Zamantakewa Compelet Book By Amina Maaji

Author :  Amina Maaji Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 2

1 to 3K   out of 4.7K words

๏ปฟ*HAD'AKAR MARUBUTAN YOBE.*

_2023_

_Daga marubuciya_.

*Amina ma'aji (maman Khairat).*

*ZAMAN TAKEWA*

```INA MAFITA```
Da sauri ta gama aikin ta agurguje saboda tanaso tawuce majalisan su, yaronta Mohammed duk kunu a bakin shi ko gyara mishi batayi ba "Mama kashi nakeji."
"kaje kayi zarah ta wanke maka, in kun gama ga can abinci a kitchen Zarah ta d'iba muku yanzu zanje in dawo bazan d'adeba kunji? In Abban ku ya dawo kuce naje duba Mara lafiya ne."

"Ummi yanzu yau ma fitan zakuyi? Kuje ku zauna kuta surutun da bashi da amfani ,duk namijin da ya wuce kuyi gulmanshi? Kuji tsoron Allah wallahi, malamin mu yace muddin zaka zauna a waje ba zaka fad'i alkairi ba toh kazauna a gidanka dan harshe masifa ne."

"Kut! Yanzu Zarah ni kike gayawa wannan banzan maganan akan dan ina fita in rage lokaci? Toh kisani ko ubanki bai isa ya hanani fita ba ko ya takura mun , shegiya mai hali irin na ubanta! Ke wato ga y'ar islamiyya? Toh ki sani ko a ciki kike baki isa kiyimin wa'azi ba shegiya baki isa ba sai nafita,kinfi son na zauna takaicin ubanki ya kasheni wallahi wannan kuma kinyi k'adan."

Ficewa Hauwa tayi tabar Zarah,Mohammed da Aliyu ta fice, tana Zuwa Maman Maimuna ce tayi magana "shegiya Hauwa wato tun d'azu nake ta gaya musu yanzun nan zamu ganki kin fitoh sai gakinan." Zama Hauwa tayi aka fara zance,wani mutum ne yazo wucewa da k'afa Hauwa tace"kai wannan mutum akwai tsayi ko ya matarshi takeyi jibgege dashi? Wannan in ya hau ruwan cikin ta ko motsi ma ba za tayi ba."
"Ke dai bari kawai,mijin Maryam ne fa haka take fama dashi shi,sai iyayi bakiga ranan muna gaishe shi yaki amsawa ba dan rainin hankali,wai shi dole ga ustazi ko d'aga ido ya kallemu bayayi."
"Hauwa tace "ni wa ya gaya mishi mijin wata yana gabana,bani da lokacin shi me zan samu ni wannan in dai mijina ne nashiga uku dan yadda yake dogo haka abun nashi yakeda tsayi."
Aisha tace "kai Hauwa haramun ne fa ku dinga wannan, taya da auren ku za ku dinga kwatancen mijin wata gaskiya baku kyauta ba ,yanzu in matarshi ta ji kufa gashi muna mutunci,yadda kuke zagin mijin wata haka namu mazajen suma ake zagin su."
Maman Maimuna tace "ni su zaga nawa mijin sankwoce dashi,sai gajarta,dan abun dai dai dani badai injishi har wuya ba kedai bari kawai."

Dariya sukayi duk Wanda ya wuce a ranan sai anyi dashi,Maman Maimuna tana siyar da kayan tab'awa Hauwa tace "Maman Maimuna bani sandar ba'are na hamsin, Zarah zata kawomiki dan Allah"
"Gaskiya bazan baki ba sai nayi sabo."
"y'ar bura'uba ke ce matsiyaciya."
Cover wayan ta tabud'e gudan dubu tad'auko "ki bani cenji kidauki kud'inki muza'a mayar talakoki banza kawai."
"Oho dai bani haka" m?Maman Maimuna ta bata cenji d'ari takwas(800),a layi suka hauci ga almajirai da manyan mutane sai wucewa sukeyi a mota da kuma k'afa , basu watse ba sai kusan bayan la'asar shidin ma Hauwa tayi bak'ine daga cikin gari sunzo. "Sai anjiman ku" ta siyi cingam tana tafiya tana taunawa....โœ

*Maman Khairat .*๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
*ZAMAN TAKEWA*
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ

``Gajeren labari```

Daga marubuciya
Amina ma,aji (maman khairat)๐Ÿ“šโœ


*HAD'AKAR MARUBUTAN YOBE*

2023

๐Ÿ…ฟ๏ธ2๏ธโƒฃ

Hauwa suna zaune ne a wata anguwa da,ake kira DABO ALIYU acikin garin damaturu babban burnin jahar yobe.


Daga shiganta da zarah tahad'u "ke waye yake kirana ?" inna ce tazo yanzo tund'azu tayi ,awa d'aya dazuwa abban kufa? yazo yafita ajiyar zuciya tayi a hankali tashiga parlour bakinta d'uke da sallama ,innace ta amsa samungu tayi ,tazauna "ina kwana inna " lafiya ya gantali shiru Hauwa tayi.


"yanzu Hauwa abunda kikayi kenan taya za,ace mace batada aiki sai gantali meyasa kike haka yanzu kigani zarah itace ta d'aura muku girki ayya Hauwa ba,irin kune masu jefa iyalenku cikin garari ba kiji tsoron Allah wallahi yanzu akace mijin ki yadawo yafita nima naga lokacin fitarshi ina shigowa.

