Kece babba makuwa dan ni an aureni dan so da k'auna bawai sai da, akasamu matsala ,aka aureni ba " a shema Anty Zuwaira gazawa kikayi bazanyi miki komai ba kinci darajan yaranki .
Fitowa Abbakar yayi daga d'aki bayan ya sauya kaya "zoki wuce kifita nace kebada ma,ayi zaman lafiya da ke " wace irin macene ke mekike nufi zansab'a miki kifita nace
Ikon Allah !
Bazan fitaba!
Kaji da kyau tureta yayi yarufe k'ofa "kiyi hak'uri Habiba " bansan matanka jahila bace sai yanzu "banason kalman nan ko bakomai matata ce ,ta farko kuma auren soyayya mukayi ya
Ta kyau tatamun Sosai yanzun uzuri zanyi mata,
Duk masifar Zuwaira da bala,in ta yajure watarana tazuba barkwano acikin buta yayi tsarki dashi ,yata tsalle tana kallon shi ,da yafuskanci itane " Zuwaira nasake ki saki uku ki tattare komai naki kibarmun gida.
Nikasaka eh ansakeki bakomai "kajira saka mako,babu ,abunda zai biyo baya sai Alkairi " ban yadda kitafimun da yara gidanku ba."wannan yaran naka masu irin halinka ,ina zanje dasu.
Washe gari akazo aka d'ebe kayan Zuwaira babu ,abunda aka bari komai an d'iba ,gida yayi shiru babu masifa yara sai samun kulawa sukeyi ,a wajen Habiba.
Watan Zuwaira uku ,a gida tahad'u da wasu qawaye masu zigata a dai dai ta ,tahau taje gidan ta ,ko sallama batayi ba ,fa,iza da Yasmin da Habiba suna zaune ,anata hira shigowarta suka gani ,tawatsa musu pertir , a jikinsu har fuskokin su ,kowa yahau ,ihu tafice daga gidan tahau a dai dai ta daman jiranta yakeyi .
"Hajiya naga kinfitih da wuri? eh nafitoh na,ajiye sak'on ne basa gida ayya " dakinbawa makwabta karwani yashigo
Habiba
Kururuwa suketayi da neman taimako bakowa a gidan fuskansu tahau zogi ido yagagara bud'uwa sunsha Azaba Sosai almajiri ne yashigo yana bara yaji ihu yayi d'akin ya gansu a cikin wani, hali yayi waje da gudu"malam katai makamusu mutane a gidan nan fuskansu ta sab'ule kayi taimako dan Allah.
Kafun meye mutane suncika a gidan aka cirosu ,suna fita d'akin yakama da wuta mutane sukayi, waje kafun kace meye gidan yacinye ,sukuma anyi asibiti dasu, babu Wanda, yakeda number Abbakar sai limamin anguwan .
Kiranshi yayi"malam Abbakar kazo gida akwai matsala ko ,dadewa bai yiba ya,iso ganin gidanshi ,dayayi ya suma,awan shi biyu ya darfad'o "ina yarana da matana karsun kwoune nashiga uku, " basu kwouneba suna asibiti tashi yayi yanufi asibiti 'yayi mamaki dayaga fuskokin yaran duk sunkoma wani kala .
Kururuwa, yakeyi akwai Wanda yayimun abun nan dule ,matsawa kusa da Habiba yayi "Abbakar nasan bazanyiba " waye yamuku haka?, Zuwaira ce "Zuwaira kuma eh ,itace gun fa,iza yayi ,itama tace Zuwaira ,duk yarikice a ranan yasmin ta rasu da Habiba ,dule ,aka kama Zuwaira akayi mata daurin rai da rai " tayi nadama Sosai nadamar da bashida amfani fa,iza ce tarage ita da Babanta sai dayayi shekara goma yayi aure shid'inma ba,a son ranshi yayiba bazaka,iya gane fa,iza ba in bakasan taba "kiyi hak'uri fa,iza haka Allah ya tsara zaki rayu ke kad'ai batare da y'an uwaba. Bazan yafewa Mommy ba " kiyafe mata
Kinji mahaifiyar kice "tacuceni kuka takeyi Sosai dan takaici tanaka sata tacuceta .
Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
```a nan nakawo k'arshen labarin Zuwaira da Hauwa darasin dake cikin labarin Allah yabaku ,ikon amfani da shi Gaskiya mata mu gyara zaman auren, mu karmu biyewa sharrin shed'an dan zai kaimu ya baromu murage kishin da bashida amfani Qawaye sunataka rawan gani ,acikin zamanta kewar auren mu , yakamata mugane munje ibada ne ,ba shiririta ba mu,kula munga yadda rayuwar Zuwaira ya kasance da Hauwa Allah ya kyauta.......βπΏ
Maman Khairat ce ```