Inna kiyi hak'uri duk ba haka bane kiyafemun dan Allah "gidan ne shiru ina fitane in rage lokaci shiyasa k'aniyar ki da rage lokaci yanzu ke ,kinfi k'arfin zama a gida sai kifita kuta gulma da cinye cinye Allah ya ganar dake wallahi duk ranan dakika kai Ibrahim bango dule yamiki kishiya.


Haba inna meyakawo zancen kishiya kuma ,duk lokacin daya k'ara kaimun k'aranki zance yayi aure shine mafita kawai ,inna tatayi mata fad'a Sosai ran inna ya b'aci Sosai


Bayan taraka inna tatafi dawowa gida tayi tagama abincin duk tazuba musu ,sukaci " zarah zanje in siyi kati a shagon maman maimuna "sai kindawo ummi,tun k'arfe bakwai da rabi7:30 tafita sukata hira har k'arfe tara da minti ashirin tadawo9:20 lokacin Ibrahim yadawo bai sametaba wanka yayi yasaka jallabiyar shi yazauna zarah takawo mishi abinci yaci yayi sallah isha,i .

Sallama Hauwa tayi yayi kaman bai gantaba tanemi waje tazauna ,sannu da dawowa abban zarah yauwa " Hauwa ina kikaje da,daren nan ?meyasa bakida hankaline meke damun ki? zakibarmun yara sukad'ai kitafi majalisan Ku ,wallahi kinfara kaini bango aure ,zanyi kisani bazan tab'a zama dake kekad'ai ba kinajina "shikenan dan ka aureni sai in zauna inta yimaka gadi bazan fitaba sokake in zauna bak'in ciki yakasheni wallahi bazai,iyu ba kasani toh kayi auren mana akwai abunda zai dameni ne"kefa jahilace ballagaza Wanda taketare da duhun jahilci bansan bakida nutsuwa ba sai dana aureki.


Nikake gayawa jahila,wallahi niba jahila bace kasani da kyau nikagayawa jahilako?eh angaya miki jahila nayi dana sanin auren ki wallahi banza Mara hankali,a ranan maganganu yagaya mata ,ko,a jikinta washe gari yana fita tana fita lokacin yaran suna d'aki.


Monday
Tunda Ibrahim yayi sallah bai koma bacci ba yata goge kayan makarantan yaranshi yagama ya had'a musu ruwan wanka sukayi wanka ya shiryasu har lokacin Hauwa tana bacci" ummi kitashi zamutafi meyasa sai katasheni ne? Kuje abun Ku ,mana karka k'ara tashina dule Mohammed yafice daga d'akin Ibrahim ne yashigo .



"Ke Hauwa wace irin matane ke yanzu karfe takwas saura kina bacci motar yarannan haryazo zasu tafi" kai abban zarah yakake so nayi ne gaskiya,kana takuramun wallahi yaye ,abunda ta rufu dashi yayi wallahi sai kintashi ,ba,a son ranta tatashi ba "mezanyi maka? Kitashi ki kimtsa gidan nan dan Allah shikenan zanyi ,karki kuskura kifita Yau kinji yauwa matana .


K'arfe tara yafice daga gidan zuciyan shi sai tsinkewa yakeyi yarasa dalili haka yaje office yazauna duk jikinshi a sanyaye yake,komeyasa haka aka ta,tambayan shi amma babu amsa ko kad'an.yana fita ko wanke wanke batayiba tafice daga gidan sai majalisa .


Maman maimuna" yanzu fa muke shirin lek'aki sai gakinan munji shiru ,kubari sai dayafita nafutoh duk mazajen Su bamasu zama,a gida bane gara mijin maman maimuna shikam kullum yana gida.

Aisha yadai kinyi shiru ,kibari kawai Yau duk jikina a sanyaye yake sai nakeganin kaman wani abu zaifaru "zaki farako ,Hauwa kenan nagaya miki abunda kedamu nane " kenima fa d'azu dana tashi haka naji zuciyata tsinkewa yakeyi hira sukatayi da gulman mutane dayawa har yaran suka dawo daga makaranta basu saniba

Anty zarah yunwa nakeji kabari in nayi sallah sai in tafasa mana taliya muci toh toh inji aliyu alwala tayi tashiga parlour zatayi sallah ,a lokacin Mohammed yashiga kitchen ya kunna gas take wuta yataso wai zai hure wutar yakai fuskan shi kenan wuta yatashi a kitchen yakama jikin rigarshi tun yana ihu har ya kasa take wutar takama gidan ta silin takeci ,Aliyu ne yace Anty zarah inaji k'aurin wuta ka zauna kayi addu,a kai in kagama sallah bazaka dinga addu,a ba ganin wuta tayi tasama fita tayi a guje take wutar takama parlour ga badaman fita tanata kiran Mohammed Mohammed Mohammed kitchen ya k'one gaparlour a guje tayi hanyar kitchen wuta yakama kayanta sai ciwutar takeyi tanata kiran ummi ummi amma koji babu Wanda yayi haka wutar tak'onasu

Mutane suntaru anata kashe wutar amma Hauwa batajiba sunata hira a majalisan su.....โœ๐Ÿฟ

๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
*ZAMAN TAKEWA*
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ

```Gajeren labari```

Daga marubuciya Amina ma,aji (maman Khairat)๐Ÿ“šโœ

*HAD'AKAR MARUBUTAN YOBE*

2023

๐Ÿ…ฟ๏ธ 3๏ธโƒฃ

Mutane sai d'iban ruwa sukeyi motan kashe gobara aka kira wata matace tayi magana"ayya yaran sundawo kuwa? dannaga lokacin da,akazo d'aukan su ,wani shima yayi magana sundawo amma tun kusan k'arfe tara naga mamansu tafita nake ganin yaran ne sukadai motar kashe gobara ce tazo .


Jin jiniya ne ya ankarar da su Hauwa kuyi shiru kaman jiniya nakeji "jiniya kuma? kemuda bakin mubazaki samu ,muyi shiruba,muci gaba an soya awara sunataci suna hira ,wani yaro ne yazo da gudu," maman zarah gobara gobara "a ina ?agidan ki wani tashi da sauri datayi yaron yace su zarah duk sun k'one dukansu " mekace yak'ara maimai tawa ko hijabi batร  d'auka ba haka tafita hango gidanta tayi mutane sai kashe wutar sukeyi ,Hauwa sai kuka kaman mahaukaciya


Wani mutum ya gigita mata mari "ballagazan uwa Wanda Allah yabaki yara bakisan yadda zaki ,kula dasuba kuka ,taketayi sosai sai rik'eta akeyi har aka kashe wutar dai dai lokacin da Ibrahim ya shigo layin dan ankirashi ,a waya yayi sauri yazo a d'ari yataho .


Take da,akace yaran sun k'one yasuma a kadawo kanshi kowa banda tsinewa Hauwa bashida aiki mahaifinta ne yazo ,yayi mata duka awajen" Hauwa ban yafemiki ba dakikayi sanadiyar, rasa jikokina harguda uku bazan tab'a yafemiki ba badai gidanki baya zaunar dakeba sai gidan mutanen da karatun bai ishesu ba.

Kinyiwa kanki dake kika k'one bazai tab'a damuna ba dakiyimun asarar jikoki duk mutanen gidan su Hauwa sunzo Harda inna mahaifiyarta duk sunzo ,an d'auko Mohammed a kitchen duk ya kone amma fuskan shi tafi k'onewa jikinshi babu in dazaka sa tsinke haka,a she tokane da k'ashi aka fitoh da gawarshi sai k'ashi a katara duk sun d'auko su zarah ne take numfashi kad'an k'adan aka fita dasu,

Ibrahim anwuce dashi asibiti dan bashi taimakon gaggawa zarah ,itama asibiti aka wuce da,ita Hauwa duk tarikice tazama abun tausayi yara uku ,atare banda kuka babu abunda takeyi Aisha " kiyi hak'uri Hauwa haka Allah ya,aiko haka aka wuce da gawar Aliyu da Mohammed gidan su Hauwa dan a yimusu, sutura bayan antattara gawan nasu kowa daban daban aka nade gawansu k'afa daban hannu daban , aka hada awaje guda,ko ina daban daba da,wani abu bak'i aka rufesu Allah yamusu rahama yasa Aljanna ce makomarsu .

Ibrahim sai da yayi awa ashirin da hudu kafun yafarka yafara ina zarah Mohammed Aliyu "bazan yafemiki ba Hauwa kincuceni kinrabani da yarana sune komai nawa Allah bazan yafemiki ba nasan sunje d'aura abunda zasuci ne .surutai yatayi sosai kaman mahaukaci dule sai anyi mishi allura yake samun bacci .


Satinshi d'aya aka sallameshi kana ganin shi ,kasan baya cikin hankalin shi kullum yana asibiti wajen zarah shike kulawa da ita, watan tad'aya itama jiki yak'i dad'i kullum hannun ta yana rik'e dana Abbanta " Abba bani nasa wutan ba Mohammed shiyasa ina sallah wai zai d'aura abinci munsamu ummi batayiba"ina sallah nabarshi ,a tsakar gida, zan mutu Abba kayafemun zan mutu juya kanta tayi a she tafiyace Allah yajik'anku da rahama .


A lokacin ko lura baiyiba sai cewa yake" beby zarah kinyi bacci kenan harzai gyara mata kwanciyar ashe tarasu yashiga tashin hankali gawan ,a ka d'auko akayi mata sutura ko,arba,in d'insu ba,ayi ba yasake Hauwa saki uku"yanzu nikasaka na fuskanci kowani irin hukunci ,agareka Ibrahim tundaga nan yahad'u da hawan jini kullum ba lafiya sai yana zaune yahau cewa zarah sannun ku da dawuwa dole aka kaishi asibitin mahaukata dan a gwada shi ,aga ko,akwai Marsala .

Hauka tuburan yakeyi an d'aurashi akan magunguna yanata amfani da shi watanshi takwas a barno kafun yawarke k'arshe barin Damaturu yayi yakoma potiskum dan nanne garinsu d'an wata anguwa je jigawa, dan bazai iya zamaba .shekarar shi hudu ba mata kafun yayi aure Hauwa duk Wanda yafitoh neman auren ta in har a kagaya mishi sai yace yafasa tayi shekara takwas kafun wani dattijo ya aureta, shekarar su goma bata haihuba har yasaketa shima rayuwa kenan....

*A nan nakawo k'arshen labarin Hauwa darasin dake cikinta Allah yabamu ,ikon amfani dashi Tammat Tammat Tammat*
Maman Khairat ce*ZAMAN TAKEWA*
(Gajeren labari)


Gaga marubuciya
Amina ma,aji(maman Khairat)๐Ÿ“–๐Ÿ“šโœ


*ยฉ๏ธ HAD'AKAR MARUBUTAN JAHAR YOBE*


2023


๐Ÿ…ฟ๏ธ4๏ธโƒฃ

*ZUWAIRA*


"Zuwaira bana gayamiki Yau karkiyimun tuwo a gidan nan ba meyasa kebake jin magana?kayi hak',uri Baban sadeeq naga bamuda komai a gidan ne shiyasa na dafa tuwon bazan sakeba sai abunda kace.

" kid'auke tuwan nan daganan ko,inyi jifa da kwanukan "Allah yahuci zuciyanka .karki kuskura muzauna inuwa d'aya dake nagayamiki toh Baban Sadeeq afuwan key d'in motarshi ya.
d'auka yafice daga gidan bansan inda yajeba cen wajen k'arfe takwas yadawo yaje,ina kaje amsa yabata naje gunda ba tuwo sukeyi ba Alsudaniya naje



*Alsudaniya* wajen da,aka tanadar dan abun cinye cinye da kayan mak'ulashi sallama yayi na amsa muda yara sunata kallo sannu da dawowa yauwa Babana Sadeeq neyayi magana fa,iza da yesmin suna zaune tashi sukayi daga parlour Zuwa nasu d'akin .

Kiwuce kikawomun abunda zanzubawa su fa,iza ,ikon Allah!! nikuma da Sadeeq zanci kitchen tanufa takawo ,abunda zasuba,aciki gashi kimik'a a su fa,iza suci dan nasan ko abincin nan basuciba sai kita kashemu da ,tuwo memukayi miki ne.

Tana hawaye ta,isa d'akin yaran nan " Mommy meyasa kike kukane?Babane ko !! kiyi hak'uri zaiwuce rungume yaran ta,tayi bata k'ara zuwa parlour ba tazauna harsuka gama cin abinci a damaturu suke dazama a wata anguwa dake hanyan maiduguri red bricks gaba da mega na NNPC layin da suke C138 anguwa ce dabaruwan kowa da kowa kullum a gida , suke basa fita ko,ina suna dawowa zasu zauna suyi karatu yaran ko assignment in an basu,kullum haka suke wajen shad'aya taje ta kwanta.


amma bafa bacci takejiba rantane ya b'acci Yau itane Abbakar yakeyi mata haka? ,kaman ba auren soyayya sukayiba,abun yana bata mamaki,sosai.


Ko b'angaren shi batajeba tayi baccin ta,a d'akinta da safe duk wani aiki tagama shi tad'auko wayarta zata shiga wani group taduba ko anturo mata sakon da,akace sai gobe tana hawa taga anrubuta maman Sadeeq gashinan tsalle tatayi saboda murna .ita kadai take,wuni in babu kowa a gidan zatayi bacci tatashi kafun tasake d'aura abinci.


Har Baban Sadeeq yadawo shinkafa da miya tayi yaji ,kayan had'i sai qamshi yakeyi "Zuwaira zauna nibata abinci nakeyiba " Akwai matsala mai gidan yace yanason gidan shi yaronsa zaiyi aure k'wana kusa dan haka, kikira k'annen ki kutattare kayan ki,zamu k'aura "toh Baban Sadeeq Allah yasa hakan ne yafi zama mana Alkairi Amin .


Cikin lokaci k'ankani suka gama had'a kayan ana kaiwa harsuka gama ,sunkoma *BENKALIYO*wata anguwa ce, duk a kan hanyar maidugurin yake nasune nakansu gyara kad'an ne ba,agama ba .


Y'an layinsu sai shigowa sukeyi saboda asada zumunci daman gata da tsohon ciki dan tana watan haihuwarta ranan tana zaune sai gawata k'awarta Aisha " Qawata sannu da zuwa yauwa kinsha hanya "kawomun ruwa ishi nakeji sosai"kodai haihuwar ce yazo kibari kawai "nagaji da zama da Abbakar San bashida mutunci yanzu yafiye rashin mutunci ,meyafaru kedai bari zangaya miki kozaki samamin mafita komeye zanyi ,bari nakawo miki abun motsa baki ki d'an tab'a yauwa kinburge,"

gashi wow qawata kaman kinsan harda yunwa dan su mama tuwo sukayi nikuwa ba shiri nakeyi da tuwo a"narasa yadda ,akayi bakwason tuwo ,duk abunda Baban Sadeeq yakeyi mata duk tagaya mata"ki kwantar da hankalin ki zamuyi maganin shi kinada 5k Akwai Qwata zanje gun wani malami in karb'o miki wani abu kibashi yasha a shayi kingama duk yayuna, shisuke amfani dashi "zanyi Aisha koma meyene a zamanin nan yadda yan mata da zaurawa sukayi yawa, gara na mallakeshi na huta ,


Da, jaraaban shi da yamma zankawo miki sai kizuba mishi ko shayi ko ,abinci bakida matsala

K'arfe shad'aya Aisha tafita daga gidan zuwaira gun malam tanufa dake anguwan bindigari tayi sa,a tasameshi " sannu malam yauwa Aisha kune tafe eh mune yagidan lafiya" daman malam nazo kataimaka ,wa Qawata wancen maganin da wasu na mallakan "bakida matsala za,a baki ko aikowa kikayi zamu baki baran tana keda kanki!

Had'a mata magunguna da yawa yabata kikai mata, wannan kuma tasaka, a k'asan pillow konata konashi mungode, ko,gida bata wuceba takawo sak'on Zuwaira "Qawata harkin dawo kibari,akanki ba,abunda bazanyi ba tunda yanzu k'arfe hudu kitayani abincin kinji su biyu suka, shiga kitchen awa d'aya sungama komai sallama sukayi da Aisha sai najiki "

shida saura k'waya 5:45 Baban Sadeeq yadawo yayi parking d'in motarshi yajidi ,kayan daya siyo ko sallama baiyiba yashigo" Baban Sadeeq yako sallama, bakayiba? "Zuwaira gidanki ko gidana? gidan Kane.


" ke mutum yadawo baki karb'i kayan hannun shiba kikeyimun ,iyayi a dule ke mai wa,azi kitafi yobe mouse kiyi,amma nida gidana babu Wanda, ya,isa yayimun gadara,Allah huci zuciyan ka tartare kayan tayi gaba d'aya takai kitchen , abinci takawo yaci ,kafun yawuce masallaci su Sadeeq suna d'akin su ,suna wasa shekarar fa,iza 10 na yesmin takwas 8 na Sadeeq biyar5 suna son junan su,sai dai Sadeeq, irin halin mahaifin shi yagado,baya d'aukan raini k'wana uku dayin magani ,yafara aiki dan yarage masifa shiru yakeyi ,bayason hayaniya yazama kaman lusarin namiji ,Aisha,takira,

"Qawata nagode gaskiya magani yafara aiki sosai ina godiya kice zank'ara bashi wani kud'in dan naji dad'in maganin bakida matsala Qawata. Kinfi haka a gareni a ranan Zuwaira tatashi da nak'uda gadan gadan asibitin maisandari sukaje sukayi sa,a Hadiza ce ke duty nadare ,awa biyu da kawota tahaihu tasamu yaron ta kekkewa dashi, shiryata ,akayi sukadawo gida y'an -uwa sai zuwa sukeyi aka cika gidan da,jama,a


Ranan suna yazagayo aka sakawa yaro sunan Baban ta Mohammed shehu,ana kiranshi da fahad a,kayi hidima sosai Qawayen ta suncika d'akin gaba d'aya haka,taron suna yak'are ,tunda suka dawo anguwan yaran suka koyi rashin ji wai sai sunfita wasa tunba Sadeeq ba ga karnuka dayawa a layin haka Sadeeq zaita,wasa da kare ko,ajikinshi.


Kullum charting Zuwaira tahad'u da Qawaye a wani group sai sudad'e sunata surutu ,har yaran sudawo daga makaranta basu samu komai ba dole in sundameta tatashi ta d'aura in tabar abu akan wuta sai ya k'oune zata tashi " Mommy kinga fa,iza ko takarb'e mun abuna "yesmin banace in kinganni da waya kidaina damuna ba!


Kib'acemun daga nan yaronta fahad, harya yiwayo yafara rarrafe haka zaifita tsakar gida yata wasa,ita kuma tana fama da waya ahannunta ..



************akan mukubari ta d'aura ruwan wankan shi,yatafasa tazo tajuye a baho tashiga d'aki d'aukan sosan wankan shi wayarta ne yayi k'ara taduba Qawarta ne Wanda suka had'u a group sunata hira ta nanta da fahad,a waje ruwan yazubar ajikinshi ,take

1 / 2